Showing 6001 words to 9000 words out of 44930 words

Chapter 3 - Yar Talakawa Complete Hausa Novels by Afrah.txt

29 Sep 2025

1467

habu yayi,ledar dake hannun sa ta fadi,idon shi ya firfito,kallon niimatu kawai yake yi,dake kwance tsakiyar titi ba rai,duk jini ya bata mata jiki ta ko ina,kamar wadda aka tunkuda,da gudu ya isa gareta ya fasa wani irin razanannan ihu,yana kuka kamar ransa zai fita, mutane suka fara cika wurin,ana ta salati.

Wani alhaji ne ya fito daga Babbar motar data buge niimatu,hankalin sa a tashe ya karaso cikin jama'ar dake wurin, mai tsire shima yana nan ya buga uban tagumi, Allah kenan yanzun nan fa yarinyar nan tabar wurin shi.

Yaya habu ya kasa tabuka komai,hawaye kawai ke fita daga idanuwan sa, ,alhajin na karasowa,yace subhanallahi,dan Allah ku taimaka asa ta a mota can sai mu kaita asibiti,ya kalli habu ya dafa shi yace kayi hakuri,yaya habu da idon shi yayi jaa,ya mike ya ciccibi niimatu,wasu samari suka taimaka masa, a bayan mota suka saka ta, habu ya shiga gaba sai gaba daya duk ya zauce, alhaji a mazaunin driver.
Jama'a sai Allah ya sawake suke fada.

Suna isa asibiti,alhaji ya kira police,aka sanar musu komai, likitoci suka shiga da ita emergency.

Habu ya kasa zaune ya kasa tsaye, hankalin shi a tashe yake kwarai, yasan umman su nacan na jiran isowar su, duk ya rikice,dan yasan idan umman su taji halin da niimatu ke ciki,ciwon ta na iya dawowa..

Alhajin dake zaune shima da gani hankalin nashi a tashen yake, ya kalli yaya habu yace, samari zo ka zauna,inshaAllah zata rayu,habu ya kasa gardamawa yazo ya zauna kusa da alhajin.
Wayar alhajin ce tayi ring, ya dauka bai dade yana magana ba ya kashe wayar, ya kalli habu, tundaga yanalin shigar shi ya gane cewar yaran ba masu hali bane,wata kodaddiyar shadda ce a jikin sa ,sai wando jeans duk ya yage, hakanan yaji ya tausaya musu.



Ya prince ne tsaye tare da wani sagent hamza,prince sanye cikin kayan sojoji,dawowar su kenan daga meeting,prince ya kalli sagent, we will be going out later kada kuyi nisa,sagent ya sara masa ok sir,prince ya juya zai shige cikin gida,dad ne ya fito a rikice, prince yace dad hope lafiya?, dad yace, abban ku ne mukayi waya dashi dazun, yana hospital, prince yadan gyara tsayuwar shi yace asibiti!?, dad na tafiya wurin motocin dake compound,yace muje muje yace ya buge wata yarinya ne, prince yace dad kaje,bari nadan canzo kaya,zan same ku acan.

An fito da niimatu, doc ya samu abba da yaya habu, hankalinsu a tashe suka ce, doctor ya jikin nata?, doc ya dafa yaya habu yace, ku kwantar da hankalinku, mun samu mun tsaida jinin,kuma ciwokan duka anyi treating dinsu,Allah yaso ba karaya, dan haka nan da awa daya zata dawo conscious.

Abba yace alhamdullilah,yaya habu ya sauke ajiyar zuciya,yayi wa Allah hamdala,abba yace doc zamu iya mu ganta?, doc din yace yes zaku iya zuwa.

A kwance suka iske ta,duk bandeji an rufe ciwokan,yaya habu yayi saurin zuwa kusa da ita, yana hawaye, saboda tsire tsinke daya, hannun ta ya riko,abba ya tausaya musu sosai,hawaye yaji suna niyyar zubo masa, ya juya da sauri,wayar shi tayi ring,dad ne dauka yayi ya fada masa inda suke,yaya habu ya mike,ya samu abba,yace zanje gida na dawo,mun bar umman mu kuma bata jin dadi sosai itama, abba yace toh shikenan, dan'uwana ma na nan zuwa,kaje zamu kula da ita.

