Showing 39001 words to 42000 words out of 155423 words
Chapter 14 - A GARIN MU Book Compelet BY HAERMEEBRAERH.docx
yunqura zai bi shi, kallon shi Lawwali ya yi, cikin hade girar shi,ya ce,
"Ina zaka je?"
Dan yaqe ya yi, sannan ya koma ya zauna, qasan zuciyar shi baqqiqirin a ganin shi ai ko ba a shiga da kowa ba, an shiga da shi, tunda shi ne wanda ke bi ma Ogan nasu, kuma shi ke kula da can daji yanzu.
Lawwali bai saki fuskar shi ba har ya shige gidan, bai jima ba sosai ya dawo dauke da jaka, ya ajiye suka tada mota, sai gidan shi, ya so ya leqa dajin ya ga ya abubuwa ke tafiya, dan yanzu ba ya so a maimaita sakin wani da suka kwamushe, asiri ya tonu,duk da ba wai tsoro yake ji dan an san da zaman su ba, ya sani yayi gagarar da zai iya ji da dik wata tarzomar mahukunta, a shirye yake a yi uwar watsi ko a mutu ko ai rai kawai.
Zaune suke a parlour'n shi, su na kasafta kudin, kamata ya yi a ce in sun raba kudin daidai su shiddan kowa zai samu kusan miliyan 42,amma sai suka yi kasafin kamar kashin dankali, na sama ya danne na qasa, Gwamna shi ne ya fi kwasar kaso mai tsoka, sannan Lawwali, sai kuma suka ware kudin kula da maboyar su, abinci,ruwa, man da za a saka a mota, da abubuwan yau da kullum, kudin shigo da makamai dama a wuyan gwamna yake, ,No 1 na ta jira ya ji kason shi shima ya dara na qasa da shi, sai ya ga an bashi miliyon ashirin, yaqe ya yi ya karba, ya na ta godiya, kamar babu komai a qasan zuciyar shi .
Sauran yaran Lawwali kuwa murna kamar za su shide, ba su taba kama kudi masu kauri haka ba, babban abin takaicin shi ne, su na samun kuɗi dan samu, amma cin su na musu wahala, saboda idanun mutane, kuma sun fi yin rayuwa a daji, duk da cewar wasun su na da iyalai, har da iyaye, amma su na tsoron fitar da dukiyar su ci, (meye amfanin dukiyar da ba za ka ci ba? An kashe mutane a banza, ba a samu rayuwar jin dadi ba, an sace mutane a banza ba a yi ninqaya da dukiyar ba cikin kwanciyar hankali, ga tsoro, ga fargaba, ga zunubin wanda ya kashe mumini akan su, mu yawaita tuna cewar Allah yace duk wanda ya kashe munini kamar ya kashe duka duniya ne, kuma wanda ya raya mumini daya kamar ya raya duka duniya ne,sannan wanda ya kashe mumini da gangan, sakamakon shi jahannama ne,zai dawwama a cikin ta,ba fita, Allah ka tsare mu ka kare mu, ya ilahi me ne jin dadi a kashe kiyashi ma balle mutum? In ya mutu kai me za ka zauna ka yi a duniyar? Ba ku tunanin yanzu ku na gama kashe mutum kuma ku bingire ku mace? Me ka/ki ka tanada a ranar lahira da zai kare ki/ka daga shiga jahannama? Me za ku ce wa Allah a ranar qiyama? Shin wutar ita kuka fi so a inda za a dawwama ba fita, ko kuma talauci da quncin rayuwa a duniya, lahira a samu aljannah madawwamiya, ba fita, ba wahala, ba qunci, ba azaba, sai zallar ni'imar Allah, da jin dadi? Zabi ya na gare mu, tare da yawaita addu'a, Allah ya sa qaddarar mutuwar kowa ba ta hannun mu, domin wasu Allah ya rubuta su ne ajalin wasu, shi yasa suke kashe kashen nan, Allah ya nesan ta mu da ga aikata kisan kai, ameen)
Su na tsaka da murna Lawwali ya ji wayar shi na qara, dubawa ya yi ya ga sunan Sultana da ya yi Saving da 'Ran ki shi dade' da sauri ya dauka, tare da yi masu alamar su yi shiru, ko motsi wajen bai sake yi ba, sallama ya yi, ya ce,
"Ran ki shi dade na neman Lawwali ne?"
