Showing 42001 words to 44363 words out of 44363 words

Chapter 15 - YAR GIDAN TSOHOWA Docment Complete Book .txt

aikin soja kud'ad'ensa suka fito,
masu yawa wad'anda har ya rasa abunda zaiyi dasu.


Snn kuma anyi posting d'insa a inda zai fara aikinsa a nan cikin garin Abuja tare da commondent general, dashida abokinsa sulaiman."


Mahmud najin hakan yasan da akwai wata ak'asa domin iya d'an zaman da yayi da Alhaji Atiku ya fara karantar wasu halayansa."


Abba da momy sai murna sukeyi, ba'a turashi wata k'asaba dama abunda sukejiwa tsoro kenan,


sunsan barinsa da akayi a garin Abuja da'ayi da sa hannun Alhaji Atiku sunyi farin ciki sosai,
Basuyi k'asa a gwaiwaba Abba da momy suka shiga mota suka sameshi har gidansa a garin Abuja suka kuma yi masa godiya,
Abba yayi godiya sosai ya nunawa Alhaji Atiku farin cikinsa a fili, yace "hak'ik'a Alhaji Atiku kai Abokine na kwarai Wanda samun irinka sai an tona, nagode sosai ina rok'on Allah yabani abunda zan saka maka da wnn halacci da taimako da kayi mana."


Wata irin dariya Alhaji Atiku ya saki a ransa yace "anxo wurin Dama abunda nakeso naji kenan."
A zahiri kuma ya b'ata fuska yace Alhaji Hassan godiyar ta ishini hakan, kanaso ka nunamun cewa mahmud d'anka ne?"
Idan ba hakan ba karka kuma yimun godiya a kan abunda nayiwa d'ana."


Hakan ya rufewa SU Abba baki, daga nan sukayi sallama suka d'auki hanyar gida."


Ranar Monday ya fara aiki a garin Abuja a ofice d'in Alhaji Atiku.


Hakan shima sulaiman duk a tare suke aikin a wuri d'aya aka ajiyesu."


Aiki suke akan gaskiya domin sun d'aukarwa k'asa Alk'awarin cewa xasuyi aiki a kan gaskiya musamman mahmud."


🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _'Yar Gidan tsohuwa_)😅














Writteng
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Bashir_)










*31*












Zaman da mahmud yakeyi a office d'in Alhaji Atiku ya fahimci mutum ne marar adalci Wanda baya tausayin na k'ana dashi."


Muddun kaga Alhaji Atiku yana sakar maka fuska tare da kyautata wa. To tabbas akwai abunda yake buk'ata daga gareka."


Mahmud ya fahimci cewa Alhaji Atiku mutum ne mai yawan mu'amala da mata
Kuma yafison matan aure,
Agaban idonsa zai aika akira masa matar yaronsa Wanda ya kwad'aitu da ita,
Yayi mata barazana da cewa ko ta Amince masa tabashi kanta ko ya sanya a kashe mijinta."


Hakan wasu matan ke amince masa, da zarar ya dad'addani xumar macce tayi masa to shikenan zai san ynda yyi ya d'auke mijinta, daga garin yyi posting d'insa can wani gari mai nisa inda ba zai iya tafiya da matarsa. Ta anan Alhaji Atiku zai samu dama ya dinga kasancewa da ita."


Wnn mugun halin nasa ya kuma sanyawa mahmud yaji ya tsanesa ya kuma tsane duk wani Abu da yake fitowa daga garesa yana masa biyayya ne kawai saboda umurnin da Abba yabashi."


Yau ne Yusra take dawowa daga England,
Inda aka shirya mata kwarya kwaryar liyafa. Alhaji Atiku baya zaune baya tsaye sai kai da komo yake yana murna yau zaiga shalelensa."




Mahmud yabawa umurnin yaje ya d'aukota airport,


Baiyi masa gardama ba, ya d'auki key d'in mota yana sanye da uniform d'insa ya nufi airport."


Xuwansa kenan jirginsu ya sauka yaja wuri d'aya yayi parking yafito hard'e da hannunsa a k'irjinsa,
ya jingina a mota, yana kallon duk Wanda ke fitowa a jirgin d'aya bayan d'aya."


A can ya hango ta tafito sanye cikin k'ananun kaya riga da wando wad'anda suka d'ame mata ajiki, duk ilahirin surar jikinta a waje take."


