Showing 6001 words to 9000 words out of 23389 words
da Alhaji Gabatari ya dawo tayi yunƙurin gaya mai amma abin yaci tura! Baby chakwai ya ƙi bata dama.
Haka kullum cikin Allah ya isa da tsine wa Ladiyo take dan san kuɗinsu da kwaɗayi ya kai su ga wannan halin, Allah sarki, Ayaman ɗin da suke ƙoƙarin kullum su cusguna mata ga shi tana jan tana rayuwarta.
A ganinta kenan.
*Ayaman*
Bayan zuwan su Addah Asiya sun zauna sun yi magana ta kuma kai kukanta wurinsu, amma duk yadda suka kai ga naci Ayaman ta ƙi gaya musu uban wannan jaririyar.
Haka da zasu tafi suka ce ta zo su tafi tare amma ta ƙeƙashe ƙasa tace babu inda zata, tana nan a gidansu zata cigaba da kula da jaririyarta har zuwa sanda Allah ya yi.
Haƙura suka yi suka bar ta dan Ayaman mutanen nan ne masu ƙaƙƙauran ra'ayi.
Rayuwa tayi rayuwa, ta fara zuwa chan wani gida tana yi aikatau domin rufawa kanta asiri, yayin da jaririyarta ta fara girma tana yo kamarta sak.
Ta ɓangaren mutane ma bata daina samun ƙyama da hantara ba, ba hali ta fita yanzu za'a fara nuna ta da baki ana shegiya uwar shegiya.
Ba laifi kuma tana samun taimako daga gidan da take aiki, da kuma ƙawarta Tsahare ko yaya ta samu sarari yanzu zata kawo mata kaya, da sauran kayan amfani
Yanzun ma tana gidan aikinta suna aiki tana ɗan taɓa hira da matar gidan, yaran gidan ne suka dawo daga makaranta, suka taho da gudu suna rungumar mahaifiyar tasu, "Momy yau munyi karatu sosai, kuma momy ina so na zama likita babba." Babba a cikin yaran ya faɗa cike da murna.
Haka suka cigaba da hirarsu ta uwa da 'ya 'ya, kafin suka bar kitchen ɗin.
Hawaye masu zafi ne suka zubo mata, Allah sarki duk da ta san kowa da kalar ƙaddararsa a rayuwar nan, amma yawancin ƙaddarorinta Ladiyo na da kaso a kai, ta rasa me ta tsarewa Ladiyo a rayuwar duniyar nan, ta ƙwallafi rayuwarta, Allah zai saka mata.
Haka ta share hawaye ta cigaba da ayyukanta.
(Allah ya saka miki Ayaman 😔)
*Ladiyo*
Rayuwa fess, duniyar Allah ta fita takaba , duk da ba wani muhimmanta takabar tayi ba dan tana cikin takabar bata fasa zuwa wurin boka ba domin a duba mata taurarinta, a haka ya tabbatar mata da cewa tabbas zata ƙara aure amma wannan auren mai cike da abubuwa ne.
A ɗayan ɓangaren kuma bata fasa amsar kuɗin hayar Ayaman ba duk da babu abinda yake shiga tsakaninsu.
Wata rana wacce har yanzu tana ganinta a matsayin ranar sa'arta.
Ta dawo daga wurin boka kenan ta ga wata ƙaramar mota golf a ƙofar gidanta.
Har tazo zata wuce ta ji muryar wani mutum, fitowa ya yi daga motar, toh a haife dai ta haife sa dan wannan bai fi sa'an yunusa ba, shekara 23-24.
"Ranki ya daɗe har kin dawo." Ta ji muryar wannan saurayin.
Da kallo ta bishi ba tare da tace uffan ba.
"Toh Hajiyata ko amsa min baza a yi ba, in ba damuwa magana nake so muyi mu shiga daga ciki."
Nan ma shiru tayi kafin kuma ta shiga cikin gidan ya bi bayanta.
Tabarma ta shimfiɗa kafin ta zauna a kujera chan nesa da shi.
Wani kallo mai kashe zuciya ya sakar mata wanda hakan ya sa ta farat ɗaya taji yaron ya shiga ranta.
Murmushin ƴan duniya Sadeek ya yi mata ganin haƙarsa ta fara cimma ruwa.
