Showing 15001 words to 18000 words out of 23389 words

Chapter 6 - Mugunta 2 Complete Hausa Novels By Khairat.txt

KHAIRAT   

13 Mar 2026

6

mutane a ka ga gidan kuma aka taya shi naira miliyan daya, duk da gidan na da girman gaske dan kuɗinsa na ainihi zai iya haura miliyan goma, haka nan Yunusa ya siyar.

Ko da aka gama cinikin gidan ya amshi kuɗin dubu ɗari ya cilla wa Ladiyo ya kama hanyarsa.
Haka ta sha kuka kuma ta yi danasanin haihuwar Yunusa, yanzu ina zata je? Sai kuma ta tuna da Sadeek...



Danasani yanzu kika fara Ladiyo.




*Ayaman*


Cikin haba-haba da farin ciki ta tarar da matan gidan ana ta kai komo domin samar da abincin shan ruwa da kuma sahur.
Girki suke yi a tare sai kowacce ta ɗiba a kularta, hadin kansu sai wanda ya gani.

"Sannunku da aiki." Ayaman ta faɗa ya yin da take tsugunawa ta na daɗa ƙare wa matan aiki. Nan suka shiga amsa sannun suna faɗin me yasa Tsahare ta fito da ita daga zuwanta.
Nan ita ma ta zauna aka fara aikin, kunu da ƙosai ne wanda sai tashin kamshi yake yi, ga kunun gyaɗa ga wanda ba ya son kunun tsamiya, sai kuma lallausan tuwon shinkafa miyar kuka ita ma sai kamshi take.

Kafin a sha ruwa sun kammala komai,nan aka fito da kankana aka yayyanka aka shirya komai.

Wato a tarihin rayuwar Ayaman za ta iya ce wa wannan rana ta 27 ga watan Ramadan shekara ta 1443 wanda ya yi dai-dai da April 27 shekara ta 2021 bata taɓa jin daɗin karya azumi irin wannan ba, ko'ina ta juya murmushi da ƙauna ake nuna mata, haka ta godewa Allah ta kuma yi salati ga manzon rahama ( S.A.W).

Bayan shan ruwan nan matan da ke sallah aka nufi masallaci domin sallar isha'i da kuma taraweeh.




More comment more typing ✍️

Domin talla, ko ƙorafi ko gyara a tuntuɓe ni ta wannan number 09036812206


Love you all 💞 🥰

Khairat ce ✍️🤍






😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈



By


KHAIRAT 🤍




*Ga masu son a tallata musu hajarsu ko sana'arsu, su tuntuɓi wannan lambar wayar 09036812206, in shaa Allah kuna da Khairat ba ku da damuwa🙌😁*

*Assalamu Alaikum, ina shahararrun marubutan suke? Ku matso wannan magana ta ku ce. Kina rubutu amma har yanzu ba ki da tsayayyen wurin da za a miki graphic design? Toh fa ga dama ta samu, domin gwangwaje ku da graphic design mai kyau da ɗaukar ido, wanda tun kafin ma karanta su karanta littafin sun san zai yi armashi, ku tuntuɓi wannan lambar wayar 09036812206 kai tsaye domin samun na ku book cover ɗin* 😍

*Ban tsaya iya nan ba, duk dai a kan marubutan namu masu albarka ❤️, kin kammala littafi kins son a haɗa miki shi document? Wannan ma babbar dama ce domin da kuɗinki ƙalilan za'a haɗa miki document mai password ko kuma mara password, shima dai ku tuntuɓi wannan lambar wayar 09036812206*








BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM


PAGE 75-76(BOOK TWO)



*Ayaman*

Rayuwa daidai gwargwado ta mata adalci a ƴan kwanakin nan, domin kuwa, so da ƙauna wanda ba'a taɓa nuna mata a gidan mahaifinta tun bayan rasuwar mahaifiyarta ba ta na samu a gidan Tsahare, dan so suke mata tamkar ƴar uwarsu.
A'ishah ta girma ma sha Allah, ga farar fatarta kamar ka latsa jini ya fito saboda haske da ɗaukar ido da take yi.
"Ayaman!."
Tsahare da tun ɗazu take kan Ayaman ta na mata magana amma ba ta amsa ba ta furta cikin ɗaga murya.
Zumbur ta dawo daga duniyar tunanin da ta lula ta na ƙare wa Tsahare kallo.
"Me ki ke tunani haka? Ayaman kin ɗaurawa kanki damuwa wallahi yanzu meye na tunani kuma? Dan Allah tashi a yi harkoki da ke kin zo kin zauna a ɗaki ke kaɗai."

