Showing 57001 words to 60000 words out of 155423 words
Chapter 20 - A GARIN MU Book Compelet BY HAERMEEBRAERH.docx
da baki hwadi min mijin ki zai tahiya Makka, yau Allah ya sa ina da kunnuwan jin dumi, na jiyo daga wajen diyan ki, se qaqa?",
Cikin fushin da Hansatu bata san ta na da kalar shi ba ta kalli 'yabbuga ta ce,
"To sai qaqa kuwa? Ko ki na hana mai tahiyar na? Yo Ni na ji ikon Allah, komi na se na hwada miki? Tunda muke a matsayin ki na makwacciya ta ke taba zuwa ki tambayen shin na ci abinci Ni da diya na? Ko ke taba zuwa ki tambayen wane na abba lahiya cikin d'iya na ko niya? Haka d'ai ki dora min jidali? Don Allah dai ki barni na ji da abinda ka damu na"
Daga 'Yabbuga har yaran sai da mamakin Hansatu ya aure su, budar bakin Amina kuwa sai cewa ta yi,
"Kaiiii Umma ke burgeni wallah, dama haka nan zaki zanka yi wa Baba"
Wani kallo Hansatu ta mata, wanda ya sanya ta hadiye dariyar ta, suka shige ciki dukan su,
"In kin qare jin Isah zai tahiya Makka, sai a tai shiyya a baza"
Habaaa nan da nan kuwa 'Yabbuga ta hau bala'i ta na fadin yarinya qanwar bayan ta na kiran ta da munahika, a haka dai ta zare ta bar gidan, cike da borin kunya
Hansatu kuwa ta gama hada wa Isah kayan shi kafff a jaka, sabbin dinkunan da yayi, da takalma da duk wani abu da zai buqata su na akwati.
Shi kuwa ya gama hada goron shi da duk wani abu da zai buqata, ya daure ya aje, gobe kawai ya ke jira ta yi.
Daren ranar Isah ya mori jikin Hansatu kamar ba zai barta ba, Ita kuwa ta ci kuka kamar ba zata bar idanun ta su huta ba, zuciyar ta na matuqar zafi da quna, a duk sanda ta tuna gobe zai tafi, duk ta bi ta qular da Isah, amma ya danne, waya ya dauko aljihun rigar shi, yar qarama, me kyaun fasali, ya miqa mata.
Da a da ne ya bata da tayi murna, amma yau ji take kamar ya na bata takardar saki, ji take kamar ta na bankwana da shi na har abada ne, rabon Isah ya lallabata haka tun ta na amarya.
Ran Isah fa ya gama ɓaci yanzu, ya na bata waya ta na gani ta qi amsa ta na kuka, tsawa ya daka mata, sai da zanin da take ta share hawayen idanun ta ya kusan subucewa,
"Keeee ! Ki na barin kukan iskancin nan ko baki bari? Ban son shashancin banza da wofi za ki karba ko na ajiye aba ta?"
Hannu na rawa ta karba, tsabar kuka duhu duhu take gani, amma dole ta shanye shi, da alama ya gama kai wa maqura a hasala, kar kuma ya kai hannu.
************************
Da rana Hajiya ta aika mota, aka kwashi Isah da su Hansatu sai Sokoto, ta can za su tashi zuwa qasa me tsarki, Hansatu ta sha warning wajen Isah akan kukan da take, ya kuma shiga jikin ta da kyau ya zauna, dan haka ta kama bakin ta ta tsuke, ba abinda take da ya wuce addu'a.
Hansatu da yara basu koma gida ba, sai da Isah ya ga magariba ta kusa, shi ne ya ce a maida su, ai kuwa Hansatu me za ta yi in ba kuka ba, cikin jin haushin ta Isah ya ja hanun ta ya tura ta mota, duk ya matse mata hannun dan mugunta, amma bata kula ba.
Kudi ya debo a aljihun shi ya qirga dubu goma ya wurga mata, ya wuce abin shi, ba sallamar azziqi.
