Showing 1 words to 3000 words out of 23389 words

Chapter 1 - Mugunta 2 Complete Hausa Novels By Khairat.txt

KHAIRAT   

13 Mar 2026

7

😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈


By



Khairat ✍️🤍




https://chat.whatsapp.com/Js1xb4FBd2v0o5mxXpssVr

*(Posting room)*


*My WhatsApp group comment section 👇 👇 👇 👇 *

https://chat.whatsapp.com/FYbZw86FTfQDpyIkILlMuN


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.

_With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.🤌💪_

https://chat.whatsapp.com/Js1xb4FBd2v0o5mxXpssVr

BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM


Page 51-52*(BOOK TWO)*



*Bayan wata biyar*

*Ayaman*

Tun daga ƙofar sashen zaka jiyo nishin mace kaɗan-kaɗan da alama tana jikin wahala.
Da alama ƙarar daga banɗaki take, kuma matsawa nayi don ganin me ke faruwa, Ayaman! Tabbas Ayaman zaune a banɗaki cikin jini alamar mai naƙuda.
Wani nishin ta kuma saki sai ga jaririya ta faɗo tana ra chanyara kuka, "Innalillahi wa'inna i'laihi raji'un." Ayaman ta faɗa a karo na ba adadi.
Yarinyar ta kuma kalla kafin ta ji wani baƙin ciki ta fashe da kuka, ƙarni da kuma zafin banɗakin ya sa yarinyar cigaba da chanyara kuka .
Sai da Ayaman ta kai kusan minti goma a wurin sannan taga shigowar innar Anas, "Hasbunallah wa ni'imal wakeel." Abinda innar Anas ta faɗa kenan sannan ta fice daga sashen cike da takaici.
Wani kukan Ayaman ta saki kafin ta miƙe da ƙyar ta nufi hanyar kitchen, wuƙa ta ɗauko ta raba mahaifar da jaririyar sannan ta ɗauko flask daga ɗaki duk da jan ciki ta haɗa ruwa ta ɗauraye yarinyar ta ɗauraye jikinta.
Ɗaki ta shiga tana ɗingisawa ta nemi zani ta rufe yarinyar ita kuma ta kwanta a gado tana jin wani uban raɗaɗi a mararta.
Wani abu mai ɗumi taji yana bin ƙafarta, jini ne tabbas wannan jini ne, wasu zafafan hawaye ne suka kuma fitowa daga idanunta.
Tabbas wannan ce rana mafi muni a wurinta, ranar da baza ta taɓa mantawa da ita ba a tarihin rayuwarta ba, dan ta kasance rana mafi muni bayan ranar mutuwar mahaifiyarta.

Muryar Anas taji a kanta yayin da ta lumshe idanunta, ɗago idanun tayi a hankali ta ƙure su a fuskarsa wadda da alama shima labarin ya riske shi na abin da ya faru.
"Ayaman...." Sai kuma ya yi shiru sakamakon wani kuka da yaci ƙarfinsa, durƙushewa ya yi a wurin yana kiran sunan Allah.
A ɓangaren Ayaman kuma duk sai taji ta takura dan bata taɓa ganin namiji yana wannan kukan ba.
A hankali kuma ya tashi tsaye, sai da ya kai ƙofa sai yace "Ayaman ban taɓa tsammanin wannan sakayyar daga wurinki ba, na nuna miki ƙauna, soyyaya da kuma kulawa, ni da mahaifiyata mun amshe ki hannu bibbiyu amma kin watsa mana ƙasa a ido." Ya goge hawaye sannan ya cigaba da faɗin
"Ayaman kin ci amana ta, baki ci sunanki ba, Allah zai saka min wannan sakayya da kika min, aurena da ke ya ƙare Allah ya haɗa kowa da rabonsa na sake ki saki ɗaya." Ya ƙarasa yana goge wasu zafafan hawaye.
Ayaman saurin toshe kunnuwanta tayi sakamakon wannan kalaman da suka mata nauyi, kuma ƙwaƙwalwarta ta gaza fahimtar su.
Kalmar ƙarshe ce tafi girgiza ta, toh ya aka yi haka? "La'ilaha illah anta subahanaka inni kuntu minaz zalumin." Sune kalmomin da suke iya fitowa daga bakinta.