Cikin dakewa ya yi maganar saboda idon yaran shi, daga can Sultana sai ta ji ba dadi, domin ba haka ta so ba, ba ta san me ta zata zai fara fadi ba, amma ta sa a ran ta he is going to say something sweet to her ,musamman tunda shi ya iya tsara kalamai, ita ma dakewa ta yi, ta fito masa a oganniyar shi, ta ce,
"Ina ka shiga tun dazu na gama ina jiran ka?"
Miqewa ya yi, tare da dan duwaqa ya na bata hakuri, har cikin ran shi bai so ta gama bai koma ba, cikin sauri ya mu su alama, nan da nan kuwa kowa ya kwashe kudin shi, da shirin su suka zo, kowa ya zo da inda zai saka na shi, su na gama kwashewa suka fita, ya rufe gidan shi, suka tafi.
Nesa da NGO din suka aje shi ya dau adaidata sahu, dubu guda ya damqa masa ya sauka a hanzarce ya shiga ciki.
Ko da ya isa a zaton shi zai gan ta a bakin mota, sai ya ga ba kowa, mota na nan yanda ya barta, sai zafi da ta dauka, ciki ya shiga ya ga duk mutanen wajen sun tafi, sai ita kadai, ta kwantar da kan ta a jikin kujera.
Kallon ta ya ci gaba da yi har da sanya hannun shi a qirji, ya na murmushi, wai fa gajiya ta yi a hakan, office dik AC, kujera kamar an yi ta da soson katifa, amma ta nuna ta gaji saboda ba a saba da wahala ba, sai ya tuna farkon zuwan su wajen, har suka koma da fara'a a fuskar ta,
'to ko dai dadewa ta ce musabbabin bata ran ta?'
"In ka gama kallon nawa za ka iya kai ni gida?"
A dan firgice ya ce,
"Na'am?"
Miqewa ta yi ta zagaye shi, tana dan tura baki, tare da ɗaukan jakar ta da wayar ta, ta fara tafiya, wurga masa key din offices din ta yi, ta ce,
"Ka rurrufe ko ina, this will serve as ur punishment, na tafiya ka dade ba tare da ka kira Ni ba,"
Shan gaban ta ya yi, ya tsaya, tare da kama kunnuwan ta duka biyun da hannayen shi, cikin murya irin ta jaruman maza da ware idanun shi fess akan ta ya ce,
"Habaa Sultyn Daddy, ki yahe ma wanga yaron na ki, mai gadin ki, kuma drivern ki, indai hukunci ne ki ban kowanne iri na Zan dauka, amma ba zan dauki hushin ki ba, murmushin ki kamar hasken da ke haska min hanya ne, fushin ki duhu ne a gare ni, so ki ke in ta tahiya cikin duhu mu fada rami? Ko..."
Muryar ta can qasan maqoshi ta ce,
"Shiiiiii, ya isa haka, ni ba fushi nake ba,da na ga baka dawo bane sai na ji...."
Shiru ta yi, tare da cizon leben ta na qasa, wanda hakan dabi'ar ta ne, da sauri ta bar wajen, Lawwali kuwa ji ya yi wadannan kalaman nata sun fi maqudan kudin da ya samu a yau mahimmanci, duk da ba ta qarasa kalaman taba, ya kula da cewar ba ta son ya yi nesa da ita ne, cikin sauri ya rurrufe ko ina, ya bi bayan ta, juyawa ta yi, ta qi yarda su hada ido, har ya je gaban ta ya bude mata mota bata kalle shi ba, kuma bata dena cizar leben ta ba, sannan murmushin ta bai gushe ba.
