Showing 3001 words to 6000 words out of 23389 words

Chapter 2 - Mugunta 2 Complete Hausa Novels By Khairat.txt

KHAIRAT   

13 Mar 2026

9

ɗakin take yi yayin da ta lula duniyar tunani.
Wai Mariya ce zata ɗaga hannu ta mare ta? Har yanzu ta kasa yadda da hakan, lallai kuwa in haka ne maganar boka ta tabbata, na cewa zasu gani a kan ƴaƴansu.

Ƙarar abubuwa da ake bige wa a tsakar gida ne ya dawo da ita daga tunani, "Wallahi ba ni ne ubanta ba, uwarta ce kuma tana ɗaki." Ta jiyo muryar Malam Surajo cikin tashin hankali.

Wasu riƙaƙƙun ƴan daba ne suka hankaɗo yadin dake jikin ƙofar, "Ke ce Delu ko? " Wani saurayi ya faɗa wanda da alama a bige yake.

Kasa magana tayi, wani uban mari ne ya daki fuskarta, kafin ta fara jin saukar wasu mugayen makamai tun tana iya gani har ta ji ƙittt bata ji bata gani.

Sai da suka mata liss kafin suka fice suka bar gidan.
Ko da ta farka sai gani tayi gari har ya waye dan sanda ƴan daban suka zo dare ne, ƙoƙarin tashi tayi taji ƙissss ƙashinta ya yi wata ƙara kuma sumewa tayi a wurin.


A taƙaice dai sai da Delu ta kai kusan kwana biyu kafin wani daga cikin ƴanuwanta ya leƙo gidan ya tarar da ita.

Mai gyaran ƙashi aka kira ya ja mata wanda a wurin Delu tayi fitsari yafi a ƙirga, da guntayen kashi da ta saki.

Mariya kuma tayi ɓatan dabo, babu ita babu labarinta, duk ƴan kuɗin Delu ta kwashe da sauran kaya masu muhimmanci.



*Cigaban labari*

"Washhh Amina ki bini a hankali mana." Delu ta faɗa yayin da ake ƙoƙarin tayar da ita domin yin wanka.
Yarinyar da aka kira da Amina ta yatsina fuska ganin fitsarin da Delu ta jibga a kan shimfiɗarta.

"Wallahi na gaji, babba da ke ba yarinya ba ki rinƙa sakin fitsari a kwance, habaa." Amina ta ƙarasa cike da mita.

Amina wata ƴar yar Delu ce da ke wani garin da zama, aurenta ya mutu shine aka kira ta domin ta rinƙa kula da delu har ta warke.
Haka dai ana masifa ana bala'i aka kammala wanka.



********************************




*Ummu Kulsum*


*WAIWAYE*

Tun lokacin da ta fito daga gidan domin nemowa Nafee fruit tayi hatsari mota ta bige ta.
Ɗanta Mu'ayyad take a wurin Allah ya ƙarɓi abinsa yayi da ita kuma ta samu matsalar ƙashin baya.
Ta kwanta a asibiti na kusan wata uku, rashin kula daga ɓangaren danginta yasa aka mai da ita gidan gajiyayyu.
Dan sai a yi sati babu wanda yazo ya ga lafiyar jikinta dan kusan kowa za'a iya cewa ya manta da shafinta da wata maƙociyarta da take ɗan zuwa akai-akai.

Tana gidan gajiyayyu ba um ba um um bata iya magana bata iya motsawa.
Iya takaicen da Nafee ta ƙunsa wa rayuwarta ya ishe ta komai, ta raba ta da gidanta, ta raba ta da mijinta ga shi ta raba ta da lafiyarta, wallahi Allah yana gani baza ta iya yafewa Nafee wannan tarin laifukan da tayi mata ba.

Kamar kullum tana kwance a kan gado, hawaye na zuba daga kurmin idanunta, ta ƙura wa ceiling idanu, nurse ɗin dake kula da su ce ta shigo.
Direct wurin Ummu ta nufa, goge mata hawaye tayi tana girgiza mata kai.

Wata nurse ce ta kuma shigowa ɗakin, da yake akwai gajiyayyu da yawa kusan su shida a ɗaki ɗaya.
"Wace ce Ummu Kulsum Hamza?"
Kallo Ummu ta bi ta da shi idanunta duk sun zaro waje.
Nurse ɗin dake gefen Ummu ce ta amsa da cewa "Gata nan."

