Showing 12001 words to 15000 words out of 23389 words

Chapter 5 - Mugunta 2 Complete Hausa Novels By Khairat.txt

KHAIRAT   

13 Mar 2026

11

baya.
Su na tafe su na hira abinsu, kwatsam sai ga Anas ya zo wucewa a babur ɗinsa, tsayawa ya yi suka gaisa da tsahare yayin da Ayaman ta sunkuyar da kanta ƙasa ta kasa ɗago sa.
Shima ganin hakan ya sa ya ja babur ɗinsa ya yi gaba ko waigowa bai yi ba, siraran hawaye ne suka zubo mata daga kwarmin idanunta.
Dafa ta Tsahare ta yi tana faɗin
"Ayaman ki kwantar da hankalinki dan Allah, ba komai bane rabuwarku, in shaa Allah alkhairi ce ita kuma wannan yarinya Allah ya raya ta."
Shiru Ayaman ta yi bata amsa mata ba, Tsahare ta cigaba da faɗin
"Amma Ayaman, waye uban wannan yarinyar?"
Shiru Ayaman ta yi ta kasa magana, zuwa chan Tsahare ta kuma buɗe baki ta ce
"Amma dai Ayaman na zata ko zaki ɓoye wa kowa abu ni bai kamata ki ɓoye min ba, hmmm amma dai shikenan."

"Tsahare , ba ɓoye miki nake ba, wallahi ina cikin tsaka mai wuya, halin da nake ciki ba mai bayyanuwa bane." Ta yi shiri kuma kamar Malam ya ci shirwa.

Haka suka cigaba da tafiya har suka iso babbar tashar garin, inda kowa ya fito a na ta hada-hada, ga masu abinci,kayan sayarwa wanda suka haɗa da kayan gwanjo, kayan koli da dai sauransu.
Motar garin su Tsahare suka nema wato Madobi, babu ɓata lokaci suka kama hanya dan dama motar a cike take mutum biyu a ke nema.
Tafiyar awa ɗaya da rabi ce tsakanin ƙauyen hazdabe zuwa Madobi, amma da yake sun samu mota mai kyau sai gashi cikin ƙasa da awa ɗaya sun iso tasha.
Su na sauka suka kama hanya dan dama sun ri ga da sun biya kuɗin motar naira dubu ɗaya ko wanne mutum, dan haka ba ɓata lokaci suka tare mashin sai cikin unguwa

Ayaman ta samu tarba mai kyau daga wurin dangin mijin Tsahare, sai nan-nan ake da ita, da yake gidan gandu ne ma'ana gida ɗaya mai ɗauke da ahali ɗaya, sai ga matan yayye da kuma ƙannen mijin Tsahare ana ta mata kara ta hanyar mutunta baƙuwarta, duk da hakan ya zama kamar al'adar gidan har dai wata a cikin matan ƴaƴan gidan ta yi baƙuwa nan fa za ki ga ana ta shigowa ana gaisawa wasu har abinci ake kawowa baƙo nufinsu ba sai kin yi girki ba tunda ki na da baƙuwa.

Umaru, wato mijin Tsahare haifaffen karamar hukumar Madobi da ke ƙarƙashin jahar Kano ne, ya taso a gidan mata uku inda ya tarar da su du na zaman lafiya, duk da ba'a rasa ƴan saɓanin zaman yau da gobe ba.
Haka nan duk wani matashi da ya isa munzalin aure, ake yankar mai wani ɓangare na gidan tunda gidan ya kasan cikakken gidan bahaushe mai filin gaske, da tsakar gidan kansa za'a iya gina gidaje biyu zuwa uku.
A haka har shima Allah ya haɗa shi da Tsahare dalilin zamanta kenan tare da facalolinta.

Bayan sun gama gaisawa, Tsahare ta ja Ayaman zuwa ɓangarenta nan suka baje, ga gajiyar tafiya ga gajiyar azumi abin dai ba'a ce wa komai, kuma sun taki sa'a akwai wutar lantarki, nan take bacci ya yi awon gaba da su...





