Showing 18001 words to 21000 words out of 23389 words

Chapter 7 - Mugunta 2 Complete Hausa Novels By Khairat.txt

KHAIRAT   

13 Mar 2026

5

ka na gasa min magana yadda ka ga dama ba kuma na ƙyale ka, ba ka kai wannan matsayain ba wallahi, kuma da kake maganar asiri da la'anta ta, ka san sai dai mu tsine wa juna, dan kaima waye a garin nan bai san kwartanci kake yi ba? A haka na haƙura na aure ka shi ne yanzu za ka zo min da wannan maganar? Dama an ce ɗan Adam butulu."
Ta ƙarashe ta na wani gunjin kuka.

Malam Surajo ya fusata jin ta kirasa da sunan kwarto, ya juya bayansa ya ɗauko muciya, ya samu ƙafarta da ta karye har ta fara warkewa ya ƙwala mata dai-dai wurin karayar, ai kuwa ta daddage ta tsala ihu
"Wayyo jama'a!!! Na shiga uku zai kashe ni." Delu ta faɗa kafin kuma ta sume a zaunen da take dan raɗaɗin azaba.
Kasancewar mutanen unguwar sun san halinsu, ko faɗa suke yi ka jiyo ihu da ka shiga cikin gidan za su hau kanka da masifi wai ba ruwanka da su, dan haka babu wanda ya yi gigin shiga ya tambayi me ya faru duk da sun jiyo , ya yi saurin ficewa daga gidan ta ƙofar baya, in da babu wanda ya gan shi.




Bayan awa biyu.

> *"Assalamu Alaikum."*
Amina ta rangaɗa sallama ta na shiga cikin gidan .( kamar yadda muka gani a baya, Amina ƴar kawun Delu ce, ma'ana ƙanwarta.)

Turus ta yi ganin Delu a kwance kamar matacciya ga ƙafarta da ke fitar da wani irin ruwa mai yawa.

Wullar da kwanon abincin da ta kawo mata ta yi sannan ta ƙarasa wajenta a rikice.
Ganin halin da yayarta ta ke ciki, ya sa ta fice da gudu daga gidan ta nufi gidansu dake farkon layin.

Babanta ta kira, in da bai yi sanya ba ya ari motar abokinsa aka sa Delu a ciki suka nufi babban asibitin ƙauyen.




*Ya labarin Nurse Haleemah da manufarta kuwa?*




*Nurse Haleemah*

Bincikenta ba laifi ya yi nisa sosai a kan Farouk, dan yanzu ƙalilan daga cikin abubuwan rayuwarsa ne bata sani ba.
Ta yi ƙoƙari sosai har ta gano asibitin da aka kwantar da Ammi.

Kasancewar asibitin state hospital ne, ma'ana duk matsayi ɗaya suke da asibitin da take aiki ya sa ta ƙudiri aniyar neman transfer zuwa asibitin da Ammi ke kwance.

Ranar Monday da safe bayan ta gama shirinta ta yi wa Gwaggo sallama ta fito.
Adaidaita sahu ta tara zuwa asibitin Aminu Kano.
Bayan gaisuwa kamar yadda ta saba da masu gadin ta wuce ciki, ofishinsu na nurses ta nufa ta ajiye kayanta ta gaisa da sauran nurses ɗin da ke wurin kana ta wuce zuwa office ɗin babban likita.

Ofishin doctor Lukman ta nufa, ta ƙwanƙwasa in da bata jira a bata izini ba ta ƙusa kai ciki haɗe da sallama.
Rubuce-Rubuce ta tarar da shi ya na yi, ɗago kai ya yi dan ya ga wanda ya shigo mai ofice kai tsaye haka.
Wani lallausan murmushi ya saki, duk da ba kyakkyawa bane amma fuskarsa ta yi kyau da murmushin.
Ganin haka ita ma ta mayar mai da maratanin murmushin da ka na gani ka san bai kai zuci ba.

"Ina kwana Sir."

Ta faɗa sannan ta yi wa kanta masauki daga ɗaya daga cikin kujerun ofishin.

"Lafiya ƙalau, Halimatus Sa'adiyyah mai tagwayen suna."
Ya faɗa ya na bin ta da wani irin murmushi da ta gaza fassara wa.