Kalamai ya fara mata wanda ba ƙaramin sanyaya zuciyar Ladiyo suka yi ba dan tun da take ba'a taɓa zubo mata kalamai irin haka ba.
A ƙarshe dai ya ƙarƙare da cewa zai aure ta idan ta yadda.
Babu musu Ladiyo ta amince dan wani shauƙin soyayyar yaron ta ɗibe ta.
*Anya kuwa Ladiyo??? Muje dai zuwa.*
*Nafee*
Cin karenta take yi babu babbaka, dan tana fantamawa a dukiyar Farouk, ta zama oga sai abinda tace shi ake yi, tayi sharrr abinta duniya tayi mata daɗi ta manta da batun an taɓa yin wata halitta mai suna Ummu Kulsum.
Ta ɓangaren Farouk kuwa, ta ko'ina gasa mishi aya ake yi a hannu, ta ɓangaren Nafee ta sako sa a gaba indai ta tambayi abu to fa dole ayi mata shi ko rai ya ɓaci, gashi a duniyar nan in akwai abinda baya so to fushin Nafee ne, ga wurin aiki ya ci bashi duk dan biyan ɓuƙatun Nafee hakan ya sa suka basa wa'adin wata ɗaya ya tattaro da kuɗin kamfani ya dawo da su ko kuma law zata yi aiki a kansa.
*Ummu Kulsum*
Wannan abun da ya zo mata daren jiya shi ya ƙara zuwar mata, tabbas tata ta ƙare yau ba makawa zata koma wurin mahaliccinta, dan abubuwan da take gani ya tabbatar mata da cewa tabbas ba na duniya bane na lahira ne.
A hankali ta saki wani lallausan murmushi wanda hakan ya sa kumatunta lotsawa, "Allahu Akbar." Shi ne abinda take ta maimaitawa a zuciyarta tana murmushi.
Tun da dare da suka yi sallama da nurse Haleemah , jikin nurse Haleemah ya yi matuƙar sanyi dan wallahi sun shaƙu da Ummu fiye da tunanin mai tunani.
Kuma tana ji a jikinta kamar haɗuwarsu ta ƙarshe kenan, haka dai ta fita ba dan ta so ba.
Wuraren ƙarfe ɗaya na dare Ummu ta amshi kiran ubangijinta, ta mutu daren juma'a mai cike da tarin ni'imomi.
Shikenan Ummu ta rasu, Nafee hankalinki ya kwanta ta bar miki duniyar mai cike da ƙalubale iri-iri, kin rabata da mijinta, ɗakin aurenta, farincikinta, ɗanta Mu'ayyad da sauran jin daɗin rayuwa, anya kuwa zaki zauna lafiya Nafee? Anya kuwa?
Da asuba mutanen dake ɗakin suka lura da rasuwar Ummu, haka suka yi wa junansu ta'aziyya, kafin suka jira isowar nurses.
Da nurse Haleemah taji rasuwar Ummu, tayi takaici tayi baƙinciki, ta yi kuka har ta gaji dan tana matuƙar tausayin Ummu irin.
*( Irin wannan rayuwar mata da yawa suna fuskantarta a gidan miji, ƴaruwa dan kinzo a ta biyu kar kice ala dole sai kin fitar da ta farko, ko kuma ke ta farko kice ta biyu baza ta shigo ba, wannan rayuwar bata dace ba sam, hakan kuma baya daga cikin tsari da koyarwa ta addinin musulunci, in kinyi haka kin zalince ta kin zalinci kanki dan Allah maɗaukakin sarki baya taɓa yafe lefin wani a kan wani, yanzu ya kuke gani in Ummu Kulsum bata yafewa Nafee ba kuna ganin rayuwarta zata yi dai-dai? Ta raba Ummu da farincikin rayuwarta, kai hatta Farouk anya zai ga dai-dai ya yi abubuwa da yawa na ɓaƙantawa Ummu, gashi a ƙarshe ta bar musu duniyar, a kula kuma a kiyaye !!! Ƴanuwana mata kar son duniya da kuma miji ya ɗebe ki ki aikata shirka!)*
Wanka aka yi wa gawar aka fitar da ita domin sallace ta, mutuwar tayi mutane sosai dan gabaɗaya ma'aikatan asibitin maza har da wasu marasa lafiya wanda suka ji dama-dama sun halacci wannan sallar, ga mutanen bakin asibitin ga wasu da wucewa suka zo yi haka aka tafi maƙabartar ɗan sarari aka kai ta gidanta na gaskiya kowa cike da alhini.
