Showing 111001 words to 114000 words out of 155423 words

Chapter 38 - A GARIN MU Book Compelet BY HAERMEEBRAERH.docx

17 Oct 2025

285

ajiyar zuciya Isah ya sauke, tare da sakin kwalin madarar a qasa, ya rungume Laminu, ya na murna,

"Kai sake ni menene haka, sai an gan mu a ce 'yan iska muke, kai jaye"

Tura Isah baya Laminu ya yi, ya na waige waige, cikin jin dad'i Isah ke bawa Laminu labarin yanda ya san an kama yaron nasu, Laminu ya ce,

"To rudewar da kayi na yasa bata idasa baka labari ba, da ta baka, da ka gane cewar an kashe shi , ko kuma ba a sanar da ita ya mace ba"

"Kaiii Laminu amma kai shege ne"

"Ahafff hauka nike da zan bari asiri na shi tonu? Kai fa ba dan garin nan bane ba, ka na iya guduwa ko baka da iyaye a Kano ,ni kuwa uwaye na da uwayen matata nan suke"

Hira suka dan taba Laminu ya ce shi zai shiga matar shi na can na jiran shi, Isah ma murmushin da bai taba kalar shi ba a rayuwar shi ya yi, tare da cewa,

"Ni ma tun dazu take min waya, bari na je gida"

Sallama suka yi, kowa ya kama hanyar shi.

Ko da Isah ya isa gidan, ya tarar da shi kamar kullum, a share, a tsaftace, abincin shi na wajen da aka saba aje masa, har da sabuwar tabarma.

Komai da yake buqata ya same shi har da qari ma, amma fa Hansatu ce kawai bai gani ba kamar yanda ta saba, ko qarfe nawa ze kai a waje, ta na nan ta na jiran shi.

Ko daya leqa dakin da kyau kwance ya gan ta, sanye da wata iriyar rigar bacci mai daukan hankali, sake leqa wa ya yi shin Hansatu ce ko wace ce? Kafff rayuwar su bata taɓa sanya rigar bacci ba, tunda ya aure ta ba ko lefe, balle ya ce ya saka a ciki.

Baccin ta take cikin kwanciyar hankali da nutsuwa, Isah kuwa hankalin shi in ya fi cikin unguwar ya tashi.

Cike da damuwa ya zauna bakin gadon, ya kai hannu zai tashe ta, da sauri ya janye, dan bai san da me zata farka ba, rashin sanin meye a zuciyar ta na sa Isah damuwa, da dakatar da shi akan abinda ya so aikatawa.

Ya kai qarfe goma da minti sha daya ya na ta kai komo, tsakanin daki da parlour, motsin shi ya yi yawa, har ya hana ta bacci, da wata iriyar miqa ta tashi, wadda ta sanya Isah kai mata runguma, turashi baya ta yi, sannan ta ce,

"Meye haka? Bacci fa ni kai, duk ka ishen da motsi, mi ka ke bid'a wanda ban aje maka ba? Ko kuwa kwanan da nikai ka ke baqin ciki na yi duk da wuni da na yi aiki?"

Zama Isah ya yi a bakin gadon, ya na kama wandon shi, jijiyoyin kan shi har sun bayyana rud'u rud'u,

"Dan Allah Hansatu ki taimaka min, ni ba ni buqatar komi sai ke, na qoshi da abincin ma ni, ki taimaka min"

Tashi ta yi, ta na wata iriyar tafiya da ni kaina sai da na yi mamakin shin anya Hansatun Isah ce? Ko kuwa Hafsatun Hajiya ce?