Yaya habu yace toh,yayi masa godiya,har ya kai kufa abba yayi saurin tsaida shi,kudi ne dubu biyu ya basa,yace kayi kudin mota,yaya habu yace a'a ka barshi,abba ya saka masa a aljihun sa,ya koma kusa da niimatu ya zauna, yaya habu ya juyo yace na gode,sannan ya fice.





β˜† Na 😘 luvβ™₯
[8/8, 3:55 PM] .: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳
πŸŽƒYAR β™‘TALAKAWAπŸŽƒ
🌳🌳🌳🌳🌳🌳



By~ afrah


+2347010902548
Episode 9⃣




dad a rikice ya shigo dakin, yayi wurin abba yace, hankalinmu ya tashi mutuka hope dai its not fatal, abba ya sauke ajiyar zuciya yace, alhndllh babu karaya, dad yace alhmdllh, bari na kira gida na sanar dasu dan kowa hankalinshi a tashe yake .



Yaya habu na komawa gida ya iske umma a zaune bakin kofa, ta buga uban tagumi tana tunanin halin da yaranta ke ciki har yanzu basu iso gida ba.

Sallamar da yaya habu yayi ya dawo da ita daga tunanin da take. Mikewa tayi zumbur tana cewa, habu lafiya kukayi dare....bata idasa maganar ba ta lura ba niimatu a bayan sa; ina ita niimatun ne? Yaya habu ya share zufar dake goshin shi, yace, umma zauna ne tukun.

Umma ta zauna hankalin ta na kanshi tace, hala ta tsaya siyan kankarar data saba? Yaya habu ya girgiza kai, baya son ya fada wa umma jiyon ta ya tashi, gashi shi kuma baya son yayi mata karya, musgutawa yayi ya gyara zaman sa, sannan ya fada mata komai.
Umma sai salati takeyi kawai, gaba daya hankalin ta a tashe yake, ta mike tana gyara zanin ta, tashi muje habu, yaya habu yayi kuri yana kallon ta, ganin dare ya tsala sosai.
Umman ta daga murya tace" kana fa ji ina magana" yaya habu yace umma kiyi hakuri muje gobe mana; Allah mutumin yana da kirki zai kula da niimatu , umma ta harere shi, kai harma kasan yana da mutumci ko, baka san masu kudin nan da san kansu ba ko, yaya habu ya mike ya riko hannun ta, umma kada ki damu, har a zuciyata naji mutumin ya kwanta min. Da kyal habu ya samu umma ta hakura, amma duk daren sallah kawai takeyi, Allah ya bawa diyar tata lafiya.

Prince tare dasu zuby da zarah, sai mum ne suka shigo dakin dasu dad da abba suke, zaune suna jinyar niimatu dake kwance, har lokacin barci takeyi.

Mum ta karasa kusa da gadon, tana cewa, Allahu akbar, gata karama, abba yace yayan nata yace shekarunta sha biyar. Zuby dake neman zama kusa da niimatun tace gata very cute wlh, zarah tace gsky she is cute.
Prince kuwa yana zaune a kujerar da dad ke zaune, tunda ya shigo yake amsa waya.
Dad yace wa abba, sunce zata tashi nan da awa hudu amma gashi harda wasu mins.
Abba ya mike yana cewa, let me call d doc, nima naga mins sun wuce, har yakai bakin kofa.
Niimatu dake kwance ta bude idon ta a hankali, tana binsu da kallo, ganin bata san su ba, tayi yunkurin tashi, amma ciwokan dake jikinta suka mata zafi, tayi yar kara kadan.
Abba ya juyo da sauri, mum tayi saurin cewa kwanta kwanta, kada ki fama ciwon ki, niimatu sai kallo kawai take binsu dashi, abba ya matso shima yace, niimatu ya jikin, jin ya ambaci sunan ta sai ta kura masa ido kafin tace a kasalance lafiya, dad yace sannu kinji yarinya, mum ta kalli su zarah, ku hada mata tea tasha.
Dad ya juyo ya kalli inda prince yake, yana ta faman waya, yace kai idan waya ta kawo ka tashi ka tafi mun yafe, prince yadan juyo ya kalli abba, sannan ya mike ya fita, abba yaja tsaki shi dai yasan yaron shi ba haka yake ba, mai tausayi ne amma yanzu kwata kwata ya canza.