Allah ya jiƙanki Ummu ya sa mutuwa hutu ce a gareki😢
More comment more typing
*Ga masu buƙatar a tallata musu haja zasu iya magana ta wannan number 09036812206*
*Ko kuma kawo shawara ko ƙorafi ko gyara ku tuntuɓi wannan number 09036812206*
Khairat ce✍️🤍
😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈
By
Khairat 🤍✍️
*(Posting room)*
https://chat.whatsapp.com/Js1xb4FBd2v0o5mxXpssVr
* My WhatsApp group comment section 👇 👇 👇*
https://chat.whatsapp.com/FYbZw86FTfQDpyIkILlMuN
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin swß vvvv. 1
Qwp sauƙi_.
_With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.🤌💪_
BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM
Page 63-64(BOOK TWO)
Mutuwar Ummu ba ni kaɗai ba, ta girgiza ɗaukacin masu karatun littafin MUGUNTA, tabbas Ummu ta cika ayi alhinin rashinta, amma zanso ku gane a haka labarin ya zo kuma a hakan zan rubuta sa, labarin Ummu da gaske ya faru, dan ni ganau ce ba jiyau ba, amma ku ƙara haƙuri domin jin yadda zata kaya. In shaa Allah na kusa kammala littafin nan .
__________ Haka aka dawo daga kai Ummu gidanta na gaskiya kowa cike da alhini da kuma tsoron Allah a zuƙatansu.
Mutuwar Ummu ishara ce ga mai hankali, ko iya binne ta da aka yi ya bawa kowa mamaki, wani danshi da sanyi-sanyi ne ke tashi a kabarin tamkar an kunna Ac, duk da yanayin zafin dake garin.
Masu haƙar kabarin sun labarta wannan yanayi da suka ji, har wata kasala ce ta kama su a yayin haƙar kabarin, kamar kar su fita daga ciki.
"In shaa Allah wannan baiwar Allah ta samu dacewa bi'iznillah."
Wani daga cikin masu haƙar kabarin ya faɗa.
Wani likita ne ya buɗe baki yana faɗin "Ay labarin wannan yarinyar ya bawa kowa tausayi, duk da bamu san akwai wani abu da ya haɗa ta da mijin nata ba amma ga dukkan alamu bai damu da ita ba."
Shiru suka yi mutanen kafin ya cigaba da faɗin "Tun da aka kawo ta asibitin nan sau ɗaya ya zo ya ganta shima cikin ƙyama ya wurga mata kuɗin ya fita yana tofar da yawu, a kan ido na komai ya faru."
Doctor ya ƙarashe da alamar tausayi a ransa.
Dr Lawan ne ya ce " Tabbas Dr maganarka haƙƙun! Ina ga har da takaicinsa ya yi sanadiyyar mutuwarta, amma tabbas mutuwarta ta zama ɗaya tamkar dubu tunda aka gina asibitin nan, ba'a taɓa samun gawar da tayi mutane kamarta ba."
Haka suka cigaba da hirarsu suna alhinin rashinta, su na kuma nemar mata gafara.
Haka a cikin asibitin su nurse Haleemah sun kasa taɓuka komai banda kuka, haka nan jininta ya haɗu da Ummu ji take kamar ƴar uwarta ta jini.
Sai wurin yamma ta sassauta kukan aka lallaɓa ta aka kai ta gida.
*A gidansu nurse Haleemah*
Mai adaidaita ne ya sauke ta ta sakko jikinta duk a sanyaye, ɗari biyar ta basa ya ɗauko ɗari da hamsin ya bata.
Ƙarba tayi ta shiga cikin gidan a sanyaye.
Madaidaicin gida ne mai ɗauke da ɗakuna manya guda biyu sai falo guda ɗaya wanda haɗe yake da ɗayan ɗaki, sai kitchen da sauran abubuwa.
Tana shiga ta ga Gwaggo tana yanka kuɓewa a tsakar gida, tana shiga ta faɗa kanta ta fara kuka.