Hijabin ta ta zira ta fita waje, fitsari ta yi, ta wanke bakin ta, dan ta yi bacci ta ji ya sauya mata, sai da ta wanke fuskar ta sannan ta koma d'akin, Isah ta gani cikin mawuyacin halin da ba zata iya kauda kai ba, ko ba dan shi ba, dan tsoron fushin da Allah da Mala'iku za su yi da ita, ta sani duk matar da mijin ta ya neme ta a shimfida komai fushin da take da shi, haramun ne matar nan ta qaurace wa mijin, in ta qaurace masa direct, ta ce ba zata ba, ko ta dinga yin wasu abubuwa indirectly har ya gaji da jiran ta ya yi bacci, to fa ta na cikin tsinuwar Allah da mala'ikun shi, har gari ya waye.

"Ni da kai akwai banbanci, domin kuwa na san Allah, na san dokokin da ya gindaya akan aure, kuma ina qoqarin kare kai na da take su, sai dai in da rashin sani, amma ka san wani abu, daga yanzu ba zan sake kwanciya da kai ba ba tare daka yi wanka ba, ba tare da ka wanke bakin ka da kyau ba, ba zan kwanta da kai ba ni ina cutuwa kai ka na mora ta ba wallah, an wuce wannan lokacin, in ka na buqata ta, ka tai zuwa wanka,in ka dawo ka wanke bakin ka, ban cuce ka ba na daina bari ka na cuta min wallah"

Komawa ta yi, ta yi wata iriyar kwanciya mai daukan hankali,a sukwane Isah ya bar dakin, ya shiga wanka, ya jima ya na dirzawa da cud'a jikin shi, sai da ya tabbata ya fita fess sannan ya dauraye jikin shi ya fita, abun ya bashi mamaki, da ya ga brush da toothpaste a ajiye a saman buta a qofar bayin, bai tsaya dogon bincike ba ya dauka ya wanke bakin shi tass, sannan ya koma dakin.

"Shin wai da ka taho ba alwala, ka yi sallar Isha'i halan?"

"Hansatu ba na jin sallah ta tana amsuwa innayi ta haka nan, dan Allah ki taimaka min"

"Watakam za ka iya yin wanka da brush dan biyan buqatar ka, amma ba zaka iya yin Sallah ba, dan cika umarnin Allah, lallai baka tashi kwana ba wallah"

Juyi ta sake, cike da kwarewa, sai da na dauki Style din juyin (lols) ta koma ta kwantar da kan ta a pillow, hankalin ta kwance.

Isah kuwa kuka ne kawai bai yi ba dan takaici, Gashi yanzu yanda ya ke hango rashin jin tsoron shi a idanun Hansatu, ba ya jin ko fada ya tsaya yi da ita zai samu riba.

Sallah ya je ya yi, a gurguje, ya koma dakin, gani ya yi ta kashe wutar dakin, a cikin duhun ya qarasa gadon......

Hansatu ta bawa Isah mamaki matuqa, ta shayar da shi zumar da ya dinga tunanin anya duk duniya akwai wadda ta fi Hanstun shi kuwa? Maqale ta ya yi gam da jikin shi, kamar ya na tsoron wani zai janye ta.

Ita kuwa kwace jikin ta tayi, ta tafi ta yi wanka, ta yi nafila raka'a biyu, tare da addu'ar Allah ya qara kawo mata zaman lafiya da kwanciyar hankali a gidan ta, sannan ta haye gado ta kwanta, kusa da Isah da ke ta sheqa munshari.

Da safe kuwa haka Isah ya debo kayan da ya samo a Makka wanda Larabawa suke bayarwa, sadaka, ya dinga bawa Hansatu ya na zuba mata qarya, ya na kurin shi ya siyo mata da kudin shi.

Ita kuwa fuskar ta ba walwala, ba fara'a take furta

"Na gode, Allah shi biya"

Isah dai ya qi shiru, sai zuba yake, qarshe da ta ga ba zai daina cika mata kunne ba, daki ta koma, ita da Ameenatu, suka bar shi da su Bilkisu a wajen.