*LADIYO*


Farkawa ta yi daga baccin asarar, gari ya waye tangararan sai rana da ta ƙwalle wacce fita a cikinta ba ƙaramin barazana ce ba ga lafiyar mutun.
Haka ta hangame baki tana hamma, babu salati babu komai, wurin randar ruwanta ta nufa, sai dai me wayam, babu komai, ta kalli gefen ɗakin Ayaman sai yanzu ta lura da kwaɗon da ke jiki,
"Hmm, ayi mutum sai dan banzan yawo? Auren fari na ya gagara ga kuma shegiya kana goyo, tabb ."
Nan ta gama surutanta ta shige ɗaki ta fito da wani yagalgallen hijabinta wanda in aka ce ya yi wata bai ga wanki ba kar ka musa, waje ta leƙa ta ga kamar babu alamar mutane a layin, chab ta hango Zakariyya ɗan maƙociyarta, yaron bai gaza shekaru bakwai ba.
"Kai Zakariyya! Zo nan." Ta ƙwala wa Zakariyya kira.
Yana wasa da kuɗin hannunsa ya taho, askin da ke kansa ya yi solll alamar an kankare gashin sosai.
Hannu ta sa ta ɗala mai duka a kan, ai kuwa yaron ya firgice ya zura a guje yana "Allah ya isa."


Sakin baki ta yi lallai, wannan ɗan karamin yaron har yana da bakin mata Allah ya isa.
Haka nan, ba dan ta so ba ta ɗauki bokiti ta nufi bore hole ɗin garin, kamar kullum a cike ga zafi ga azumi, ta kawo hannu za ta sa bokitinta wata mata ta hankaɗe ta sai ga ta shirim a gefe, wata ƙara ƙugunta ya yi, dan haka cike da masifa ta ɗago za ta zazzage wa matar nan buhun rashin mutunci.
"Dallah malama ba ki ga kin bige ni ba? Ko ke makauniya ce ?"

Ko kallo bata ishi matar ba balle ta tanka mata, hakan kuma ba ƙaramin ɓata mata rai ya yi ba.
Kallon kayan jikinta ta yi, duk sun ɓaci da taɓon wurin ga ruwan datti, haka ba dan ta so ba sai dan bata da yadda za ta yi ta bar wurin cikin fushi.
Ta zo wucewa ta hango gidan Delu, sarai ta ji me ya faru da Delun dan har gida aka kawo mata gulma, amma ta yi biriss ta wuce ba tare da ta yi tunanin shiga ta yi mata jaje ba.

Gidan maman Zakariyya ta nufa tunda kusa ta gidanta suke kuma su na da rijiya a gidan, dan haka ba ruwansu da zuwa bore hole.

"Assalamu Alaikum." Ladiyo ta rangaɗa uwar sallamarta haɗ da kutsa kai cikin gidan.

Shiru gidan alamar ba kowa, kuma sallama ta yi ta ji shiru hakan ya ba ta damar ɗaukar gugar da ke gefe ta fara cilla ta cikin rijiyar.
"Kehh! Kehh me zan gani haka?" Ce war Binta maman Zakariyya.
"Au ashe ki na ciki ki na ji na ki kai shiru, ruwa na zo ɗiɓa."
Ladiyo ta faɗa ciki-ciki ta na cigaba da abinda ya kawo ta.

"Wallahi Ladiyo ba na son neman rigima, haka kawai ki shigo gidan mutane ki fara ɗiban ruwa ba tare da izininsu ba? Haka ake?"

Ganin Ladiyo ta yi banza da ita ya sa ta yi azamar riƙo gugar ta na wancakalar da Ladiyo a gefe, ay kuwa ta faɗi himm a wurin banɗakin gidan inda har wanke-wanke yi ake a wurin.
Nan fa suka hau faɗa da Ladiyo ana ta rigima duk da Allah ya sa matar ita ma ba daga baya ba wurin bala'i.
Haka nan ba dan ta so ba ta ja bokitinta ta yi gaba ta na sakin mugayen alkaba'ir a kan wannan rijiyar.



*NAFEE*

Babu abinda ya mata zafi, daɗinta kawai take ji, dan ma yanzu rashin lafiyar Ammi ya ɗaga wa Farouk hankali duk ya daburce.
Ganin ba wasu kuɗi ne ke shigo mata ba ya sa ta siyar da gidanta a bisa shawarar ƙawarta Lubna.
Dan haka ta cigaba da flexing ta na jin daɗin rayuwarta, ga samari da maza da take tarawa Farouk a cikin gidansa a sirrance.