Hansatu kuwa tunda suka dau hanya take kuka, har suka isa gidan ta, Yaran kuwa farin ciki ne danqare a zukatan su, amma ba halin bayyanawa.
***********************
Bincike ya tsananta akan neman Mubaraka, hakan ya yi wa Lawwali dad'i, ya kuma kwantar masa da hankali, a qalla dai hukuma ta shiga lamarin, ya na saka ran za a gan ta.
Shi ma bai zauna ba, duk inda ya san ya dace ya je dan neman ta, bai gajiya ba, neman ta ya zama masa ibadar shi, tunda dama bai damu da ibadar ba.
Kwanan su uku basu hadu da Sultana ba, Ita kuwa ta na son ta dan ja aji ta ga ko zai neme ta, tunda ta gama bayyana masa me ke ran ta game da shi, amma shiru, ba waya ba saqo, ba kuma zuwa da kai.
Yau Lawwali a daji ya wuni, idanun shi na kan kowa da komai, ya kula da wani abu guda, wanda ya sanya shi zargin ko dai No 4 ba shi da lafiya, ko kuma ya na boye masa wani sirri, dan haka kiran shi ya sa a je a yi.
Lokacin da saqon kiran Lawwali ya riski No 4 ,ya shiga gingimemen tashin hankali, bai san sanda ya furta,
"Niiii? Mi an ka ce na yi???"
Da qarfi ya fadi hakan,
Da mamaki 'yar Aiken ta kalle shi, ta yi tafiyar ta.
Jikin shi na rawa zufa na digar masa ya tafi amsa kiran Oga.
Ko da ya shiga ya tadda Lawwali na qoqarin neman Network ya na son magana da Sultana.
Lawwali bai ko kalle shi ba ballantana ya san halin da yake ciki, cikin Muryar shi ta Oga Lawwali ya ce,
"Akwai matsala ne Taheer? Ina nufin gida lafiya suke ba bu matsala? Kwana biyu na ga baka cikin nutsuwar ka"
Wani qololo ne ya tokare wuyan No 4, da kyar ya furta,
"Ran ka shi dade Oga, diya ta ta ba lahiya, ina buqatar zuwa gida amma ba hali, Kuma kuddin waje na basu isa yin jinya"
Lawwali sai a lokacin ya kalle shi , akwai mamaki, wanne irin ciwo ke damun diyar shi da kudin da suke samu a kwanakin nan kamar hauka ba su isar shi? Lawwali bai tsananta bincike ba, ya miqe, ya bude inda yake aje kudi, ya ga babu, ya kai su can gidan shi na cikin gari.
"Baka da matsala, in dai kudi na Taheer, kar ka manta, tun ranar da mun ka hwara haduwa, na hwadi maka damuwar ka tauwa ta, ka zanka sanar da ni,mi zan yi da kuddi in ku baku wadata ba? Ka biyo ni gida na anjima mu tai ka amsa, kuma ka zauna wajen iyalin ka har sai sun samu lahiya"
Daga kai kawai No 4 ya yi, hawaye na zuba masa,tabbas in ya riqe wannan magana bai sanar da Lawwali ba, ya ci amanar Lawwali, domin shi ne ya jawo shi wannan harkar da suke samu, ya taimaka masa sanda mahaifiyar shi ba lafiya har aka mata dashen qoda,kuma shi ke temaka masa a duk sanda matsala ta iyali ta taso, amma ace a hada baki da shi a na cutar da shi?
Gashi in ya sanar da Lawwali sunan shi matacce, in ya bari Lawwali ya gano da kanshi su nan shi matacce, ya zai yi?
Jiki ba kwari ya fita, dukkanin abokan aikin shi sun kula da sauyin da ya koma da shi, ciki har da No 1 Dan haka waje ya ja shi, suka bar sansanin nasu gaba daya, su na zuwa qasan wata bishiya No 1 ya finciki No 4 su na fuskantar juna, ya ce,
"Ka sanar da oga komai ko?"
