Showing 117001 words to 120000 words out of 155423 words
Chapter 40 - A GARIN MU Book Compelet BY HAERMEEBRAERH.docx
ya iya irin wannan soyayyar bai sani ba.
Sultana kuwa tun ta na kukan hana ta magana da mahaifiyar ta da ya yi, har sai da ta manta kowa da komai, jin ta kawai take a duniyar da Lawwali ya kai ta, mai cike da ni'ima da nishad'i, mai cike da gamsar wa, duk wata nutsuwar da ke tattare da ita ta kwace, ba abinda take gani a idanun ta, sai Auwal din ta, ta na tsaka da amsar saqon salon soyayyar shi mai wuyar fassara ta ji ya na qoqarin cimma burin shi, da sauri ta bude ido, dan kuwa bata gama warkewa ba, kyabe baki ta yi, irin na shagwabar nan, Lawwali ya kalle ta da rinannun idanun shi, da alamar tambaya, sauke idanun ta tayi, ta kalli qasa, ta na wasa da qirjin shi ta ce,
"Da zafi fa, ban warke ba"
Da sauri ya d'aga ta, ya na nuna nadamar abinda yake son aikatawa, ganin hakan da ya yi, sai ya bawa Sultana dariya, hancin shi ta ɗan ja kad'an tare da kai wa lips din shi kiss sau daya ta ce,
"You are so cute,"
Murmushi ya yi sannan ya ce,
"Sannu Sultana, ki yafe min, ban San zaki ji ciwo ba, ko za mu tai gari ki ga likita?"
Kwantar da kan ta tayi a qirjin shi, a ran ta ta na ayyana, da ta san inda aka kwantar da mahaifin ta da sun je asibitin ko daga nesa ne ta hango shi, hawaye ne taji su na zuba a idanun ta, da sauri ta sa hannu za ta goge, lawwali ya riga ta, cikin murya mai sanyi ya ke magana,
"Sultyna ki dena kukan ga, ya na karyar min da zuciya, na ji kamar na faasa abinda na ke da niyya, ke dai san quduri na da yasa na ke abinda nake a yanzu, ki bani goyon baya komi zai wuce,in shaa Allahu"
"Allah ya yarda, ina son ka miji na"
Wani irin dad'i ne ya lullube Lawwali, kalmar da ba wanda ya taba furta masa bayan qanwar shi sai Kuma ita, amma a bakin Mubaraka kad'ai ya fara jin wannan kalma, se ga shi ya samu matar dake yawan furta masa, yi ya yi kamar bai ji ba ya ɗan had'e gira ya ce,
"Na'am mi ki ka ce??"
Murmushi tayi dan ta gane me yake nufi, so yake ta maimaita masa, tashi tayi ta haye jikin shi, ta kwantar da shi a saman gadon sosai, ta yanda suke fuskantar junan su, sai da ta sumbace shi sosai sannan ta kalli kwayar idon shi ta ce,
"Cewa nayi....ina son hancin ka, da idon ka, da nan wajen..(ta nuna lips din shi) ina son kowacce gaba da ke jikin ka...ina son ka, ko da ace ni makauniya ce, kuma kurma ce, sannan bebiya ce, zan qirqiri kowacce hanya ce dan sanar da kai ni Sultana ina son ka Auwal, ba zan taba dena son ka a raina ba, har sai sanda na dena numfashi a duniya, ina maka son da ban taba yi wa wani ba, kai ne na farko a cikin zuciya ta, kuma kai ne na qarshe"
Wani irin numfashi mai sauti Lawwali ke saukewa ya rasa kalar dad'in da Sultana ke sanya shi ji a wanan lokaci, rungume ta ya yi sosai a jikin shi, har sai da ta saki wata siririyar qara, sannan ya sake ta ya na murmushi.
"Yi hankuri Sultyna, ji nikai kamar na bude fata da tsokar jiki na, na balle qashin da ya yi wa zuciya ta rumfa na ajiye ki a can ciki ki zauna daram, saboda yanda nake jin...."