"Wallahi NAFEE bana son irin wannan!!! Da aurenki fisabilillah? What kind of life is this? Sai kace s*x machine? Kullum ba kya gajiya da abu ɗaya?". Farouk ya faɗa ranar da ya kama ta da Tee boy, wani saurayinta tun kafin bikinsu.
Da dubara ta shashantar da Farouk da yake ga aikin boka, ga kuma kissa da kisisina iri-iri duk bata rabo da su.
Da ƙyar Tee boy ya fece, ira kuma Nafee ta bawa Farouk haƙuri da alƙawarin har abada ta daina kawo maza gidan.




*Nurse Haleemah*


Kamar yadda Ummu ta buƙata, bayan ta farka wuraren ƙarfe tara na dare ta yi wanka ta shirya cikin wata jar atamfa me haɗe da ash color, sai ga ta ta fito ɗass abinka da farar fata.

"Gwaggo sai na dawo." Haleemah ta faɗa tana kuma juyawa a gaban Gwaggo dan ta shaida kwalliyarta. Ai kuwa Gwaggo ta shaida, dan haka ta rinƙa yabon kwalliyar Haleema har da bata dubu ɗaya a bisa kuɗin siyan kwalliya.
Haka ta fice cikin annashuwa da ƙaunar kakar tata, ta tare napep ta gaya mai in da zai kai ta.

Direct hotoro tsamiyar boka da ke garin Kano ta nufa, babu ɓata lokaci ta biya mutumin kuɗinsa ya ja babur ɗinsa ita kuma ta shiga daidai layin da take ganin shine wanda za ta iya tunawa a mafarkin.

Exactly mai shagon ta gani, ai kuwa ta yi mai sallama haɗe da gaishesa suka gaisa cikin mutunci .
"Dama kuɗi ka ke bi na na zo ba ka."
Haleemah ta faɗa tana ciro dubu ɗaya ta miƙa masa.

Cike da mamaki mutumin ya amsa, yana ce wa
"Baiwar Allah yaushe kika karɓi bashin?"
Damurcewa Haleemah ta kusan yi tana inda inda ta ce
"Eh, ko ka manta ne ɗari biyar na amsa amma kamar ba kai ne a shagon ba."

Haka nan mutumin ya amsa ya bata chanji, ƙin amsa ta yi tana ƙoƙarin fita daga shagon.
Kichiɓis ta yi da mutum, ba ta gama tantace waye ba, ta ji tana ƙoƙarin faɗuwa ƙasa, ta yi taga-taga zata faɗi Allah ya taimaka akwai freezer a gefe sai ta yi saurin dafe ta.
Cikin fushi ta juya ko ganin mai wannan ikon, abin mamaki Farouk! Lallai ko sau ɗaya ta ga Farouk a mafarki tana zaton za ta iya tantance shi.

Hayaniyar da ta ji su na yi da mai shagon ce ta juyo da ita daga duniyar tunani,
"Wallahi ba zan baka ba, bashin dubu tara da ɗari biyu fa nake bin ka, kuma har yanzu shiru ba labari, shine za ka zo ka ce na ara ma har dubu biyar? Habaa ka yi lissafi mana Farouk."
Mai shagon ya gama faɗa yana cigaba sa harkonkinsa, ganin ba sarki sai Allah ya sa Farouk ficewa daga shagon wanda ko tantama ba ta yi hawaye ta gani cike da idanun.

"Hajiya kina buƙatar wani abun ne?"
Mai shagon ya faɗa ya na kallon Haleemah ganin ta tsaya a wurin kusan minti goma.
"Dan Allah waye wannan wanda ya fita?"

"Hmm, wannan mutumin da ki ke gani, yana ganin jarabawa, ya auro wa kansa jaraba da bala'i, ai ba ki san wani abu ba, komai na sa yana kan idonmu..." Nan fa Musa kai shago ya saki baki yana ɓarin zance, dan tun tarewar Farouk da Ummu har aurensa da Nafee.
Daga ƙarshe dai Musa ya ƙarashe da faɗin
"Ai in gaya miki da girman kai babu wanda be nuna mana ba, wulaƙanci kala-kala, matarsa kafin ta ɓace kar ki so ki ga wulaƙancin da yake mata shi da amaryarsa ba, daga ƙarshe dai ko hatsari ta yi daga nan bamu sake jin labarinta ba."
Nan suka ƙarƙare hirar, Haleemah ta kama hanyar gida da tunani kala-kala a ranta, "Dole na samo asalin Nafee!!!!." Ta faɗa a ranta.