Idonta sanye da k'aton glass bak'i kanta ba ko d'ankwali
Kai da ka ganta sai ka rantse da Allah kace ba 'yar musulmai bace."










*yasin yau wuyar typing nkeji kuyi hkr da wnn*🤓🤓


🌹 *DEEJAMAH*🌹
( _'Yar Gidan tsohuwa_)😅














Writteng
By
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Bashir_)










*32*












Kallo d'aya yayi mata ya kauda idonsa gefe,
Domin baya son ya kuma kallon nakasanshen jikinta wnda ta ke tallatashi a kan titi."


Baiyi yunk'urin zuwa ya tarbotaba kamar ynda sojoji suke mata."


Waige waige tashigayi tana Neman wad'anda daddy ya turo mata domin su d'auketa, amma bataga kowa ba."


Anan take ranta ya b'aci, ga zafin rana yana dukanta duk ta had'a zufa,
Mahmud yana gefe cikin inuwa yana kallonta cike da tsana,
bazai iya zuwa ya tarotaba bare ta ganshi duk lokacin da ta hangoshi da kanta tana iya zuwa sutafi."


Ranta ya b'aci ta d'aga waya takira Daddy cikin hushi, "daddy halan bakayi farin ciki da dawowata bane kabarni cikin rana tana dukana."


Ya kwantar da murya "haba shalelen daddy ai daddy bai isaba, ki duba naturo mki masoyinki Mahmud domin yazo ya d'aukeki, ki dubashi tun d'azun yazo wurin kinsan halinsa wani irin kalar hali garesa Wanda da wuya ka iya gane inda ya dosa."


Kidubashi yana wurin,
Bata jira ta kuma jin abunda yake fad'aba,
ta kashe wayar da sauri
Domin jin ya ambaci sunan mahmud."


Duk wayar da takeyi da abunda take cewa mahaifinta Mahmud yana kusa da ita jingine a motarsa yana kallonta, kuma yana jinta,
bata ganshiba, ta gabansa tabi ta wuce janye da kwatin kayanta amma ko kallo bata ishesaba."


Hand bag d'inta ta sub'uce ta fad'i k'asa a gefen k'afarsa, cikin sauri ta duk'a domin ta d'auka
tayi tozali da zararan ya tsun k'afarsa wad'anda suna d'aya daga cikin abunda yake burgeta a jikinsa."


Bata d'auki jakarba tayi saurin mik'ewa da sauri cike da murna tayi kansa ta rungumasa tana fad'in "haba sweety duk ka wahalar dani wurin nemanka a she kana tsaye kana kallona."


Bata k'arasa maganartaba ya finciketa da k'arfi daga jikinsa yayi wurgi da ita, sai da ta kusan fad'uwa k'asa. Ya juya yyi shigewar sa mota ya zauna ransa duk a jagule yake,
yana jiran tashigo su wuce."


d'ago kai tayi ta kallesa, ta kuma kallon mutanen dake kallonsu mafi yawansu duk sunsanta sunsan ko waye haifinta."


Dakewa tayi ta k'ak'aro murmushin dole ta kuma duk'awa ta d'auki kayanta ta nufi motar Wanda tuni ya tayar da ita yana Neman tafiyar sa."


Da kanta ta bud'e but ta sanya kayanta abunda bata tab'a yiba a rayuwarta,
snn ta zagayo tashiga gidan gaba had'ida kallon fuskarsa Wanda take burgeta tayi murmushi."


Mahmud bai dubeta ba illah ya yatayar da mota ya d'auki hanyar gida."


Kallonsa tayi taji wani irin sonshi ya durar mata a zuciya, ta kashe murya tace "akan sonka na shirya d'aukar duk wani Abu daga gareka, INA sonka kuma sai ka aureni ko da kai baka sona."


Da sauri ya juya ya kalleta yyi mta kallon tsana, yace "ni kuma na tsaneki bana sonki saboda ke nakashashiyace, ki daina yaudarar kanki akan cewa sai kin aureni, har Abada bazan tab'a aurenki ba."
Baki cikin tsarin matar da zan aura."
Yana kaiwa nan, bai kuma saurarenta ba yaja mota da k'arfi saura kad'an kanta ya daku a motar irin ynda ya fisgeta."


Idonta ya cika da hawayen Kalmar da ykirata da ita ta nakashasshiya,
Ta kallesa ta d'aga murya da k'arfi tace "karya ne mahmud niba nakashasshiya bace,


Ka dubeni da kyau inada cikar halittar da akeso a kowacce macce."