Shiru Ayaman ta yi ta na kallon Tsahare kamar bata taɓa ganinta ba, kafin ta buɗe baki da ƙyar ta ce
"Ba za ki gane ba maman Auwal."(Auwal shi ne Asalin sunan ɗanta)

"Dama ta ina zan gane tun da ban ɗaurawa kaina damuwar banza ba, ba ma wannan ba tashi ki shirya mu je amso ɗinki."

Girgiza kai kawai Ayaman ta yi kafin ta miƙe ta ɗauko hijab ta zira haɗe da sa takalminta.
Ita ma Tsaharen haka ta yi, ta kullo ɗakin saboda yara da ke hada-hada kar su je su ɓata mata.
Sallama ta yi wa mutanen gidan a kan ce wa za su je su amso ɗinki.
Sun fito kenan, A'ishah ta taho daga wurin yaran dake waje ta na ta surutanta, da alama dai wasa suke yi.
Kuka ta dasa a kan sai ta bisu, ba yadda ta iya haka ta ɗauko ta suka nufi titi.
Wurin da ɗan nisa dan haka sai da suka tare tasi suka hau suna faɗa mishi in da zai kaisu.
Shagon ɗinkin suka nufa bayan mai tasi ɗin ya sauke su, da yake Tsahare mace ce mai son ƙwasƙwas da gayu, shiyasa bata kaiwa masu ɗinkin unguwa ɗinkinta a ce war ta basu ƙware ba.

A bakin titi wurin yake, hakan ya sa ba shi da wahalar gane wa.
Maza ne a shagon sai ƴanmata da ke zuwa koyon ɗinki a wurin.
Bayan an gaggaisa telan ya fito da kayayyakin ya na nuna musu
Sun nisa wajen kallon kayan suka ji ihun mutane ana salati, a razane ta ɗago ai kuwa ƙirginta ya buga dumm sakamakon ganin abin da ya girgiza kwanyar kanta.









*FAROUK*






Alhamdulillah, jikin Ammi sai san barka, dan kuwa yanzu ta na iya motsa wa har ta buɗe idanu.
A yau ne abokansa, wanda suka haɗa da Don jezzy(Abdullahi), Kamal, da kuma Mubarak suka kawo mai ziyara ta musamman zuwa asibitin domin duba jikin Ammi.
Bayan gaisuwa da addu'oi suka tura masa naira dubu ɗari tara, da niyyar a cigaba da kula da jikin Ammi.
Ya yi kuka kuma ya godewa Allah, dan ba dan wannan taimakon ba ya rasa yadda zai yi.
Fitowa suka yi daga ɗakin da aka kwantar da Ammi, dan su wuce masallaci dan gabatar da sallar la'asar, nan fa Kamal ke shawartar Farouk ko an haɗa da maganin gargajiya a cutar Ammi? Dan akwai lauje cikin naɗi game da wannan rashin lafiyar.
Amsa masa ya yi da a'a, sa'annan suka wuce abinsu.

Kafin su tafi sai da Kamal ya bada shawarar neman maganin gargajiya, in da a nan Farouk ya amince da niyyar gobe zai kama hanyar Madobi wurin wani mai bada magani.





*NAFEE*

Rayuwar sharr abinta, babu wata damuwa, yanzu sabon saurayin da ta yi mai yaayi da kuɗi sai kashe mata zuciya yake yi.
Duniya suke ci da tsinke, babu abinda ya sha musu kai, dan ya fi Farouk komai, ita wani sa'in ma mantawa take yi da wani Farouk a rayuwarta, dan ta watsar da batun auren shi ta na shagali abinta.

Karuwa kenan!!!



Wai ni kam ya labarin NABEELA? Mu je zuwa.



*NABEELA*



Gidan Alhaji Gabatari na nufa, babban gidan mai cike da kayan alatu na rayuwar duniya taƙaitacciya! Wannan gidan saboda tsaruwarsa da kyaunsa ba za ka taɓa aiyanawa a ranka akwai wani mahaluƙi da zai sha wahala a cikin wannan gida.