Farar takarda wannan nurse ɗin ra miƙa wa ɗayar nurse ɗin, "Saƙo ne aka kawo mata." Sannan ta fice.

Buɗe takardar nurse Haleemah tayi, hawayen da bata shiryawa ba ne suka zubo mata.

"Ni Farouk Aliyu Datti na saki matata Ummu Kulsum Hamza saki biyu."
Abinda ke rubuce a jikin takardar kenan sai signature ɗin Farouk.

Kuma kallon Ummu nurse Haleemah tayi, duk ta lalace ta fita hayyacinta, wannan yawan tunanin ma ya isa ya zugar da ita , take wani kukan ya kuma kufce mata kawai ta miƙe ta fita daga ɗakin.
Tana tsananin tausayin Ummu yarinya mai shekaru ƙalilan ta shiga irin wannan masifa.
Da ido Ummu ta bita haka kawai taji zuciyarta na bugawa da sauri.






(Allah sarki Ummu 😭❤️‍🩹)





*Nafee(p.o.v)*






Sai mun haɗu a next page more comment more typing ✍️


Khairat ce ✍️🤍.


Love you all 💞 🥰




😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈



By




Khairat 🤍✍️


https://chat.whatsapp.com/Js1xb4FBd2v0o5mxXpssVr
*(Posting room)*

*My WhatsApp group comment section 👇 👇 👇*

https://chat.whatsapp.com/FYbZw86FTfQDpyIkILlMuN



💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.

_With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.🤌💪_



BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM


Page 57-58 (BOOK TWO)




*Nafee(p.o.v)*


Duniyar Allah, duniya tayi mata daɗi komai na tafiya tsaff, yanzu ma suna ƙasar Dubai a Abu Dhabi, wani wurin shaƙatawa ne ya mutane manya da yara.
Sun ci sun ƙoshi ita da Farouk tana kwance a jikinsa suna taɓa hira, yanayin mai kyau ne, ga iska na kaɗawa a hankali.
Tashi suka yi suka nufi wani wurin da ake ɗaura mutane a kan raƙumi suna zagaye wurin, biya suka yi suka hau kai, wayarta ta miƙa wa wasu ma'aurata dan su ɗauke su hoto.

Haka suka dinga zagaye wurin cike da nishaɗi da ƙaunar juna yayin da wannan ma'auratan ke ta ɗaukan su hoto.



*WAIWAYE*

Tun lokacin da ta aiki Ummu Kulsum siyo fruit tayi sauri ta kira Lubna a wayarta, "Hello Nafee." Lubna tayi magana ta ɗayan ɓangaren.

"Wallahi ta tsallaka maganin." Nafee ta faɗa tana leƙa Ummu da ta kusan kai bakin gate.
"Ayyiriri, toh albishirinki ita da dawowa gidan nan lafiya har abada, ta tafi kenan." Lubna ta faɗa ta cikin wayar.
Sakin wayar Nafee tayi tana ihun murna, shikenan, ta gama da Ummu Farouk ya zama nata ita kaɗai.

Haka ta zauna cike da murna dan ji take kamar an mata hajji da umara.


Tun daga lokacin Farouk ko kuma tambayar Ummu be yi ba bare ƴan uwansa su Ammi.
Suka kuma shiga duniya suna yawon shakatawa da cin amarci....



*CIGABAN LABARI*

Kwanan su ashirin da biyu a Abu Dhabi suka dawo gida Nigeria.



*Farouk*

Kwana biyu ko bacci kirki baya iya yi, mafarkin wata mata yake da yaro a hannunta suna kuka suna neman taimakonsa, yana ji yana gani suka tafi daga wurinsa.

Kullum cikin tunani yake, gani yake kamar akwai abinda ya rasa a jikinsa, haka kawai yake jinsa ba dai-dai ba.
Da ya matsawa kansa da tunani sai kansa ya fara ciwo, duk ya daburce ya rasa mai yake mai daɗi.



Asiri gaskiyar mai shi.....




