Showing 3001 words to 6000 words out of 58231 words

Chapter 2 - DAN SHAYE SHAYE NE BY OMH TEEMERH S1.txt

10 Jul 2024

5899

da wani 'katon saurayi suna aikata alfasha akan bed d'ina wannan abun yayi matu'kar gigitamun 'kwa'kwalwa, dan haka najuya nafuta, tunda har lokacin basu san nashigoba...


Futa nai nazauna akan 1sitter ina runtse idona,na jingina kaina akan kujerar bayan kamar 9m dafutowata sai naji suna 'kyal'kyala dariya suna fad'in komai yayi dai² suna tafawa.....




Jinai tace "Gobema kadawo kaji, wannan shasha Shan d'an shaye²ⁿ bazai gane anshigoba zan gyara masa komai kafun nafuta, kaga mun huta da zuwa hotel ma nan ya ishemu kohhh...!!!!




"Kwarai kuwa tunda tsawon 3week’s kenan muna zuwa ba'a ta6a kama muba kinga kud'ina ma yahuta nakama d'akin da nake kullum a hotel....!!!!


"Aikam baby saikana bani kud'in kooooo.....?
Hakane kam yanzuma zan yimiki transfer d'insu dan kin cancanci hakan harma fiye da hakan.......


Dariya suka saka suna shewa, hakan yasani jin zafin abunda naji tana fad'a, kenan wannan bashine nafarkoba, sannan kuma nine shasha shan d'an shaye²....


Tashi nai nabanka d'akin rai a6ace, abun takaicin har lokacin, ita bata saka kayaba, amman shi yasaka komai nasa kamar basuyi komai ba....!!


Duka nafara kai masa saiya kauce, na'kara kai masa duka sai taja towel ta d'aura, tanayo inda muke tsakiya tashiga tana fad'in wlh ka'kara dukan sa saina d'au *MATAKI* ...!!!




Kallon tanai cikin mamaki nace " *MATAKI KUMA..!!?*
Tabbass ko kana tunanin bazan iyaba...!!
"Matakin me zaki d'auka dan ina dukan wanan d'an iskan shine zaki d'auki mataki, to bisimillah...


Hhhh tasa dariya tana fad'in d'an iskaaaa... Kace fa.....
Aigwara shi kaida kahad'a biyu ga bin matan banza ga shaye sheyen d.......


Ban bari ta 'karasaba cikin zafin nama, wlh bansan lokacin dana d'auketa damariba...
Fad'uwa tai, sai ta tashi tace wlh zakai nadamar wanan marin dakai mun...


Kiran kwarton nata tai tabud'e sirrin tacciyar 'kofata tacikin d'akin tace yagudu....


Nikam mamaki nakeji dan bansan ya akai tasan da wanan 'kofar ba...
Ina cikin wanannmamakin ma yasa banje nabisuba.....
Ina tsaya dan jiran tadawo sama da minti 10 amman shiru zama nai abakin kujerar dressing mirror na inajiran dawowarta...!


Dan nai alkawarin dukan ta yau sosai, koda hakan zaisa Hjy Hindatu tazageni.
"Dan basau d'aya ba, basau biyu ba, ansha zuwa ana gayamun Ikilima nabin maza, idan nagayawa Hjy bata yadda saitace naiwa 'yarta sharri.


Ko kuma idan naje gayawa Abbie tace yau ma ansha an bugune za'aiwa "yata sharrin da'aka saba, tunda tafad'a maka 'karya ko....
Muna fiki kawai, wlh Alhaji 'karya yakeyi, haka zata 'karyatani agabansa, shima Abbie saiya yadda yace ba'a yadda dazancen d'an shaye²....


Wanan shine kalaminta da zarar nafad'i wata kalma akan yaranta...
Kuma Abbie ya yadda...


Ina cikin tunanin nan sai naji ana nocking sosai da 'karfin gaske, yadda kasan za'a ciremun 'kofar parloun, futa nai dasauri ko itace tadawo tanan, amman sai naga Abbie da Hjy Hindatu ina bud'ewa, ganin fuskar Abbie babu annuri shida Hjy Hindatu yasani shiga cikin kokonto.....