Ko a mota ma ta kasa daga ido ta kalle shi ta madubi, shi kuwa idanun shi ya kasa barin fusakar ta da ta kawar gefe, mamakin irin kunyar ta yake yi, kamar ba wayayyiya ba, kamar bata yi karatu a qasar waje ba, kamar shekarun ta ba su haura ashirin da biyar ba. (Kunya halittace, ta wani ta fi ta wani, kunya ado ce, wanda ba shi da ita ya yi hasara, kunya ni'ima ce, wanda aka azurta da ita ya dace)
Ko da suka isa gida kafin ya fita ya bude mata, ta fara qoqarin budewa, ji ta yi qofar a kulle, daga ido ta yi ta kalle shi, su na hada ido ya kashe mata ido daya, dariya ta saki mai sanyi, shi ma haka,
"Yanzu dai an dena fushi da ni ko?"
"Ehhh"
"Tau na gode, sai da sahe,"
"Allah shi kai mu sahiyar lafiya,"
"Ameen"
Fita ya yi, ya bude mata kamar yanda suka saba.
Mubaraka ce ta tafi da gudu wajen su, kafin Lawwali ya yi magana ta rungume shi tare da fadin,
"Yah Auwal dina na yi kewar ka sosai sosai sosai"
Cikin dan hade fuska Sultana ta kalle shi, ina ya je dazu?
Wayance wa ya yi, ya juyar da Mubaraka ya na zaro mata ido, sannan ya ce,
"Baraka na hoo, dazu dazu mun ka rabu, amma har ke yi kewar Yah Auwal, ni ma na yi kewar ki Baraka naa"
Ya dan ja kunci ta ya na mata alama da ido ta yi shiru, shiru ta yi cikin tunanin me yake faruwa.
Sultana kuwa mamakin ta ne ya kau, sha'awar soyayyar da ke tsakanin yaya da qanwar ya kama ta.
Jakar sultana Mubaraka ta amsa, suka shiga ciki,
"Ina jiran ki a gate"
Juyawa Mubaraka ta yi, ta ce,
"Tau gani nan zuwa, yanzun ga,"
Su na isa ta ajiye jakar Sultana inda jakunkunan ta suke, sannan ta kalli dakin da ta gyara ya yi tass ta ce,
"Aunty Sultana jiya baku dawo da wuri ba, shi ya sa yau na ce ni ma zan jira ku har ku dawo,"
"Allah sarki, aiki ne ya yi yawa shi yasa akwai damuwa ne?"
"Babu komi, haka kawai Ni ka son ganin ki, bari na tai, yah Auwal na jira na"
"Na gode Mubaraka, Ni ma ina son ganin ki ko da yaushe, ki na da hankali, da nutsuwa"
Miqewa ta yi, ta bude wardrobe din ta, ta debar wa Mubaraka wasu kayan ta da ta ware za ta bayar, har da 'yan kunnaye da sarqoqi, guda uku uku, sai kayan kwalliya, da turare biyu, takalmi biyu sannan takalle ta tace,
"Ni kuwa Mubaraka cikin jakkunan ga wacce ta hi kyawu?"
Mubaraka kallon su ta yi, ita bata damu da kayan kyale kyale ba, burin ta a rayuwa kadan ne, ta ga ta saka sutura ta mata kyau kawai, bata damu da kyawun suturar ba ko tsadar ta, amma ta na da kalar da ta fi so, fari da ja, sune kalolin ta, dan haka wasu jakunkuna masu kalar fari da ja ta nuna tace,
"Wagga da wagga sun yi kyawu kwarai,"
Hannu Sultana ta sa ta dakko su, ta na fara'a, in zata yi kyauta wani irin dadi take ji a zuciyar ta, wanda baya boyuwa, har wanda zata wa kyautar sai ya ji abun da aka bashin kamar dama nashi ne dawo masa da abin shi akai.