"Uhmm."
Kawai ta faɗa kafin nan ta yi ƙasa sa kanta ta yi shiru, ganin shirun ya yi yawa kuma ta na jin idanun doctor Lukman a jikinta ya sa ta buɗe baki da ƙyar ta ce
"Alfarma nake nema doctor."

Da sauri kamar jira yake yi ya ce
"Faɗi kanki tsaye Halimatu."

"Dan Allah transfer nake so zuwa ɗayan branch dake hanyar rijiyar Zaki."
Ƙurr ya mata da idanu ya na jin babu daɗi a ransa, yanzu in ta tafi ina zai samu damar kallon wannan kyakkyawar fuskar tata mai cike da nutsuwa?

"Transfer kuma Halima?"
Ya faɗa da sigar tausayi dake sauƙaƙa zuƙatan masu sauraron sa.

"Ehhhh ranka ya daɗe."
Ta faɗa cike da girmamawa.

"Tohh, ki rubuta takarda zuwa ofishin supervisor wannan huruminsa ne."

"Okay Sir, na gode sosai."
Sannan ta fice daga office ɗin ta bar doctor Lukman zuciya babu daɗi .

Shi kuwa doctor Lukman da kallo ya bi bayanta, ya rasa wannan taurin kai na Halima, sai bin kanta yake ta so shi amma ta ƙi har ya haƙura da ita.

Ita kuwa Haleemah da ƙaramin tsaki ta fita daga office ɗin, ita a ganinta ko maza sun ƙare ba za ta taɓa auren doctor Lukman ba....




Kamar yadda ya bata shawara haka ta yi, ta rubuta letter zuwa ofishin supervisor.
Ta nufi office ɗin bayan ta ɗau break daga wurin aiki.

Ta shafe kusan awanni biyar ta na jiran supervisor, haka ta wuce ba tare da ta samu abinda take so ba.




*Ya labarin bokan kan tudu?*


Tun ranar da yake tattaunawa da Ladiyo a ɗakin tsafinsa ya ji abubuwa ba kamar yadda ya saba ba, har wani birkice wa aljanun dake taimakawa tsafinsa suka fara yi, ilay kuwa BARQAAAN ne ya bayyana cikin haske mai ɗaukar ido.
A gaban idonsa Ladiyo ta rikice ta na iface-iface shi kuma aka ɓatar da shi zuwa fadar matsafa.

Durƙushewa ya yi a gaban (Uwar kowa) kamar yadda suke kiran shugabarsu.

Tsawar da aka daka masa ce ta dawo da shi daga tunanin Ladiyo tunowa da ya yi a wurin da yake.



Sai mun haɗu a next page.


Shalelen ce ©



😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈




By



*© Shalelen Jajirtattu (Khairat)*



> *BISMILLAHIR RAHMNIR RAHIM*


*Page 81-82*




Tsawar da aka daka masa ce ta dawo da shi daga tunanin Ladiyo tunowa da ya yi a wurin da yake.

A nan muka tsaya yanzu zamu cigaba .

Buɗar bakin shugaba ya ce
" Talle(sunan bokan), ba za mu zuba maka ido ka cigaba da aikin da maƙiyanmu ba, dan tabbas BARQAAAN maƙiyi ne, maƙiyin da bai chanchanci yafiya ba ta har abada....



*BARQAAAN*

Shin waye wannan BARQAAAN din? Kuma meye matsayinsa a wannan littafi? Ku biyo ni..



*Takaitaccen bayani a kansa*


BARQAAAN za'a iya kiransa ruwa biyu, wato rabi Mutun rabi aljan, mahaifinsa ya kasance masunci, wato masu kamun kifi, kuma ya haɗu da mahaifiyarsa a cikin ruwan ta fito shan iska.

Tun ya na jin tsoro har ya dawo shaquwa ta shiga tsakaninsa da ita, wadda ba shaƙuwar hankali bace.

A wata rana ya fito sunci kamar yadda ya saba, ya tsaya a bakin ƙoramar ya na kallon ta in da Suhain za ta fito kamar yadda ta gaya mai sunanta.

Chanbya hango igiyar ruwa ta taho da ƙarfinta, hakan ke nuni da ita ce ta taho, ya gyara tsayuwarsa ya na jiran ƙarasowar ta.

Bayan ta diro a gabansa ya tsaya ya na ƙare mata kallo, tabbas kamar yadda ake faɗa matan ɗan Adam sun fi na aljanu kyau nesa ba kusa ba, duk da a suffar mutane take zuwar kai hakan bai taɓa tsorata sa ba.

