Showing 144001 words to 147000 words out of 155423 words

Chapter 49 - A GARIN MU Book Compelet BY HAERMEEBRAERH.docx

17 Oct 2025

290

shi wajen Baban su, a da ya so shi zai aurar da ita da kan shi,amma ganin mahaifin su na nan da rai, kuma shiriya ta zo masa, ya yi nazari shi ya fi cancanta da ya aurar da diyar shi, sai dai in ya wakilta shi,zai so hakan.

Sallama Sultan ya yi wa Lawwali ya tafi gida.

Ko da ya isa duk sun yi bacci, abinci ya ci, ya je ya kwanta shima, cike da tunanin yanda zai mallaki  masoyiyar shi Mubaraka.

*************************

Su Yayah Musah sun sha wahala kwarai kafin Isah ya hakura ya rubuta wa Hansatu saki,dan sai da suka had'a da barazanar za su had'a shi da hukumar qasar, a sanar da duk abinda ya aikata wa matar shi, ya tsorata kwarai dan ya san bai aikata daidai ba,gashi Saudiya ba sa wasa da jinkiri wajen yanke hukunci, Isah na kuka har da majina, ya rubuta wa Hansatu saki d'aya.

A satin suka juyo gida Nigeria Yayah Abdullah murna a qasan ran shi kamar me, amma a fuska ya dinga jimamin lamarin, ya na jaddada rashin adalcin da Isah ya aikata wa Hansatu.

Ko da suka iso gida, Hajiya ta yi farin ciki da samun nasarar raba Hansatun ta da azzalumi Isah, Hansatu kuwa yaqe ta dinga yi, ko ba komai akwai sabo, kuma shi ne uban yaran ta.

Da dare sai da ta ci kuka ta godewa Allah, ta na tsaka da kukan ne ta ga wayar ta ta yi haske, ko da ta duba sai ta ga baquwar lamba, sallama ne kawai sai gaisuwa, da jajanta mata abinda ya faru da ita, mamaki ne ya kama ta, bayan ita da mutan gidan su wa ya san meke faruwa da ita? Lallai lamarin duniyar nan abun tsoro ne labari har ya baza gari.

Ba tare da ta amsa gaisuwar ba ta ajiye wayar, koma waye, ta ji da safe, yanzu dare ya yi.

Tunda Isah ya sawwake wa Hansatu auren wahalar da ta ke fuskanta, duk ta rame, ta zama wata kamar mara lafiya, a so samun ta, ya gyara halayen shi, su ci gaba da zama hakan, sai dai kashhh sanin abubuwan da ya aikata sun ja mishi rabuwa da ita, ba dan an ce sabo turken wawa ba ma, da ko tunanin shi ba zata yi ba, amma ta saba da shi, da halayyar shi, da kuma son shi, su ke wahalar da ita, kafin ta saba da rashin shi zata dau lokaci, wanda bata fatan hakan.

************************

Yau Mubaraka ke so ta koma gidan su, Sultana da Sultan sai lallaba ta suke akan ta yi zaman ta,ta qi sam,ta ce ya kamata taje  ta ga halin da iyayen ta ke ciki, mussamman tunda ta jima ba ta gidan .

Hajiya Ikee ta yi ta mata godiya, da za ta tafi ta rasa me zata bawa Mubaraka, Mubaraka ta fahimci hakan, dan haka ta cewa Hajiya,ta sa mata albarka kawai, ya ishe ta, shi ne babban kyautar da ta ke so ta mata, albarka kuwa Hajiya ta saka mata, suka raka ta har bakin gate, Lawwali na mota ya na jiran ta.