Sun kula da niimatu sosai, har sai karfe goma sannan driver yazo ya tafi da mum da dad da abba, aka bar su zuby su kula da ita.

Tunda safe umma ta shirya ta zauna a bakin kofa tana jiran habu ya shigo.
[8/8, 3:55 PM] .: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳
πŸŽƒYAR β™‘TALAKAWAπŸŽƒ
🌳🌳🌳🌳🌳🌳



By~ afrah


+2347010902548
+2347010902548
Episode 1⃣0⃣




Yaya habu na shigowa umma ta mike ta rarumi poseπŸ‘ dinta, yaya habu yayi yar dariya ya gaisheta, bata amsa masa ba tace muje, yaya habu yayi gaba sukayi hanyar asibitin, suna shiga dakin suka iske , zarah na kwance a kujera tana chatting, sai zuby dake zaune kusa da niimatu tana rike da hannunta, ita dai yarinyar na mata kyau, duk da ta nura Yar TALAKAWA ce.
Da sallama su umma suka shiga, niimatu na ganinta ta fashe da kuka, tana yunkurin tashi, umma tayi saurin zuwa gurinta ta rungume ta tana shafa bayanta, yaya habu dake bakin kofa yana mamakin ganin yan'mata a dakin ba abba ba.
Zuby ta gaishe shi hakama zarah, ya amsa a sake sannan ya zauna shima. Ana haka su dad da abba da mum da mami, sai faruk dake rike da hannun ameer suka shigo, abba yayi saurin mikawa yaya habu hannu suka gaisa, hakama dad da yaya faruk.
Mum da mami suka gaisa da umma a mutumce, . Bayan wasu yan mintoci, an gama gaisawa, su dad suka wuce office.
ameer ne ya matso kusa da gadon niimatu yana kallon ta, ya juya ya kalli mum yace, grany, she looks like barbie ko? Duka dakin akayi dariya, mum tace ai kaine barbie din, zarah tace na mata duk boys na kallon cartoon din maza but you, sai nasu barbie da sofia the first, yaya faruk dake shirin zama yace kuma ga papan dinsa soja ba, aka sake kwashewa da dariya.


Satin niimatu daya a hospital, aka sallame su, kullum su mum da mami na zuwa hospital din, umma tun tana jan jikin ta dasu, ganin matan manya ne har dai ta saba dasu dan kullum suna zuwa harma dasu abban.
, ameer kuwa ya saba da niimatu sosai gata dama uwar fara'a , duk family din suna son ta , prince kuwa tun ranar bai sake zuwa ba, yama koma lagos bakin aikin sa, dan a cewar sa bai ga dalilin da duk gidan suke tafiya hospital su tare a wurin Yar Talakawan nan ba.

Ranar da aka sallameta, yaya faruk da ameer suka kaisu gida, ba karamin tausaya musu yayi ba, ai kuwa yana isa gida yake fadawa su dad da abba. dad yaja lumfashi yace ya kamata mu taimaka musu dan na lura mutanen kirki ne, abba yace nima ina tunanin nan, amma taya zamu taimaka musun....abba na rufe baki mum ta shigo falon dauke da drinks, mika musu drinks din tayi sannan ta zauna itama.
Dad yace mai zai hana muyi sponsoring din abubakar din yayi karatu, abba ya kada kai hakan yayi tunda shine babba.
Mum ta gyara zaman ta, tace maganar su neena kuke? Dad ya amsa da eh, mum tace yarinyar ta kwanta min sosai, mai zai hana mu dauke ta as nanny din ameer, naga jinin su ya hadu.
Faruk yayi saurin cewa, yes mum hakan ma yayi sosai, abba yace toh ba matsala gobe sai kai faruk kakai ni gidan nasu nayi magana da umman tasu.