Kallon diri da kuma surar da Allah ya mata yake yi, nan fa ta zo mai da labari mara daɗin ji, na ce wa a masarautarsu an tilasta mata auren ɗan uwanta kamar yadda al'adarsu ta gabatar, amma a wannan lokaci ta na jin gaskiya ba za ta biye musu ba domin ta cutu, ta gwammace ta fice daga masarautar har dai basu yadda da aurenta da shi ba.

In dai abu an haramta sa a addini, Allah shi ya san dalilinshi na haramta wannan abu ko halasta shi, kamar yanzu haramun ne keɓewa tsakanin namiji da mace, dan na ukunsu tabbas sheɗan ne.

Sheɗan ya taka muhimmiyar rawa wurin aikata ɓarna a wannan wurin, dan kuwa babban al'amari ya gifta tsakanin wannan matasan mutum da aljan.


Haka ta wuce zuwa masarautarsu domin jiran faruwar next plan da suka shirya...








*LADIYO*


Galala ta saki baki ta na kallon Sadeek da ya nuna ko a jikinsa game da matsalar da ta zo da ita, sai ma maida hankali da ya yi wurin scrolling a manhajar facebook.

"Sadeek magana fa nake maka."
Ta furta a ɗan zafafe dan wannan hali na ko in kula da ya nuna mata ba karamin ɓata mata rai ya yi ba.

Nan ma banza ya bawa ajiyarta ko uffan bai ce ba sai ma dariya da ya saki ganin wani post mai abin dariya.

Da sauri ta miƙe haɗe da ƙwace wayar ta cillar da ita a ƙasa ta tsaya ta na kallan sa.

Cike da tijara ta miƙe ta na faɗin

"Tun ɗazu ka mayar da ni mahaukaciya sai magana nake maka da yake ga sabon kamu ko kallo ban ishe ka ba ko Sadeek? Cutar nan ma ina da tabbacin a jikinka na kwasa dan jita-jitar da nake ji a gari na neman matan banza da kake yi ashe da gaske ne, lallai kam mashahurin ɗan iska....."

Ai ba ta kai ga ƙarasawa ba ta ji saukar mari zazzafa a kuncinta na dama

Cike da zafin rai Sadeek ya hayayyaƙo mata

"Yo ai mahaukaciyar ce Ladiyo, in ba hauka irin naki ba da daƙiƙanci da dabbanci ina kika taɓa ganin saurayi kama ta ya zo wannan ƙauyen har ya aure ki ? Ƙazama da ke tsohuwa kin san dole akwai manufa, kuma tun da na kammala manufata shikenan sai kowa ya kama gabansa."

Ya faɗa kafin ya fice da sauri.

Zubewa ta yi daɓasss,me hakan ke nufi kenan?



*Ayaman*


Cike da tashin hankali ta bi bayan A'ishah dan ƙwaƙwalwarta kasa fassara komai ta yi a wannan lokacin, kafin kuma da ƙarfi ta fara faɗin.
"A'isha ta! A'isha ta! A'isha ta! Aun kashe min ita, sun kashe min maraniyar Allah wayyo Allah na, A'ishah dan Allah kar ki mutu ki bar ni, ke kaɗai ce sanyin idaniyata a wannan lokacin dan Allah kar ki barni."

A kiɗime Kamal ya saka A'isha a bayan motar sai Ayaman da ta shige a rikice ta na kiran a kai ta asibiti kar ta mutu, bayan mantawa da ta yi cewa mutuwa a hannun Allah take, mutum lafiyayye ma sai ya mutu mara lafiyar na nan har sai san da lokacinsa ya cika.
Tsahare ma bayan motar ta shiga sai Farouk da ya shige gaban motar ya na jin kansa na wani sara masa dan har ga Allah kukan matar ya cika masa kunne.

Asibitin wellness hub (wanda aka kwantar da Ammi suka nufa tun da ba wani nisa suka yi ba wannan iftila'in ya afku) Kamal ya nufa da su, in da cikin gaggawa a ka shige da A'ishah emergency ɓangaren yara.

Bayan wani lokaci likita ya fito nurses na biye da shi a baya, ganin yanayin fuskar likitan ba ƙaramin kiɗima su ya yi ba.
"I'm sorry to say, she's no more."

