Showing 150001 words to 153000 words out of 155423 words
Chapter 51 - A GARIN MU Book Compelet BY HAERMEEBRAERH.docx
fada ta yi, ta na ta kuka,
"Auwal di na ne ya mutu Hajiya? Ki na so ki sanar da ni Auwal d'i na ne ya mutu? Inaaa ba gaskiya na ba wallah, ban yarda ba, ba gaskiya na ba, bari ki ga na kwanta sai da sahe, gobe zan koma gida na, tunda fatan mutuwa ki ke wa miji na"
Juyawa ta yi hawaye na zuba a idanun ta, ta kwanta, kasa kwanciyar ta yi, ta miqe tsaye, Hajiya Ikee ma miqewa ta yi, ta taro ta, saboda qoqarin faduwa da take,
"Ina zaki?"
"Gida za ni in ga ko ya na can ya na kwana,"
Riqe ta Hajiya ta yi, ta na kuka ta ce.
"Sultana kar ki zama mara tawakkali ga Allah mana, tunda ke san gaskiya Auwal ya rasu ki nutsu ki hwara yi mai addu'a,yanzu ita ya hi buqata, rasuwar mahaifin ku, mun yi aiki da jahilci mun biyewa kidimewar mutuwa mun dimauce, wannan karon bai kamata mu manta da Allah ba, bai kamata mu yi aiki irin na jahillai ba"
Shiru Hajiya Ikee ta ji Sultana ta yi, jikin ta ya sake, komawa gado ta yi da ita, ta kwantar da ita, ta na maimaita
"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel, Innalillahi wa inna ilaihirraji'un"
Duk da ba daidai ta ke fada ba, amma dai ta koma ga Allah, (a yanzu fa abun ya zama ruwan dare, ka ji babbar mata ko qarama ba su iya fadin wasu kalmomi na tasbihi ga Allah ba, amma magana mai amfani da mara amfani fal harshen su, kalmomi na tasbihi kuwa na shan baqar wahala a harsunan su)
Ruwa ta yayyafa wa Sultana, ta farfado, ta tafi ta debo mata mai kyau, dan ta bata ta sha.
Ko da ta dawo, zaune ta ga sultanan ta yi shiru, ta na kallon waje guda, ta yi tayi ta bata ruwan ta qi qarba, kuma ta qi magana, sun jima a haka, har qarfe biyu da rabi na dare,
Sultana mai yawan ibada ce, kallon lokaci ta yi, ta ga be kai lokacin tashin ta ba, cikin dauriya ta miqe, ta fada bayi, har ta yi tsarki ta daura alwala ta gama bata zubar da hawaye ba ko d'igo, sai da ta yi kabbara sallah ne, ta gan ta tsaye a gaban mahaliccin ta, kawai sai ta fashe da kuka.
Daga farkon sallar nan zuwa qarshen ta, ta yi ta ne cike da qasqantar da kan ta ga mahaliccin ta, ta na nemawa mijin ta, da mahaifin ta gafara, da rahamar Allah.
Ganin haka ne ya sa Hajiya Ikee ma yin alwala ta hau nafila, duk da cewa ba ta saba ba.
Washegari da safe kuwa.............
*Allah ya kai mu washegarin, dan Allh ku yi min hakuri akan mutuwar Lawwali, na san ba za ku so hakan ba, amma dukkan mai rai lokacin shi na zuwa, lokacin Lawwali ne ya yi, shima, namu muke jira Allah ya kyautata qarshen mu*
💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻
BY HAERMEEBRAERH
PAGE 65:
Washegari kuwa tun asuba Sultana ta ce wa Hajiya ta bata wayar ta, dan ta gano ita ga boye dan kar ta ji wannan mummunan labarin, Hajiya Ikee ba musu ta duqa qasan gado ta zaro waya, dake da qafa ta tura ta, santsin wajen ya sa ta shige can ciki, sai da ta wahala ta samu fiddo da wayar.