*Ladiyo*



Tafiya take tana faɗa a ranta ƙasa-ƙasa, tana fatan wannan rijiyar ta ƙafe ko kuma wani mugun abin ta same ta.
Wasu mata ne su biyu suka zo wucewa, ay kuwa ta jiyo su su na gulmarta, abinka da mai neman kuka an jefe shi da kashin awaki nan ta hau surfa masifa da bala'i a kan hanya har ta kai ta gwada ƙwanji tsakaninsu da matan, abin asara a ka fasa mata bokitin gida biyu, kuma nan suka bar ta kamar za ta haukace.

A daburce ta yi hanyar gida tunawa da ta bar ɗakinta a buɗe kuma akwai kuɗaɗe masu yawa a kan gadon.
Tun daga nesa ta hango mutum ya fito daga gidan yana sauri, da gudu ta isa tana ihun ɓarawo, amma kash har mutumin ya ɓacewa ganinta.
Tana isa gidan ta shige ɗaki, sai dai me kuɗi suka ce ɗauke ni inda ki ka ajiye, wayam ga kaya baja-baja alamun an mata bincike, sif ta buɗe, ihu ta sa haɗe da durƙushewa tana zubewa a ƙasa sumammiya..





Amma kema Ladiyo da sakacinki, toh Allah ya kyauta sai mun haɗu da ku a kashi na gaba , na gode.

More comment more typing ✍️

Khairat ce 💙

Love you all 💞 🥰.






😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈


By



Khairat (SHALELEN JAJIRTATTU 🤍)





Posting room 👇

https://chat.whatsapp.com/HxEIWhndU7REHF43SVBdYF


My WhatsApp group comment section 👇 👇
https://chat.whatsapp.com/JNgqE1jHaacFt85y33FgDv




*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️



*BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM*



*PAGE 73-74(BOOK TWO)*




_____ "Wayyo!!! Innalillahi, ina kuɗina? Ina kuɗina?"
Abinda take ta faman maimatawa kenan tana watso kayanta.
Duk ihu da kururuwar da take yi a cikin gidan bai ishe ta ba har sai da ta fito waje tana birgima a cikin ƙasa.
Sanin hali ya sa ba wanda ya bi ta kanta, dan ita ma in wani abu ya sami mutum daga ta yi mai dariya sai Allah ya ƙara, ko ta saka ma idonta kwalli ta balbale shi.
Zuwa chan ta ta ga duk kururuwar da take ba wanda ya kula ta ya sa ta koma cikin gidan, ay kuwa tana yin arangama da kayanta ta ji zuciyarta ta ce dumm, ta kuma faɗi ƙasa sumammiya.



*FAROUK*

Rayuwa ta yi mai juyin-juyi, tabbas ya yadda da karin maganar da hausawa ke cewa ba kullum ake kwana a gado ba watarana dole a kwanta a ƙasa, toh kuwa ba shakka hakan ta faru da shi, bai gama girgiza ba sai da ya ga debit alert daga bankinsa alamar an cire mai kuɗi.
"Innalillahi wa'inna i'laihi raji'un!" Ya faɗa sakamakon ganin an ciri kuɗi daga bankinsa har naira miliyan daya da dubu ɗari takwas, wanda kaf duniya ya rantse su kawai ya mallaka a halin yanzu, bugu da ƙari ga kuɗin asibitin Ammi dan ba ta iya numfashi da kanta sai an sa mata oxcygin wanda a ƙalla a rana ana kashe mata #150, 000 kuma hakan ba ƙaramin giɓi ya yi masa a kuɗinsa ba.