"Shi ne kai na da naka suke a jikin mu? Kai sake min taguwa ni, in ji da abinda ka damu na,"
Fizge kan shi ya yi, ya koma baya ya na shafa kan shi, cikin damuwa, da kyar ya furta,
"Na yi wa Oga qarya,...Oga ya min taimakon da ba wanda ya taba yi min shi a rayuwa, amma ina ha'intar shi, Oga ya min abinda ku ba ku min ba, yanzu ina cikin tsaka me wuya, in sanar da gaskiya in mutu, in yi shiru ya gano da kan shi in mutu, wa zai kula da ahali na?"
"Kai banza na wallah, ka manta kuddin da Excellency yayyi muna alqawari,sun ninka wanda Oga ya taba bamu a rayuwa,"
"Amma wanda ya taimake ka lokacin da ka ka buqatar taimako ba ya shi a rayuwa"
Wata dariyar mugunta No 1 ya yi, sannan ya daki kafadar No 4, ya ce,
"In ka na ganin rayuwar ka bata da anhwani dan Allah tai ka sanar da Oga inda qauna tai take"
Ya na gama fadar haka ya bar wajen, No 4 kuwa qara ya yi ta saki, ya na kuka, ya rasa ina zai saka ran shi, me ne ne makomar shi in ya sanar da Lawwali?
*Ku ba wa No 4 shawara mutan group ya na cikin tsaka mai wuya*
💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻
BY HAERMEEBRAERH
PAGE 29:
Lamishi ce zaune ta buga uban tagumi, hankalin ta ya fara tashi a 'yan kwana biyun nan, wai a ce dan mutum a neme shi a rasa kamar kwabo a tsakanin barayi?
Sallamar qawa kuma aminiyar ta ta ji, wato 'Yabbuga, nisawa ta yi kafin ta amsa, cikin jimami, 'Yabbuga ta ce,
"Ohhh ki na nan zaune in da na barki? Hummm Allah dai shi kyauta muna wanga lamari,...dazu ina ta so na tambaye ki, wai an ce jiya da bani nan na tai gidan su Dan jumma, wai diyar gwauna ta zaka? Mi ta zo yi halan?"
Cikin sanyin murya Lamishi ta ce,
"Ta zo ta ji ko an samu wani labari akan wannan yarinyar, ke san da shike sun saba,ta na son Mubaraka kwarai aran ta, ko jiyan ma sai da tayyi kuka da ni ce har yanzu shiru"
"Allahu akbar, rayuwa kenan, za a gan ta,ni da zuwa nayi ki taimaki wagga farar qahwa tawa ki sa min lalle, amma fa a gida na, dan ka na zaune baka san wa zai fado ba, se de ka ji ana gahwara kayya kayya" (Lawwali)
"Mi ki ka nuhi? Gidan namu gidan qauraye na?"
Kama bakin ta 'yabbuga ta yi ta ce,
"Uhmm uhmmm, ba ki ji wanga batu daga gare ni ba, ki na samin ko ah ah?"
"Ban wallah bin ki gida sa lalle, in ki na zama nan na sa miki Lalle tauuu, in baki zama yi ta tahiyar ki"
Kyabe baki 'Yabbuga ta yi ta zauna, lokacin azahar ya yi, madadin su bari su fara sallah, sai suka yi kamar basu ji ma kiran sallah da ake ba,kwaba lallen Lamishi ta yi, Yabbuga na ta uban surutu, rabin surutun zagin Mai Buruji ne, dan ma Lamishi na taka mata burki, ta kan ce, ta tsani me zagin kishiyar ta, domin watarana zai zage ta ita ma.