Cike da tashin hankali Gwaggo ke kallonta, tana tambayar ta me ya faru.
Gwaggo kakar nurse Haleemah ce ta wurin Uba, tun sanda ta zo karatu Kano take zaune a wurinta yayin da iyayenta ke zaune a Kaduna.
Mutuwar Ummu da ta gayamata ya tada mata da hankali, dan labarin Ummu kullum sai taji sa daga wurin Haleemah.
Rarrashin ta ta fara yi har ta samu tayi shiru, sannan tayi wanka ta ci abinci ta sha paracetamol dan kanta ba ƙaramin ciwo yake mata ba.
Bacci ta kwanta ta fara yi....
Labarin Haleemah kuma??? Toh mu dai je zuwa.
********************************
*Ladiyo*
Saurin amincewa da tayi da Sadeek ya matuƙar yi masa daɗi, haƙarsa ta cimma ruwa.
Har sun saka rana a kankansi ba tare da neman shawarar wani ba.
A ɓangaren Ayaman ma bata fasa abinda tayi niyya ba.
A ɓangaren ƴarta kuwa Nabeela, kullum so take ta samu lokaci taje ta kai mata ziyara ta samo arziƙi.
Ga kuma munanan mafarkai da take yi kwana biyu, ko taje wurin boka iya kaci yace ta tashi ta bar mai kogo bar shirya mutuwa ba.
*Delu*
Jikinta ya fara yin sauƙi dan yanzu tana iya tashi da kanta amma sai ta riƙe sanda.
Duk sa tana jin wani zafi a tsakiyar gwiwarta amma ta alaƙanta hakan da warkewa ciwon yake yi.
Ga Mariya tayi ɓatan dabo, babu ita babu labarinta kowa sai gulma yake a gari na cewa karuwa ce shiyasa Alhaji Gabatari ya fasa aurenta.
Tayi kukan kuma tayi takaici, Malam Surajo ma kansa bawan Allah ya samu chanji daga wurinta, wannan masifar da take yawan yi mai ta rage ko dan cutar ne oho, amma dai ya ƙudirci a ransa sai ya saki Delu komin dade wa.
*Ammin Farouk*
Farar matar cike da fararen kaya ce tsaye a gabanta, murmushin budurwar take mata ita ma ta mayar mata, chan gefe kuma Farouk ne tsaye daff da wata rigiyar wuta sai tafarfatsi take.
"Ammi !!! ". Muryar da taji tana kiranta kenan kafin kuma diff ta dena ji ta dena gani, ji tayi an rirriƙe mata jiki ta kasa ko motsi.
Farkawa tayi daga wannan mummunan mafarkin nata, amma abin mamaki ko addu'a bata iya yi ba sakamakon nauyin da bakinta ya yi, ga shi ta kasa motsa kowacce gaɓa ta jikinta.
Zuciyarta bugu take sosai kamar zata fito daga ƙirjinta, ga duhu da ya mamaye idanuwanta.
Ita dai gata nan a kwance, bata gani bata ji bata iya motsi, ta kai kusan aƙalla awa biyu a wannan yanayin taji ana taɓa jikinta.
Jijjigata ake yi amma tsam ta kasa motsi.
Kuyi haƙuri da short page ɗin rashin comment yana karya min gwiwa.
More comment more typing
GASKIYA BANA JIN DAƊIN RASHIN COMMENT ƊIN KU, KU ƘOƘARTS DAN ALLAH KU RINƘA COMMENT
Khairat ce ✍️🤍
*Domin shawara ko ƙorafi ko gyara ku tuntuɓi wannan number 09036812206*
*Ga masu son a tallata musu haja su nemo wannan number 09036812206*
😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈
By
Khairat 💙
(Posting room)
https://chat.whatsapp.com/Js1xb4FBd2v0o5mxXpssVr
My WhatsApp group comment section 👇 👇 👇
https://chat.whatsapp.com/EoTRoZq4KA0JFbynkYp9wi
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.
_With strong passion, we change pain into strength,and dreams into stories. We are Jajirtattu Writers born to share powerful words.🤌💪_
BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM
Page 65-66(BOOK TWO)
____Mai aikin Ammi kuwa, Badi'a jijjiga Ammi take amma shiru, a guje ta fito falo, ganin ba kowa ya sa ta yi saurin fita tana kiran maigadi,
"Baba! Baba! Ammiiii!"