'Daukeni da mari Abbie yafarayi yana cewa tana ina....!!!!!!!
Tana inaaaaa nace maka.....!!!!!!
"Janyomun kwalata Hjy Hindatu tai tace dan ubanka ina "yata take, ina fatan baka keta mata haddiba dai kooo........?????




"Haddi kuma.......?
"Au tambaya kake, kajimun mara kunyar 'karya, shegen yaro, d'an shaye² kawai......!!!
Wani abu naji yadakarmin 'kirji sosai nad'ago idanuna dan tambayar wasuke nema, amman banyi auneba naji wani saukar Marin, dafe wajen nai ina sake d'ago kaina danyin mgn..
Wani saukar marin na'karaji, kafun nayi wani motsi naji wani.....


Ba magana nake makaba Fawass ina Ikilima take dan uwarka....
"Tunda bata baka tarbiyyaba shine zaka 'ketara 'kanwarka ubanku d'aya da ita...


"Kenan bayan shaye² harda zina ka had'a, kai fasi'kine dama, ina ganin wanann 'kaddarace Allah yajarrabeni da ita na fara shaye²ⁿ nan naka ashe kace harda zinama zaka fara..
wa'iyazubillahi Abunda nafurta kenan.....!!
Au kajimun d'an iskan yaro Alhaji mune shed'anun kenan ina kakaita nacee......!!!


Kuka Abbie yasaka yana 'kara shararamun mari yace ina kakaimun yarinyata.....
Bari inje induba tunda nagakai bazaka ganeba danba kaine kad'auki cikin nataba tsawon wata 9 dazafi da sanyi da damuna duk ban gajiyaba, nai mata tarbiyya tsawon shekara 22 amman yanzu ka kasa magana ma wanan d'an iskan d'an shaye²ⁿ yanuna maka Ina yasa ta tunda yayi mata fyaden, da Nasma ce ai bazaka bisa ahankaliba amman dayake "yatace shiyasa kakebinsa sannu sannu...


Shiga tafarayi tana dubata, d'akina tashiga shikuma yajawoni yayi wajen d'akin dani yana kaimun naushi yana cewa ita take....!!


Har bakina yafara futar da jini amman nakasa koda motsine dan nakasa gane kan komai wlh.....




Muna shiga d'akin muka tarar da Ikilima akwance akan gado gawani jan abu yana zubowa ta'kafarta tana kuka sosai kamar nagaske.....


Inna lillahi wa inna ilaihi raju'un....
Nashiga uku Alhaji yayi mata fyad'e zokagani....
Wayyooo Allah naaaa wlh yacutar mun da yarinyata, yagama illata mata rayuwa......




Wayyooo Allah naaaa...
Yanzu waye zai aureta yakashe mata rayuwa
"Dan uwanka ya illataka wannan ai masiface wlh, najikinka yacutar dakai....


Allah ya isa tsakanina dakai, duk halaccin danai maka nari'keka tsawon shekara 11 amman da wanan zaka sakamun.....


Ita tambad'ad'd'iyar uwar taka tuda ta tafi aiharyanzu bata dawoba haka tabarku kaida Nasma inashan wahalarku, amman karasa dame zaka sakamun saida wanann kooo, Allah yatsine maka Albarka, daman menene amfanin ajiye d'an shaye² acikin gidan ma'aurata, wata ranama aisainima yace zai ketamun haddin...


Kama Ikilima tai tana cewa tashi muje kigyara jikin ki akira doctor yazo yadubaki yaga idan kina da ciki azubar dashi dan wlh bazan lamuntaba, abarni da wannan kayan ba'kin cikin ma, naketa miki haddi dayay, wlh da da aure tsakaninku saika aureta, mema zanyi da shegen d'an shaye² kawai ...


Alhaji ka kira Doctor yazo yadubamun yarinya, Tunda ba'asan tun yaushe yake mata hakan ba, yaunedai Allah yabata sa'a ta tona masa asiri.....


Shikuwa Abbie mutuwar tsaye yayi yana fad'in kacuceni wlh kacuceni Fawass Allah yasaka miki Ikilima...




Shiga da ita akai bathroom tagyara jikinta aka kira doctor tunkafun tafutoma, data futo yazo , fara dubata yafarayi, Hjy Hindatu kuwa sai kuka takeyi tana tsinemun albarka....


