Showing 141001 words to 144000 words out of 155423 words

Chapter 48 - A GARIN MU Book Compelet BY HAERMEEBRAERH.docx

17 Oct 2025

288

gaisa, suka mata ta'aziyya, Mubaraka ce ta zauna kusa da ita, ta na sake mata ta'aziyya,

"Ameeen na gode, amma dai nan za a bar ki ko? Sai an yi arba'in"

Kallon Lamishi ta yi, ta na neman izini, da ido,daga baya ta maida duban ta wajen oga Lawwali, ta dire shi akan Sultan,da ya kafe ta da ido ya na jiran jin amsar ta, kowa ya yi Mamakin yanda Lamishi ta yi sanyi, ta koma kamar ba ita ba,

"Ki zauna, ba ya da komi, ai duk ɗaya ne"

A tare Mubaraka da Sultana suka ce

"Na/na gode Ummaa"

Wani qayataccen murmushi ne ya bayyana a fuskar Lawwali, miqewa ya yi, ya ce in sun gama su masa magana, zai maida su gida

Duk wani motsin Mubaraka na kan idon Sultan, duk ya sa ta ta kasa sakewa, qarshe sai da suka hau sama yin Sallah, sannan ta samu ta ji kamar an zare mata wani abu da ya takura walwalar ta.

Sun kai kimanin awa guda,kafin Baraka ta raka su waje.

A bakin motar shi ya tsaya, ya na jiran su, da kan shi ya budewa Lamishi mota, ta shiga, ta na mai jin dadi, da da suke tsananin maitar mota ma ko kusa da ita ya hana su zuwa, amma yanzu gashi shi ke bude musu su zauna.

Sallama suka yi da Mubaraka, ya ce zai debo mata kayan ta, in ya kai su Lamishi, nan ta fara shagwaba, ita Umman ta ne za ta debar mata kayan, ta yi ajiya ba ta so ya gani, yafitar ta yayi, ta kai kunnen ta saitin bakin shi,

"Na hwa san mi ki ke boye min, yo ni ma mata ta ta na da su, ko d'azu a gida sai da na wanke mata su, mi na na acciki to dan na gani, ni ne fa Yah Auwal d'in ki"

Dariya take son ta yi amma dole ta daure, dan ko ba komai gidan rasuwa suke

Shi kuwa fita ya yi da mota ya na dariya,.

Lamishi kuwa cikin ran ta, ta na jin wani irin dad'i na ratsa ta, a baya haushi take ji, ta ga Lawwali na fifita Mubaraka akan su, amma yanzu sai ta gane hakan ba wata matsala bace da zata sa ta dinga jin haushi, hakan na nuna su din su na son junan su, da bawa juna kulawa.

Bayan sun Isah gidan, ya sha mamakin ganin Icce da gawayi buhu uku, a aje a rumfar da Dan Talo ke ta yi da kan shi, juyawa Lawwali ya yi bayan motar ya ce ma su Lamishi,

"Wa ka sai da ic-ce a unguwar  nan?"

"Baban ku ne, ya ce yanzu in shaa Allahu ba zai sake zaman banza ba,da kuddin da ka bamu, ya samu ya siyo komai da shika bid'a, abokan shi  na masa dariya, shi ko ko a jikin shi, sai da ya qare ya siyo motar icce guda an ka juye mai, ya sa gawaiyi, har da barahuni (kananzir)yaka sayarwa"

"Ikon Allah"

Daga haka bai qara magana ba, fuskar shi dauke da murmushi ya qarasa rumfar.

Sallama suka wa juna, Dan Talo ya dinga neman afuwa da gafarar Lawwali, ya ce ya nemi gafarar sauran yaran shi, ya kuma yi alqawarin zai zama uba na gari

"Allah shi bada iko baba, ni ma ka yahe ni, in shaa Allahu, sana'ar ga sai tayi albarka, yanzu mi ka ke buqata a qaro?"