Shiru ya yi bai furta ba, a hankali ta daga kan ta, cikin wani kallo mai kashe jiki, ta na lasar leben ta na qasa ta ce,
"Me ka ke ji?"
"Ina jin son ki Sultana, ina jin qaunar ki sultana, ba na son rabuwa da ke har bayan mutuwa ta, amma na san zai wahala mu had'u, saboda kowa makomar shi d...."
Ba tare data shirya ba ta ji saukar wasu hawaye Masu zafi, a kuncin ta, dan kuwa ta fuskanci me yake so ya fada,
"Subhanallahi, haba haba Auwal, ka dena kalar wannan tunanin, rahamar Allah mai yalwa ce, Allah ba so ya ke ya sanya bayin shi a wuta ba, Allah so yake bayin shi masu zunubi su tuba domin ya yafe musu, ya lullube su da rahamar shi komai laifin su, wanda ma ya yi shirka ga Allah in ya tuba kan ya mutu Allah na yafe masa ballantana kai, da baka taba duqawa gaban boka ko malam ba, sannan baka sani ba, ni din da ka ke wa kallon zan shiga aljannah wataqila Allah ya sanya ka a aljannah din mu zauna tare saboda ni din, sannan Allah zai iya jarabta ta da wani abun, ni kuma na yi wasa da shi na aikata zunubin da zai kai ni wuta, hadisi ne fa guda, akwai mutanen da za su yi ta aikata ayyuka irin na 'yan aljannah, saura kad' an su shiga aljannar, amma se su aikata aiki irin na 'yan wuta, se Allah ya sanya su a wutar, sannan akwai mutanen da za su yi ta aiki irin na' yan wuta, sauran kad'an su shiga wutar se kawai su yi aiki irin na 'yan aljannah, sai Allah ya kare su ya sanya su a aljannah, ka gani? Allah ba ta inda baya wanzar da rahama da ikon shi"
"Sultana ban taba shirka ba, amma ina taimaka wa masu yi, duk abinda mahaifin ki ya buqata da sauran 'Yan siyasa a baya ko mene shi ina samar musu shi, duk da na san tsafi za a yi da abun"
Hawayen ta ne suka qaru, jin cewar har da mahaifin ta a aikata shirka,
"Ka yi istigfar Allah zai amsa, ka yi da kyayyawar niya, Allah zai yafe maka"
"Allah na tuba ka yahe min, Allah ka yahe min manya da qananan zunubbai na, Allah ka yi min rahama, ka cika min buri na,"
"Ameen,"
Kafin bacci ya ɗebe su, sun tattauna akan abubuwa da dama, sun kuma tsara duk wani abu da ya kamata su aikata a gaba, a haka bacci ya dauke su suna manne da junan su.
***************************
Kamar yanda Isah ya yi alqawari, ya siyi goro mai yawan gaske, dan tafiya Makka, wanan karon dubu hamsin casss ya cake wa Hansatu, amma bata ci su a banza ba, sai da ya mori jikin ta da kyau da kyau, dan duk girman ta, da jarumtar ta, sai da ta dinga shiga ruwan zafi, Ita dai ta sawa ran ta, ba zai sake ganin wani rawar kan son shi awajen ta ba, tunda ta yi a baya bai mata amfani ba, sannan ba zai sake ganin murmushin ta ba, tunda a baya sai da ta ce wa audiga bata iya murmushi ba,ta fita iyawa, duk bata samu ribar murmushin ba,hakan kuwa na matuqar damun Isah, kula da cewar ko sau nawa zai neme ta ba zata qi ba,shi ya sa ya ke fanshe haushin rashin sakewar a jikin ta.