*Amarya Nabeela*


Shiru ba wanda ya leƙo ɗakin, kuma ga hayaniya na tashi a falon, leƙawa tayi ta kofa, maza ne danƙam a falon sai Alhaji Gabatari da ta gani a zaune kan kujera cikin babban kaya sai kuma wani saurayi a gefensa.

Alhaji Aminu da Alhaji Ahmed kawai ta sani a wurin sai kuma wasu manyan mutane, fatan alkhairi taji ana ta yi ana fatan Allah ya basu zaman lafiya, duk a zatonta a kan aurensu ake yi.
"Baby chakwai Allah ya baku zaman lafiya." Taji muryar Alhaji Ahmed yana dariya.
Wanda aka kira da baby chakwai ne ya rufe fuskarsa alamar kunya.
Kan Nabeela ne ya kuma ɗaure wa, sakamakon ganin Alhaji Gabatari ya kai wa wannan saurayin da aka kira baby chakwai kiss.
Idon baby chakwai ne ya kai kan Nabeela dake tsaye, yatsina fuska ya yi kana yace " Alhaji wannan fa." Ya faɗa yana nuna Nabeela.

"Ni ce nan matar gidan." Nabeela ta faɗa cike da rashin kunya.
Marin da baby chakwai ya wanka mats ne ya sa ta yin shiru, Alhaji Gabatari ne ya janyo baby chakwai, " Ki kwantar da hankaliki, wannan ƴar aiki ce na ɗauko miki."

Kuka Nabeela ta fashe da shi tana shigewa cikin ɗaki, su Alhaji suka cigaba da sharholiyarsu har dare ya tsala taro ya watse.


********************************

*Ladiyo*


Fess zuciyarta, abinda ta daɗe tana shiryawa ya tabbata, a ƙarshe dai Ayaman tayi abinda ko kare baze ciza ba.

"Yanzu aka fara wasan....."
Ta faɗa.



********************************


*Ayaman*

Bayan tayi wanka taji wani daɗi a jikinta amma mararta da gabanta sai zugi suke.

Kuma kallon jaririyar dake hannun ummansu Tsahare tayi, ta kuma sakin wasu hawayen .
Umman Tsahare tana gefe riƙe da yarinyar taji wani bugun ƙofa, a zatonta yaran ne suka dawo hakan yasa ta yi biriss da su.

Muryar baban su Tsahare da ta ji ne ya sa ta saurin miƙewa domin buɗe masa.
"Wannan karuwar zaki ajiye min a gida, toh wallahi baki isa ba dalla malama tashi ki fitar min daga gida." Baban su Tsahare ya ƙarashe faɗa yana kallon Ayaman.
Razana Ayaman tayi ta miƙe cikin hanzari ganin yadda baban su Tsahare yake zare idanu.

"Haba malam..." Bata ƙarasa faɗa ba yace
"Ki ka kuma magana a bakin aurenki sai ki zauna da ita."

Haka Ayaman jiki na rawa ta goya jaririyar ta fice da sauri.

Ai kuwa tana fita kamar jira suke yaran suka fara bin ta suna mata ihu, ganin babu inda take da shi sai gidan mahaifinta ya sa ta nufar gidan.
Tana isa ta shiga ɗakin Ladiyo in da mahaifinta yake zaune cikin tashin hankali.
Durƙusawa tayi ta fara kuka mai taɓa zuciya, tsakanin ɗa da mahaifi sai Allah, duk da asirin Ladiyo amma Malam Isyaku yaji tausayin Ayaman sosai.
"Baba.... Dan Allah ka saurare ni, wallahi zan gaya ma waye uban yarinyar nan." Ta ƙarasa cikin kuka.
Juyowa Malam Isyaku ya yi yana kallon Ayaman.

Ta buɗe baki ta fara magana kamar haka.....






Sai mun haɗu a next page more comment more typing ✍️ 🤍


Khairat ce ✍️🤍




Love you all 💞 🥰





😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈



By



Khairat✍️🤍

*(Posting room)*
https://chat.whatsapp.com/Js1xb4FBd2v0o5mxXpssVr

*My WhatsApp group comment section 👇 👇 👇*
.https://chat.whatsapp.com/FYbZw86FTfQDpyIkILlMuN


💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.