"Babu komi, in ma akwai ina da kud-din siye, yafe min da ka yi ma ya ishe ni, ban san cin iyali na ba, ban san shan su ba, ban san suturar su ba, balle wajen kwanan su, ba su da lahiya, ko su na cikin b'acin rai, da quncin rayuwa duk ban sani ba, a da ji na nikai kamar wanda an ka d'ebewa tunani,amma yanzu hankali na ya dawo jiki na, na san fari na san baqi yanzu, da yardar Allah sai iyali na sun yi farin ciki da ni kamar yadda kowanne iyali ke jin dad'in mai gidan su"

Lawwali ya kasa cewa komai, sai murmushin jin dad'i kawai ya ke zubawa, nan ya zauna su ka yi ta hira da mahaifin shi, daga qarshe shi ma ya yanke shawarar Kano zai dinga zuwa ya na kasuwanci, duk qarshen wata ya na dawowa.

************************

Zaman mubaraka da su sultana ya sa sun rage kewa kadan, dan kuwa, tare suke haduwa, da Sultanan su yi ta karanta qur'ani, Hajiya Ikee ba a iya karatu ba, ita daga qulhuwallahu sai Fateeha su ma a sallah take yin su, da mutum zai saurara zai rantse da Allah Yaren mutan China take ba larabci ba, rayuwar ta kafff ta qare ta ne wajen neman duniya, amma harafin alif da baa na mata wuyar haɗawa, balle ta kai ga karanta qur'anin sukutum.

Mubaraka ta kula da hakan, dan haka ta qudirta a ranta, za ta taimaka wa Hajiya, dan ganin ta samu tagomashin alkhairi da ladan da ake samu, wajen karanta littafin Allah.

A hankali kuwa Hajiyan ta fuskanci me Mubarakan ke so ta yi,da sauri ta ajiye girman kan ta, ta na koya, Mubaraka ta yi amfani da koyar da Hajiya ta na rage mata kewa, da yawan tunani.

Da ta gilma ta gan ta tana kuka, ko tunani, za ta ce,

"Hajiya, in an had'a, ba'un da fataha, da mimun da fataha, me zai baki?"

Sai ta yi shiruuuu ta na nazari, can sai ta washe baki ta ce,

"Bama"

"Yeeehhh Hajiya za ta ci Bama"

"Yannema ni dai a dinga  yi min kad'an kad'an, kar karatun ga shi yi min yawa, in taho banni gane komi"

"Ganewa ki kai inshaa Allahu, kahin Ramadan mai zuwa ke zaki zanka ja wa Aunty Sultana baqi, ita kau ta na fassarawa,tafsirin cikin gida za mu yi"

Dariya sosai suke yi, in Mubaraka na musu irin wannan barkwancin.

Sultan kuwa da ya gan ta zaune da su Hajiya, shi ba ta masa hira kamar ta su Hajiya, sai ya yi ta bata rai,ya na wani abu kamar qaramin yaro, ya na sane sai ya zubar da ruwa, ko tea, ko ya b'ata waje,ya kwala mata kira, Ita kuwa ta gane me yake nufi, ba ta kula shi, sai dai ta je ta gyara wajen, fuskar ta dauke da Murmushi, kallon ta zai ta yi, kamar ya samu TV, da ya ga za ta tafi, zai qara yin wata barnar,dan kawai ta tsaya.

Watarana suna can sama su na hira, Hajiya na basu labarin yanda ta hadu da Daddy, har suka yi aure.

Sultan ya zubar da tea, ya kwalawa Mubaraka kira, tare da sanar da ita ta je da abun gogewa.