Hajiyar Hansatu da Yaya Musa sun yi qoqari sosai wajen ba Isah wasu kudin da zai qara akan jarin shi, sai da ya musu sallama sannan aka bada mota kamar wancan karon aka kai shi airport, wannan karon ko kwalla Hansatu bata yi ba, balle ta koka, Isah kuwa ya ji haushi matuqa, sannan ta ce ba zata yi rakiya ba, a fusace ya fad'a mota, aka tafi kai shi,ko da takoma sai ta ce wa Hajiya ita bata so ta ga ya tafi ya barta, kuka za tai, kuma bata so ta daga masa hankali,dan haka Hajiya bata ce komai ba, sai suka ci gaba da hirar su.
Isah sun isa airport, ya sauke kayan shi da komai, cikin dabarar da suke yi kar a gane goro ne, ya na tsaye wani mutum fari ya tsaya gefen shi, sallama ya masa shi ma ya amsa, sai ya ji maganar kamar ta Inyamuri ko bayerabe,
Mutumin ya fara yi wa Isah magana da turanci, Isah ba turanci, fuska ta muzanta da kunya, sai bawan Allahn ya gane Isah fa wala ingilishi, cikin gurbatacciyar Hausar shi ya ke tambayar Isah, Makka zai je ko Madina in sun isa Saudiya?
"Makka zani"
"Masha Allah, ni ma can nake da zama, ina da gida da iyali a can, kai fa ina ka ke zama?"
"Ni a hotel kawai nake sauka, banda gidan zama,"
"Allah Sarki, ka fad'a min inda ka ke sauka in na samu natsuwa zan neme ka, se ka dawo gida na da zama, tunda duk qasar mu d'aya, in a foreign land in ka ga d'an qasar ku ji ka ke kamar d'an uwanka ne"
Sunan hotel din da yake sauka ya sanar da bawan Allahn nan ya na ta murna, a qalla ba shi ba biyan kudin hotel, zama suka yi tare, suna ta hira, kamar abokan juna, duk inda CCTV camera yake a wajen bawan Allahn nan ya sani, kuma daidai gwargwado juya bayan shi yake, ba ya bari fuskar shi ta hasku, ya yi shiga irin ta larabawa ya saka face mask, se surutu yake wa Isah da gurbatacciyar hausar shi, Isah kuwa banda washe baki ba abinda yake.
Sai da aka shiga jirgi ne suka rabu, saboda wajen zaman su ba daya bane.
Tafiya ta miqa zuwa Saudiya, Isah ba abinda ya ke banda tunanin Hansatu, wannan karon ji yake kamar ya bar wani bangare na jikin shi, qudirtawa ya yi in Allah ya sauke shi lafiya, ita zai fara kira su gaisa.
**********************
A hanyar su ta zuwa garin na Zamfara duk wani motsi na Mubaraka na kan idon Taheer, zuciyar shi kuwa na ta kakkaryewa zuwa qananan pieces ,ya yi zurfi akan son ta ba tare da ya sani ba, wataqila dalilin gano ya na son nata, rabuwar da ta zo musu ba tare da shiri bane, da ya kula ya na son ta tun da, da ya yad'a manufar shi a wajen ta, gashi yanzu lokaci ya qure masa.
Mubaraka ce ta yi qarfin halin yi masa magana, ta ce,
"Yah Taheer akwai damuwa ne?"
Da sauri ya sanya murmushin yaqe ya ci gaba da tuqi, bai ce komai ba, tafiya suke kamar ba zai magana ba, can kamar wanda aka shaqe ya ce,
"Yanzu in kin tafi shikenan? Mantawa zakiyi da mu ko? Ga yaran ki can kin bar su suna ta kuka, ke kad'ai ka lallashin su in su na rikici, sun hi sabawa da ke,gashi zaki tafi ki bar su"
"Yah Taheer ku din wani bangare ne mai girma a rayuwa ta, ba zan taba manta wa da ku ba, ka sani na jima ban ga yayana ba, ina kewar shi sosai, amma in na je na gan su, ai zan koma wajen ku, in Allah ya yarda"
Wani irin murmushi Taheer ya sake, har da sosa kai, murmushin shi ya bawa Mubaraka mamaki, sai ita ma ta fara murmushin, cikin daurewar kai, dan ta kasa fahimtar inda Yah Taheer din ya dosa da wannan bayyanannen farin cikin................