"Tauuu Mubaraka 'yammata kema ga kayan 'yammata ki zanka sawa ki kyawu, maza ki tai Auwal na jiran ki"
Baki Mubaraka ta bude cikin mamaki, da tsoron yawan kayan da aka bata, da gani babu tambaya kaya ne masu tsada, ita kam da ta san Sultana za ta mata wannan kyauta mai yawa da bata jira su ba, kar sultana ta ga fa kamar dan abin duniya take son ta, ita kam sam ba haka bane, domin Allah take son ta, cikin hanzari Mubaraka ta ce,
"Haba Aunty, wanga kyauta ta yi yawa, ban tsaya ku dawo dan ki yi min kyauta haka ba, na tsaya ne domin ina son ki domin Allah"
Mubaraka ta qara shiga zuciyar Sultana kwarai kwarai, halayen su kusan daya ne, cikin fara'a sosai ta nemi babbar jaka a dakin, ta zuba mata komai, ta saka mayafi ta riqo hannun Mubaraka, suka fito zuwa parlour ,Hajiya Ikee na zaune ita da Sultan su na hira, ta ga su kamar wasu 'yan uwan juna,
"Ke Sultana meye haka ni ke gani? Me aikin ki ke riqewa haka? Ko dake ba zan mamaki ba a halayen ki na shegen son cudanya da tallaka, kee! Kama hanya ki tai, ba ke qare aikin ki ba?"
Cikin rawar jiki Mubaraka ta nufi hanyar fita, Sultan ne ya kira ta, tsayawa ta yi cak tare da juyawa,
"Yarinya taho nan"
Hajiya sake baki ta yi, ta na kallon yanda yaran nata ke nuna wa mai aiki mahimmanci, kamar ba yaran Gwamna ba,
Cikin magana mai taushi Sultan ya ce,
"Ya sunan ki?"
"Mubaraka suna na"
"Ok, ke ce diyar Lamishi ko?"
Daga kai ta yi, bata amsa ba,
"Me ya hana mata zuwa kwana biyu?"
"Ta yi turmushe na ,(tayi targade ne) amma ta ji dama, gobe ta na tahowa"
"Ok, in kin tai ki gaishe ta"
"Ta na amsawa"
Hajiya Ikee kallon su kawai take da mamaki, duk masu aikin gidan ba wanda basu sani ba, ita da take tare da su shekara da shekaru ma ba kowa ta sani ba, amma su har sun kula da wata bata zuwa.
Ledar kayan Sultana ta miqa mata, sannan suka yi sai da safe, a gurguje ta fita ta bar gidan.
Ko da Mubaraka ta fita Lawwali ya ga fuskar ta ba walwala, sai ya hade girar shi waje daya, ya Qura mata ido, kula da yanayin shi ne ya sa ta sakin fuskar ta.
Ta sani kadan da aikin shi ya koma ya musu ba dadi.
"Mi ya hwaru?"
"Babu komi, kalli abinda Aunty Sultana ta bani, duk sai nij-ji ba dadi, kar ta ga kamar ina son ta ne domin azziqin su"
"Shi daya ke sa ki bata fuska? Ko wani abu aka maki?"
"Ba wanda ya min komi, Yah Auwal mu tai zuwa gida yunwa nika ji"
Dan zare ido ya yi, sannan ya kama hannun ta, suka tafi gidan shi,
Wanka ta yi,ta samu wata riga mai kyau, da mayafin ta, a cikin kayan da Sultana ta bata, ta saka, ta sanya takalmi kalar kayan, Lawwali tsayawa ya yi ya na kallon ta, kamar ba Barakan shi ba, Lallai Indai haka kayan 'yan gayu ke mata kyau, zai maida ita sarauniya a cikin mata, ba shi da wanda zai kashewa dukiyar da ya tara sama da ita.
Shopping ya fara kai ta duk da kukan yunwar da take ta yi, ya sai mata jaka kalar da za ta shiga da kayan da ta saka, ya qirga dubu goma ya saka mata a ciki, dan ya san wannan din ma sai ta tambayi ina ya same su, ko ba yanzu ba, daure fuska ya yi saboda ba ya so ta hau shi da wa'azin ta da bata gajiya.