Nan yad'auki fitsarinta yayi test yace bata da ciki, yabata magani sanan yace yanasan yayiwa Abbie bayani, amman 'kememe Hjy Hindatu tace suje yagaya mata basai angayawa Abbie ba sbd shi baisan ciwon taba...




Koda tabishi, data dawo saita'ki fad'in gaskiya sai tace yace wai arin'ka taka cancan dani sannan yakamata araba mana guri da ita....




Mamakin danake cikine da kuma 'kazafin zinar da akaimun yasakani nakasa fad'ar komai...


Saidaga baya natuna da *CCTV camera* din gidana nace wa Abbie yazo in nuna masa CCTV camera yagani wlh ban mata komai ba hasalima da wani naganta akwance akan gado na....


Wani wawan mari Hjy Hindatu tasakarmun tace ma'karyaci muje agani d'an shaye² kawai....


Tafiya mukai d'akin da na ajiyeta mu duka nakunna CCTV camera aikuwa..


✴✴✴


Kukantane yadawo dasu daga hirar dasuke.
Cikin hanzari tami'ke zaune tana sakin kuka....
Tasowa sukai gabaki d'aya suna kallonta, lpy meke miki ciwooo.
Kallon Fawass tai tace....... ✍🏻✍🏻✍🏻








*TSOKACIN👉🏻👌🏻*




*JINKIRIN AURE*


*JARRABA NE DAGA ALLAH!*


Komai kusancinka da alakarka da *MACE* , kar ka tambayeta:


• Yaushe za ki yi aure?
• Ba ki yi aure ba har yanzu?


Irin wadannan tambayoyin, akwai wadanda saboda takaici da ciwo, har KUKA suke in sun shiga daki.


Kai ba zaka gane irin radadin da suke ji a ransu ba narashin auren, dakuma san dasukeyi suga suma sunyi auren ba.


Kamar kai ne ka gamu da jarrabawar ka *SPILLOVER* a jami'a, shekaru 2 kana zuwa gyara; wani ya tambayeka cewa, " *ME YA SA HAR YANZU BAKA YI GRADUATION BA?"*


*AURE* a karan-kansa, ba kan kowa ya wajaba ba, matukar ba zaka afkawa alfasha ba.


Akwai wadanda aure ya zame musu wajibi, wasu mustababbi (abin so), wasu makruhi, wasu ma haramun ne a kansu su yi auren.

Wannan ka'idar tana hawa kan kowanne jinsi, 'namiji' ko 'mace'.


*AURE BABBAR NASARA CE A RAYUWA*


*MUSAMMA GA 'YA MACE*


Amma babu inda addini ya ce, in mace ba ta yi aure ba, ta zama 'wata mai laifi' ko in ta mutu bata yi aure ba zata shiga 'Aljanna' ba.


Ba laifi ba ne ina mace ta zauna ba aure, matukar zata kiyaye mutuncinta.


A al'adarmu ake ganin, in mace bata yi aure ba, tamkar wani *LAIFI* ta aikita, ko a cikin gidaje, a gaban iyayenta, a yi ta tsangwama mata, kullum a cikin takaici take saboda batayi aure ba.




*JAN HANKALI GA IYAYEN MU*


Kada ku takurawa yarinya akan lalle ² saitayi aure dan zata iya kwaso koma waye ta kawo muku, batare dako tanasan saba ko kuma batasan saba.


Sanan kuma kada ku tilastawa yarinya akan lalle saita auri ra'ayinku, tabar nata.


Wad'an nan matsalolin guda biyu suna haifar da babban 'kalubale acikin rayuwar aure sosai....




Aduk lokacin dakukaga yaranku basuyi aureba kamata yayi kudage da addu'a, ku dage da ro'kon Allah yakawo musu miji nagari, baku takura suba, ko kuma ku tsangwamesu.....✍🏻✍🏻