Har za ta miqe Hajiya ta ce,

"Zauna, baki zuwa, ni bari na je, na goge masa, in ba ze zo ya ce  Hajiya aramin ita ni ma muyi hira ba,ba ki zuwa yi mai aiki, danneman rainin wayo kai, ya zaci ban gane komi ba, tunda takkwala na ke, na hi kowa qaramar kwanya gidan ga"

(Tunda daqiqiya ce ni na fi kowa karamar ƙwaƙwalwa a gidan nan)

Da kan ta ta shiga dakin na shi, Sultan an sha wanka da wata shadda da akai wa d'inkin half jumpa, kan shi ba hula, sai qamshi yake zubawa, ya na tsaye jikin TV, ya na rage volume Hajiya ta shiga, ba tare da ya juya baya ba, ya fara magana,

"Mubaraka, ki yi hankuri da aikin da ni ke saka ki, ta haka ne kawai zan gan ki, dan na kula yanzu ke hi son su Hajiya akai na, jiya Daddy ya cika kwana arba'in da rasuwa, ina fatan nan da wasu kwanaki mu bayyana wa h......"

Maganar shi ce ta maqale da ya juya suka yi ido hudu da Hajiya, fuskar ta ba wani emotion a jiki, ji ya yi gaban shi ya yanke ya fad'i, dube dube ya fara yi, ya na neman Mubaraka, bai gan ta ba,

"Ha...haaajiya Mum, inaa Mubaraka?"

"Dama kenan ta san ka na son ta?"

Yanayin yanda ta yi maganar ya so ya bashi tsoro, cikin zuciyar shi ya fara tsoron kar dai Hajiya har yanzu ba ta dena qin jinin talaka ba? Bai san ya zai da rayuwar shi ba in ta ce ba zai auri mubaraka ba.

Juya baya ta yi, Sultan na nan tsaye ya kasa magana, saboda rashin sanin me ne ne a zuciyar Hajiya Ikee game da zabin shi..........

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻

BY HAERMEEBRAERH

PAGE 62:

"Dan Allah Hajiya kar ki qi wannan auren, Mubaraka alkhairi ce a gare mu baki d'aya in shaa Allahu, ban ga wata mace da zan iya aura na ji dad'in rayuwa ta ba sama da ita,Kuma na ga yanzu ki na son ta, ko?"

A hankali Hajiya Ikee ta samu waje ta zauna, idanun ta sun sauya kala, daga farare tass zuwa jajaye, saboda hawayen da ke barazanar sauka mata, hancin ta ta ja, sannan ta dora idanun ga a saman fuskar Sultan, da ke a tsugunne a gaban ta, kamar me neman gafara, ya na jiran ya jin kalar hukuncin da za ta yanke.

"Wato Sultan na koyi darrussan rayuwa a qarshen shekarar ga, ba kadan ba, na koyi abubuwa kala kala, ciki ko har da sanin darajar Dan Adam, a baya ba kalar wulaqancin da ban yi wa iyayen yarinyar ga ba, da ita kan ta, amma ka diba ka gani, a yanzu ita ka qoqarin kwantar muna da hankali, saboda halin damuwar da muke ciki,ita ke qoqarin ganin na san wane ne mahalicci na, na shekara d'ai d'ai har shamshin da shidda amma ban iya karanta qur'ani ba na bata rayuwa ta a banza ban san wanene ubangiji na ba, ban taɓa karanta kalma ɗaya ta alqur'ani ba tsabar rashin rabo, boko kuwa ko da baturiyar qasar Amurka sai mun buga, ka diba ka gani, a wata d'aya yarinyar ga ta hwara sawa ina iya karanta wasu kalmomi na larabci, na qara yarda da cewa, kyawun huska, ko wani kyau na halitta, ba shi kad'ai ne  kyau ba, kyau shi na cikin kyakkyawan hali da d'abi'a, wanda ya rasa su, komai kyawun huska shi mummuna ne, ina goyon bayan auren ku, dubu bisa dubu ma Sultan, Mubaraka ita ce ta hi dacewa da rayuwar mu baki daya,Allah shi yi muku albarka"

Hannun Hajiya Ikee Sultan ya riqe a nashi gam gam, sannan ya sumbace su, cike da murna, ya dinga godiya,a haka su Sultana suka tadda su, Mubaraka kuwa tun da ta ji Hajiya na yabon ta taso guduwa, amma Sultana ta riqe ta, sai da suka gama, magana sannan Sultanan tai gyaran murya, ta ce,

"Mu shigo an bamu izini? Kar ku ce mun yi maku labe, mun ji shiru ne shi na mun ka taho mu ji ko lahiya?"