Ganin yawan fashinsa ga kuma sama da faɗi da ya yi da kuɗin Company ya sa suka salleme shi, inda Allah ya taimake shi ma sun haƙura basu nemi kuɗinsu ba.
Abinda Farouk bai sani ba shine NAFEE ce ta cire wannan kuɗaɗen, a bisa shawarar Lubna, domin shi kansa Farouk bai san ta san pin ɗin cire kuɗinsa ba, haɗe kuma da babban sakacin da ya yi na barin katinsa a gida.
Haka nan ya rasa madafa ya kira Anty Haleemah, ta na ɗaga wa suka gaisa kamar kullum, sannan Farouk ya ke gaya mata abinda ya ke faruwa.
"Wallahi Farouk mu ma yanzu fama muke, kamar ka manta mijina takarar gwamna yake? Duk kuɗaɗensa ya zuba su a harkar siyasarsa, yanzu ba kamar da ba, amma turo account na sa ma ko #100,000k ne sai a sai mata magani ." Anty Haleemah ta faɗa ya yin da Farouk ke gaya mata ba shi da kuɗi a hannunsa.

Cikin kuka Farouk ke faɗin,
"Big sis #100,000k ya yi kaɗan, ko kuɗin oxygen ba zai siya mata na rana ɗaya ba, dan Allah ki taimaka, ki tuna fa mahaifiyarmu ce baki ɗaya."
Ba tare da Anty Haleemah ta kuma ce wa komai ba ta kashe wayar, ta na banbami, "Habaa, ni kaɗai ce ƴarta? Ita Raihana da ke ƙasar waje ba za'a tuntuɓe ta ba sai ni? Wallahi abinda na yi niyya shi zan saka." Ta ƙarashe cikin masifa.
Haka nan ta tura masa 100k ɗin, a ranta ta na raya irin ƙoƙarin da ta yi.

Farouk bai yi ƙasa a gwiwa ba ya kuma kiran Raihana, nan fa take zayyana masa halin rayuwar da suke ciki ita da mijinta, dan rayuwa a ƙasar waje ba abu bace mai sauƙi, yanzu ma shirin dawowa gida Nijeriya suke yi.

Haka ya haƙura ya tura wa asibitin kuɗin a ka basa magungunan Ammi, abin mamaki haka ta yini bata buƙaci Oxygen ba, Allah kenan mai duba bayinsa a duk yanayin da suke ciki.






*Ladiyo*

Sai wurin isha'i ta farka, shima kuma Sadeek ne ya tashe ta dan ya shigo gidan ya same ta baje a tsakar gida.
Ladiyo ta kai mai wata chafka ta na faɗin
"Ina kuɗina? Kaine ka ɗauke mun kuɗi ko?" Ta faɗa kamar wata zararriya.
Hannu ya sa ya bige na ta ya na faɗin "Lafiyarki kuwa Ladiyo? Anya baki haukace ba? Wasu kudi kike magana a kai?"


Ay kuwa ta zabura jin ya kuma yin maganar kuɗi,
"Wallahi sai ka biya ni kuɗina,na uwarka ne za ka ɗauka."
Sadeek ya zuciya jin ta ambaci uwarsa, ya kaure ta da wani shahararren mari wanda sai da ya sa kwanyar kanta ta daina aiki na wasu daƙiƙu.
Haka faɗa ya kaure tsakaninsu har sai da suka haɗa wa juna jini da majina.


*Kwana biyu kafin sace kuɗin Ladiyo*

Abinda baku sani ba shine, kwana biyu da suka wuce Yunusa ya shigo gari, wanda hakan ba ƙaramin ɗaga wa Ladiyo tunani ya yi ba.
Zuwansa ke da wuya ya tayar da husuma a kan shi fa ala dole sai an siyar da gidan nan tun da gadonshi ne, dan shine kaɗai yaron Malam Isyaku sai Ayaman wacce ba sa ɗaukanta a matsayin ƴa mai cikakken iko da gidan ubanta, Nabila da Nafeesa duk agololi be.

Ganin Ladiyo ta tayar da nata ruwan bala'in, ta in da take shiga ba ta nan take fita ba ya sa Yunusa cin alwashin komai dare dole a siyar da gidan nan.
Ai kuwa kiran sallar magariba ke da wuya , Yunusa da mutanensa suka dira a kan Ladiyo, manyan makamai ne a hannuwansu wanda ba karamin firgita Ladiyo suka yi ba.
Dan kare lafiyarta, dan ya san a kan siyar da gidan nan Yunusa zai iya nakasa ta har ƙarshen rayuwarta duk da kasancewarta mahaifiya a wurinsa .

Wurin Alhaji Maude, babban dillalin garin suka nufa, ba tare da ɓata lokaci ba ya turo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login