Haka kau akayi washe gari faruk yakai abba har gidan su niimatu, umma ba karamin murna tayi ba, gashi ance duk weekend niimatu zata ringa zuwan mata, yaya habu kuwa kasar Jordan zasu kaishi, murna sosai sukayi, ranar su abba sunsha addu'a a wurin umma.


Yau ne ranar farko da niimatu zata fara aiki a mansion din. Driver aka tura yaje ya daukota, da ledar ta, ta sako kaya kala uku da zata ringa maneji har na kwanaki biyar.

A babban falo driver ya ajiyeta, sannan yasa mai aikin gidan ta fadawa mum. Tunda ta shigo take waige waige, bata taba shiga gida mai shegen kyau irin wannan ba, maganar mum ce ta dawo da ita daga tunanin ta.
Mum na murmushi tace sannu da zuwa neena, niimatu tayi mata nata murmushin tace ina kwana, mum tace lfy lau yasu umman naki, tace lafiya lau suna gaida ku.
Mum tace, muna amsa tashi na kaiki dakin da zaki zauna.
Sunje har wani katafaran dakin yayi kyau sosai, mum tace nan ne dakin ki, dakin dake kallon naki kuma na ameer ne, yana barci yau bazai je school ba, karfe sha daya lesson teacher dinsa ke zuwa, da yamma kuma yana islamiyya.
Niimatu ta kada kai, tana murmushi, mum tace jummai zata zo ta kawo miki abinci, nizan wuce office, Niimatu tace toh sai kin dawo.

Mum na fita ta zauna a bed side, ta sauke ajiyar zuciya, yau itace a irin wannan dakin, lallai ta gode wa Allah, tana cikin tunanin nan , jummai ta shigo dauke da plate na abinci, suka gaisa sannan jumman ta fita.
Da kyal ta iya cin abincin, dan duk bata iya ci ba, tana yi tana matse fuska, a haka ta kammala.

Karfe goma ta nufi dakin ameer, yana kwance saman tautausan gadon sa, karasawa tayi cikin dakin tana kalle kalle tana murmushi, can idon ta yakai pic din dake bisan side drawer din shi, dauka tayi tana kallo, woow ta furta a bayyane, prince dauke da ameer yana shekaru biyu, sunyi mutukar yin kyau, niimatu ta shafa pic din tana murmushi, mutum sai kace aljani.....
"Hes my papa" muryar ameer taji...da sauri ta ajiye pic din tana kallon ameer, dariya yayi mata yace, my papa is cute ko? Niimatu tayi murmushi kawai, sannan ta mika masa hannunta, ya kama, tace muje nayi maka wanka, ameer ya make kafada, ni nake wankana....niimatu tayi dariya daga yau nizan na maka , ya sake make kafada
[8/8, 3:56 PM] .: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳
πŸŽƒYAR β™‘TALAKAWAπŸŽƒ
🌳🌳🌳🌳🌳🌳



By~ afrah


+2347010902548
Episode 1⃣2⃣




Murmushi niimatu tayi musu, tace dazu nazo, zuby ta mike rike da hannun ameer tana cewa, su little anyi new nanny, ameer yayi tsalle yace, yes yes tafi sauran, wadan nan duka kazamai ne, yuks ya wani bata fuska, zarah dake shirin hawa sama ta kwashe da dariya, nawawo su little ansan tsabta, zuby tace kyeleshi haka zai tashi kamar babansa.
Niimatu dake tsaye tana jinsu tayi murmushi, tazo ta mikawa ameer hannunta, lets go na sake koya maka leason dinka, ameer yayi dariya yayi waje da gudu, niimatu ma ta bisa tana kiran sunan sa.