"Ku shigo, 'yan sa ido, kun dai taho ku ji mi muka fadi, to kun dai jiya, Hajiya ta amince na auri B love di na"

"Tauuuu mi na na kuma B love?"

"Sultana ba kyau sa ido, ba ruwan ki, ni kadai na san me na ke nufi da hakan,kalla yadda Mubaraka kanta ta baza kunne ta na so ta ji ma'anar B love, ban fad'i to, yarinya rufe kunnuwan,"

Cikin jin kunya ta sa hannayen ta ta rufe fuskar ta, tabbas kuwa ta tsaya ne ta ji me ye ma'anar B love din, kuma ya gano ta.

Juyawa ta yi da sauri za ta fita ta ji ya kira sunan ta, da wata iriyar Muryar da ta sanya ta tsayawa cak ba tare da ta shirya ba, daga Hajiya har Sultana ba wanda ya qara magana, dan su ma za su so jin me Sultan zai fadi da mahimmanci haka, har da sauya murya.

Takawa ya yi zuwa gaban ta, ya tsaya, kallon idon ta yake so ya yi amma ta maida kan ta qasa, kunyar Hajiya take ji, amma ta kula su ba ruwan su,

"Kalle ni Mubaraka,"

Da kyar ta d'aga kai ta kalle shi, idanun su na haduwa da na juna, ta ji kamar an kafe nata, kasa kauda kan ta tayi daga barin kallon shi,

"Mubaraka za ki aure ni? Za ki taimake ni ki tausaya wa Maraya Sultan ki aure shi? Ki sani ba ni da dukiya, ba ni da aikin yi, amma ina tare da dimbin soyayyar ki, wadda na ke jin ta ishe ni qarfin guiwar zama komai da na ke so na zama a rayuwa, da izinin Allah, so Mubaraka za ki aure ni?"

Wasu irin hawayen farin ciki ke mata gudu a kunci sai qaiqayi suke mata, gashi ta kasa daga hannu ta sosa kuncin nata, jikin ta ya mace murus, yau wai ita namiji had'add'e kamar Sultan ke neman aure ta wannan sigar? A gaban mahaifiyar shi, da qanwar shi, ita d'in wace ce? D'iyar tallaka, qanwar tallaka,sannan ita kan ta bata mallaki komai ba, ita ba wani kyau na a zo a taru a sha kallo ba, Sultan ya fita komai, kyawun shi ma abin kallo ne, kyawun shi ma kyakkyawa ne, ga kyawun hali, da d'abi'a, anya bai fi qarfin ta ba, ta sani ba wani namiji da take wa so irin na soyayya bayan shi, amma a yau sai ta ji gaba daya bata cancanci zama matar shi ba.

Cikin murya mai cike da rawa, ta ce,

"Yah Sultan ka dai san kai ba sa'an aure na bane ko? Ka hi ni komi da komi a rayuwa, ba...."

Sultana ce ta katse ta, ta hanyar sanya hannu ta share mata hawayen ta, sannan ta ɗan ja kumatun ta, ta ce,

"Kar na ji kalmar rejection ta fito a bakin ki, zan qi komawa gidan Yayan ki, Hajiya mu basu waje, wataqila kunyar ki taka ji, ke ko kin zauna dirshan ki na kallon su awa ke samu TV"

Dariya sosai Sultan da Mubaraka suke, Mubaraka na dariya hawaye na qara saukar mata, yau rana ce mai cike da farin ciki a wajen ta, ina ma ace Yah Auwal na nan, yaji yanda Namiji kamar Sultan ke bayyana mata ra'ayin shi akan ta.