*Allah kai ku lahiya ke dai, mu ai mun gane murmishin meye😂😂*
💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻
BY HAERMEEBRAERH
PAGE 53:
Jefi jefi suke hirar su, cikin nishadi, da kuma sabo, Taheer na matuqar jin dad'i da girmama wannan lokaci da hirar tasu baki daya, domin bai sani ba, ko na qarshe kenan da za su hadu har su yi hira haka, ko kuma akwai rabon haduwar su a gaba.
Sun isa garin zamfara da misalin qarfe 12 na rana, saboda gudu sosai da yake zubawa, hamdala Mubaraka ta yi, sannan ta kalli Taheer, ta na qoqarin motsa baki tai magana ta ga wasu sojoji na nuna ta, amma ba su tsaida motar su ba, sunkuyar da kan ta tayi qasa, dan ta san dalilin da ya sa suke nuna ta, da an basu dokar kama ta, yanzu an janye.
Sai da suka shiga gari sosai, Taheer na qoqarin daukan hanyar dajin nasu Mubaraka ta cire nauyin baki ta ce,
"Yah Taheer Dan Allah tsaya,"
Bai tsaya jin dalilin tsayawar ba, ya samu gefe ya tsaida motar, Sannan ya tattara duk wata nutsuwar shi ya miqa mata a hannun ta, d'an cizon leben ta tayi na qasa, cikin tsoron me zai je ya zo ta ce,
"Dan Allah ka fara kai ni gida wajen su Umma, dan ban sani ba ko Yah Auwal zai bari na je na gan su, dan Allah kar ka qi, in ka qi kai ni na ga Ummana zan yi maka kuka, kuma Yah Auwal zai ga na yi kuka, kuma..."
"Tau ya yi haka nan, ban ce ki bani tsoro ba daga shigowa ta, tau yanzu in munka tai ya ji labari fa? Kin dai san in kin tsira ni ina ruwa ko?"
Cikin zumudi da murna ta ce,
"Ba abinda zai yi maka, Indai na ce ni ta ni nace ka kai ni, Please Yah Taheer ka kai ni naga su Umma" ta qarasa magana cike da shagwaba.
Taheer dai bai so ba, amma an sa shi na dole, tiryan tiryan take nuna hanya, har suka isa, ya na tsaida motar ta fita a guje, ta fad'a gidan,shiru ta ji ba kowa, daga iyayen nasu, har yaran.
Cikin sanyin jiki, ta dinga leqa d'akuna,ta fita, gidan da ke manne da nasu ta shiga, suka gaisa,mutane ne na kirki, masu dattako, tambayar su ta yi inda iyayen ta suke, nan suka sanar da ita Kareeman 'Yabbuga ce ta haihu, yau suna, dan haka su na can gidan Kareema.
Sallama ta musu da godiya ta koma wajen Taheer jiki ba kuzari, idanun ta sun cika da kwalla.
Hakuri ya bata bayan ta masa bayanin komai, ya ce in sun je, ta roqi Auwal, ya san zai kai ta da kan shi.
Hanya suka miqa sai daji.
A can dajin kuwa Sultana da Lawwali sai zumud'in zuwan mubaraka suke, sun yi kwalliya, sun sha ado gwanin ban sha'awa, kamar masu tarbar wani hamshaqin, su Barira da yaran Lawwali kuwa ,sun matsu su ga wace ce wannan yarinyar da ta shiga ran Ogan su? Ya take? Shin ta kai wadda za a gigice da so ko bata kai ba?
Abinci da abun sha, mahallin kwana, da duk abinda za su buqata komai an tanadar musu, su kawai ake jira.
Da misalin qarfe hudu da arba'in su Mubaraka ne a cikin jejin Oga Lawwali, tun daga hanya Mubaraka ta tsure, ganin mutane dauke da makamai, kamar masu zuwa yaqi,Taheer ne ya yi ta kwantar mata da hankali.