*Allah yasa mu amfana* 👏🏻👏🏻👏🏻


*Keep waiting my fan's....* 🤗🤗😍
*Mrs Hallsad😍😘*
*Omh teemerh_🌹 🌹*






*Gamasu san sufara biya da wuri saiku tun tu6i wannan number 08032762588*
*_Idan kuma ta account ne_*
*_Acc 0110015052_*
*_SADIYA ABDULLAHI UMAR_*
*_ECOBANK_*


```Idan kuma katin wayane na
#400 ne kachal```
```Comment section kuma
#200 ne kachal wannan sau'kine agareku
My special group kuma
Da```
*'Dan shaye shaye ne* 🍾
*Am 16 years old* 💃🏻
*Sanadi* 😭
```Duka #400 ne zaku biya wannan kyautar girmamawatace agareku saboda comment d'inku mai sharhi yana burgeni, yana sani nishad'i wlh, Idan banga comment dinku ba harjina nake wani iri, inayinku wlh🥰🥰.
```
[01/10, 8:51 PM] Omh Teemerh 🥰😘🥰: _*📲 TYPING📲*_
_*"🍾DAN SHAYE SHAYE NE🍾*_
_*paid book #300 only*_
_*By*_
_*OMH TEEMERH*_
_*👑THE QUEEN OF THE WRITER'S👑*_




🤍🤍🤍🤍⚜️⚜️⚜️🤍🤍🤍🤍
_*DASHEN🌲ALLAH*_
_*WRITER'S 📖 ASSOCIATION*_
******************************
*'KUNGIYAR DASHEN🍃ALLAH* _'kungiyace tajajur tattun marubuta kuma tsayayyu masu aiki da ilimi wajen rubutunsu_
*Dan ganin sun kawo muku labari wanda zai wa'azantar daku ilimantar daku, fad'akar daku, kuma ya nishad'antar daku*
*AL'KALAMI✍🏻 YAFI TAKOBI🗡*
******************************
🤍🤍🤍🤍⚜️⚜️⚜️🤍🤍🤍🤍


_*WANNAN BOOK TUN DAGA FARKONSA HAR 'KARSHE SADAUKARWACE AGAREKI AUNTY ZAHRAH*_
_*FATIMA ZARAH*_
_*BLOODY NAH*_
_*🥰🤍🥰*_




*EPISODE* 7⃣⏩8⃣






...............Kallon FAWASS tai tace "Ina fruit d'ina suke kabani"
"Kayi hkr komai zai zama labari"
"Nidai kabani fruit d'ina nasan idan naje gida kasheni ne kawai baza'aiba wlh....
wani kukan ta'kara sakawa mai ta6a zuciyar mai sauraron ta, gashi kanaji kasan yaci 'karfinta sosai...


Fawass ne yaruntse dara²ⁿ idanunsa dasuka fara canja kala, jin kukan natayay kamar zubar dalma acikin zuciyarsa..


Matsawa yay kusa da ita yace
"shiiiiiiiiii yana d'aura hannunsa akan tattausan la66ansa"


Saka hannuwanta tai guda biyu tana ri'ke bakinta, wasu sababbin hawaye suna sauka akan kuncinta....


Zama yay acan gefe kusa da ita cikin tattausar muryarsa yace mata
"Kiyi hkr za'abaki fruit d'inki, yanzu kigaya mana inane gidanku saimu maidake.....!


Kallonsa Tahir yay dasauri yana cewa "kasan me kake cewa kuwa....?
Kanne masa ido yay yace "yes"


Jinjina kansa yay, alamar yafahimta
Shima matsowa yay gefen Fawass d'in, cikin sigar kwantar mata da hankali yace, kigaya mana inane gidan ku kinji 'kanwata kinga kaiki zamuyi, mubawa iyayenki ha'kuri, muce matsala aka samu jiya kinyi accident ne mu muka bigeki......!!


Kanta kawai take jijjigawa alamar a'a, takasa furta komai, dan tarigada tasaba da wannan warning d'in nan awajen KAUSAR dan data daketa take mata hakan dantai shiru, idan ta'kiyi tazaneta, sabon dukama kuwa.....!




OMG kinga kinutsu kinji karki sakawa kanki damuwa, kinutsu kinji ko bakijine....., babu abunda zasuyi miki, kinga yanzu jikinki bai gama warkewaba, idan kika tafi acikin wannan yanayin zaki samu matsala kinji....




To nii daiii kawai kubani fruit d'ina intafi...
Fawass ne ya yun'kuwa yad'auko allura yahad'a sannan yace mata "Kigaya mana inane gidanku ko kuma inmiki allura har guda 10 yanzun nan....!




Zare ido tai dan tanadajin tsoron allura sosai, cikin sar'kewar murya tace " sorry please ....!