Su na had'a ido da Sultana ya marairaice fuska, shi adole ya na so ta tausaya masa ta koma haka, ba ya so ya furta, tunda ta yi babban rashi, ba zai so a ga rashin hakurin shi ba, bayan Mubaraka ta shiga Mota ne, Hajiya Ikee ta ce,

"Allah shi kiyaye, muna godiya,kwarai kwarai, Allah shi yi muku albarka, Auwal in ka kai ta gida, ka biyo ka dauki matar ka ku wuce haka nan, Allah shi bada lada, Allah ya jiqan Daddyn su, rashi dai an riga an yi shi, ba a zauna ba ba tare da an koma zaman aure ba, zaman ya isa haka nan, gani ga Sultan babu komi, da ka Kaita ka dawo ku tahi"

"Ni fa ba yanzu zan koma ba"

Da sauri Lawwali da ke ta murna ya kalle ta, cike da mamakin yanda ta ke qin komawa qarfi da yaji, ga mamakin shi kuwa sai ya ga su na ta mishi dariya, dama wasa ta ke,

"Auuuu zolaya ta ki ke ko? Ke dau bashi wallah"

Jan motar shi ya yi, ya bar su nan tsaye su na mi shi dariya, Mubaraka ma dariya take.

Kamar yanda Hajiya ta alqawarta kuwa, haka ya je da dare ya dauki Sultana, wadda ta sha gayu kamar amaryar da za a kai dakin miji, sai qamshi take zubawa, ta yi haske,ta ciko sosai, har Lawwali na mamakin qibar da ta yi, ita da take cikin jimamin rashin mahaifin ta.

Sultana kuwa ta matsu su je gida ta masa babban albishir.

Ko da suka isa gidan,ta yi matuqar farin cikin ganin yanda ya gyara gidan sosai,kamar baquwa haka ya dinga shiga da ita sashe sashe na gidan,ta na gani.

A dakin su suka tsaya, ta na tsaye ta na kalle kalle ya dauke ta, qara ta saki saboda matse mata ciki da ya yi, da sauri ya ajiye ta, cike da shagwaba ta kai masa dukan wasa a qirji, ya tare hannun ta, ya na bata hakuri,

"Ko dake ni za ki bawa hankuri, kin ji baya na, awa zai qalle, ke yi nauyi yanzu mi ki ke ci ne haka?"

"Ba dole na yi nauyi ba, tunda ka min babbar ajiya,"

Cikin rashin fahimta ya ce,

"Shin ajiyar mi na yi maki kamar wani maye? "

Ta na wani irin kyakkyawan murmushi ta kama hannun shi ta ɗora a saman cikin ta, ta na shafawa, tare da cizon leben bakin ta na qasa,

"Ga ajiyar nan, ita ta ke sani cin abinci sosai, har na yi qiba,"

Lawwali wata iriyar zabura ya yi, ya yi baya, ya na toshe bakin shi da hannayen shi dika biyun, murna ce sosai da bata iya boyuwa a saman fuskar shi, Ita kuwa bin shi ta yi ta fada jikin shi,ya kuwa rungume ta ya na sumbatar ta ko ta ina, su nata dariya, a hankali ya kai bakin shi kunnen ta ya ce,

"Na gode Sultyna, Allah shi yi miki albarka, da ke da abinda ke cikin ki, Allah ya sauke ki lahiya, ya bani ikon kula da ku, Allah ya raya mana Muhammad, in mace ce kuwa Ayshaa nika so a sanya mata"

"Ameen ya Allah miji na, kuma uban yara na,Sunan mahaifan ka ne?"

Kama ta yayi, suka zauna a bakin gadon su, ya ci gaba da shafa cikin nata, da in ba an fadi ta na dauke da ciki ba ma, ba mai ganewa,

"Ahh Ahh, ina son sunan Muhammad ne saboda ina fatan Allah ya sa ya yi koyi da Annabi Muhammad, in mace ta kuwa, ina so ta yi koyi da Nana A'ishah, domin kuwa yanzu ba ni da abin kalla in na zauna ni kadai ga YouTube sai wa'azi , da duk wani abu da nissan zai amfane ni, anan na ke jin tarihin su,"

Sultana ta ji dadi matuqa,cikin murmushin da ta kula ya qi barin fuskar shi tun da ya fara maganar Annabin rahama, ta fara kissing din shi, sannan ta ce,

"Ya kamata na baka tukuicin amfani da lokacin ka akan abinda ya dace"

Juya ta ya yi, ya kwanta a saman ta, ya na kallon cikin idon ta, fuskar su dauke da fara'a ya ce,

"Ya kamata na baki tukuicin kular min da ajiyar da na baki, sannan ki karbi hukuncin qin sanar da ni da wuri da baki yi ba"

Cizo ya kai mata a wuya, na wasa,daga nan na ga ya fara......sai na gudu, saboda an hana ni sa ayis a gidan mutane.....

