Showing 33001 words to 36000 words out of 38424 words
Chapter 12 - Surbajo Book Complete document by Zahra Muhammad Mahmud .txt
bakya ganin kamin nakai kaduna yanzu dare zeyi sosai amman ko ajikinki meyasa kike son zama mara tausayine?,pls kibarni na kwana da safe sena tafine."
"Tab'd'ijan ay wlh sede kafad'i duk abinda Kaga dama amman wlh bazaka kwana agidannanba inko kace seka kwana to wlh ni bazan kwana acikiba, dan haka kajuya katafi dannasan aranka sokake katafin gulma ce kawai irin taku ta maza masu bakin ganga Kaga kawuce ni na rufe k'ofata".
Murmushin taka'ici yayi,yajuya yafice daga gidan,hotel yakama yakwana washe gari yawuce kaduna,shi abunma dariya yake bashi wato da gaske ne kenan zancan da maza sukeyi nacewa in matanka suka had'a kai to wlh ubanka zasuci, shide ko ba haka bane shi yayarda tunda gashi sanadin had'in kannasu kowa batason shiga hakkin kowa shi Kuma sun maidashi kamar ball wannan ta buga ta ba wannan.
Maman Yusuf
[4/13, 9:59 AM] βͺ+234 703 962 5239β¬: ππππππππ
*SURBAJO*
ππππππππ
Zahra Muhammad Mahmud
*this page is dedicated to Muhammad indimi family more especially Presido Adama,maryam,hauwa,Allah yakareku a duk inda kuka shiga nagode*
*pure moment of life writers*
*p.m.l*
*page 85-86*
Ya iso kaduna lfy a kitchen yasamu Aisha tana wanke wanke,tabaya yaje ya rungumeta yace,
"Ta honey me ake tanadarmana ne haka",da sauri tajuyo tana kallonshi cike da mamakin ganinshi zatayi mgn yarigata,
"wlh koroni tayi ko gidan bata bari nakwana ba wai dole sena dawo gurinki nasan cewa zakiyi Meya dawo Dani yanzu to koroni akayi kuma wlh bawacce zata K'ara korata na koru,nadawo nan bayan Sati biyu zantafi laifin damuka yimata ta yafe, so banason wani dogon turanci,"yafad'a yana d'aure fuska gudun kartaga k'ofar rainashi.
Abun dariya yaba Aisha ganin yadda yake kumbura, janshi tayi suka koma d'akinshi taimakamasa tayi yayi wanka yashirya suka sakko suka ci abinci sannan yakira Surbajo awaya bayan sungaisa yaba Aisha nan fa suka shiga hira bame cewa kishiyoyine, seda kud'in wayar yak'are suka hak'ura.
Rayuwar su taci gaba da tafiya Cikin so da k'aunar juna babu meson ganin bacin ran d'an uwansa.babban fili Al-ameen yasiya a Kaduna a anguwar governor road yasa aka gina masa gini nagani na fad'a gidan samane akayi part uku amman anyi babban falo tsakiyar sannan se step Kowanne b'angaren danashi anyi kuma k'ofofi ta waje wanda kowa zefita yashigo batare da wani yaganshiba.
Dukiya yazuba agidan bata wasaba ba abinda babu harda garden da swimming pool da filin ball madaidaici kai komai de yaji, cikin Surbajo na wata tara suka tare a gidan ita da Aisha yayinda shima yanemi transfer zuwa Kaduna da ayki, gidan inka shiga kaga yadda kowa ke tattalin kowa abun seya burgeka babu kishi na fili agidan sede na b'oye wanda a ko'ina akwaishi,
Yanzu Yusuf yakoma hannun Aisha Itace keyimasa duk abinda yakeso,hakan bak'aramin dad'i yakewa Surbajo ba haka shima uban tafiyar,
Wata safiyar laraba Surbajo ta tashi da ciwon nak'uda Wayyo Jama'a zokuga Aisha zaka rantse da Allah Itace take nak'udar dan Surbajo ma tafita dauriya, ko a asibiti dasukaje haka taita rusa kuka harse da Allah yasauki Surbajo lfy inda tasake haifar namiji zokuga murna gurin Al-ameen jiyake kamar ya goya Surbajo dan dad'i.
Ranar suna yaron yaci sunan baban Aisha suna kiranshi da hanif,kukan da Aisha tayi na godiya ga Surbajo baya fad'uwa rasa inda zata sa hanif tayi sonshi take fiye da kanta jitake tafi Surbajo sonshi har tausayinta Surbajo tadunga Ji, yayinda taci gaba da addu'ar Allah yaba Aisha haihuwa Itama taga d'anta .