Bayan kwana uku, mum ce ta shigo dakin ameer dauke da wata leda bag, lokacin niimatu na fama da ameer yasha custard dinshi amma yaki, sai gudu yakeyi yana hawan gado.
Mum na shiga tayi mishi tsawa, come on dear idan baka shanye ba, I wont phone your papa today, ameer yayi saurin zuwa ya zauna kusa da niimatu, ya bude baki yace haaa, niimatu tayi smiling ya fara basa yana amsa, mum ta zauna a bed side, ta mikawa niimatu bag din dake hannunta, gashi zan aike ku gidan sister dina, tare da ameer sai ki bata wannan.
Niimatu ta amsa tace toh shikenan.
Tana gama canza mishi kaya, sukayo kasa, a dinning suka iske zuby, tana cikin abincin rana, zuby tace wa ameer sai inaa little , yayi gunta yana dariya gidansu fu'ad zamuje, zuby tayi dariya, toh a gaida ikram ,ameer na tafiya waje yace okay.

Sun isa kantamemen gidan sister din mum, driver yayi parking , niimatu ta fito sannan ta budewa ameer shima ya fito, ameer ne ja gaba har kofar shiga gidan, sunyi knocking, ba'a fi minti daya ba aka zo aka bude musu.

Mai aikin gidan ce, niimatu ta gaishe ta, ameer kuwa ciki yayi da gudu yana kiran sunan fu'ad.

Wata kyakkyawar matashiyar yarinyar ce ta fito daga wani daki dake cikin falon, sanye take cikin wata english gown purple, bako dankwali a kanta, sai yanga take abunta, niimatu na ganin ta tayi saurin cewa, ina wuni? A tunanin ta ko yarinyar ce matar gidan, tunda tana da jiki.

Yarinyar ta juyo, ta wani watsawa niimatu kallon banza, ameer yayi gunta yayi hugging dinta, smiling tayi kawai tace dear, sai yau zaga daman zuwar mana? Ameer yace aunt ikram ina fu'ad? Da mummy? Ikram na shirin zama tace fu'ad ya fita da ya moha mummy na sama je ka kirata.
Ameer yayi saman da gudu, niimatu kuwa ta rasa yama zatayi, ita ba halin ta zauna tunda basu bata izini ba, gashi ita bata da jumurin tsayuwa.
Ba'a dade ba ameer ya sauko tare da wata mata, da ganinta kasan hutu ya kwanta mata, taci ado abunta.
Niimatu tayi saurin cewa, ina wuni, waigowa tayi ta wani kallo ta, ta yamutse fuska, sannan ta zauna, niimatu ta karasa ta ajiye mata leda bag din da mum ta bata , sannan ta koma ta tsaya. Mummy ta kwala wa mai aikin ta kira, lusy!!!! Lusy ta shigo cikin sauri yes ma, mummy ta nuna mata ledar da niimatu ta ajiye tace, ciro min kayan dake ciki, lusy tayi saurin ciro wa ta ajiye mata a centre table, mummy ta kalla sannan ta kalli niimatu kice mata sunyi, niimatu tace toh, sannan ta kalli ameer, muje little master, ameer ya make kafada kije nizan jira fu'ad a nan, niimatu tace no muje akwai leason yau, ameer ya kara shigewa jikin mummy yana cewa no bazani ba, niimatu kuwa ta dage suje.
Tsawa ikram ta mata, keeee ki kyele shi mana, or r u his mum ne, yace bazai biki ba sai ki tafi ai, niimatu ta saddar da kai kasa, sallama sukaji, da gudu yaron da suka shigo tare da wani saurayi yayi wurin ameer, shi kuwa saurayin yayi wurin mummy ya zauna a kasalance, ohh God, am darm tired, bazan sake gingin fita da yaron can ba, mummy ta shafa fuskar sa my boy, sannunka da kokari, just jiya ka dawo daga china, yau ka biyewa acicin nan kuje wani yawo.

Samarin ya tabe baki, ya na iya da rigimar sa, mummy ta kallo wurin da niimatu take a tsaye, kee shiga kicin kice wa lucy ta kawo wa moha drink yasha, niimatu tace toh tana murmushi ta mai karawa fuskar ta innocent, tayi hanyar inda taga lucy ta fito,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login