Showing 21001 words to 23389 words out of 23389 words
Abuja domin su sheƙe ayarsu da suka saba.
Ta gama shirinta tsaf, ta kama hanyar Abuja ko iya kuɗin mota Alhaji Ahmed ya tura mata miliyan daya, ga kuma alƙawarin mota bayan ta je.
Sun sha honeymoon din su (waiyazubillah) a garin na Abuja, duk gurin cin abinci da outing ba wanda Nafee bata sani ba, sun yi abubuwa kam abin sai wanda ya gani.
Ana saura kwanaki biyu ta koma garin Lagos Alhaji ya buƙaci da ta shirya za'a zo a kawo ta guest house dinsa tunda ita a hotel take zama.
Bata musa ba, ta shirya cikin danƙareren leshinta ta yi tsaf, har da bankaɗar magungunan mata kala-kala, ta zauna ta fara cin abinci kenan sai ga yaron Alhaji ya zo, suka taɓa hira sama sama sannan suka shiga Mota suka kama hanya.
Ganin an kauce hanya anyi wata hanyar daban ya sa ta kalli Maude, ta ce.
"Aah Maude ya na ga ka wuce hanyar?"
Ko kallonta bai yi ba sai da ya faka motar a bakin titi sannan ya shammace ta ya bige mata kai da ƙarfi, nan take kuwa ta suma sai ga jini ta hanci da baki, hannunsa ya kai kan hancinta ya ji da sauran numfashi ai kuwa ya kuma dagewa ya bige ta da gwiwar hannu, nan take rai ya yi halinsa...
Wata dariya Maude ya yi kafin ya chaje jakarta ya kwashe dukah
kudin dake ciki, haɗe da mukullin motar da Alhaji ya bata.
j ce ta ga dacewar a shiga a duba ko lafiya tunda yanzu kwanaki uku kenan bata fito ba, kar su je ta mace musu.
Nan kuwa matan gidan suka yi ayari aka shiga ɗakin Ladiyo, wata mai ƙaramin ciki ce ta fito ta na faɗin hhhhh
"Innalilahi wa'inna ɓhhi'laihi raji'un."
Kafin kuwa ta fara amai kamar zata amayar da ƴaƴan cikinta.
Nan da nan sauran matan suka fito daga mai mai amai sai bai tofar da yawu abindai ba kyan gani dan haka nayi shahada na shiga domin ganin me wannan mata suka gani suke tushe hanci.
Ladiyo ce kwance cikin kashi da fitsari ga wani farin ruwa kamar kumfa dake fitowa daga gabanta.
Ba shiri mutanen gida suka bazama neman ƴan uwan Ladiyo da ƙyar dai aka samo Wani kawunta, ya ce zai riƙe ta, ɗakin waje na shago aka ajiye ta dan yace kar ta shigo cikin gidan kar ta hallaka mai yara da mata.
MUGUNTA 😈😈😈
By
Khairat...
Bismillahir rahamnir rahim
Page 87-88
Ina Delu?
Tabbas ta tabbatar rayuwar nan ba wurin madawwama bace, daga karshe dai sai da wata kungiya ta ɗauki nauyin aikin cire kafarta, dan kuwa Cancer ce mai ƙarfi mai hallaka mutum , da ƙyar aka cire kafar ɗaya Allah ma ya sa ɗayar bata kamu ba.
Dan haka nauyin abincinta ya koma kanta, wurin kwana ne kawai yayanta yake bata dan haka sai ta fita ta yi Bara take samun abin ci.
"Allah ya baku mu samu, a taimaka dan darajar Annabi masoya Annabi a taimaka ."
Abinda take ta nanatawa kenan a bakin hanyar babbar kasuwar garin.
Waro idanu ta kuma yi dan ta tabbatar da abinda idanuwanta ke kokarin nuna mata,
"Ayaman!!!!"
Ta furta da ƙarfi, Ayaman kuwa jin an kira sunanta ya sa ta juya dai-dai in da ta ji maganar .
Delu kuwa kuka ta fashe da shi na ban mamaki, rayuwa kenan, tabbas duk wanda yace tukunyar wani baza ta tafasa a toh tabbas ta sa ko dumi baza ta yi ba, a ce Ayaman da suka so ganin ta gaza a rayuwa, wadda suka so rayuwarta ta lalace ta zama wulaƙantacciya sai gashi sune suke a wulaƙance, gashi nan yau tana bara ita kuma Ayaman fess da ita.