Murmushi ya saki Wanda ya kuma fitar mashi da kyawon fuskar sa, ganinta da yyi cikin b'acin rai yasanya rayuwarsa tayi


Kai tsaye gidansu ya nufa inda aka shirya mata kwarya kwaryan liyafa daddy tare da mommy zaune suna jiran isowarta gefen Dama da hagonsu sojoji zagaye dasu."


Ana ganin isuwarsu ko wanne soja yanufi motar domin tarbo shalele."


Batabi takansu ba kamar ynda tasaba yi masu, ko kallo basu ishetaba bare ta amsa gaisuwar da suke mata kai tsaye wurin daddy ta nufa ta rungumeshi had'ida sakar masa kiss a gefen kunci,"


Shima cike da murna ya kuma k'ank'ameta yana mata oyoyo suna dariya,
Tajuyo ta kalli mommy tace hy mommy snnu da gida."


Kallo d'aya mommy tayi mata ta kauda kanta, domin ta tsani rayuwar da 'yar tata take gudanarwa Dan hakan take cewa bata sonta daddy ne kawai yake sonta."


Mahmud na ganin hakan, yayi Allah wadai da rayuwar da suke gudanarwa ya kuma jin tsanarta da ta mahaifinta ya mere baki had'ida Jan dogon tsaki ya bar wurin."


Wuri yasamu nesa dasu ya zauna amma duk abunda ake gudanarwa yana gani."
Zaune yake yana latsar wayar hannunsa pix d'in dijama yake kallo wad'anda yayi ta d'aukarta tana sanye da uniform a lokacin da ya je makarantarsu, kallo yakeyi yana murmushi har ya mnta da b'acin rain yusra."


Sallama yaji anyi masa a gefensa d'aga kai da zaiyi wazai gani fareeda ce matar sulaiman janye da yaronsu."


Cikin fara'a da sakin fuska ya suka gaisa har da d'an zolayarta yyi, yana fad'in bata iya kwana biyu idan bata sanya sulaiman a idoba."


Tana dariya tace "eye naji Dan Allah jeka ka kiramun shi."


Shima dariyar yakeyi yace bara na taimaka mki nkira mki shi."


Ya mik'e tsaye ya nufi inda sulaiman yake a can kusa da Alhaji Atiku ya take masa baya hannunsa rik'e da bindiga saboda tsaro."


Sulaiman mutum ne Wanda baya wasa da aikinsa a cewarsa aikinsa shine gatansa shine uwarsa shine ubansa marayane gaba da baya, a hannun k'anin mahaifinsa ya tashi Wanda shima talaka ne abincin da zasuci wuya yake masu."
Kuma a hakan ya aurawa sulaiman 'yarsa fareeda Wanda suka tashi cike da soyayyar junansu."


Da taimakon Allah kamar da wasa aka fitar da form d'in soja fareeda ta sayar da kayan d'akinta tabawa mahaifinta ya sayawa sulaiman form d'in,
Cikin ikon Allah sunansa ya fito, wnda gashi a yanzun ya fara wadata a aikin soja, domin ya sayawa k'anin mahaifinsa k'aton gida ya kuma bud'a masa babban shago na sayar da atamfofi."


Kai tsaye mahmud ya tunkari wurin inda akeyin liyafar domin kiran sulaima, yusra tana ganinsa takar masa murmushi tana Neman ta bar wurin tazo wurinsa,
Alhaji Atiku na ganin hakan yayi saurin rik'o hannunta ya dawo da ita a inda take yana mata magana k'asa k'asa Wanda su kad'ai sukasan abunda suke cewa."


Mahmud bai damu dasuba kai tsaye wurin sulaiman ya nufa yashiga yimasa magana cikin harshin turanci cewa fareeda tazo gata can tana jiransa."


Jin hakan sai da yasaki murmushi jin dad'i yacewa Mahmud ya kaita masaukinsu da ke nan cikin gidan can layin sojoji, ya ajiyeta,
Had'ida kawo mata ruwa da abinci tasha kafin yazo."


Murmushi Mahmud kawai yyi ya juya ya tafi,
Idon yusra akansa tanajin wata kalar wutar k'aunasa tana ruruwa a zuciyarta domin mahmud jarumi ne daga ganinsa zaiyi jarumta wurin tafiyar da macce a kan gado."


Tunshigowar fareeda wurin idon Alhaji Atiku ya sauka a kanta, yana ganinta yaji gaba d'aya hanlinsa ya tashi so yakeyi kawai yajishi ya kad'aice da ita."