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻

BY HAERMEEBRAERH

PAGE 63

A rumfar Dan Talo ya tsaida motar shi, Lawwali har qasa ya durqusa ya gaida mahaifin shi,cikin jin nauyin haka Dan Talo ya amsa, dan bai saba ba, shi kan shi Lawwalin be saba ba, ganin Mubaraka na yi ne ko da yaushe, ya sanya shi yi a yau.

Abokan Dan Talo da ke zaune a rumfar sai mamaki suke, daya bayan daya suka dinga zamewa su na barin wajen,hira suka dan tab'a, Lawwali na tambayar shi yanayin kasuwancin,

"Kassuwa dai gata mun godewa Allah, tafi zaman banza, ka ga ana samun na cefane,ga kuma hirar dai ana yi, abukkai na na zuwa kullum muna hirar mu, "

"Da kyau, Allah shi taimaka, ai dama shi rai dangin goro ne,ya na bidar damshi,"

"Haka nan na, ka ga ban samu na koma gidan rasuwar nan ba gashi har an yi arba'in,Allah shi jiqan gwamna"

"Ameen, ai ba komi,ga Barakana nan, ta je, ta zauna musu, ai ta wakilce mu dika,barakana shiga gida,gani nan zuwa"

Amsawa ta yi da "to" sannan ta shige ta bar su, anan Lawwali ke sanar da Dan Talo abinda ke faruwa tsakanin Mubaraka da Sultan, ya yi farin ciki sosai, sannan ya amince Lawwali ya zama waliyyin ta, Lawwali ya yi ta godiya dan kuwa dama yana son hakan.

"Amma fa nan za su zo, tambaya, dan zan so koma me za a yi ya zama an yi shi a nan gidan, nan ne tushen mu, da nan muke taqama,"

Dan Talo wani irin abu ya ji mai sanyi na kwaranya a zuciyar shi,ba ilimin addini, balle ya godewa Allah akan ni'imar da ya mishi, haka dai ya ke ta jin daɗin shi, a zuciyar shi, har suka gama magana Lawwali ya shiga ciki.

Ya tarar da Matar Yahai na ta bada labarin abinda ya faru da mijin Asshibi da Hansatu, sai zaqewa take da qarin gishiri, su na hada ido da Lawwali wai ita wayayyiya, a dole ba ta tsoron shi, ta ce,

"Ango ka sha qamshi"

Daga mata hannu ya yi, sannan ya ce,

"Sannu, sannu uwar gulai uwar munahurci, watakam waccan qandarabushe munahikar lungun ta dena zuwa, ke kin karbe ta ko? To ki kiyaye zuwa gidan ga ki na kawo gulmar mutanen unguwa, nan nan na wuce ta qofar gidan Malam Zakari, mata na ta zuwa makarantar Allah (islamiyya), su na daukan karatun da zai amfane su duniya da lahira, ke ki na nan ki na baza gulma,to daga yau na fada Maki, in ba alheri na zai kawo ki gidan ga ba, kar ki koma zuwa"

A yau ta hango abinda Yabbuga ke tsoro a idanun Lawwali, wani irin tsoro da nauyin shi ta ji ya baibaye ta, yaqen ma kasa shi ta yi,sai nishi take fiddawa,wanda ya sanya Mai Buruji dariya, ta rasa me ya sa in Lawwali ya ritsa matan unguwar su ke shiga tashin hankali haka, cikin zuciyar ta tace,

'Na raba ki da mutane irin su Lawwali Mai Buruji, bar ganin ya shiryu, yanzu zai juye ya tuna da,ku din ma ai tsoron shi kuke'

Kama bakin ta tayi dan kar dariyar ta ta fita fili, saboda hada ido da suka yi da Ta Yahai, idanun ta sun yi qanana qanana, sai zufar kan hanci ke tsattsafo mata, munafurci be ba a rayuwa .