Duk wata kulawa da dawainiyar yaran Aisha ce keyi kullum yayinda Surbajo itake ke yimusu girki kullum gami da gyaran gida sam ta hana Aisha yin komai d'akinta kawai take gyarawa se kuma na Al-ameen ranar datake da girki,kai dole Rayuwar gidan ta burgeka, ko ruga Surbajo zataje tare suke zuwa haka Itama in zata gidansu.wani lokacin har mantawa suke waye me girki acikinsu se shine ke tuna musu wacce keda girkin.duk abinnan Al-ameen jin surbajo yake tazama shi yazama ita dan yasan zaman lafiyar gidanshi yasamune ta dalilinta son dayake mata ko da wasa baza'a had'ashi dana Aisha ba ji yake in yarasa Surbajo shima yagama ayki.
Maman Yusuf
[4/13, 7:20 PM] βͺ+234 703 962 5239β¬: ππππππππ
*SURBAJO*
ππππππππ
Zahra Muhammad Mahmud
*this page is dedicated to my fans on facebook thanks for the care and support*
*pure moment of life writers*
*p.m.l*
*page 87-88*
Waiwaye adon tafiya
Ruky tunda ta auri baballe bata tab'a sanin meye sana'ar saba.kullum cikin cin dad'i suke hankalinsu akwance kwatsam wani dare y'an sanda suka dira agidan su abin yabata mamaki dataji suna zargin baballe da laifin fashi da makami har sunshiga gidan wani Alhaji sunyiwa y'arsa fyad'e,shine aka kama sauran suka tonashi tanaji tana gani aka tafi dashi police station.
Kotu aka shigar dasu K'ara inda aka yanke musu hukuncin Kisa ta hanyar harbi da bindinga bayan Kotu ta kwace duk wata kadara dasuka mallaka, Ruky haukane kawai batayiba tana gani aka harbe mijinta wanda tafiso fiye da rayuwarta,tashiga halin k'unci da bakinciki dole takoma gidan iyayenta da zama domin yin takaba.
Zuly kuwa taci gajiyar soyayya domin cutar zamani musa yad'ebo ya shafa mata tana cikin mawuyacin hali gashi yak'i dena halinnashi yace seya shafa ma mutane da yawa shima, Zuly Itama fatanta kenan tashafawa Jama'a acikin burinnata shine aminanta yadace tafara sawa,wato Ruky da Aisha.
Yau gidan su Ruky Zuly taje da niyar yimata gaisuwa, bayan sungaisa suka shiga hirar duniya,Ruky tamik'e zata fita,carab Zuly tace," ina zuwa kuma muna hira?"
"Kinga wallahi yaro zankira na aykeshi yasiyomin reza Zan yanke farce na sun taru,"
Murmushi najin dad'i Zuly tayi,sannan tace,
"lah karki bata kudinki Inde reza ce inada ita ajaka sabuwa zauna ma na yanke miki farcen",Abun yayiwa Ruky dad'i bamusu ta zauna Zuly tafara yankemata farcen da rezar data yanke hannunta jininta yashafa dama tayine dan tayi amfani da ita gurin aykata manufarta,tana Cikin yanke mata ta yanke ta da gangan nanko jini yasoma tsartuwa agigice tasaki hannunta kamar gaske tafara kuka wai bata sani bane,murmushi Ruky tayi tace,"haba kawas dan tsautsayi yafaru shine kike kuka Wlh karki damu kanki bari nasa kalanzir."
Ranar wuni Zuly tayi agidan su Ruky inda a karshe suka tsaida shawarar Sati biyu masu zuwa Lokacin Ruky tafita takaba zasuje gidan Aisha subata hak'uri amman zuciyar Zuly ba haka bane manufarta dabam.
Aji dad'i
Yaude Aji dad'i tasha alwashin sake kiran Al-ameen, Lokacin data kira Surbajo ce Kusa da wayar Al-ameen yafita training, da kamar karta d'auka cande ta d'aga muryar mace taji tana fad'in,
"Haba namijin duniya don Allah Kadena wulak'antani wlh sonka nakeyi ni ko bazaka yimin komaiba don Allah Ka kusanceni ko so d'ayane wlh na kwad'aita dakaine Shiyasa."