Tabbas ko me Anas ya yi dai-dai, dan ko addinin muslunci idan mace ta kai wata shida a ɗakin mijinta ta haihu toh ba shakka ana kyautata zaton ɗansa ne amma akasin haka na janyo cecekuce.
Indai tana ƙirge yau wata biyar da kwana uku da aurensu, ga kuma jaririya wacce da alamu lafiyayya ce hakan na nufin ta cika wata tara a cikin mahaifiyarta.

Sai da ta ɗau wani lokaci kafin ta tashi ta goya yarinyar da ko arziƙin ɗan kamfai bata samu ba balle kaya.
Sannan ta ɗauko wani ƙaton hijabinta wanda ya rufe ko'ina ta zira a jikinta, takalmi ta saka kana ta fara tafiya kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki.
Rumfar innar Anas ta nufa, sallama tayi mata ta amsa, cike da takaici innar Anas tayi wa Ayaman kallon banza sannan ta tofar da yawu.

"Innata, innata ki jiyo ki kalle ni, Ayaman ce, yarinyar da kika ɗauka a matsayin ƴarki ta jini, innata wallahi ban aikata abinda kuke zargina da shi ba, ba zan taɓa iya wa ba, nima abin ya zo min bagatatan ban sani ba wallahi." Ta ƙarashe cikin muryar kuka sosai.
Ƙara kawar da kai inna tayi dan bata son kallon Ayaman, wani irin kallo take yi wa Ayaman ya za'a ce mace daga zuwa gidan miji wata biyu ta haihu? Ay bazai taɓa yiwuwa ba.
Ayaman ta gaji da durƙuson ta miƙe ta fice daga gidan.
Tafiya take amma ji take kamar ba a duniya take ba, ina ma ace tun lokacin da mutuwa ta zo ɗaukar mahaifiyarta ta haɗa da ita, meyasa, ta yadda da Allah kuma ta yadda da ƙaddararsa, amma wannan jarabawar tayi mata tsauri da yawa.
Haka dai ta ƙarasa ƙofar gidansu tana ta surutai, tsaye tayi ta rasa shiga zata yi ko kuwa, ta san ta ta ta ƙare, dan Ladiyo ba raga mata zata yi ba.

"Assalamu Alaikum." Ta faɗa a hankali tana shiga gidan.
Ladiyo na tsakar gida ta amsa sallamar, abin mamaki yau Ladiyo ce da amsa sallama? Durƙushewa Ayaman tayi a ƙasa tana wani kuka mai ban tausayi.
"Kar dai raɗe-raɗen dake yawo a gari na cewa kinyi cikin shege har kin haife sa ne ya tabbata?" Ladiyo ta tambaya tana zazzaro idanu.

Sakamakon zafi da kuma takura da jaririyar ta samu ne ya sa ta chanyara kuka wanda yasa Ladiyo sakin kwanon dake hannunta.

"Hehehe wato dai ya tabbata, cikin shege ya tabbata shikenan Ayaman kin gama da mu, munafuka tsinanniya." Ladiyo ta ƙarasa tana dungurewa Ayaman kai har ya yi sanadiyyar faɗuwarta ƙasa.
Wani uban kuka jaririyar ta saki, Ayaman na kuka a lokaci ɗaya kuma tausayin yarinyar na kuma lulluɓe ta.

"Jama'a! Jama'a! Wayyo Allah! Ayaman tayi cikin shege ta haife sa, ta biyo halin uwarta, karuwanci taje tana yi a gidan miji." Ayaman ta jiyo muryar Ladiyo tana kururuwa tana sanar da mutanen gari.
Kafin kace me gidan ya cika da mutane, yara da manya kowa yazo kallon Ayaman da tayi cikin shege.

Wata maƙociyarsu ce ta buɗi baki tace "Shegiya zata janyo mana bala'i a gari, wannan hukuncinta kawai kisa ne dan in bala'i ya tashi ba ruwansa da mai laifi ko akasin haka."
Haka dai kowa ya dinga tofa albarkacin bakinsa kafin lokacin da malam Isyaku ya shigo.
Idanunsa duk sun yo waje ya tsaya yana kallon Ayaman, rasa mai zai ce mata ya yi kawai ya nuna mata ƙofa.
"Fitar min daga gida!!" Shine kalmar da ta ji daga bakin mahaifin na ta.
Tsugunnawa tayi tana kuka har da sheshsheƙa.
"Baba...."