_With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.🤌💪_


BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM



Page 59-60(BOOK TWO)




_______Ihun da Ayaman ta saki be ya janyo hankalin Ladiyo wacce shigowarta kenan.

Shigowa ɗakin tayi da gudu ta tarar da malam Isyaku riƙe da zuciyarsa jini na fita ta hanci da bakinsa, sai Ayaman dake gefe tana matsanancin kuka.

"Kashe uban naki kika yi? Innalillahi wa'inna i'laihi raji'un." Ladiyo ta faɗa cikin tashin hankali.
Ita ma kukan ta fara suka saka Malam Isyaku a gaba suna rusa kuka, "Allah yaaaa miiiikiiii aaallbarkaaaaa....." Malam Isyaku ya faɗa a ɗan rarrabe, kafin ya cika da imani, Allah ya karɓi abinsa.

Sun kai kusan minti goma a ɗakin kafin Ladiyo ta fita ta fara kwantsama ihu.

"Innalillahi, ta kashe shi, wallahi Ayaman ce, ta kashe shi, ." Haka ta rinƙa ihu.

Kafin kace me gidan ya cika mutane na sauraren surutan Ladiyo wanda ko ganewa ba sa yi, wasu manya aka samu aka wanke gawar Malam Isyaku wanda da ƙyar aka raba Ayaman da ita.

Haka ana rirriƙe Ayaman aka fita da gawar aka sallace ta aka kai ta gidan gaskiya.

Ana dawowa aka fara tsegumi a kan mutuwar, wasu na zargin Ayaman ce ta kashe shi wasu kuma suna ganin bazai taɓa yiwuwa ba.

Nan fa aka samu wasu marasa kunya daga cikin samarin garin suka shiga har gidan suka fara yi wa Ayaman video a kan cewar tayi cikin shege kuma ta hallaka mahaifinta har lahira, domin posting a kafafen sada zumunta domin samun mabiya.

Washegari sai ga Yunusa da muƙarrabansa, wai sun zo gaisuwa, haka dai suka gama shirmensu suka tashi.

Haka aka yi zaman makoki na ranar ɗaya, washegari Ladiyo da Yunusa suka tada bala'i wallahi sai Ayaman ta bar gidan.

Kai tsaye fadar mai gari aka nufa dan Tsahare ta tsayawa Ayaman dole sai ta samu wani kashi na gidan dan tayi amanna cewa Ayaman na da gadon gidan.

Ana isa mai gari ya turo da mutane domin a yanka gidan a ga wani kashi Ayaman take da shi, ay kuwa aka tabbatar da rabi da kwata na ɗakin da take ciki nata ne ƙwata ne na su Ladiyo.

Nan aka ƙarƙare cewa Ayaman zata dinga biyan kuɗin hayar wannan ƙwata dan Ladiyo ta rantse baza ta bar ta kyauta ba.

Ana kammala rabon gidan sai ga su Addah Asiya dan sun samu labarin rasuwar Malam Isyaku.
Da gudu Ayaman ta riƙe su, jaririyar da suka gani a hannunta ne ya ɗaure musu kai.



Har yanzu dai, wane ne uban yarinyar nan?????




********************************



*Ummu Kulsum*

Bacci take mai daɗi, kawai taji alamar ana tashin ta, wata baƙar halitta ta gani mara kyau ga muni.
Tsurawa halittar kallo tayi, ga dare ga kuma ba bakin magana, shaƙe ta wannan halittar tayi.
Ta kasa motsi ta kasa ihu, sunan Allah kawai take faɗa a zuciyarta.
Cikin ikon Allah ta ji shaƙar tayi sauƙi, hamdala tayi a zuciyarta ta cigaba da kiran sunan Allah a zuciyarta.
Idonta biyu har asuba tayi gari ya fara wayewa, nurse Haleemah ce ta shigo fuskarta ɗauke da damuwa.
"Ummu, ya kk?" Ta tambaya tana ƙoƙarin yin murmushi.
Hawaye ne suka zubo mata, saurin share su tayi sannan ta ɗaga Ummu ta kai ta banɗaki tayi brush tayo fitsari sannan ta ɗauro alwala.
Dawo da ita ɗakin tayi ta chanja mata kaya ta kwantar sa ita ta tayar da sallah a kwance.




********************************



*Nafee & Farouk*

Kwance take a kan cinyarsa, "Babe, ka ga wata yarinya tayi cikin shege ta kashe ubanta." Ta faɗa tana nuna mai wayar.