Sai da ya ga Ahmad na qoqarin balle stone din wata riga, ya tattare duk haushin Hansatu da yake ji na qin kula shi da ta yi, ya gaurawa yaron mari, ai kuwa ya gigice, ya dinga zindima ihu, murmushin mugunta Isah ya yi, dan ya san zata je bada hakuri, ya qara bankawa yaro mari, Ameenatu na ta yi wa Hansatu magana akan ta je ta bawa Baban nasu hakuri, ta yi Murmushi ta ci gaba da gyara dakin ta abun ta.

Isan da yaga ba wanda ya kula shi sai ya hau masifa da zage zage, nan ma ba wanda ya ce masa ci kan ka.

Haka ya qaraci masifar shi ya bar gidan, tare da tabbatar mata da a sati na sama zai koma Makka,tunda abin nata iskanci ne.

Shirun da ta masa ne ya qara tunzura shi ya bar gidan gaba daya.

**************************

Ya kasa zaune ya kasa tsaye, saboda labarin da ya samu, Gwamna Halliru ya raba hotunan Mubaraka, ma jami'an tsaro dake tare motoci a hanya su bincika, ko da za a ga Mubaraka akai masa ita direct wajen shi, babban abun takaicin shi ne Dan Talo da kan shi ya bada hoton diyar tashi, ba tare da ya san me ke faruwa ba.

Sultana ce ta kwantar da kan ta a bayan shi, ta rasa da me zata kwantar masa da hankali, gaba daya naman jikin shi rawa yake, hankalin shi a tashe yake, damuwar shi what if aka kama su Mubarakan shi fa? Ina zai saka ran shi, ya zai ya cika mata alqawarin da ya daukar Mata na bata kariya? Daga shi har ita ba su da kowa mai qaunar su domin Allah sai junan su, in wani abu ya same ta ba zai taba yafewa kan shi ba.

Zama ya yi a qasa dabar, ya fashe da wani irin kuka mai ban tausayi, Sultana ma kukan take, duk ta bi ta rame, saboda rashin kwanciyar hankali.

Kallon ta ya yi, ya rungume ta sannan ya ce,

"Ki yahe min Sultana, ban zama miji nagari a gare ki ba, ban san ya zan da raina ba in wani abu ya same ta, kin dai san ta na shiga hannun mahaifin ki kashe ta zai ko? "

Ta na qoqarin kwatanta yanda yake ji a ran shi, amma bata san ya zata bayyana masa hakan ba, ba tare da ta yi tunanin komai ba, ta kai bakin ta nashi,wannan shi ne karo na farko da suka jima su na sumbatar junan su, kuma shi ne karo na farko da sumbatar ta zarce, har sultana ta cire duk wani tsoro, da tsaro, da kuma dokar da ta shimfida a tsakanin su, na sai ya fara sallah zata yarda ya Kusance ta, tunawa ta yi a ran ta cewar, ita addu'ar saduwa tsakanin ma'aurata, ba dole sai namiji ne kawai zai yi ta ba, mace da namiji duk ana so su yi, in daya be yi ba, saboda wani dalili, misali mantuwa, ko rashin iyawa, wanda ya iya zai iya yi shi.

A yammar Lawwali ya yi nasarar karbar haqqin auren shi a wajen matar shi ta sunnah kuma diyar fitaccen maqiyan shi,Lawwali bai taba hango cewar rayuwar aure dama haka take da wani sinadari, da dandano ba, sai a yau, wanda da ya san haka abun yake, da bai kai wannan tsahon lokacin ba, ba tare daya karbi haqqin shi a wajen Sulty Baby ba.