Badi'a ta faɗa cikin tashin hankali tana nuna kofar shiga falon.
Saurin tashi Baba mai gadi ya yi yana bin bayan Badi'a, har sun zo shiga ɗakin ya tsaya yace
"Mene ne Badi'a? Lafiya kuwa?"
"Ammi ce tun ɗazu nake girgiza ta bata motsi, kuma sai kallo na take.". Ta ƙarashe cikin kuka.
"Toh kinga baza ayi haka ba, bai kamata na shiga ɗakinta ni ba muharrarimta ba, bari na kira Alhaji(Farouk)."
Ɗaga mai kai tayi ta shige ɗakin shi kuma ya ciro wayarsa ya nemo number Farouk ya kira shi.
Yana kwance a gado Nafeesa na kwance a jikinsa ya ji kira ya shigo wayarsa, Baba maigadi ya gani a screen ɗin wayar.
Cike da mamaki ya ɗauki wayar yana tunanin me ya sa zai kirasa da sanyin safiyar nan.
"Assalamu alaikum."
Amsa sallamar ya yi kana suka gaisa cikin mutunta juna.
"Dama Alhaji jikin Hajiya ne ba daɗi, tun asuba Badi'a ke motsa ta amma shiru kuma tana nan tana kallon mutane..."
Bai karasa ba Farouk ya tsayar da shi da. "Whattt???? Ammin?". Sannan kuma ya jefar da wayar ya yi sauri ya miƙe.
Nafee da tayi wasarairai a jikinsa tana danna wayarta taji ya sake ta ta bige da katifa.
"Baka da hankali ne zaka wullar da ni haka?" Ta faɗa a fusace.
"Nafee Ammi fa? Ammi ba lafiya." Ya faɗa kamar zai yi kuka.
"Koma wacece ."
Ta ja uban tsaki ta kuma kwantawa.
Mamakin Nafee ya tsayar da shi chak, wato koma wacece? Lallai uwarsa bata da wani daraja a idonta.
Zarar key ɗin motarsa ya yi ya fita parking space, shiga motar ya yi, ya sa key kenan ta nuna masa babu mai a ciki.
Dukan stiyarin ya yi jikin fushi wanda ya yi sanadiyyar fitowar hawaye a kumatunsa.
Rasa me zai yi ya yi, kawai ya fita ya fara tarar adaidaita, har sun fara tafiya yaji mai adaidaitan yana cewa
"Ina muka nufa ranka ya daɗe?"
Sai yanzu ya tuna ko gaya mai inda zasu bai yi ba, " Hotoro tsamiyar boka."
Haka suka cigaba da tafiya har suka iso.
Su na isowa ko jira ya gama parking bai yi ba ya fito ya yi cikin gidan da sauri, kiran da mai adaidaita yake masa ne ya tuna ko sisi bai fito da shi ba, kawai ya shige cikin gidan.
Yana isa ya shige ɗakin Ammi ya tarar da Badi'a zaune tayi tsuru tana kallon ta.
Tsugunawa ya yi a ƙasa yana sakin kuka mai ciyo.
Bai jira ba ya ɗauki key ɗin motar Ammi, shi da Badi'a suka kama suka fitar da ita zuwa mota.
Har ya fito ya tarar da mai adaidaitan tana jiransa, laluba motar ya yi ay kuwa ya samu wata dubu ɗaya ya cilla masa.
Tuƙi yake yana kuka a hankali, lokaci zuwa lokaci yana kallon Ammi dake shimfiɗe a bayan motar, asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano suka nufa, suna shiga ya tuna ko waya bai ɗauko ba bare ya kira family Doctor ɗinsu.
Office ɗin sa ya nufa ya gaya mai yanayin da Ammi ke ciki, haka suka duƙufa a kanta, su kuma su Farouk da Badi'a na waje suna jiran fitowarsu...
*Ayaman*
Yamma ce lis ta dawo daga wurin aikinta kenan sai tafiya take tana tafiya kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki har ta iso gidan.
Tana isa ta tarar da Tsahare ta zo tana zaune a ƙofar ɗakinta, da sauri ta ƙarasa kusa da ita tana