Hankalin Surbajo ne yay mugun tashi kashe wayar tayi, dabara ta fado mata ta tura text da cewa,
"Tunda kin takuramin kizo kisameni agidana nikad'aine agidan kizo yanzu kuma namiki so d'aya bazan sakeba," tatura mata gami da Address. Lokacin da sak'on yashiga wayar Aji dad'i jitayi kamar tazuba ruwa ak'asa tasha fad'i take,"wato nid'in mesa'ace ashe rabon sake ganinshine yakawoni Kaduna gaskiya nagode wa Allah,"tashi tayi tashirya cikin wasu tsinannun kaya tasha magungunan tsumi harda na matsi sabida aji komai zam zam. Kai tsaye gidanshi ta nufa.
Surbajo ko tana gama tura text d'in d'akin Aisha taje da gudu ta sanar da ita zasuyi bak'uwa da manufar zuwanta ,nanfa suka ruga da gudu zuwa kitchen domin tarbar bak'uwar tasuπ
Maman Yusuf
[4/14, 10:13 AM] βͺ+234 703 962 5239β¬: ππββππ
*K'ARSHEN WAHALA*
ππββππ
*written by*
Aishat A muh'd
_Wannan shafin sadaukar wa gare ki nafeesat anka naji dad'i da nuna kulawar ki a gare ni ina miki fatan alkhairi Allah ya bar xumunci ameeen_β£
*~Pg 84~*
Abin da yaji lokacin da xai shiga d'akin jiddah waya take da farida kawar ta tana cewa
" ni fah har yanxu buri na bai cika ba tunda bai sake shegiyar yarinyar nan ba duk da sharrin da muka had'a mata na tura wani d'akin ta matsayin d'an iskan da suke watse wa Wlh na d'auka lokaci d'aya xai dankara mata saki har uku gashi har ta haifa mishi twins ina tsoron ya dawo da ita gidan nan na tsani er iskar yarinyar nan "
Abin da yaji kenan ya banko kofar da k'arfi har jiddah ta tsorata a firgice ta mik'e tsaye ganin yanda ya koma lokaci d'aya ita bata ta6a ganin shi a irin wannan yanayin ba amman ta maxe tace
"sojana xuwan yaus........ "
Kafin ta K'arasa fad'in "yaushe" ya kwashe ta da wani mugun mari Kafin ta dawo hayyacin ta ya sake bata wani daga nan ya fara ball da ita da kafar shi tana ihun kuka tare da bashi hak'uri belt d'in jikin shi ya cire ya fara tafkar ta son ran shi yana cewa
"jiddah kin cuce ni kin raba ni da nauwara daman sharri kika k'ulla mata xaki yi bayani duk abin da kike min ban ta6a d'aukar mataki ba a kanki amman wannan Karon xan baki mamaki wallahi"
Sai da yayi mata lilis ko motsi bata iya yi balle kuka sai faman ajiyar xuciya take saki tsugunna wa yayi dai dai kan ta yace
"na tsane ki jiddah kin raba ni da sanyin idaniya ta muradin rai na kije kema na sake ki baxan iya xama da ke ba"
Wani irin ihu ta saki Duk da muryar ta bata fita sosai bai kula ta ba ya janyo ta tun daga upstairs har k'asa xuwa farfajiyar gidan ya watsa ta a bayan mota sannan ya kirawo Joseph ya fad'a mishi ya kai jiddah gidan su sannan ya wuce cikin gidan xuciyar shi kamar xata tarwatse saboda yanda take bugu yana shiga cikin d'akin shi ya fara jifa da komai na d'akin yana fasa su tuni d'akin yayi kaca kaca duk ya yanke a hannun shi fuskar shi ta yi jawur da ita hannun shi yasa cikin lallausan gashin kanshi yana yamutsa shi ya rasa inda xai sa kanshi yaji dad'i
Bayan ya gama tarwatsa komai na d'akin a k'asa gefen bed ya xube yana wani irin shashshak'a idanun shi sunyi matuk'ar yin ja can kuma suka fara xubar da wasu xafafan hawaye suna sauka kan face d'in shi Allah sarki abduljabbar ya bani tausayi sosai yanxu mai xai cewa nauwara da wani ido xai kalle ta har ya bata hak'uri shi yasa ake son mutum ya dunga bincike Kafin ya aiwatar da abu kada yaxo yana da nasani wani xaxxafan xaxxa6i ne ya rufe shi tuni ya fara karkarwa hannun shi ya mik'a ya d'auko picture d'in nauwara tayi kyau sosae tana sanye da english wears tana er dariya mai ban sha'awa duk dimple d'in ta biyun sun lotsa baisan lokacin da ya saki wata er k'ara irin wanda mutum ya shiga cikin mugun damuwa yayi rungume photon yayi a kirjin shi yana wani irin kuka kamar ba soja ba kodan so ba ruwan shi
Lokacin da joseph Yayi parking a kofar gdn su jiddah dakyar ta iya fito wa ta shiga gidan duk jikin ta jina jina tana wani irin kuka ita duk duka nan da yayi mata bai dame ta ba irin sakin da yayi mata yaraf ta xube a tsakar gidan nasu da sauri mamee ta k'araso inda take hankalin ta a matuk'ar tashe ta d'ago ta cikin kid'ima da ganin yanda Jiddah ta koma duk fuska a kumbura yasa tace
"lafia jiddah me yafaru wane yayi miki hka??? "
Jiddah ba baki dole Hka ta hak'ura ta had'a ruwa mai d'umi ta gasa mata jikin ta sannan ta bata paracetamol ta kora sannan tace
"kiyi min bayani jiddah wane yayi miki hka"
"Abduljabbar ne? "
Nan take mamee ta had'e rai sai da gaban jiddah ya fad'i tace
"me ya had'a ku ki fad'a min gaskia bana son k'arya "
"wai wai akan hmm....."