"Ki fitar min daga gida nace!!!!" Malam Isyaku ya faɗa cikin ɓacin rai wanda kana ganin idanunsa zaka tabbatar da hakan.
Jiki a saɓule ta fara jan ƙafafunta yayin da mutane ke bin ta suna tofin alatsine.
A ƙofar gidan ta tsaya tana kuka mai ban tausayi amma hakan bai hana yaran dake mata ihu dainawa ba.
"Shegiya uwar shegiya." Shine kalmar da yaran ke faɗa suna jifan ta da dutse wasu kuma suna tofa mata yawu abubuwa da yawa dai kuma manyansu na kallonsu babu mai hana su.

Muryar maman su Tsahare ta jiyo tana kora yaran amma duk da hakan basu tafi ba, jan Ayaman tayi suka fara tafiya duk da hakan yaran basu ƙyalesu ba abin yana neman shafar ummansu Tsahare.

Suna isa gidan tayi sauri ta rufo ƙofar amma sai da yaran suka san yadda suka yi suka turo ƙofar suka shigo.
Da ƙyar ummansu Tsahare ta kora yaran ta rufo kofa a hakan ma sai da ta saka abubuwa a bakin ƙofar.
Juyawa ummansu Tsahare tayi wurin Ayaman, "Kwanto yarinyar." shine kawai abinda ta faɗa.

Ba musu Ayaman ta kwanto ta ta miƙa wa umma.
Bayan ta amshi yarinyar ta tsaya kallon ta, jikinta duk jini da kuma sauran ruwan mahaifa ga ƙarni da take ga gumi da ya game jikinta.
Yarinyar sai ajiyar zuciya take ta sauke wa da alama ta jigata, wuta ta haɗa sannan ta wanke yarinyar ta ɗauko wasu tsofaffin kayan jarirai duk da sun daɗe amma tsaf suke babu datti dan ana wanke su wani lokacin.
Bayan ta shafa mata mai ta saka mata kayan ay kuwa jaririya ta fito fess abinta tayi kyau sosai dan ba ƙarya ta biyo bayan hasken mahaifiyarta.

Shiru suka yi dan sun rasa me zasu cewa juna, ruwan zafin da umma ta ɗaura ne ta juye wa Ayaman tayi mata wanka na gargajiya dai.




********************************


*_Ladiyo_*

Tun bayan lokacin da wani farin haske ya ɗauke boka babu shi babu alamarsa, wannan duhu da ya baibaye wurin yasa ta tsalla ihu, cikin ikon ubangiji ta samo hanya ta fito daga kogon.
Haka tayi ta gudu a dajin Allah ga duhun dare ga kukan wasu namun daji.
Tana isa cikin gari ta fara haɗuwa da mutane da yake dare ne kuma wata ba wani haske ne da shi ba kuma ba wutar nepa bace yasa ba wanda ya gane ta.
Da gudu ta ƙarasa cikin gidan ta shige ɗaki ta rufo, baya-baya take yi dan gani take wannan duhun zai biyo ta, hannu taji ya taɓa ta ay kuwa ta kurma uban ihu "Wayyyyooo Allah na, dan Allah kuyi haƙuri bok...." Bata ƙarasa faɗa ba taji muryar Malam Isyaku " Lafiyarki kuwa Ladiyo?"

Tsaki ta saki kana tace "Dama kaine asrarre kana aikin kenan zaman kashe wando." Ta ƙarasa faɗa cikin masifa, yayin da a cikin zuciyarta godewa Allah take da yasa bata yi wa kanta ɓaranɓarama ba dan indai malam Isyaku ya san asiri tayi mai shikenan aikin ya lalace.
Zani ta nema ta rufe jikinta tana ta yiwa malam Isyaku masifa, da ya gaji da bala'inta ta miƙe ya bar mata ɗakin.
Yana fita ya ci karo da wata kyakkyawar mace a dai-dai kofar ɗakin Ayaman.
Kamar ya san fuskar amma ya manta a ina ya san ta, yana fara ƙoƙarin tunano ta kawai sai wani ciwon kai mai tsanani ya ratsa sa sai kuma bacci mai nauyi ya kwashesa.
Hakan yana yawan faruwa da shi a duk lokacin da ya yi ƙoƙarin tunano wannan matar.