Ilai kuwa, Nabeela na mawuyacin hali a wannan tamfatsetsen gida. Kwance ruff da ciki na same ta a kan tiles, dan yanzu baby chakwai ya dawo da ita wani ɗaki a chan ƙarshen gidan ba tare da sanin Alhaji ba.

Kallo na ƙare mata tsaff, ba dan tsayin da take da shi ba, haɗe da faffaɗan kwankwaso da wallahi na ce ba Nabeela ba ce, wata halittar ce daban, ta rame ta jeme, banda istigfari babu abinda ke iya fita daga bakinta, shima kuma ba dai-dai take iya faɗa ba.

"Astangafurullah." Ta ke ta maimaitawa, sannan ta cigaba da faɗin
"Kaicho duniya! Mai kyalkyalin banza, ban taɓa zaton duniya za ta juya min baya ba, duniyar da na yi sabon Allah dan in mallake ta ga shi ta juya min baya, ta rikiɗe ta zama wani abin daban! Na bi san zuciya da kuma huɗubar uwa kamar Ladiyo na yi shirka, babu ilimin addini, ban san komai game da Allah ba, ga irinta nan, yanzu zama ma ya gagare ni, wayyo ni."
Ta na ƙarashewa ta kece da wani irin kuka mai cike da nadama da ciwo, tabbas a tunaninta yanzu kam rayuwarta ta zo ƙarshe ba ta da wani amfani.

Ta na cikin kukan ta jiyo hayaniya mai tarin yawa daga waje, daddafewa ta yi ta miƙe sai ga wani ruwa mai yauƙi da warin gaske ya zubo daga hq ɗin ta.
A hankali ta bi ruwan da kallo ta na sake fashe wa da wani irin kuka, window ta kalla, abinda ta gani ya sa ta kuma murza ido domin tabbatar da abinda take gani, ƴan sanda! Ta faɗa da ɗan ƙarfi.
In kuwa ta tabbata ƴan sanda ne , lallai addu'ar ta bata faɗi ƙasa banza ba, duk da ta na da tabbacin bai dai-dai take addu'ar ba saboda ƙarancin ilimin addini.

Iface-iface ta ke jiyowa daga falo, ta yi ƙoƙarin fita amma ba dama tun da ƙofar a garƙame take.

Ihun neman taimako ta kurma wanda ya taimaka wani daga cikin jami'an ya jiyo ta, kofar yake ƙoƙarin buɗewa amma a kulle take, ya saita harsashinsa a wurin mabuɗin kofar ya harba, sannan ya samu bude ƙofar.

Wani wari da ya ziyarce shi ne ya yi sanadiyar ja baya da ya yi, ita kuma Nabeela da jan ciki ta fito wajen.

Ƙare musu kallo take yi ɗaya bayan ɗaya, jami'ai ane wanda ya tabbatar da ba yan sanda bane amma sun fi kama da jami'an NDLEA wato hukumar yaƙi da sha da kuma sufurar miyagun ƙwayoyi.
Manyan mutane ne, Alhaji Ahmed , Alhaji Abubakar, Alhaji Mamman, da kuma Alhaji Gaɓatari, sai baby chakwai da ke gefensa, wata jaka ce a gabansu wadda da alama miyagun kwayoyi ne (cocaine) suna rabawa a tsakaninsu, wanda bata daɗe da shigowa ƙasar ba.

Ba tare da ɓata lokaci ba aka yi motar jam'ian da su gaba ɗayansu, ita kuma Nabeela aka wuce da ita asibiti.





*Ladiyo*

Ladiyo ikon Allah!

Tun bayan abinda ya faru, bayan sati biyun sun cika ta tattara kayanta ta nufi shagon Sadeek, bayan sun gama tattaunawa a kan hakan.

Nan fa suka ɗaura aure a tsakaninsu, suke kuma cin karensu babu babbaka.

*Sati uku bayan tarewar ta a shagon Sadeek.*

Tafiya take a hankali kamar ƴar maye, haka dai ta daddafa har ta ƙarasa babban asibitin ƙauyen.


Kwana biyun nan zazzaɓi mai zafi take yi hade da wata irin gudawa kamar ruwa, ga ciwon kai mara misaltuwa, da ciwon jiki da dai sauransu.
Bayan fuskantar wulaƙanci daga wurin ma'aikatan asibitin ta samu aka ɗebi jininta, biyan kuɗin test din ta yi.