Lawwali ne ya taimaka mata ya maida ta saman gadon su, duk qasan carpet din ya ɓaci, cikin tausaya wa ya ce,

"Sannu Sultana, yanzu ya za mu yi? Na ga kin ji ciwo,ni ban san ya zan yi ba"

Duk da ciwon da take ji a jikin ta, bai hana ta, murmusa wa ba, tare da godewa Allah, da bai yi ta mazinaciya ba, hannun shi ta kama ta sumbata, shi kuma cikin damuwa ya kalle ta ya ce,

"Ki sanar da ni, mi zan yi yanzu? Ban san me zan ba, na ga har yanzu jini na zuba a jikin ki"

Cikin dasasshiyar murya ta ce,

"Ina so ka yarda da Allah,ka yarda Allah ne kawai zai iya bawa Mubaraka kariya ba kai ba, ka yarda cewar mubaraka ta na cikin kariyar ubangiji, ba wanda ya isa cuta mata sai idan Allah ya so,ina so daga yau ka min kyakkyawar kyautar da zata faranta raina,kyautar da har na koma ga mahalicci na ba zan daina jin dad'in ta ba"

Kafin ta sauke numfashi Lawwali ya ce,

"Na miki alqawarin baki duk abinda na mallaka, na kuma amince Allah shi ne kaɗai wanda zai kare min Barakana a duk inda take"

Murmushi ta yi, gefen idanun ta kuwa hawaye ne ke zuba da gudu,

"Ina so ka koma bautawa Allah, kamar kowanne musulmi cikakke, kuma nagartacce, wannan ita ce kyautar da nake so, a matsayi na na matar da ta kawo mutuncin ta gidan miji"

Lawwali bai san sanda ya rungume ta ba ya na kuka, tare da fadin

"Allah na tuba, Allah ka yahe min, ban san wanne aikin alkhairi na aikata ba ga rayuwa ta, da ka bani mace kamar wagga, Allah ka yahe min, Allah ka tausaya min ka yahe min ba dan hali na ba, Allah na san ka na so na da rahama ne ya sa ka azurta ni da mace kamar Sultana, Allah ka bani ikon sauya halaye na ka yi min afuwa"

Daga shi har ita kuka suke, da kyar suka lallashi kan su, suka yi shiru,

"Ka ce wa Barirah ta kawo ruwan zahi, kai kuma ka je ka yi wankan tsarki, ka shirya ka je gidan mu, ka taho da Sultan,ba tare da kowa ya sani ba, ka ce zaka kawo shi waje na mu gaisa, in ka yi haka, Daddy ya ji labari daga baya, ba zai sake ya cutawa Mubaraka ba har ta iso nan lahiya, ko ka na da wata shawara da ta hi wagga sauqi?"

Lawwali sake fashewa ya yi da kuka, ya rungume Sultana, yau zuciyar shi ta koma danya shataff a gaban matar tashi,su na haka, ta koya masa yanda ake wankan, ya tafi ya yi, ya kuma bada umarnin a kula da ita, ya bar dajin.

Kamar yanda suka tsara kuwa haka aka yi, tun Sultan na ganin nisan waje,har ya fara tambayar shin ina za su ne? Lawwali kuwa budar bakin shi sai cewa ya

"Za mu tai ne ka ga inda Daddyn ku ya bamu dan mu zauna ni da mata ta"

Mamaki ne fal ran Sultan,yanzu duk gidajen da suke da shi a cikin gari a rasa inda Sulty Baby na ta zauna sai kauye?????......

*Hummmm Sultan kenan, U never see anything*

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻

BY HAERMEEBRAEH

PAGE 51:

Mutanen da ya gani sanye da qananan kaya da bindigogi, sun tsoratar da shi matuqa,nan take ya tuno da kalaman iyayen shi akan Lawwalin, amma ya rasa dalilin da ya sa ya kasa gasgata maganar su a qasan ran shi, har yanzu ya na ganin Lawwali a matsayin mutumin kirkin da ya ke gani a baya.

Su na isa sansanin Lawwali ya bude mota ya fita, ya na jiran Sultan, Sultan cikin daurewar kai ya fito,kwakwalwar shi da kowacce gab'a ta jikin shi na so a masa qarin bayanin abinda idanun shi ke gani.