Murmushin gefen baki yayi dan shibaisan ma tana tsoron ba yadai fad'ane kawai, saidai yafad'i hakan ne kawai saboda yasan mata da tsoron allura sosai....




Tahir ne yayi murmushi yace "to yanzu kifad'a mana inane gidanku, da kuma sunanki da kuma sunan mahaifinki dana mahaifiyarki....?


Wani dummm taji acikin zuciyar ta dataji yace mahaifiyarta, wasu alll mata daga cikin idan ta.....




Oohhhhhh sorry Fawass yace, dan an tambayeki sunan ki dana iyayenki...


Jan hanci takeyi tace "No, ba haka bane...!
"Menene to"
Cikin sar'kewar murya tace "wani abu natuna dayace yasunan mahaifiyata"
"Ayya.., sorry kinji.. "
Tahir ne yace "to ina mahaifiyar taki take....?
Cikin sanyin murya tace "Nima ban san taba....!
"Baki Santaba....? Fawass yamai maita.
"Kallonsa tai da luluh eyes d'inta masu d'aukar hankali tace cikin sar'kewar muryar ta data fara dashewa sbd kuka
"Tamutu randa tahaifeni, nima ban ta6a ganin ta....... "
Kukan dayaci 'karfin tanema yasata takasa 'karasa maganar datakesan yiii..!

Wani irin tausayinta yaji yakamasa, baisan lokacin daya ''karasa wajen datakeba ya saka hannunsa yatallabota yace mata "Is okay dear, sorry "
"Sorry please , sorry ... "


Jan zuciya tafarayi hartai shiru kuma
"Fawass yace "To yanzu gaya mana address d'inki dakuma number dakika haddace ta"yan gidanku...


"To Amman idan kakira kar kace kai kabugeni, kace Wanda yabugeni , bai tsayaba guduwa yayi kaine kazo wucewa kaganni...


"Zare ido yay jin tana shirga 'karya...
"😦what...?
"Please kace musu haka idan bahakaba, zasumun wani 'kazafinne cewa zasuyi bun maza natafi zan 6ige dacewa kabugeni....
"Bin maza kuma....?
"Ummmm"
To meyasa....?
"Sbd anta6a bigeni, dasukazo sai suka had'a baki da Wanda yabugeni sukacewa daddy na wai asabon gari yaganni nida kwartona shikuma yazo wucewa bai saniba yabugeniii
...
"Lokacin saidai daddy na yayi kuka,yazaneni sosai saida nakwana 10 ko bud'e idona bana iyayi...
Sai daga baya yakirani yanatamun fad'a yace mun ba haka mommy na takeba, kuma idan nasake saiya kasheniii....
Jinjina kansa yay yace "toooo"


Shikuwa Tahir duk mamakin Fawass ne yakamasa, danshi Sam bamai san magana bane, saikai taiwa Fawass magana bai kula kaba, kuma ko acikin abokanai bai fiya zama ba dan bayasan takura, da hayaniya......


Koda sukai karatunsu a'kasar China har yagama yadawo baida aboki ko d'aya haka ma budurwa, dan lokacin dasuka gama ma sunje Turkish nan ma sun dad'e kafun suka wuce Landon Amman koda wasa bai kula mace, duk kuwa danacin dasuke masa...


Dan "yan mata sunsha kwana a'kofar gidan da suka zauna awaje danya kulasu, Amman ko iskar data ibosu baya kallo bare ma har susa ran zai tanka musu


Amman yau yazauna sai zance yakeyi shida wannan yarinyar, wadda bata wuce sa'ar "kanwarsa ba.....
Indai kaga zancen Fawass toka tabbata shida NASMA ne
Ko kuma da mara lpy ne, Shima mara lpyr dan yasan Menene matsalarsa, yabasa maganin daya dacene, dakuma kyaky kyawar kulawa.......


"To inajinki gayamun....! "
"Ni sunana fateemah, amman ana kirana da Imhal......


"Damm Fawass yaji danaji tace Fateemah, kuma ana kiranta da Imhal.


Dankewa yay dan yanasan yacimma gaci azancen nata...


"Kuma gidan mu na a bayan filin sukuwa wajen gidan Commissioner 'yan sanda, kafun muje titin gidansa....!


Fawass ne yace " Okay Number nawane

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login