Ana bata ta kunna, ta kira Sultan, da fari bacci ya samu, a zaune a gefen gadon da Mubaraka ke kwance, ta na kira qarar wayar ta tashe shi, ya duba sai ya ga sultana ce, da sauri ya shafe idanun shi, ya qara dubawa, ya so ya qi dagawa, sai ya ga message din ta ya shiga wayar shi,
'Yah Sultan na san komai, ka sanar da ni inda kuke, gamu nan zuwa'
Sake kira ta yi, Sultan ya dauka, jin Muryar ta a dashe ne ya sanya shi qara jin matsanancin tausayin ta, ya san tabbas ta sha kuka, har ta bawa zuciyar ta hakuri.
Sanar da ita inda suke ya yi, sannan ta ce masa ga su nan zuwa ita da Hajiya, ai kuwa ta na kashewa ta tada Hajiya da ta fara bacci, rasuwar Daddyn su ta kwana ba bacci amma ba ta yi Sallah ba, ita a wajen ta, sallar ce ta kashe mata jiki, har ta sanya ta jin bacci.
Sultana ta so ta tuqa motar da kan ta, kan su isa Hajiya ta ɗan rintsa, Hajiya ta qi sam, ba yanda Sultana ta iya, dole ta zauna wajen mai zaman banza, dan bata son magana balle ta yi ja in ja da Hajiya .
Ko da suka isa asibitin shida da rabi na safiya ya yi, har inda aka aje gawar Lawwali aka kai Sultana,d'an da ke cikin ta kamar ya san me ke faruwa, haka ya dinga motsawa, ta jima akan gawar ta na masa addu'a ,tare da koka rashin shi, kafin a ce za a dauke shi a maida shi gidan iyayen shi,Sultana na cikin motar da aka sanya gawar Lawwali dan kai shi gida, duk yanda aka so kar ta shiga qi ta yi, ta dinga kuka ta na fadin,
"Dan Allah ku barni da shi, na wannan lokacin na yi masa addu'a ,daga yanzu ba zan sake gani nai ba sai in na mutu,kar ku hana ni wannan damar ta kasancewa da shi dan Allah"
Haka aka barta kuwa, har suka isa gidan su Lawwalin bata dena masa addu'a ba, ta na yi ta na hawaye, tunanin farkon haduwar su ta fara yi, har ranar da suka rabu da shi, dan zuwa dauko amarya.
Su na isa kuwa Hajiya ta fara shiga gidan, su Lamishi ana zaune bakin murhu ana kunna wuta, za a dora abincin karyawa, ga wasu baqin nan ba su gama tafiya ba.
Ganin Hajiya Ikee ba karamin fadar mata da gaba ya yi ba, cikin wani irin yanayin da ta kasa fassara shi ta hau yi wa Hajiya maraba,kafin ta juya ta shiga gaba sultana ta shigo, salati Lamishi ta sanya, cikin sauri ta fara tambayar Hajiya Ikee,
"Hajiya lahiya? Tunda na gan ki da sassahe haka nissan ba lahiya ba, me ke faruwa? Sultana menene na ganki kamar wadda ta shekara kuka?"
Dakin Lamishi Sultana ta wuce, ta samu qasan dakin ta ta kwanta, ta kalli gini, shiga akai da gawar Lawwali, Hajiya Ikee kuka ta sanya a daidai lokacin da ta ga yanayin da Lamishi ta shiga,
"Innalillahi wa inna ilaihirraji'una, yau na shiga uku na lalace, (haramun ne fadin wannan kalma ta na shiga uku na lalace,kaico na da sauran kalamai marasa kan gado a yayin da akai rasuwa), wa nake gani awa Lawwali? Laaaha'ila ha illallahu, na banu na lalace, wayyyoooo Allah na na shiga uku, d'ana ya mutu, na shiga uku na lalace"
Sai ihu take zundumawa, da kyar aka samu aka rirriqe ta, ta na ta ihu ta na yarda tufafin ta,tare da cizgar gashin kan ta,ba kadan ba mutuwar ta shige ta, amma hakan da take ba dacewa bane, ko Hajiya Ikee da take ajin su daya wajen jahilci ta dauki hakan a rashin dacewa.