Ya faɗa da ƙyar kafin ya wuce ya bar su Ayaman shiru dan basu fahimci me yake faruwa ba, yayin da Kamal ya saki wani dogon salati ya na nanata innalillahi wa'inna i'laihi raji'un.

Ɗakin da likitan ya fito ta shige kamar a guje ta na baza idon in da za ta ga A'ishah.
Karaf!!! Idanunta suka hango mata farin ƙyalle shimfiɗe a saman A'ishah, buɗe fuskarta ta yi, fari tass kamar za ka mata magana ta amsa.

Zubewa ta yi a wurin ta fara gunjin kuka mai taɓa zuciya, yanzu shikenan ita komai na ta daga ta fara jin daɗin rayuwa sai ta katse? Mai yake faruwa ne? Mamanta ta rasu tun ta na da ƙarancin shekaru, ta faɗa uƙubar kishiyar uwa da ƴaƴanta, cikin shege ta haife shi a gidan Anas wanda hakan ya yi sanadin datsewa alaƙarsu, mahaifinta ya rasu, yanzu kuma ƴar da ta zama sanyin idanunta ta rasu? A haka za ta gama rayuwarta cikin kunci a kullum?
"Ya hayyu ya qayyum ka kawo min mafita."




Sai mun haɗu a next page.




😈😈😈 MUGUNTA 😈😈😈



By


*Khairat**shalelen (j.w.a)*


Page 83-84



*Ladiyo*

Ta sha kuka na lokaci mai tsawo, kafin ta hakura ta ɗauki dangana.
Wayyo ita kam san zuciyarta ya jawo mata masifa, yanzu ina take da arzikin magance wannan matsala da ta same ta? Ta na cikin tunane-tunane har bacci mai nauyin gaske ya yi awon gaba da ita .
Ta na cikin barcin ta ji motsii amma ba ta gama tantance mene ne ba, ta juya ta cigaba da sharɓar bacci.
Shi kuwa Sadeek cikin sanɗa ya ɗebe kayan shi kaff, ya juya zai tafi ko mai ya tuno oho ya dawo a hankali ya buɗe lalitar Ladiyo ya kwashe kudin dake ciki bai bar mata ko kabo ba ya fice abinsa.

Sai wuraren bayan la'asar ta farka daga nannauyen baccin, tsayawa ta yi ta na ƙarewa ɗakin kallo sai ta ga kamar akwai abubuwan da babu a ciki, kawai ta bar tunanin ta miƙe.

Fita waje ta yi ta kalli sauran matan dake ta aikinsu, dan a gidan haya ta kama saboda ba za ta iya zaman shago ba.
Ci kanki basu ce mata ba ita ma haka ta ɗauki buta ta nufi da babban ɓanɗakin tal dake cikin gidan.

Gida ne babban,mai ɗauke da ɗakuna sha biyu in da mutane mabanbanta ke rayuwa a ciki, in da kowacce mata ke sana'arta domin rufawa kai asiri, wasu na suyar masa, wasu ta wainar fulawa da wasu kayan miya suke siyarwa, wasu kayan gwanjo, da dai sauransu.

Kun dai san yanayin gidan haya ba sai na tsaya baku labari ba.

Lukutar matar da ta gani a cikin banɗakin sai bahaya take yi ya sa ta yi saurin ja da baya ta na sakin tsaki, ai kuwa Iyabo bayerabiyar da ta kasance maƙociyar Ladiyo a cikin gidan dan ɗakinsu na kallon juna, ta fito da azama bayan ta gama abinda ta je yi, ta na surfa masifa, ita za'a biyo banɗaki ana kalla, wato gulmarsu bata tsaya iya wace ba har sai an biyo ta banɗaki.
Haƙuri Ladiyo ta fara bata ta tuno banɗakin waccan gidan nata da in Ayaman ta wanke har hana ta shiga take yi yau ita ake ƙarewa tanadi akan banɗaki gidan haya.

"Aikin banza!! Wallahi Ladiyo ki kiyaye ni, kuma ki kiyayi gamuwar mu ni da ke, na ji an ce baki da mutunci, ko ki sa a ranki na dame ki na shanye kuma dai-dai nake da zamaninki."
Iyabo ta faɗa cikin gurɓatacciyar hausarta sannan ta juya ta tafi ta na ta juya ɓaka-ɓakan mazaunanta ta na cigaba da sababi.