"Dan Allah Ayaman ki yafe min, dan Allah wallahi na ga izina a kanki, babu kalar tsafin da bamu miki ba, da niyyar lalata rayuwarki, amma cikin ikon Allah sai gashi mune muka ƙare a haka, wallahi Ayaman nayi nadama, tun daga lokacin da muka yi miki baƙin tsafi, dan Allah kiyi haƙuri kuma akwai wani sirrin da nake son gaya miki." Ta ƙarashe cikin kuka mai ban tausayi.
Tuni Ayaman da sauran matan masu saurin kuka sun fara sakin hawaye, mutane kuwa suka tsaya kallon ikon Allah.
"Ki faɗa min ina jin ki." Ayaman ta faɗa tana sheshsheƙar kuka.
" Ladiyo da ni mu muka yi sanadiyyar mutuwar mahaifiyarki, saboda son zuciyarmu, sannan cikin shegen da aka ce kin yi, Yunusa ɗan uwanki ne uban cikin!"
Da sauri Ayaman ta juya tana ƙare wa Delu kallo, "Bannn gaaanneee baaa?"
"Ehh kwarai abinda kika ji shine , a ranar wani asiri zaku aiwatar a kan auren Ladiyo da Sadeek, dan haka boka yace sai ɗanta ya kwanta da ke sannan auren zai yiwu." Ta numfasa sannan ta cigaba.
"A lokacin wani magani aka shaƙa miki, kika fita daga hankalinki, har aka gama abinda aka yi, in kin tuna ai make ya shigo gidan yana tangaɗi."
Durkushewa Ayaman ta yi, hawaye masu zafi da matuƙar ciwo suna zubo mata,
"Innalilahi wa'inna i'laihi raji'un, dan Allah Delu mai na muku? Na cutar da ku ne? In zan tuna bayan biyayya da girmamawa da nake muku babu komai, amma kuka cutar da ni cutarwa mafi girma, innalilahi wa'inna i'laihi raji'un ɗan uwana na jini kuka sa ya lalata ni, na haifi cikin shege, babu kalar tsangwama da kyara da ban gani ba, duk kuwa da bayan azabtarwar da na samu daga wurin Ladiyo, wannan abin shi ya yi sanadiyar mutuwar mahaifiyata da mahaifina, ribar mai kuka ci yanzu? Kun cutar da ni, kun cutar da rayuwata, Allah ya isa tsakanina da ku."
Daga nan Ayaman ta cigaba da kuka mai ban tausayi, wannan wace kalar rayuwa ce, mai ta tsare wa wannan mutanen?
A zabure ta miƙe, "Wallahi wallahi Delu bazan taɓa yafe muku ba, Allah zai bi min hakkina." Sannan taja hannun Tsahare da ta daskare a wurin suka nufi gida.
A ranar Ayaman ko abinci bata ci ba, kuka ta yi sosai, dan ji tayi rayuwar gaba ɗaya ta fitar mata daga rai, ga kuma mutuwar mahaifanta da ta dawo sabo.
Farouk
Cikin ikon Allah yau aka ɗaura auren shi da Halimatu a kan sadaki 200k , an yi shagali sosai sannan aka kai amarya ɗakinta.
Washegari sai ga kiran Ammi a kan yazo da sauri, yana zuwa ya tarar da wani babban mutum, sai ga Hajiya a zaune.
Gaisawa suka yi, sannan mutumin ya fara gabatar da kansa ga Farouk,
"Ni abokin kasuwancin mahaifinka ne, kusan shekaru 20 kenan bana ƙasar sai yanzu da na dawo nake samun labarin rasuwar tasa, Allah Ubangiji ya jikansa da rahama ya sa ya huta."
Dukkan su suka amsa da Ameen.
Ya cigaba kamar haka " a lokacin mun saka hannun jari a wani kamfanin wayoyi dake China, kuma alhamdulillah kuɗin sun haihu fiye da zato, ina neman yafiyarku na riƙe muku kuɗi da nayi dan bani da labari, a yanzu tunda ga babban ɗansa ai alhamdulillah, dan damƙa amanar kuɗaɗen zuwa wurinsa ya cigaba da juyawa."
Nan dai suka cigaba da tattaunawa, saboda yawan kuɗin da Farouk ya gani kasa motsi ya yi, billions!!!
Cikin ikon Allah aka raba kuɗin, kowa ya samu rabonsa har ƴan uwansa dake ƙasar waje, nan kuwa ya zuba hannun jari mai yawa a kamfanin Dangote, ya buɗe katafaren supermarket a garin Kano, ya cigaba da running kanfanin da Alhaji ya rasu ya bar musu.