Mai Buruji kuka Lamishi kuka, Jameelu da Kamalu da Dan Talo da ke ta shaqar bacci har a wannan lokacin ba su yi sallar asuba ba, ihu da kururuwar Lamishi ne ya tada su, har rige rige suke su isa cikin gidan, arba suma suka yi da gawar Lawwali, wanda aka budewa fuska , gaba dayan su kuka suka saka, su na ta hargowar kuka, da kiran sun lalace, sun shiga uku.
Mubaraka kuwa na can asibiti, kwance, Sultan ya je ya yi sallah, ya siyo ruwa, da dan juice yunwa yake ji sosai, dan rabon shi da abinci tun bakwai na yammar washe garin ranar.
Ko da ya sha sai ya ji ma ruwan ya daure masa ciki, zama ya yi kusa da Mubaraka ya na kallon fuskar ta, kamar wadda ta jima ta na ciwo, duk ta zabge ta rame.
Wani irin tausayin ta ne ke ratsa dukkan wani sashe na jikin shi.
Da misalin takwas da minti ashirin ta farka,da sunan Allah ta budi bakin ta, sannan ta fara neman Yah Auwal din ta, Sultan ne ya fara bata hakuri, ya na sake mata bayanin me ya faru, komawa ta yi ta kwanta, ta rintse idon ta, hawaye na zuba ta gefen fuskar ta, masu zafin gaske,ba ta so ta yi kuka irin na jahilai,ba ta so ta furta kalmar da zata sanya ta aikata zunubi,Dan haka shirun shi ne ya fi.
Su na nan zaune wayar Sultan ta hau qara, ko da ya duba Sultana ce, dauka ya yi, ya mata sallama,amsawa ta yi sannan ta ce,
"Da yanda za a yi Mubaraka ta zo ta ga Auwal kafin a kai shi gidan shi na gaskiya kuwa?"
Da jin haka ya kalli Mubarakan, ya gan ta kwance, amma ya sani za ta so matuqa ta ga yayan ta kafin a kai shi makwancin shi, dan haka ya ce,
"Eh gamu nan"
Sallama suka yi, ya wa Mubaraka bayani, cikin iya saurin da take ganin za ta iya ta miqe,
"Ina zuwa na je na kira likita na fada masa, sai a sallame mu, ko kuma mu je mu dawo"
Daga masa kai kawai ta yi, cikin sauri ya fita, bai jima ba ya dawo da likita, duba ta ya sake yi, sannan ya ce za su iya tafiya, taimaka mata ya yi, ta sauka daga saman gadon, ta natsaye ta duba jikin ta, rigar jiya ce dai a jikin ta, me dauke da jinin yayan ta, wasu hawaye ne masu zafi suka dinga sauka daga idanun ta.
A haka suka tafi motar Sultan, ya zaunar da ita a gefen driver, ya shiga sai unguwar Tudun Faila.
A can kuwa Sultana ta kasa ta tsare ta hana a fitar da gawar Lawwali har sai Mubaraka ta iso, a tunanin malam liman da suka sallaci gawar ta Lawwali, ko ba ta so a kai shi ne, shi ya sa ta fake da hakan, nasiha ya dinga yi mata, ya na lallashin ta, motar su Mubaraka na zuwa ta miqe daga jikin gawar, ta koma gefe, idanun mutanen da ke wajen a tsaitsaye a bakin soron gidan ne ya koma kan su Mubarakan, waje aka ba wa su Mubaraka suka shige, ta na shiga Jameelu ya tura qofar soron, masu leqe da son ganin ya Mubaraka za ta yi suka dinga jin haushi (wai rasuwar ma sai an mata gulma, kamar ba za a mutu ba).
Durqusawa ta yi a gaban gawar, hawaye na ta kwaranya a idanun ta, Lamishi kukan ta ne ya qaru, dan kuwa ta fi kowa sanin irin shaquwar da ke tsakanin Mubaraka da yayan ta, akan Mubaraka rayuwar Lawwali ta zama duk yanda ta zama, domin kawai ta ji dadin rayuwa,kar ta wahala kamar yanda ya wahala.