"Ni hwa ban ga lallen ga na kamu ba" inji Lamishi, Yabbuga tace,
"Ke dai bari shi yi awa guda ki na ganin yanda zai yi kyawu kwarai"
Su na tsaka da saka lalle Mai Buruji ta dawo daga aiki, ga lalle an qunshe wa 'Yabbuga hannu da qafa da shi, ko da Mai Buruji ta dakko kwanukan cin abinci yawu ya fara ambaliya a bakin 'yabbuga, ta ji haushi saka lallan nan a hannu, da ta sani da a qafa kawai aka saka mata.
Ko da aka raba aka zo cin abinci sau biyu Mai Buruji ta bawa 'yabbuga a baki, suka yi ta cin abin su suna hira, Lamishi ta ce Allah shi kiyashe ta bawa qatuwa abinci a baki.
Ran 'Yabbuga in ya yi dubu ya ɓaci, ta kame bakin nan ta gume shi gum, a haka gyangyadi ya dinga dibar ta.
************************
Shigar su gidan Lawwali ke da wuya, ya qirga kudi dubu dari biyar ya bawa No 4, No 4 kuwa cikin dakiya, da danne abinda ke ran shi,ya dinga murnar dole ya amsa ya na godiya.
Lawwali na ta kallon shi, kallon da Lawwali ke masa ne ya fara shiga kowanne lungu da saqo na jikin shi,cikin hanzari ya fara qoqarin tafiya, Lawwali kuwa zama ya yi a daya daga kujerun da suka zagaye madaidaicin parlourn , ya dora qafar shi daya saman daya,No 4 na kallon zaman da Lawwali ya yi, ya tabbatar ba lafiya, cikin sarqewar murya ya ce,
"Oga na tafi..se..se..see da swahe,"
Hannu kawai Lawwali ya daga masa, idanun shi sun kad'a sun yi jawur, qafafun No 4 na rawa ya nufi bakin qofar, ko da ya murda ya ji ta a rufe, juyawa ya yi ya ga Lawwali na kallon yatsun hannun shi, sake jan qofar ya yi, ya ji ta gam, cikin tsananin tashin hankali ya juya tare da zubewa a wajen,ya sake jakar kud'in a qasa ya na kuka, zufa da hawayen shi duk sun hade waje daya.
"Oga don Allah ka yi min rai, ka rufa min asiri ina da iyali, ka sani, ka san mahaifiya ta, ka ɗauke ta awat-taka,Oga ina da niyyar sanar da kai tsoro nika ji kar ka kashe ni, ina da qananan yara ka sani, har takwara na yi ma oga"
Har gaban Lawwali ya isa ya kama qafar shi ya na kuka ya na bashi hakuri, wani irin naushi Lawwali ya kai mishi sai da jini ya yi tsartuwa a qasa, bakin No 4 ya fashe.
Kasa ihun ma ya yi, dan ya san ya cancanci sama da haka ma, idanun Lawwali ba bu mai fatan ya gan su a wannan lokacin.
"Taheer ni zaka ci wa amana? aza ka ke bani ganewa? To na ji duk abinda kun ka ce kai da wancan qaramin dan iskan, ina kun ka kai min qauna ta?"
"Oga na san inda suke zan kai ka da kai na, Oga ka yahe min, ba da son rai na ba an ka ɗauke ta, ba ita mun ka tai dauka ba, qawar ta mun ka tai dauka, sun ruhe fuska bamu san da ita ciki ba"
"Yi min shuuu ! Munahikin banza, ka na jin har akwai wata sauran yarda a tsakanin mu? Ba bu yarda tsakani na da kai, maza ka gaggauta kai ni ga qauna ta, sai dai zai zama siri tsakanin mu, kamar yanda gwauna da wancan shegen basu son na sani, ban yarda ka sanar da kowa ba,in kuma ka sake cin amana ta a karo na biyu, zan kashe ka, zan kashe uwar ka, dan ba uwa ta ta ba, zan kashe matar ka da diyan ka,"
"Oga ko na hwarko ma tsautsayi na wallah ban koma cin amanar ka, Nagode oga na go..."