Lawwali bayan ya gama wanke Ta Yahai, ya gaishe da iyayen shi, ya wa Mubaraka Sallama ya tafi gidan shi.

Bayan fitar shi ne Lamishi ta juya dan yi wa Ta Yahai magana ta ga wayam, Mai Buruji da dariya ta suqe ta har ta na zama a kujera,ta ce,

"Ai ya juya ku na gaisawa ta sa kai ta hice, ke ga idanun Ta Yahai? Ita da ka wa Yabbuga dariya akan tsoron Lawwali ita ma yau ta shiga layi,"

"Ke dai Allah shi yi miki sauqi, mi ne ne abun dariya to anan?"

"Yaya ke ma hwa dariyar ki ke,ke wallah zaman gida ya hi dadi akan shegen zaman gulmar nan da mu ke, haba, mi za ai da gulma da tsintse?"

"Walle kau, ke gani dai hankali kwance ba ruwan mu da damben unguwa, walle in ba qarya zan yi ba, har wani dan fari na ga muna yi,...ke wagga ke dawo ba mu ko gaisa ba, ya su Hajiya ?"

Mubaraka da ke ta gaishe su suna hira ce ta sake gyara zaman ta a tabarma ta ce,

"Su na lahiya, yau ma Hajiya tace Aunty sultana ta shirya, in Yah Auwal yamaishe ni gidaa ya bi ya dauki mata tai, ai dai an qare zaman makoki"

"Ai ko ta kyauta wallah, Allah dai shi jiqan gwamna,"

"Ameen, shin Umma da gaske ne abinda ya faru da Aunty Hansatun Isah?"

"Humm haka dai labari ke ta yawo, yanzu haka shi Laminu an yanke mai hakuncin zaman gidan maza shi na can, Asshibi kuwa ta murje ido, ta toshe kunne da tsintsen mutanen shiyya, tunda bata san mi ya ka aikatawa ba, shi da kan shi ya wanke ta,ita ko Hansatu an ce uwatta ce ta tafi har can qasa mai tsalki ta amso mata takardar saki (kun ji yanda mutane kan juya zance komai qanqantar shi ko? Su Yaya Musa ne suka amso takardar saki, amma an ce Hajiya ce, duk yanda labari yake mutanen duniya sai sun juya shi, shi ya sa dole ne mu godewa Sahabbai da duk wadan da suka yi sanadin hade mana Alqur'ani da hadisai har suka riske mu lafiya ba dad'i ba ragi, Allah ya yarda da su, ya shirya masu qirqirar hadisan qarya, da labaran qarya)"

"Ohhhh Allah shi kyauta, amma Ni Ko Umma ba dan kar a ce na ce ba, da sai in ce na wa Aunty Hansatu murnar rabuwa da Isah, mutumin nan azzalumi na wallah, Allah shi bata mafi alkhairi"

"Ameen ke dai diyar ga"

"Umma akwai tuwo? Na yi kewar cin abincin ki"

"Akwai, bari na debo miki, Allah ya yi da rabon ki, kahin su Jameelu su tai wajen koyon dunki da Yayan ku yassa su, sai da sun ka kusan canyewa suka bar kingi"

"Masha Allah, ashe sun sara zuwa, ya fadi min kuwa zai saka su, amma ban san sun fara zuwa ba, bana dinkin mu ba zai kwantai ba ashe, Allah ya taimaka"

"Ameeen ya Allah"

Mubaraka na zaune Lamishi ta kawo mata tuwon ta kuwa zauna ta gyare shi, dan kuwa Lamishi ba dai iya girki ba.

***************************

Wata biyar kenan da kai kayan lefe, da duk wani abu da ake kai wa na bidi'ar aure,na Mubaraka, duk da cewa Lawwali ya ce a taqaita bidi'a amma still kaya sun qayatar da kowa, ranar aure kuma na ta qaratowa, dan kuwa bai fi saura sati Uku ba.