Bayan sakamakon ya fito aka tura ta ganin babban likita, shima a wurin sai da ta daɗe kafin ta samu shiga office ɗin.

"Wasu alamu kike ji ko sauyi a jikinki?"
Likitan ya tambaya bayan ta zauna.

"Likita ni kaina na fuskanci chanje-chanje a yanayin jikina, ina yawan yin amai, kasala da ciwon jiki, sai kuma zazzaɓi, sannan kuma ka ga yadda tafukan hannayena suka yi."

Ta karasa ta na nuna mai tafukan hannayenta da suka sauya launi suka koma yellow.

Tashi likitan ya yi ya matso kusa da idanunta, ya haske wata ƙaramar fitala, sannan ya koma.

Cike da gajiya da kuma kasala Ladiyo ta buɗe baki ta fara ce wa

"Likita ka gaya min me yake damuna, na zata malaria ce da na saba yi, amma da na je Chemist ɗin Hamisu ya bani maganin malaria na sha na ji ban warke ba, kawai na garzayo asibiti."

(Da yawan mutane su kan alaƙanta ƙanƙantar cuta da malaria, wanda ba haka bane, kamata ya yi a daure a je asibiti a gwada kafin a sha magani, Allah ya kyauta)

Ƴan rubuce-rubucensa likitan ya yi kafin ya ɗago ya kalle ta ,
"Ki na da aure?"

Ɗago wa ta yi ta amsa mai da "ehh"

Kuma rubutun ya yi kafin ya ce,
"Mijinki na bin mata ne?"

Banbarakwai ta ji maganar, hakan ya sa ta ɗan haɗe rai tare da furta
"Wannan wace irin tambaya ce likita? Cewa na yi ka duba ni ba wai ka zo kana tambaya ta mijina na bin mata ba ko shigen haka."

Furzar da iska likitan ya yi sannan ya ce
"A gaskiya a iya binciken da na yi, ya tabbatar da kina da ɗauke da cutar hepatitis B."

Da ayar tambaya ta ce
"Me hakan ke nufi likita?."

"Cuta ce da ake ɗaukar ta ya yin da wata mu'amala ta haɗa ka da mai wannan cutar, tana addabar hanta ne, kuma a iya bincikenmu ta fi cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV illa."

Salati Ladiyo ta rafka ta na zubewa a ƙasa tare da fashewa da kuka, ita kalaman likitan ne ya fi daga mata hankali, ta fi HIV ILLA? Akwai tashin hankali.

Likitan ya cigaba da faɗin
"Wannan cuta ba wai ta na nufin ƙarshen mutum ne ya zo ba, a'a, za ka iya magance ta tun kafin ta yi ƙarfi a jikin mutum, amma ga wasu daga cikin hanyoyin da ake ɗiban wannan cuta
*1- Ta hanyar kitso ko aski, wannan ƙarfen na riƙe cuta sosai, kuma wannan virus na hepatitis na zama a jikin ƙarfe na tsawon awa 7 zuwa 8, kuma da zarar jini kaɗan ya taɓa ƙarfen, shikenan dan ita ba ta raina wurin.*
*2- Amfani da banɗaki mara tsafta, tabbas ƙazanta na da kaso mafi girma a wanzuwar wannan cutar*
*3- Na uku kuma mafi girman hanyar da ake kwasar wannan cuta ita ce, hanyar saduwa da mai irin wannan cutar, ko yaya take kuwa.* Dan haka ku kare kanku daga saduwa barkatai da mutanen banza.


Haka dai Ladiyo ta taho hanya riƙe da sakamakon gwajin a hannunta, ga yunwa ga cutar da ke nuƙurƙusarta.
Siraran hawaye ne ke zuba daga kurmin idanunta, Yanzu ina mafita?







Sai mun haɗu a next page more comment more typing ✍️



*SHALELEN JAJIRTATTU CE (KHAIRAT)*




😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈



By




*KHAIRAT(SHALELEN JAJIRTATTU)*




*BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM*


*PAGE 77-78*



*LADIYO*

Ganin ba ta da wata madafa ya sa ta nufi shagon Sadeek, a zaune ta tarar da shi ya na shan garin kwaki da ya ji gyaɗa da kuma madarar gari.
Zama ta yi kusa da shi cike da sanyin jiki, shi kuwa gogan ko kallon in da take bai yi ba.
Dama ta lura a kwanakin nan kawai dai ana rayuwa ne, amma sam Sadeek ya daina damuwa da ita, ban da danne-dannen waya ba abinda ya iya ko kallon arziƙi ba ta samu daga wajensa.