Cikin zuciyar ta take addu'ar,dan ko labban ta ba ta so ta motsa,
'Ya Allah ga bawan ka nan Auwal, ya dawo gare ka, ya Allah ina roqa masa gafarar ka, ina roqa masa rahamar ka, ya Allah ka tausaya mishi kai mai tausayin bayin kane, Allah duk abinda ya aikata na zunubi Allah ka yafe masa, domin kai mai yawan gafara ne,Allah ka ni'imta qabarin shi, ka yalwata masa shi, ka haskaka masa shi,ya Allah ka masa hisabi mai sauqi a ranar tsayuwa, ya Allah ka bashi ikon amsa tambayoyin kabari cikin sauqi, Allah ka mishi rahama, ka gafarta masa'
Duqawa ta yi, bakin ta na rawa saboda kukan da ke taso mata, ta sumbaci goshin shi, sannan ta shafi fuskar shi, murmushin shi mai kyau ta ke so ta gani, amma ta san har abada hakan ba zai sake samuwa ba, kalmomin shi masu cike da so da qaunar ta take so ta ji, amma ta san hakan ba zai samu ba, kifa kan ta tayi, a qirjin shi ta rungume shi, ji take kamar kar a dauke shi, kamar ya farka ya ce Barakana wasa ta ni kai miki, Sultana ce ta duqa cikin qarfin halin da ke bawa Kowa mamaki, ta daga Mubarakan, ta rungume ta, sannan ta ja ta suka shiga ciki, su Jameelu suka bude qofar aka sake rufe Lawwali yanda ya dace, aka dauke shi sai makwancin shi na gaskiya.
Tunda suka shiga dakin na Lamishi, ba mai magana, sai kuka, Lamishi ta tabbata ta yi babban rashi, rashin da ko sanda iyayen ta suka rasu bata ji zafin shi kamar haka ba, tunawa da kalaman shi take, a kullum ba shi da burin da ya wuce iyayen shi su so shi shi da qanwar shi, a basu kulawa kamar sauran yara,amma daga ita har uban shi, sun gaza.
Rafka salati ta yi, ta fashe da kuka, na kusa da ita na ta bata hakuri, kukan 'Yabbuga da salatin ta ne ya ja hankalin mutane gare ta,
"Mun yi babban rashi, mun yi babban rashi, sannun mu da hankuri Lamishi Sannun mu da hankuri,kaiiii duniyar ga ba matabbata ba ce wallah,jiya jiya mun ka rabu ina ta bawa Dan Jumma labari har magana mun yi da Lawwali asheee asheee Lawwali kau gawa ce tsaye, mai rai ba bakin komi shi ke ba wallah,sannun mu da hankuri jama'a sannun mu da hankuri"
Surutai kawai 'Yabbuga ke zubawa, wanda ke nuni da cewa tabbas mutuwar Lawwali ta daki zuciyar ta, wani dogon numfashi ta ja sannan ta ce,
"Ina can hangame da baki, ina kwanan wahala, Dan Jummaa yaddawo yatas-san,ya ce daga gidan ga shike Lawwali ya mutu,la'ilaha illallahu"
Wata mata ce ta ce,
"Boyar Allah hankuri zaki, hankuri kowa shi ke yi wajen ga da kiggane mu, mata tai da qauna tai na ciki, su ma hankurin suke"
"Keeee wagga banni, banni yanda kin ka ganni, ba ki san ya nika ji ga zucciya ta ba,....Ohh rayuwa kenan, ina Mubarakar take, boyar Allah"
Miqewa ta yi ta bazama zuwa dakin, zaune ta gan su, da su Hajiya Ikee da Sultana, sai Mubaraka da ke kwance kusa da Sultanan, ta na ta sauke numfashi da kyar,ji take iskar shaqa ta mata kadan, amma haka take daurewa, ko dan kar Sultana ta sake samun wata damuwar.
"Sassanun mu da hankuri bayin Allah, Allah shi jiqan Lawwali, Allah shi gahwarta masa, sannun mu da hankuri, Hajiya Sannun mu da hankuri"
Amsa mata suka yi, tare da yi mata godiya.