Taɓe baki Farouk ya yi, dan wallahi a gajiye yake haka jiya ta hana sa bacci kwana suka yi suna abu ɗaya har ya gaji duk da kasancewar yana da buƙata sosai.

*******************************


*Nabeela*

Tun da ta shige ɗaki bata kuma fitowa ba, kwanciya tayi a kan gadon abinka da ba'a saba ba duk sai ta takura ta sauko ƙasa.
Shiru tana jira taji shigowar Alhaji Gabatari kasancewar yau ne daren su na farko.

Har ta gaji tayi bacci.

Gari ya yi haske sosai san da ta tashi, dan rana ta game ɗakin da take ciki, a hankali ta buɗe idanunta, miƙewa tayi ta fita domin samar wa kanta abin da zata ci.
Alhaji Gabatari da baby chakwai ta gani a falo, baby chakwai namiji ne cikakke amma farin fata ne da shi kamar na bleaching.
"Kehh!!!" Ta jiyo muryar baby chakwai yana kiranta.
Tsaki ta ja ta rinƙe buɗe kofofin domin nemo ta kitchen.
Tsawar da Alhaji ya buga mata ne ya razana ta kaɗan, amma da yake rashin kunya ta cika ta sai ta mai banza.
Tashi Alhajin ya yi ya chafko ta, maruka ya sakar mata kafin ya fara jibgar ta kamar Allah ya aiko sa.
"Wato ko kin zata ban san dan kuɗina kika aure ni ba? Na zo ina son Mariya ku ka yi asiri ke da matsiyaciyar uwarki a zaton ku zaku mallake ni, hehehe." Alhaji ya ƙarasa cikin wata shaƙiyiyar dariya.
Duka suka haɗu suka yi mata ba na wasa ba dan har jini suka fitar mata.
Barin falon suka yi, ita kuma ta ja jiki ta shiga ɗaki.
"Allah ya isa tsakani na da ke Ladiyo kin cuce ni ." Abinda take ta maimata wa kenan cikin kuka.
Wanke fuskarta tayi ta fito falon, ƙofar fita ta nufa ta fice, har ta kai bakin get wani ɗan sanda ya hankaɗo ta da ƙafa, ai kuwa ta faɗi ra bige kai.
"Dan Allah ka barni na tafi gida, dan Allah." Abinda ta roƙi ɗan sandan kenan amma ko ɗigon tausayi babu haka dauko bulala zai dake ta in bata tafi ba.
Ganin ga ciwon dake jikinta taya za ta kuma bari a jibge ta, hakan ya sa ta nufi ciki da gudu.


Tunda ta shige ɗaki bata kuma fitowa ba, chan taji fitar Alhaji, kafin taji ana murɗa ƙofar ɗakinta.
Baby chakwai ne ya shigo, wani mayen kallo yake bin ta da shi.
Tuno irin dukan da ta sha ɗazu, ya sa ta fara ja da baya.
Matsowa baby chakwai yake yi ita ma tana ƙara matsawa.
Janyo ta ya yi da karfi, hakan ya sa ta saki wani ihu zuciyarta kamar zata fito.
Yakice rigar dake jikinta ya yi, taɓe baki ya yi "Ji bi jikin naki ko kyen gani babu, duk kin yamushe sai kace tsohuwa amma bari nayi maleji." Ya ƙarasa faɗa yana kai wa na shanunta chafka.
Wani ihun ta kuma saki, cire kayansa ya yi, ya juyo da ita, ɓaƙar azabar da ta ji a duburarta ya sa ta sume wa.....




Sai mun haɗu a next page more comment more typing ✍️


Khairat ce 🤍✍️




Love you all 💞 🥰










😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈


By


Khairat ✍️🤍



https://chat.whatsapp.com/Js1xb4FBd2v0o5mxXpssVr
*(Posting room)*


*My WhatsApp group comment section 👇 👇 👇*


https://chat.whatsapp.com/FYbZw86FTfQDpyIkILlMuN



💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.

_With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.🤌💪_



BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM

Page 61-62(BOOK TWO)



________ A taƙaice dai Nabeela ba ƙaramar azaba ta sha ba a wurin baby chakwai, ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login