Bayan fitar su Hajiya Sultan ya sake roqon Mubaraka, akan ta amince da auren shi, dan tura baki ta yi, cikin shagwaba ta ce,

"Ni dai ka dena roqo na haka, dan kuwa ba ni da wani abun baka,mutum guda na zai iya baka amsa, shin zan iya auren ka ko ban iya wa,"

"Ni dai dan Allah kar ki had'a ni da Auwal"

Cike da dariya Mubaraka ta ce,

"Ashe ma ba ka so ka aure ni, wajen shi za ka je wallah, in yace shi na baka niii, to zan aure ka, in yace ba zai..."

"Ya isa haka nan, zan je wajen shi,kuma na tabbata, in da zan je da sadaki na a lokacin zai aura maki ni, "

"Me zai hana ka tai da sadakin gaba ɗaya, domin na mallake ka a matsayin miji na cikin gaggawa"

Yanayin yanda ta yi maganar ya kawar masa da komai, na tunanin ko dai bata yi da shi,zuciya bata da qashi, dan har ya fara tunanin ko Taheer take so, sai ya ji kalamai masu ɗauke da gaskiyar abinda ke zuciyar ta.

Cikin jin kunya ta bar dakin nashi, shi kuma ya bi ta har bakin qofa ya na murmushi, har ta sauka qasa gaba daya bai bar wajen ba, ya na nan tsaye ya na murmishi.

Sultan kuwa bai bata lokaci ba, da daddare ya sha wankan shi, da manyan kaya, ya nufi gidan Lawwali, ya tarar da shi ya na waya da Sultana, sallama ya mata, ya ce zai sake kira ya yi baqo.

Sai da suka gaisa, Lawwali ya sake yi masa ta'aziyya, sannan Sultan ya kalli gidan, ya ga yanda Lawwali ya qayata shi, ya gyara shi, kamar gidan sabuwar amarya.

"Lallai ka na ji da matar ga taka, irin wanga gyara kamar za a kawo maka sabuwar amarya? "

"Ka gyara kalaman ka, dan kuwa Sultana sunan ta kin fi amarya"

Sultan kuwa langwabe kai ya yi, ya yi kalar tausayi, sanan ya ce,

"Allah Sarki,mu gamu mu na son a bamu tamu amaryar amma ba wanda ya damu da halin da muke ciki, har yanzu an kasa gane mun isa aure, a aurar da mu, sai mun aje kunya a gehe mun roqa a muna aure"

Lawwali me zai yi in ba dariya ba, shi ma Sultan d'in dariya ya dinga yi, cikin dariya Lawwali ya ce,

"Yanzu dai ka ce aure ku ke so, kuma maganar neman aure ta kawo ka ko?"

Gyara zama Sultan ya yi ya ce,

"Gaskiyar kenan, ni na rasa iyakar son da Mubaraka ke yi ma, wai na yi na yi ta amsa min buqatar auren ta da na je mata da shi,ta ce sam sai ka amince"

Murmushin jin dadi Lawwali ya yi, sannan ya ce,

"Indai ni ne na amince, na baka goyon baya ka ci gaba da saye zuciyar qauna ta, har sai ta amince ba wani namiji sama da kai a rayuwar ta,"

"Tabdijam, ka dai ce ba wani namiji da zata so da aure sama da ni, amma har duniya ta tashi kaine namijin farko kuma na qarshe da take so, na gode sosai da amincewar ka"

Nan dai suka yi ta hira, Lawwali na bashi labarai akan Mubaraka, abinda take so da wanda bata so, har qaddarar da ta fad'a mata tsakanin ta da No 1,Sultan ya tabbatar masa da cewa, ba namijin da ya dace ya auri Mubaraka sama da shi, ta sanadin Daddyn su haka ta faru, dan haka shi ke da alhakin auren ta, ko da ace ma ba ta sanadin Daddyn su bane, shi dai ya ji ya kuma gani ya na son ta a duk yanda take, ita yake so ba jikin ta ba,shi ma Sultan haka ya dinga fadawa Lawwali abubuwa akan sultana, daga qarshe Lawwali ya kira Mubaraka, ya fada mata amincewar shi, cikin jin kunya ta yi masa godiya.

Lawwali ya bawa Sultan shawara, akan ya tura magabatan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login