A hankali ta shiga banɗakin, wari da zarnin da ya ziyarci hancinta ya kusa hallaka ta,anya ma ba a nan ta kwashi cutar nan ba?


*Nurse Haleemah*

Alhamdulillahi al'amurra suna tafiya daidai yadda nake so ta tura letter kuma an yi accepting,dan haka ta shirya komawa chan next Monday.

Ko da ranar Monday ta zo ta shiga asibitin, ta tsaya suka gaisa ta kuma gabatar da kanta a gaban sabon supervisor ɗin ta.

Ɓangaren adults aka kai ta dama kuma nan ne Field of study ɗin ta.



*Bayan wata ɗaya*

Haka ta fara aikinta ba ji ba gani, kuma ta san yadda ta yi ta fara duba Ammi, kamar wasa shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu.
Ammi ta ɗauki Halima kamar ƴar cikinta, haka ma Halima ta ɗauki Ammi kamar mahaifiyarta, har Gwaggo ta ɗauko ta duba ta.

"Kai Ammi, ki daure ki ƙarasa shan faten nan, kin ga saura kaɗan ko so kike Dr ya ce ba za'a sallame mu ba?"

Ammi da murmushi a kan fuskarta ta ce
"Halimatu ya kike so na yi ne? Ko so kike cikina ya fashe ."
Ta ƙarasa faɗa suka fashe da dariya duka su biyun.

Farouk ne ya shigo ɗakin riƙe da da ledojin fruits.




Sai mun hadu a next page



*MUGUNTA 😈😈😈*




Written by





KHAIRAT ✍️✨





Bismillahir rahamnir rahim


Page 85-86




Bayan wata biyu...


Kafin kace me soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakanin nurse Haleemah da Farouk, soyayya suke gudanarwa mai tsaftar gaske, komai nasu a cikin tsari kuma Ammi ma ta yi na'am da hakan, dan haka ba'a ɓata lokaci ba manya suka shiga cikin maganar.

Yanzun ma Farouk ne a ƙofar gidan su Haleemah suna taɗi, magana suke a kan sa ranar da aka yi nan da wata guda, hira suke yi sosai ta masoya kafin ya ji wayarsa ta hau ruri.
Ciro ta ya yi daga aljihunsa ya ga special number ce, sai ya yi tunanin ko kamfani ne amma kiran na katsewa wani ya kuma shigowa, sanin kamfani ba sa kira so biyu ya sa shi ɗaukar wayar ya kara a kunnensa.

"Assalamu alaikum."

Wata babbar murya mai cike da dattijantaka ta maza ta yi mai sallama, amsawa ya yi ya na son tuna a ina ya san wannan muryar amma hakan ya gagara.
"Farouku ka na ina ne."

Wannan sunan na Farouku ya sa shi dubar lambar da sauri,
"Baba Alhaji."

Ya faɗa da ƙarfi, Baba Alhaji ya amsa mai da ya zo gida ya na nan.

Haleemah kam tsayawa kallansa ta yi, kafin ta ankare har ya shige cikin wata adaidaita da bata daɗe da sauke wata mata ba ya shige ya na mata bye-bye.
Murmushi ta yi ta kada kai ta shige cikin gidan, ta na tunanin ko ma waye wannan ya kira Farouk toh ba ƙaramin matsayi yake da shi a wurinsa ba.

Ta ɓangaren Farouk ya na shiga gidan jikinsa ya yi sanyi ganin Ammi na kuka, kuma ta na shaƙar iska a hankali daga oxygen.
Baba Alhaji ya kasance babban mutum mai faɗa a ji a garin Kano, kuma ya kasance abokin baban su Farouk tun yarinta, amma Alhaji ya fi babansu kuɗi nesa ba kusa ba.

Bayan gaishe-gaishe da kuma bayanin bayan rabuwa, nan Alhaji ya sauke musu sha tara ta arziƙi, ga babban gida da ya mallaka musu, ga kuma wani ƙaramin Company da yace tare suka bude shi da Alhajin su Farouk kafin ya rasu, dan haka ya yi signing a kan yanzu kamfanin ya koma hannun su Farouk da yayyensa...




*Ya labarin Nafee*


Bariki ta buɗe sosai a jahar Lagos bayan shawarar da ƙawarta Lubna ke ɗora ta a kai, ana cikin wannan halin wani babban Alhaji daga Abuja ya bukaci ganinta a nan garin na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login