Tafiya tai tafiya har ta kai ga Alhaji Gabatari ya kawo kayan aure kuma ansa ranar ɗaurin aure, shiri ba wanda Ladiyo bata yi kuma tun daga lokacin ko taje wurin boka ba ya iya sauraron ta .
Tun a wurin ɗaurin aure ake mamakin Alhaji Gabatari da dukiyarsa, dan sadaki million ɗaya ya bada, mutane suna ta tuntuɓar malam Isyaku anya ya yi bincike kuwa? Dan da ayar tambaya a kan sa.
A cikin gida kuwa zo kiga yadda Ladiyo ta sume domin daɗi tun da aka kawo kuɗin sadakin ta ƙanƙame su a hammata ta hana kowa gani ita a tunaninta sace wa zasu yi.

A wurin ɗaukar amarya ma an sha ruwan mamaki, dan rantsa-rantsan motoci Alhaji ya turo domin ɗaukar amarya kuma a ƙalla sun kai goma sha ɗaya kuma kowacce mota babu irinta a garin.
Ladiyo kuwa kasa rufe baki tayi dan abin ba'a cewa komai, haka ta shige gaban mota dan ta rantse da ita za'a kai amarya.
Tafiya ake ta yi har aka shigo cikin garin Kano, kuma har aka zarce ƙarshensa wurin garin Tudunwada dake kano aka nufa.
Tun da suka shiga layin babu gida ko ɗaya sai na Nabeela shi ma ɗin kamar villa dan ba ƙarya gidan ya tsaru ga shuke-shuke ta ko'ina furanni da abubuwa da dama.
A cikin gidan kuwa mutuwa ce kawai su Ladiyo da sauran ƴan ɗaukar amarya basu yi ba, dan komai na gidan sabo dal kuma na zamani, kama daga italian chairs, bed set kayan kitchen komai Alhaji ne ya yi dan cewa ya yi kar su ɗauko ko cokali.
Girma da kuma ƙayatuwar gidan bazai misaltu ba sai wanda ya gani a ido ne zai tantance.
Sai da suka yi wa komai na gidan ɗai-ɗai suka fayyace biri har wutsiyarsa sannan suka fara shirin tafiya.

Ƙiri-ƙiri Ladiyo tace babu inda zata, ga godan hutu ina zata koma ƙauye, haka dai suka janye ta suka chusa a mota dan ba hauka ake ba da za'a bar uwa ta kwana gidan ɗiyarta ba.

Amarya Nabeela na cikin mayafinta ta fara jiyo hayaniyar mutane kamar ana biki.












More comment more typing, ga book two nan dai fatan zaku ji daɗinsa .




Khairat ce ✍️🤍





Love you all 💞 🥰



😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈


By



Khairat ✍️🤍


https://chat.whatsapp.com/Js1xb4FBd2v0o5mxXpssVr
*(Posting room)*


*My WhatsApp group comment section 👇 👇 👇 👇*

https://chat.whatsapp.com/FYbZw86FTfQDpyIkILlMuN



💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.

_With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.🤌💪_




BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM


Page 53-54 (BOOK TWO)



*_Amarya Nabeela _*

Hayaniyar kuma matsowa kusa da ita take, ƙara rufe fuskarta tayi dan ta zata abokan ango ne suka rako sa.
Shiru kusan minti talatin babu wanda ya shigo ɗakin ga kuma hayaniyar ta ƙi ƙarewa kamar biki ake sosai dan har ƙarar buɗe lemuka take ji ita a tunaninta sun tsaya yin shagali ne kafin su shigo dan haka ta kuma rufe fuskarta.




*_WAIWAYE_*



*_Ayaman_*

Ita dai a rayuwarta bata taɓa samun wannan chanjin yanayin jiki irin haka ba, cikinta ba wasa ya fara ɗagowa, ka ƙafarta da ta fara kumburi kaɗan har yanayin mamanta basu kai girman da ba.

Ta alaƙanta hakan da sauyin yanayi da ta samu da kuma cima, ta sanar da Innar Anas ko wani ba lafiya ba, amma innar tace ta yiwu hutu da ta samu kwana biyu ne ya sa ta ƙiba haka amma fa chan ƙasan zuciyarta tana da abin faɗa kawai dai tana jiran lokaci ne.

Haka ranar tana ji aminiyar innar ta zo suna magana, "Kice sirikar taki har ta ɗauki ciki, kai ma sha Allah." Hajiya Shafa'atu ta faɗa tana shan ruwan da aka kawo mata.