Wani qayataccen wajen cin abinci ya kai ta, aka Kawo Mata abinci kalar wanda bata taɓa mafarkin gani ba ballantana ci.
Nan da nan kuwa ta yi Bismillah ta fara ci tana ta murna, zuciyar shi cike da so da qaunar ta ya ke kallon yanda farin ciki ke bayyane akan fuskar ta, sai ya samu kan shi cikin nishadi da walwala.
Bai maida ta gida ba sai bayan magariba, ta sha yawo, duk ta gaji, ga kaya niqi niqi da suka shiga da su, har su Jameelu sai da su ka musu siyayyar suturun sawa da abubuwan buqatu na yau da kullum, kamar yanda ya bata dubu goma suma haka ya basu, su Lamishi kuwa dubu ashirin ashirin ya basu, ya so basu sama da haka, amma shegen surutun su ya ja musu.
Kafin ya tafi se da ya buga warning kar wanda ya karbewa Mubaraka kayan ta, tunda ya na cikin kudi sosai yau, ko musu ba wanda ya masa.
***********************
Tun safe har dare Mai unguwar Tudun Faila, da manyan unguwar ke ta kai kawo su na neman dan mai unguwar, mai suna Isyaka, babu inda ba su duba ba sama ko qasa a unguwar nan babu shi babu bayanin shi, mahaifiyar Isyaka ta yi kuka har ta gaji, har da aljanu se da ta tayar, Isyaka yaro ne dan shekara tara, yaro ne mai shiga rai, ba shi da qiwa, ba shi da rikici, in mutum ya zauna da Isiyaka sai ya ji kamar kar su rabu, duk cikin yaran Mai unguwa ya fi qaunar shi, duk da cewa ya na da manyan yara.
Mai unguwa ne ya zauna cikin gajiya da yawon da ya sha, ya kalli matar shi da ke ta turje turje irin na masu aljanu ta na kiran sunan dan ta, duk dauriyar da mai unguwa ke yi, sai da ya karaya, hannun shi ya sanya a idanun shi ya fashe da kuka,
"Dan Mutum? Dan Mutum za a nema a rasa awat-taguwa? Kaiii Allah shi yi muna maganin wanga hali da muke ciki"
*AMEEEN*
A GARIN MU
WRITTEN BY HAERMEEBRAEH
PAGE 23:
Washe gari ma haka aka tashi da neman Isyaka, ba a gan shi ba, kusan duk wanda ya san yaron da wanda ma bai san shi ba, ya taimaka wajen neman shi, shiru kamar an shuka dusa.
A da ne in ana neman mutum ake zuwa gidajen rediyo, talabijin da jaridu neman shi, amma yanzu saboda yawan batan yara da manya da ake, a filin cigiya da sanarwa kadai in aka saka awa biyar ya yi kadan a fadi yara da manyan dake bata, a wannan qasa tamu.
Roqon Allah aka durfafa domin shi kadai ne zai taimake su, su ga yaron su cikin koshin lafiya.
Mijin Asshibi ne ya ja Isah daga cikin mutane, suka koma nesa sosai suka tsaya,
"Isah ban taba zaton za ka min haka ba, ni ne na koya ma wagga harka, amma ka zagaye ta bayan ido na ka dauki kaya, baka sanar da ni ba,"
"Wanne kaya? Ni ban dau kowanne kaya ba, to in ma na dauka ka san ban da wajen ajewa, dole kai din dai zan kawo wa"
Mamaki ne fall zuqatan su, tabbas sun sani ba su dauki Isyaka ba, to waye ya dauke shi?
**********************
Yau kwana biyar kenan Gwamna Halliru bai kwana a gida ba, sakamakon qaratowar zabe ba zama, daga wannan qauye zuwa wannan unguwa, haka za a dinga nuna shi gidan talabijin yana ayyukan alkhairi, kamar