Lawwali ya kasa zama, sultana sai dariya take masa,Sultan da ke tsaye ya na kallon su, shi ma murmushi yake ta zabgawa, Lawwali na hango motar su No 4 ya zabura zai yi wajen, Sultana ta d'an kwalla qara kadan, juyawa ya yi ya kalle ta, ya ga ta dafe cikin ta, da sauri ya duqa gaban ta, ya na mata sannu, a lokaci daya kuma ya na juyawa dan ganin rabin ran nashi.
Sultana bata d'aga daga duqawar da ta yi ba sai da ta ga Mubaraka ta fita a motar, cikin washe baki, da murna, Sultana ta kwace hannun ta daga na Lawwali ta kwasa da gudu, ta nufi Mubaraka, suka rungume juna, mamaki da haushi ne suka kama Lawwali, kawai sai ya tsaya ya kama qugu, mutanen wajen kuwa me za su yi banda dariya.
Sultan kuwa har ya na duqawa dan dariya, ga dai Lawwali qatoto, maji da qarfi, amma Sultana yar firit ta masa wayo,Mubaraka gani ta yi ba shi da niyyar zuwa wajen ta, sai ta shanye dariyar ta ta daga murya ta ce,
"Yah Taheer mu juya kawai, ka kaini wajen su Umma na, tunda Yah Auwal din baya son gani na"
Wata harara Lawwali ya zuba mata, sannan ya taka da sauri, Itan ma da sauri ta ke zuwa wajen shi, rungume ta ya yi kamar ba zai rabu da ita ba, Ita kuwa kukan farin ciki ta saka, wani abu ya ji ya tokare masa maqoshin shi, wanda ya ke bayyana tsananin kewar ta da ya yi, ji ya ke dama zai iya kwaranyar da hawaye wataqila da ya ji sauqin abinda yake ji a ran shi,sake qanqame ta ya yi, ya na godewa Allah, da ya dawo masa da ita lafiya.
Sun jima a haka, sannan ya dago da kan ta ya juya ga mutanen da ke wajen, fuskar su dauke da kallo na sha'awar soyayyar da ke tsakanin yaya da qanwar shi.
"Kunga yanda qaunata ta dawo gare ni lahiya? Na muku alqawarin zan maida ku ga iyalin ku lahiya, da yardar Allah, ba zan gaji da neman yahiyar ku a gare ni ba, ku yahe min, ko ba yanzu ba, ko bama tare ne, ku yahe min dan Allah"
Hayaniya ce ta karade wajen, Sultan na gefe ya na murmushin jin dad'in ganin shaquwa da aminci da ke tsakanin Oga da mutanen shi.
Ta gaban shi su Sultana suka wuce, shi ma ya bi bayan su.
Kafin su qarasa ciki Mubaraka ta gaida shi, amsawa ya yi, cikin sakin fuska, sannan ya tambaye ta ya hanya, ta bashi amsa da,
"Alhamdu lilLAAHi"
"To masha Allahu, sannun ku da zuwa"
"Yauwa Muna godiya"
No 4 da Lawwali sun tsaya daga waje, su na tattaunawa, kafin daga baya suyi sallama, ya tafi tsohon dakin shi, da ya samu baqi a ciki, amma still gadon shi na nan, a ciki, ga abinci nan da abun sha an aje masa.
Sai da Mubaraka ta fara wanka, sannan suka hadu dikan su a saman carpet suka ci abinci, su na yi su na hira.
Sultana kan ta ta sallama, ta sani ba zata tab'a samun kalar soyayyar da Lawwali ke wa qanwar shi ba, Mubaraka ta yi gaba, ta na bayan ta, ta yarda da hakan, kuma bai dame ta ba, domin dama kowa da matsayin shi .
Ranar Lawwali ya sha labarin Kano, har tsokanar ta ya soma yi da cewar,