Cike da mamaki Inna ta kalle ta, "Ciki fa kika ce Shafa'atu?"
"Eh mana baki lura bane, kuma da alamu cikin ya kai kusan wata biyar dan ga cikin nan ya taso."

"Kai Shafa'atu sai dai wasa, dududu watansu ɗaya da kwana sha tara da aure fa." Innar Anas ta ƙarasa cikin mamaki.

"Toh wallahi Maryam(innar Anas) in zaki yadda ki yadda dan yarinya dai ciki ne da ita."

Ayaman dake madafa tana girki taji cikinta ya bada ƙululu, ciki fa? Toh ta ina? Wata ɗaya da aure kuma tace cikin har ya kai wata biyar?
Shafa cikin tayi sai taji ya yi tauri kuma ya ɗan taso ba kamar da ba.
Wani uban gumi ta share a fuskarta, taya za'a ce ciki, in shaa Allah ba haka bane ta ƙarasa tana cigaba da girkinta.
Wajen bayan isha suna hira ita da Inna dan Anas bai dawo ba innar take tambayar ta, "Ayaman yaushe ne baki ga al'adar ki ba?"

Shiru Ayaman tayi kafin tace "Inna wancen satin ma nayi."
Wata ajiyar zuciya Inna ta sauke tana bagarar da zancen cikin da Shafa'atu ta dasa mata.

Kuma wani ikon Allah, cikin bashi da girma dan hakan kowa ya zata tumbi ne kuma yarinyar bata cika motsi ba balle Ayaman taji motsi, bugu da ƙari tana ganin al'adar ta.

Kwatsam a wata ƙaddararriyar safiya Ayaman ta tashi da wani azababban ciwon mara da baya, innar Anas na ganinta ta tabbatar wa kanta Ayaman da ciki ta shigo gidan, gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi bata taɓa tsammanin wannan sakayyar daga wurinta ba.



Abinda mutane ke zargi ya tabbata, amma tambayar anan ita ce, taya Ayaman ta samu ciki? Sannan waye ubansa???





********************************


*Delu*


*WAIWAYE*





Kuyi haƙuri da short page ɗin



More comment more typing



Khairat ce ✍️🤍


Love you all 💞 🥰


😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈



By



Khairat 🤍✍️




https://chat.whatsapp.com/Js1xb4FBd2v0o5mxXpssVr
*(Posting room)*



*My WhatsApp group comment section 👇 👇 👇* https://chat.whatsapp.com/FYbZw86FTfQDpyIkILlMuN


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.

_With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.🤌💪_



BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM



Page 55-56(BOOK TWO)




*Delu*


*WAIWAYE*


Ihun da ta ƙwantsama ne ya sa Mariya da Idi dake kwance suna aikin ashsha miƙewa, sauri Idi ya yi ya sa kayansa ya fece da gudu ya zo dai-dai ƙofar fita yaji an ƙwantsama mai taɓarya, juyi ya fara yi a ƙasa yana ihun neman taimako yayin da Delu ta cigaba da dukansa da hannuwanta.

Da ƙyar ya samu ya fece daga hannunta yana cin alwashin komai dare sai ya rama abinda tayi mai.

Kan Mariya ta juya, "Tsinanniya wato karuwanci kika fara a gidan nan? " Ta ƙarashe tana zabga mata wani mari.
Bata dire hannunta ba Mariya ta mayar mata da maruka zafafa guda biyu wanda sai da Delu ta ga taurari sun ratsa mata.

"Mariya nii..?" Bata ƙarasa ba wani kuka ya ci ƙarfinta, ƴar da ta haifa da cikinta ce ta mata wannan abin? Ta kasa gasgata hakan.
Juyawa Mariya tayi ta shige ɗaki ba tare da ɗigon tausayin mahaifiyarta ta ba, ta bar Delu na zubda hawaye.

Ta kai kusan minti ashirin a wurin kafin taji shigowar Malam Surajo, sallama ya mata bata amsa ba dan haka ya yi sauri ya fara ayyukansa dan yanzu tana barinsa ya fita.

Tashi tayi daga wurin ta shige ɗaki cike da ƙunci.

Ta kwanta a kan gadon ne ba wai dan tana jin bacci ko gajiya ba, kallon saman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login