"Dalla miqe ka je ka kai ni ga qauna ta"
Jiki na rawa No 4 ya miqe, a bakin kofa ya tsaya ya na jiran Lawwali ya bude qofar shi, sai da ya dauki makullin mota, ya lodawa bindigar shi harsashi sannan suka fita suka bar gidan.
Kafin su isa magriba ta gabata sosai, bai fi awa daya a kira ba, su na zuwa No 4 ya bawa Lawwali shawara su aje mota a nesa su qarasa da qafa, haka kuwa aka yi, sun isa qofar gidan, suka tarar an kulle da kwado, No 4 ne ya zari makulli a aljihun shi zai bude qofar, bai ankara ba ya ji an dafe qeyar shi da duka,
"Dan iska, makullin ruhe qauna ta na hannun ka, amma kullum muke haduwa baka taba hwadi min ba"
Su na shiga su ka ji gidan shiru kamar ba kowa, dakin da aka ajiye yaran suka shiga, ko da suka je sai ba su ga Mubaraka ba, sai su Murjanatu, tambayar su Lawwali ya yi ina take, cikin kuka Saliha ta ce,
"Wannan d'ayan mugun ya dauke ta, kullum in ya zo sai ya dauke ta ya hita da ita, daga baya sai ya dawo da ita, ta na kuka"
Wani irin ashar Lawwali ya saki,lallai in abinda yake zargi No 1 ya yi da Barakan shi,tabbas a yau dinnan zai kashe shi.
A guje Lawwali ya kama hanya zai fita daga gidan, No 4 ya yi maza ya kulle ko ina ya bi bayan shi da mugun gudu,shan gaban shi ya yi ya na haki, wani naushi Lawwali ya kai mishi a ciki, sai da ya duqa
"Oga ka san mutanen ga basu da dad'i, na sani Gwauna da kai ya ke taqama a duniyar siyasa,amma ba a cin munahuki da yaqin gaba da gaba, shi ma ka hito mai ta inda bai zata ba, babbar nasarar da an ka samu shi na ka san wanda ya dau qanwar ka,"
Tabbas maganar No4 gaskiya ce, to ta yaya zai rama abinda gwamna ya masa?
Kan shi cike da tunani ya shige mota, ya bar No4 a wajen, No4 komawa ya yi, ya gargad'i su Murjanatu, akan kar su kuskura su sanar da zuwan su, da yayan Mubaraka, su na sanar wa za a kashe su nan take.
Tsoro ya kama su, dan haka sun yi alqawarin ba za su fad'a wa kowa ba, har ita kan ta mubaraka din.
************************
'Yabbuga bata farka daga baccin da ya kwashe ta ba sai da ta ji qarar bude qofar gidan da qarfi, a kidime ta farka ta na fadin,
"Wayyoo Allah mun shiga uku, mi ya hwaru, ake bude gambu kamar ana girgizar qasa?"
"Me ki ke yi a gidan nan a wanan lokacin,"
Bude baki 'yabbuga ta yi iya qarfin ta takurma ihu, marin kan ta tayi, wai ko za ta tashi, wataqila a baccin wahalar da ya dauke ta ne ta ke ganin shi a idanun ta.
Qafa ya sa ya kwashe kujerar da ta dora qafafun ta ya yi wurgi da kujerar, kafin ya qara kaiwa d'aya kujerar duka 'yabbuga ta miqe, ta taka qafafun ta biyu a qasa, ta diba waje a guje, tsantsin ledar na diban ta, kai ba ko dan kwali, gashi duk ya tuttuje haka ta isa gida.
Dan jumma na ta gyara ma'ajiyar abincin su da awaki suka shiga suka yi wa barna, gani ya yi ta afka gidan ba ko sallama, zani qanqame a hannun ta, kai ba dankwali, duk Leda a qafar ta, tsoro da tashin hankali ne suka rufe Dan Jumma, dan a tunanin shi ko masu kidnapping ne suka dauke ta ta gudo, tunda yanzu abun qara yawa yake.
"Daga ina ki ke? Wa ya