Bayan watanni uku.
Kuɗi sun zauna a jikinsa, yayin da Halimatu ke ɗauke da ƙaramin ciki dan wata biyu, ta ajiye aikinta Farouk ya bata kuɗi masu kauri ta fara business da su na atamfofi, ai kuwa cikin ƙanƙanin lokaci ta karɓu ta zama hajiyar kanta.
Kwatsam wata ranar Lahadi suna cikin shaƙatawa a garden ɗin dake cikin gidan, kasancewar Farouk ya danƙara uban gida mai manyan part guda biyu, ya ɗauko Ammi ta dawo gidan da zama, sai ga mai gadi ya zo da sauri ya durkushe yana kai gaisuwa.
Amsa mai suka yi sannan yace
"Alhaji Allah ya sa ban yi laifi ba, wata mata ce ta dage sai ta shigo wai tana son ganinka, tace nace ma ko mafi, ko Nafee ne na dai manta Alhaji."
Ɗan dagowa Farouk ya yi, yace "Nafee???" Zuciyarsa na bugawa da ƙarfi.
Halimatu dake kwance a cinyarsa da cikin ta haihuwa yau ko gobe ya mike tana cewa "Nafee ce, tabbas ita ce!!"
Da sauri ta mike zata fita Farouk ya riƙo hannunta, suka tafi tare.
Amai ne ya kwacewa Halimatu ganin Nafee da ta yi "Innalilahi wa'inna i'laihi raji'un,"
Runtse ido Farouk ya yi, ganin wata halitta mara kyan gani, "Wannan halittar fa? Ka fitar da ita!!!!" Ya ƙarashe a ɗan tsawace.
"Farouk ni ce, Nafeesa, Nafeen ka ce."
Kuma kallon ta ya yi, bayanta ta durkushe alamun ƙusumbu, ga bakinta da ya turo kamar na kare,fatarta duk ta zazzago ta zama wani abin ƙyanƙyami.
" Dan Allah Farouk ka yafe min." Ta ƙarashe cikin kuka.
"Na san na cutar da kai da Ummu, wallahi sharrin shaidan ne na kashe baiwar Allah da bata ji ba baga gani ba, dan Allah ku yafe min."
Nan fa ta fara sumbatu, tana faɗan mugayen abubuwan da ta yi.
Halimatu kuwa kuka ta fashe da shi, "Innalilahi wa'inna i'laihi raji'un, yanzu meye ribar cutar da wani, kin kashe ta yanzu kina tunanin Allah zai bar ki??"
"A'a wallahi na tabbata wutar jahannama ce makomata."
"Hmm"
Farouk kuwa mai gadi ya bawa umarnin fitar da ita daga gidan ya yar da ita a bakin titi.
Halimatu tace ba za'a yi haka ba, ta sa aka ɗauko ƴar ƙurƙura aka jibge ta a nan, aka nufi garinsu da ita.
Suna zuwa garin kuwa neman duniya babu wanda ya gane ta, da ƙyar aka samu wani mutumi ya gane ta yace zai kai ta wurin mahaifiyarta, wata bola suka nufa, ai kuwa sai ga Ladiyo ta taho da gudu tana wata dariyar hauka, "Gurin boka zan kai ku? Hehehehe zan kaiku wurin boka wlh, bokaaa hhhhhhhh." Haka dai ta rinƙa soki burutsu ga wani ruwa mai wari da yake fitowa daga gabanta.
Ajiye Nafee suka yi, mutumin yace "Tabbas ita ce Nafeesa ƴar Ladiyo, a halin yanzu Ladiyo ta haukace hauka take yi tuburan kun ganta nan dai."
Jike da jimami mutanen suka juya suka bar wurin.
Washegari.
Wannan gari ya tashi da wani mummunan masifa, dan kuwa Ladiyo ta mutu a cikin bola, sai da ƙyar aka samu wanda zasu mata wanka, aka yayyaɓa mata likafani, aka kai ta zuwa maƙarbarta.
Sai dai wani ikon Allah duk kabarin da aka haƙa sai a ga micizai sun fito manya kuwa, a haka sai da aka haƙa kabari 5 amma duk same micizai ne suke fitowa, a haka aka haƙura aka zo za'a sa ta, amma sai dai me ƙasa ta ƙi karbanta, da an saka gawar Ladiyo sai ƙasa ta bulluƙo da ita, aka yi aka yi amma ƙasa ta ƙi ƙarbanta, da aka dage da addu'a da kuma nema mata yafi sannan aka samu kasa ta karɓe ta ga kuma micizan da suka nannaɗe ta suna saranta ta ko'ina.