Ta kasa K'arasa fad'i saboda tsoro batasan wanne irin abu mamee xata yi mata ba Idan taji abin da ta aikata kuma dole ta fad'i gaskia ko don ta samu ta roki mamee tasa Abduljabbar ya mayar da ita baxa ta iya rayuwa babu shi ba tayi nadama kuma irin wadda ake so baxa ta k'ara gigin aikata hkan ba ta tuba tsawar da mamee ta daka wa jiddah shi ya katse mata tunanin da take yi harara ta watsa mata sannan tace
"kin xaunar dani ke fah nake jira??? "
Tsugunna wa tayi a k'asa ta rik'e kafafun mamee cikin kuka ta fara rokan ta ta yafe mata kuma wallahi ta tuba baxa ta k'ara ba nan ta kwashe komai ta fad'a wa mamee tun daga lokacin da farida ta bata shawarar ta kai wani d'akin nauwara matsayin tana aikata fasikanci da maxa don abduljabbar ya sake ta har xuwa yau da asirin ta ya tonu yayi mata sannan uban dukan tare da yi mata saki bata rufe bakin ta ba mamee ta dalla mata mari har biyu Sannan ta fashe da kuka tana cewa
"ashe duk abin da kika aikata a baya jiddah baki yi nadama sai da kika kuma aikata wani kin raba mata da mijin ta saboda shegen kishin ki wallahi abduljabbar yayi min dai dai naso ma yayi miki abin da yafi hka da nasan Hkane wlh da ban kula ki ba ga Ki ga gidan sai kixo mu xauna tare kici uwar da xaki ci bari baban naki ya dawo"
Tana gama fad'in hka ta hankada jiddah ta fad'i sannan ta mik'e tsaye ta fita waje tana goge hawayen fuskar ta ta bar jiddah tana cin uban kuka a d'aki tayi nadama ta tuba kuma ba tuban muxuru ba na tsakani da Allah Indai abduljabbar ya mayar da ita xata xauna da nauwara tsakani da Allah
Baban jiddah da mamee ta fad'a mishi komai ba abin da yace kuma ko kallon jiddah Inda take bai yi ba hakan ba k'aramin k'ara tsurar da jiddah yayi ba
******
Tana nan kwance taji k'arar Shigowar message d'in takai hannu xata dauki wayar don ta duba su umma suka yi sallama suka shigo d'akin murmishin yak'e ta hau yi nan suka gaisa aka hau yin hira na'eem da ameer suna mak'ale a jikin ta umma ta kalli nauwara da ammi tace "Ohh na mance waya ta a gida ina son kiran Abba naji fa'iza ta taho kuwa"
"gaskia ya kamata a kirawo aji "
Cewar ammi "nauwara ban wayar ki na kirawo shi"
Umma ta fad'i tana mik'a hannun ta ba tare da wani abun ba ta mik'a mata kura wa screen d'in kallo umma tayi mamaki d'auke a fuskar ta ganin mssg da abduljabbar ya turo mata bud'e wa tayi a hankali ta fara karanta wa xumbur ta mik'e tsaye tana fad'in Innalillahi wa'inna ilaihir rajiu da sauri ammi da nauwara suka yo kan umma suna tambayar ta lafia amman ta k'asa magana da sauri nauwara ta d'auki wayar ta duba wa tayi ita ma ta karanta wani kuka ne ya kufce mata daman tasan ai K'arshen alewar k'asa shekara wajen uku baka xaune gidan miji sai gidan iyayen shi daman ai wannan abin ne xai biyo baya balle ga irin xargin da yake mata wayyo Allah gani gare ka ka kawo min agaji acikin wannan halin da nake ciki....