Su na nan zaune mutanen unguwa aka fara kawo abincin sadaka, ai kuwa kafin kace me, masu zaman makoki an miqe an fara warwason abinci, kowa na son ya samu abinda zai kai bakin salati.
Sai a sannan ne Hajiya Ikee ta tuna Sultana ma bata karya ba, ga ciki, waya ta yi wa Sultan, ta ce ya samu ya ɗan siyo ko da kayan shayi ne me yawa da bread a kawo, saboda su karya, ai ba a zauna ba abinci ba.
Nan da nan kuwa ya aika su Jameelu, aka kawo kayan shayin da bread,bayan sun debi wanda za su yi amfani da shi, ta sa aka fidda sauran.
Duk yanda ta so ta matsa wa su Sultana su ci abinci qi sukai, dole ta hakura, ta ci ta bar su.
Haka akai ta zaman makoki, har kwana bakwai, sannan Hajiya Ikee ta tafi ta bar Sultana a gidan, ita da Mubaraka sun zama kamar hanta da jini, a koda yaushe su na tare da junan su, kowacce su na kallon 'yar uwar ta a matsayin Lawwali, domin su din masoyan shi ne, ya na ji da su.
Sultana bata bar gidan ba sai da aka yi arba'in a lokacin cikin ta ya shiga wata na tara, Mubaraka ke raka ta ganin likita, Sultan ya yi hakuri iya hakuri, domin ba zai iya bijiro da maganar kai masa amarya a wannan lokacin ba, amma tabbas ya na da buqatar matar shi.
Cikin Sultana har ya haura wata tara, ta wuce EDD din ta, haihuwa shiru, kuma ciki kullum aka je ganin likita zai ce lafiya qlou take.
Yau ma sun shirya tsaf dan zuwa asibiti ganin likita, Sultana ce ta ke ta yi wa Mubaraka magana akan ta hanzarta Sultan na jiran su a qofar gida.
Cikin sauri ta qarasa sanya hijabin ta ta sake yi wa Lamishi sallama suka fita, zaune yake a motar ya sha gayun shi da wata brown din shadda da baqar hula, hasken shi ya qara fita sosai, ya yi wani irin kyau,tunda suka shiga motar Suka gaishe shi, Mubaraka ta ja baki ta tsuke, lokaci zuwa lokaci ta na satar kallon shi ta madubi.
"B love ki kalle ni kan ki tsaye, ni din naki ne, ke kadai, ba sai kin yi ta satar kallo na ba kamar wani baqon saurayi a unguwa"
Kunya ce ta kama ta sosai, ta sa hannun ta ta kare fuskar ta, ta na kallon waje.
Sultana kuwa murmushi ta yi, tunawa da nata masoyin sai ya sanya kwalla taruwa a idon ta, har suka isa bata san wainar da su Sultan ke toyawa ba a motar.
Su na zaune a asibitin Mubaraka ta hango Hansatu riqe da Ahmad sai wani mutum a gefen ta, Hansatu ta yi shar da ita kamar ba Hansatun Isah da ta sani ba, ganin Ahmad ne ya sake tabbatar mata da cewa Hansatun ce dai.
Ta gaban su za ta wuce, har sun gota su ta koma baya,
"Ahhh Ahhh Mubaraka d'iyar albarka, kwana da yawa"
"Aunty Hansatu ina kwana, ya gida, ya su Ameenatu,"
"Lahiya qalou, ya bayan rabuwaaa? Ina mutanen shiyyar mu, ya su Lamishi, ya yayan ki, ina hwata kowa lahiya"
Cike da murmushi Mubaraka ta ce,
"Kowa lahiya lau Aunty Hansatu, Yayana ne dai Allah ya yi mai rasuwa har an yi arba'in ma, waccan matar shi ta, mun ka kawo ganin likita,"
Salati Hansatu ta yi, sanan ta ja Mubaraka su ka ɗan koma gefe,
"Allahu akbar, Allah ya jiqan shi, dan Allah ki gaishe min da su Lamishi, ina nan tahe, ban sani ba, ban da labari, dan tunda na