"Kar ka samu damuwa ran ka shi dade Sultan, mu je za ka san duk wani abu da ka ka buqata, Sultana na ciki na jiran mu"

"Wai dan Allah da gaske anan Sultana ke rayuwa? Ko dai wasa ka ke min, me ya had'a ku da irin wadannan mutanen?"

Gaisuwar da Sultan ya ga ana miqawa Lawwali ne ya sake sanya shi cikin rudani, sun kusan isa dakin su sultana, sultanan ta fito cikin wata iriyar kwalliya, mai ban sha'awa, ta yafa mayafin ta kalar shaddar da ke jikin ta, ta saka flat shoe, sai qamshi take zubawa, Lawwali na dora ido akan ta, ya ji duk wata soyayyar ta da yake ta qoqarin dannewa, da wadda bai ma san ya fara yi mata ba, ta taso ta lullube shi, wani qayatacce, kuma sassanyan murmushi yake zuba mata, Itan ma haka, sai dai kunyar shi ta fi yawa a tattare da ita a yanzu, bata iya hada kwayar idon ta da na shi, Sultan tsaye yake ya na kallon ikon Allah, cikin gyaran murya, da gyara tsayuwar shi ya ce,

"Baby Sulty ta dena so na yanzu,"

Da sauri ta kauda kan ta daga kallon qasan ido da take wa Lawwali, ta fara takawa, cikin tsananin kulawa dan kar su gane sauyawar tafiyar ta, ta isa gare shi, rungume ta ya yi, ita ma ta sa hannayen ta biyu ta rungume shi, sai da suka gama farin cikin ganin junan su, sannan Lawwali ya saqale hannun shi daya a qugun ta,  sannan suka shiga ciki.

Lawwali ya yi mamakin yanda aka gyara wajen, sai kamshi ke tashi, ga abinci nan an kawo, da abun sha.

Aikin Barirah ne wannan.

Zama suka yi gaba dayan su, tare da yiwa Sultan Bismillah, kame hannayen shi ya yi, a qirjin shi, sannan ya ce,

"Ni fa ba zan iya sanya ko da ruwa ba ne a ciki na, ba tare da na san mi ya kawo ku dajin ga ba, shin sace ku an ka yi ko mi na na?"

"Mun yi maka kama da wanda anka sace?Kai dai aka sato, domin kuwa a yanzu haka in ba mun samu abinda muke so ba a wajen mahaifin ku, ba zaka koma cikin gari ba"

Wata dariyar rainin hankali Sultan ya yi, ya kalli Lawwali ya ce,

"Habaa habaa suruki na, ai ni nafi qarfin a sace ni, in ka ga an sace ni to qaddara ta ce ta zo da haka, ni da ka gane ni ban wasa da azkar, ban wasa da addu'ar hita da shiga gida, ka ko ga me sace ni sai ya shirya"

Sultana ce ta yi dariya ta ce wa Lawwali,

"Kira Daddy"

"Ban gane shi kira Daddy ba, me ke faruwa ne? Ku na ta sa wa kai na na daure wa,"

"Yah Sultan in har ka bamu goyon baya akan abinda muke shirin yi, na maka alqawarin sanar da kai komai game da iyayen mu, wanda nake boyewa ba na so ka sani, dan kar ka shiga damuwa"

Kallon su kawai yake, ya ma kasa magana, kenan ta tabbata sato shi aka je har qofar gidan su aka yi, kuma ya zo ba tare daya san sato shin akai ba.

"Excellency sir, ka na lahiya?.....yi hankuriii ba fada ne yasa na Kire ka ba, wasu kadarorin ka ne a waje na, wanda duk duniyar ga baka da kamar su, ina mai tabbatar maka da cewar in baka dakatar da neman qauna ta ba, ta iso gare ni lahiya, zan manta da wai an tai central mosque an daura min aure da diyar ka, zan sa bakin bindiga na halbe ta, d'anka da na tai na dakko dazu...."

Cikin wata iriyar tsawa Gwamna Halliru ya miqe tsaye daga saman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login