Mahmud na tafiya ya kalli sulaiman ya masa nuni da hannu a lamar yaje wurin matarsa ya kuma zaro kud'i cikin aljihunsa dubu ashirin ya mik'a masa yace kasaya mata kayan motsa baki."


Cike da murna sulaiman ya runsuna ya karb'a yana godiya, yatafi wurin fareeda."


Da isarsa mahmud yana fitowa daga d'akin,
Cikin murna sulaiman ya tareshi yana dariya yana fad'a masa Alherin da Alhaji Atiku yayi masa."


Gaban mahmud ya fad'i ya zaro ido yace "ina fatan baiga shigowar fareeda ba?'


Sulaiman yasaki dariya yace "maiya faru idan har ya ganta?"
Mahmud yace "no bakomai tambaya ce kawai nayi, yayi wucewarsa, yana tunanin tambas Alhaji Atiku fareeda yagani tunda har yabawa sulaiman kyautar kud'i, Dama hakan yakeyi da zarar ya kyallara ido yaga matar yaronsa in dai har ta kwanta masa zai dinga yiwa yaron nasa Alheri na Jan hankali."


*******************


Bayan an watse daga wurin liyafar kowa yakoma wurin aikinsa,
Alhaji Atiku da shalale sai zuba mashi shagwab'a takeyi akan wutar son mahmud dake ruruwa a zuciyarta."


Ransa ya b'aci ganin ynda shalele take zubar da hawayenta akan wani d'a namiji kuma yaronsa, Wanda yake da iko dashi har da mahaifinsa."


Janyota yayi a jikinsa ya shiga share mata hawayen da ke zuba a fuskarta yace "daga yau kukanki ya k'are indai akan mahmud ne."


Wayarsa ya d'auka yashiga kiran number Alhaji Hassan mahaifin mahmud."


Abba yana ganin wayar Alhaji Atiku tunkafin ya d'auka sai da yasaki dariya snn ya daga wayar had'ida sallama,
Alhaji Atiku ya amsa masa yana mai sakin fara'a a fuskarsa."


Bayan sun kammala gaisuwar ne Alhaji Atiku yake shaida masa gobe yyi sauri yazo garin Abuja akwai meeting da zasuyi game da harkokin siyasa."


To Abba yace yana mai d'auke da fara'a da jin dad'i a fuskarsa, snn sukayi sallama ko wanne ya kashe wayarsa."


Ya juya ya kalli yusra yasaki dariya mai sauti yace "nayi mki Alk'awarin bazaki tab'a Neman wani Abu kirasaba, ki sanyawa rayuwarki a gobe za'a tsayar da ranar aurenki da Mahmud ko yaso ko baya so wnn matsalarsa ce."


Washe gari bayan Abba ya sauka garin Abuja sunshiga meeting da manya yan siyasa, anan take da San hannun Alhaji Atiku aka tsayar da Abba a matsayin d'an takarar gwamna. Kasan cewar Alhaji Atiku shikeda jama'a dan haka ko wanne d'an takara yakeyi masa biyayya."


Sauran mutunen wurin sun Amince da zab'en Alhaji Atiku anan aka umurce Abba da ya biya kud'in k'ungiya naira milyan talatin."


Abba yayi shuru domin baya da miliyan talatin, ganin shurun da yayi yasa Alhaji Atiku ya fahimce cewa baya dasu, yasaki murmushi a ransa domin hakan yakeso ya gani."


Anan take Alhaji Atiku ya cika cak d'in kud'in ya bayar."


Zaro ido Abba YAYi cike da mmki zaiyi magana Alhaji Atiku ya dakatar dashi alamar yayi shuru idan aka tashi akwai maganar da zasuyi."


Bayan kowa ya watse daga meeting d'in akabar Alhaki Atiku da Abba a office d'in Abba sai godiya yake zuba masa wanda har yarasa abunda zai fad'a."


Alhaji Atiku ya dafa kafad'arsa yace dainayi mun godiya hakan ta isheni, kasani duk abinda nayi maka ban fad'i ba saboda kai abokinane kuma aminina na gaskya. Komai nawa ina iya mallaka maka shi a kyauta"


Wnn dalilin yasa saboda mu kuma dank'on zumunci mu ya d'ore har d'iya da jikoki na yanke shawarar mu had'a 'ya'yanmu Aure mahmud da yusra."

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login