Aishat A muh'd
[4/14, 3:11 PM] βͺ+234 703 962 5239β¬: πππππππππ
*SURBAJO*
πππππππππ
Zahra Muhammad mahmud
*INA KUKE MARASA AYKIN YI SENA GULMA?KUZO GA AYKI NA SAMAR MUKU, TUNDA NAGA RASHIN SHINE YASA KUKA TASA NAMANA D'ANYE KUNA CI.NAYIWA INDIMI FAMILY DEDICATION YASA KUNKASA ZAUNE KUN KASA TSAYE TSOHON BASIR YA MOTSA TO GAWANI SABO*
*THIS PAGE IS DEDICATED TO ALHAJI ALIKO DANGOTE FAMILY ALLAH YAY MUKU JAGORA AKOINA KUKE A FAD'IN DUNIYA NAGODE*
*pure moment of life writers*
*p.m.l*
*page 89-90*
Duk abinda yadace su tanadarwa bak'uwar tasu shi suka tanada.suka dawo falo suna jiran isowarta.
Aji dad'i tunda ta iso k'ofar gidan yawunta ya k'afe sabida kyan da gidan yay mata,take zuciyarta ta ayyanamata dama ta auri mamallakin gidan.koda tazo gurin sojojin dake gadin gidan basu hana ta shigaba sabida madam tace zasuyi Bak'uwa in tazo su barta ta shiga.
Shigewa tayi cikin gidan tana wani karayraya ita adole tazo kwartanci, cikin falon gidan tashiga inda megadine yanuna Mata hanyar,
Su Aisha ko jin motsine yasa suka tashi da gudu suka b'oye a cikin labulen bakin k'ofar shigowa har ta shigo bata Lura dasub, kan kujera taje tazauna tadora k'afa d'aya kan d'aya aka k'ara baza gashin atachimen d'in datasa tana taunar cingom ji tayi kamar alamar akwai mutum atsaye akanta da sauri ta juyo zabura tayi tamik'e,ganin Aisha da Surbojo kowa d'auke da muciya sun nufota neman hanyar gudu take amman ina sun cimmata ayko nan suka shiga kirb'a mata muciya ta ko ina,ihu take tana neman taimako Amman ina babu me cetonta,dukanta suke bada wasaba, daganan suka kwantar da ita ta k'arfi suka yimata matsi da garin barkono wani azababben ihu tashigayi bana wasaba ga jikinta duk inda suka fasa seda suka cikeshi da garin yaji Aji dad'i ihu take har numfashinta na d'aukewa.
Dede lokacin Al-ameen yashigo gidanshi ganin masu gadi yayi tsaye cirko cirko abakin k'ofar falon gidan tambayarsu yashiga Yi akan abinda ke faruwa, nan suka shaida mishi bak'uwa ce tashigo gidan yanzu shine kuma suka jiyo kukanta ga kuma sautin dukanan sunyi sunyi su bud'e k'ofar sunkasa,da sauri Al-ameen yafara dukan k'ofar yana kiran sunansu amman ina ba wacce ta kulashi cigaba sukayi da operation d'insu, ganin bazasu bud'ebane yasa yabi ta kofar part d'inshi wacce d'azu daze fita tanan ya fita kuma besa key ba, dagudu yabi hanyar yak'araso falon ganin abinda sukeyi bak'aramin mamaki yabashi ba tunaninshi me yakawota gidanshi?,tayama tasan yadawo kaduna?, ganin baze samu amsoshinbane Yasa yaruga dagudu yayi kansu dakyar yakwaceta a hannunsu se zunduma ihu take iya k'arfinta tana tsalle tsalle sabida yajin da suka yimata matsi dashi,Surbajo ce tace afusace,
"Dan kan ubanki kad'an muka yimiki dan wlh yau so mukayi muyi miki abinda ko sunan namiji kikaji an ambata sekin firgita bare har kice zaki yi mu'amala dashi shegiya tsinanniya me lalata mazan mutane,"Aisha ta amshe da cewa,
"Bar matsiyaciya de muna nan muna tattalin mijinmu ke kinaso ki b'ata mana ginin damuka dad'e munayi wlh kinsha k'arya kuma koda wasa