Amarya Mubaraka ta ga gata wajen Iyayen ta biyu, wato Mai Buruji, da Lamishi, sai kuma qawar amana wato Mama 'Yabbuga kamar yanda Mubaraka ke kiran ta, duk wani sabani ya kau, an shirya, an dinke, Ta Yahai ma ba a barta a baya ba, wajen hidimar biki.

Yanzu matan unguwar sun hade kan su, duk da in gulmar su 'Yabbuga ta motsa sai sun tab'a amma an samu sassauci, mutane sun fahimci abun ya zame musu kamar wani ciwo ne, (Allah ka raba mu da ciwon gulma da munafurci).

Ango kuwa na can na hidimar biki, a bangare daya kuma ya na ta zuwa neman aiki, duk da gwamnati mai ci ta ce za ta taimaka masa, a matsayin shi na dan tsohon gwamna,amma shiru ka ke ji, ba wanda ya kira shi.

Ya aika takardun shi ko ta ina dan neman aiki, kuma ya na saka ran albarkacin addu'ar da yake, da kuma tawassuli da kyawawan ayyukan da ya ke a rayuwar shi, Allah ba zai bari su wulaqanta ba, shi da mahaifiyar shi, da qanwar shi.

Cikin ikon Allah kuwa ana sauran sati biyu auren shi, ya samu aiki, aikin da bai taba zaton samu ba kuwa, nan da nan kuwa ya bugawa Hajiya Ikee waya ya sanar da ita, murna ta dinga yi da sanya albarka, suna gama waya da Hajiya ya kira Mubaraka, ya na murna ya sanar da ita, sujjada ta yi ta godewa Allah, kafin daga baya ta dau wayar ta yi ta zuba masa addu'a ta kariya daga dukkan abun qi, da nema masa alkhairi da albarkar da aikin ke tattare da shi .

*************************

Cikin Sultana na da watanni bakwai cif cif yanzu, Hajiya Ikee kan ce bata taɓa ganin wadda ciki ya yi wa kyau ba sama da Sultanan ta, Ita kuwa sultana kan ce son kai ne kawai, amma akwai wanda suka fi ta kyau.

Lawwali ya gama aika sauran 'yan kudaden shi Kano, ya na so kafin ya isa Taheer ya buda masa shago ko qarami ne,Taheer kuwa ya dage sai dai Lawwali ya amshi babban shagon shi, shi ya nemi qarami ya ci gaba da kasuwancin,tun Lawwali na ahh ahh ahh, sai da Taheer ya ja ran Oga ya kai ga ɓaci har ya bada umarni, sannan ya dena jayayya da Lawwalin.

Sun gama tsara bayan bikin Mubaraka, za su dunguma gaba daya shi da Taheer su tafi Kano din.

************************

Lawwali na matuqar bawa Sultana kulawa, kulawar da duk wani miji na gari, kuma uba na gari ya kamata ya bawa matar shi, musamman ma mai juna biyu, har Sultana na mamakin inda ya san yanda ake kula da mace mai juna.

Ta na bincike a wayar shi ta gano, internet yake shiga ya yi ta research akan yanda zai kula da ita.

Yau ma kamar kullum, ta na zaune ta ce da shi, Ita dai so take ta ci qosai, irin wanda ake saidawa a bakin hanya din nan, akwai wata mata akan hanyar shiga unguwar Tudun faila, ta na qosan to ita ta tuna, shi ne take ta rikici ita qosai take so, gashi bai jima da dawowa daga unguwar ba, ba ya so ya koma, amma haka ya hakura ya shirya, ya fita.

A bakin titin fita daga Unguwar su ne ya ga wannan tsohuwar da yanzu kusan kullum sai ya gan ta, dunqule a waje daya, da kwanon barar ta a gaban ta, matsawa ya yi da motar shi, ya aje mata 1k a kwanon ya yi gaba, ya tabbata duk yanda akai, matsafan unguwar ba irin ta suke so ba, shi ya sa har yanzu take

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login