"Sannu da gida." Ta furta murya a karye kamar mai shirin yin kuka.

In kun tanka toh shima ya tanka, haka ya yi banza da it.

Wani malolo ta haɗiye kafin ta miƙa mai takardar sannan ta ce
"Dama asibiti na je ga sakamakon nan." Ta faɗa sai kuma ta rushe da wani irin kuka mai ban tausayi.

Fizge takardar ya yi, kana ya buɗe ya karanta.
Wani murmushin makirci ya saki kafin ya cilla mata takardar ya cigaba da abinda yake yi.

Tsayawa ta yi ta na ƙare mai kallo, toh me yake nufi da hakan bai damu ba kenan?









*Farouk*




Washegari ya tashi da shirin nufar hanyar madobi tare da Kamal domin ziyartar wani mai bada maganin gargajiya musamman abinda ya shafi tsibbu ko asiri.



Ya kwantar da kansa a jikin kujerar mai zaman banza yayin da Kamal ke tuƙin motar .

Wani wawan birki da Kamal ya ja ne ya yi sanadiyar bige kansa da jikin motar.

"Innalillahi wa'inna i'laihi raji'un."
Da Kamal ke ta maimaitawa ya sa shi fitowa da sauri daga cikin motar.

Wata kyakkyawar farar yarinya wacce ba za ta gaza shekara ɗaya ba ya gani kwance jikin jini a kwalta.
Wasu mata biyu ne suka iso wurin, ɗayar da ya fi tunanin ita ce mahaifiyar yarinyar ta zube sumammiya a wurin sakamakon wannan mugun ganin da ta yi,ɗayar kuma cike da ruɗu take tashinta.










*AYAMAN*



Salatin da suka jiyo ne ya sa su ɗagowa daga kallon ɗinkin suka kalli wurin da mutane suka taru.
Gefenta ta kalla ta ga babu A'ishah a wurin, zuciyarta ta buga dumm!!! Ta nufi wurin da ta ga mutanen Tsahare na take ma ta baya.

A'ishah da ta gani kwance a kan kwalta ga jini duk jikinta ya sa ƙwaƙwalwarta ɗauke wa kafin daga bisani ta rasa in da kanta yake.







*NABEELA*



Tun san da ma'aikatan hukumar yaƙi da sha da kuma fataucin miyagun ƙwayoyi wato NDLEA suka ɗauke ta zuwa asibitin ta kasa gane wani hali take ciki.

Idanunta ta lumshe sannan ta ƙara buɗesu tarr a ɗakin asibitin da take ciki, farin fenti da fararen zanin gado ya daki idanun nata ta damƙe su ƙam, kafin kuma a hankali ta buɗe su ta na ƙarewa ɗakin da take ciki kallo.


Sai mun haɗu a next page more comment more typing ✍️🤍.


Khairiyya ce💘🌹


😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈





By



*SHALELEN JAJIRTATTU ()KHAIRAT()*





BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM



> *PAGE 79-80*




Wai ya labarin DELU ne?


Ta ɓangaren Deluwa kuwa, abu babu daɗi sam, asirin da ta yi wa Malam Surajo ya karye sakamakon ruwan sama da aka sha a wani daren Lahadi har ya yi sanadiyyar rugujewar kabarurruka a maƙabartar ɗandolo ta garin.
Ta gane hakan ne sakamakon masifa da faɗa da Malam Surajo ya shigo gidan ya na yi mata, ta tanka, ai kuwa ya hau zage-zage da tsinewa Delu, ga wasu daga cikin kalaman da yake faɗa.
Lbl
"In ba dan aikin asiri ba, ina ni ina ke Delu, matsiyaciya la'ananniyar Allah kawai, wallahi ki je za ki gani, dan haƙƙina da na sauran mutane ba zai taɓa barin ki ba."
Sai kuma ya yi shiru ya na mayar da numfashi, Delu da tunda ya fara magana zufa take tsatstsafo mata daga dukkanin wata kusurwa ta gashi a jikinta.
Da ƙyar dai ta buɗe baki dan ta tabbatar da ko asirin har yanzu ya na nan ta ce
"Ka ga Malam ba fa kai matsayin da za ka zo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login