Kowa kuwa a garin banda faɗan munanan abubuwa a kan Ladiyo babu abinda suke, har da masu tsine mata sanadiyyar cutarwar da ta musu.
*Innalilahi wa'inna i'laihi raji'un 😭, ƴan uwa mu hankalta, duniyar nan ba madawwama bace wata rana dole zamu mutu mu bar ta, mene amfanin bin bokaye, wani la'ananne fasiƙi, gashi nan dai ina fatan mutuwar Ladiyo ta zamo izina a gare mu, Allah ya kyauta*
Ta ɓangaren Delu kuwa tun da ta samu labarin mutuwar Ladiyo da kalar azabar da aka gani, tuni ta mayar da hankalinta wurin neman yafiyar mutane, wasu su ce sun yafe wasu kuwa suce basu yafe ba, a haka dai ta mai da hankali wurin neman yafiyar Allah, istigfhari baya wuce bakinta, sallah ma a lokaci.
Bokan kan tudu
Yana cikin tsafinsa wani irin ciwon kai ya dirar masa, tuni ya fara ƙaƙƙafewa kamar mai farfaɗiya, ga wata farar kumfa da take fitowa daga bakinsa, babu mai taimako haka ya mutu a wulaƙance a wurin tsafinsa. Yana mutuwa kuwa kayan tsafin suka fara jijjiga, duk suka rufto masa a kai, ga wani baƙi da ya yi nan take.
Farouk& Halimatu
Rayuwa suke gudanarwa mai cike da tsafta da nutsuwa, Halimatu ta haifi ƴan biyu mace da namiji, duk aka sa musu sunan mahaifan Farouk, sannan gwaggo ta koma Kaduna da zama wurin danta wato gidan su halima.
Kyawawan yara ke ta wasan su a tsakar gidan, sai ga motar Farouk ta shigo cikin gidan tuni suka nufi wurin suna kiran "Daddy! Daddy!".
Robar ice cream ya miƙa musu ai kuwa tuni suka nufi part ɗin Ammi suna nuna mata, bin su yayi ya yiwa Ammi sannu da gida sannan ya wuce part ɗin su ya bar twins a wurinta
A parlor ya tarar da Halimatu tana sa turaren wuta, murmushi ta sakar mai sannan ta nufe sa ta rungume sa, kiss ya sakar mata a wuya yana shaƙar humrarta mai daɗin gaske.
"Baby nah." Ya faɗa yana jan dogon numfashi, cakk ya ɗauke ta, sannan ya raɗa mata a kunne
"Muje a yi wa twins ƙani."
Ɗakinsa suka shiga suna dariya ni kuma na fita daga gidan ina musu fatan alkhairi.
Ayaman.
Bayan ta hakurƙurtar da zuciyarta ta cigaba da rayuwa a gidan su Tsahare, cikin ikon Allah mai kamfanin Mudassir and brothers wato Alhaji Mudassir ya ganta a lokacin da suka je siyan atamfofi a kasuwa, ai kuwa tuni ya bi ta.
Ba'a ɗau lokaci ba aka sha biki dan kuwa ita ma Ayaman ya kwanta mata, biki a ka yi gagarumi wanda ya girgiza garin Kano.
Ga lefe da aka danƙara mata kusan akwati 50 tare da kyautar mota.
Bayan wasu shekaru...
Zaman lafiya ya wanzu, Ayaman ta haifi yara biyar, akwai ƴan uku gabaɗaya maza, sai kuma mace sai wani namijin, suna rayuwa a danƙareren gidansu daga G.R.A.
(Ya kamata ni da masu karatu mu je mu ga gidan dan faɗar tsaruwarsa ɓata baki ne🤭😁)
Cikin falon na shiga ai kuwa na hango Hajiya Ayaman zaune a kan cinyar Alhaji Mudassir, ƙaramin yaron sai kuka yake wai zai hau cinyar Maama( Ayaman) ai kuwa sai dariya suke mai.
Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah!
Dukkan yabo su tabbata ga Allah Ubangijin talikai, ina mai addu'ar duk wani darasi da za'a ɗauka a cikin littafin nan ya zama abu mai kyau, abinda na rubuta ba daidai ba kuma Allah ya yafe min, ina godiya sosai ga masu karantawa, sharing da masu comment ku sani ku na daban ne a zuciyata🥹🤍 ina godiya Allah ya saka da alkhairi.
Bye, by KHAIRAT SHALELEN JAJIRTATTU ✍️ 🎉