Showing 3001 words to 6000 words out of 38424 words
Chapter 2 - Surbajo Book Complete document by Zahra Muhammad Mahmud .txt
guda sannan yadawo
Yauma bata gidan kuma tasan zedawo tatafi yawonta tunda
yake daita betaba jin bacin rai irinnayauba kuma yasha
alwashin yau seyayi maganinta
Yanazaune afalo tadawo kokallo be ishetaba tawuce dakinta.
Seda tajima dashiga dakin sannan yamike yabi bayanta
yanashiga kamar kullum yauma wayar take da kawayenta
Daga gidan ubanwa kike alameen yawurgamata tambayar
Seda tambayar tafirgitata amma dayake Kai na hayaki setace
daga gidan ubanka nake ubana
wani wawan Mari yakifeta Dashi seda tafado daga gadon
Belt din jikinshi yacire yashiga dukanta takoina ran yanmaza
yabaci haba ay yayi kokari tsawon shekara biyar yana hakuri
Aisha tun Tana ihu harseda ihunma yagagara seda yatabbatar
da tayi laushi dankanshi yakyaleta
Sannan yadakamata tsawa Tana kwance akasa jikinta duk jini
sabida tadoku ahannun soja Dan dukan kato yamata
yaci gaba dacewa cikin fushi anfadamiki tsoron ki nakeji ne
dazaki dunga yimin abinda kika dama ina kyaleki wallahi
Aisha nayi danasanin auranki danasani nabarki kinsake shan
fiya fiyar ki mutu wlh daan rage mugun irin
Damutuncina agari amma agidana bandashi to wlh kinyi
kadan dama nasamiki idone banza kazamiya kuma wlh kitashi
yanzu ki gyaramin gida awa guda nabaki inba hakaba nalahira
seyafiki jin dadi yafadi yayin dayayi kwallo da ita yafice daga
dakin
Jikinta narawa tamike tafara aykin dukda ciwon dake jikinta
besa tabar aykinba tanayi jiri nadibarta Dan yanzu wani mugun
tsoronshi takeyi hhhhhh nace su aee anji maza
kafin lokacin yacika tuni gidan yayi clear dattinko data kwashe
seda yacika katon dustbin
gidan se kamshi yakeyi komai yayi normal araina nace oh
Aisha tazama zuma seda wuta
alameen tunda yafito daga dakinta garden din gidan yashiga
seda yatabbatar lokacin daya dibamata yacika sannan yashiga
cikin gidan mamakine yakamashi ganin yadda gidan lokaci
kadan yasauya sewani kamshi yakeyi dakinshi yaleka komai
normal harda sabon bedsheet tashimfidamasa har cikin ranshi
yaji dadin ganin gidan ahaka sabida rabonshi daganin sa
hakan tunranar daaka kawota gidan
dakinta yanufa yana shiga yaga Tana morping a tsugunne tana
kuka tausayintane yakamashi amma yayi saurin kawar dashi
sabida sanadin tausayinne yajefa kanshi acikin halin dayake
yanzu
Tsawa yadakamata sannan yace Dan rashin mutunci a
tsugunne kike moping din dalla malama tashi
Jikinta se Bari yake tace Dan Allah Yaya kayi hkr bazan sakeba
Mamakine yakama alameen sabida rabonshi dajin irin wannan
kalaman abakinta tun sati biyu da auransu
dalla yimin shuru sumumu kasau kawai bacemin dagani
Jikunta narawa tadauki ruwan moping din taje toilet tazubar
tawanke toilet din fitowa tayi tana rabe rabe inda alameen
yakorata taje tayi wanka da gudu tashige bayin Dan tadauka
yabiyota abayane
so uku Tana fitowa bayan tayi wankan yana maida ita tasake
wani wai bata fitaba hakama brush seda makilin oral b yakusa
karewa dan seda bakinta yasoma jini sabida brush sannan
yakyaleta kantama adaren tatsefeshi tawanke shi tas haka ma
shaving duka seda tayi
ita dakanta taji dadin kanta Dan har wata iskace take ratsata
nace oh ji yiwa Kai mugunta
rigar vacci kawai tazira tahaye gado tuni bacci yayi gaba da
ita dayake alameen yabar dakin
dawowa yayi yaga Tana bacci duka yakaimata abaya afirgice
tafarka tadiro agadon
ubanwa yabaki damar bacci bayan baki sallameniba hkr
tashiga bashi Tana hawaye alameen bakunya yakamota
yashiga sarrafata bata hanashiba Dan Tana gudun shan duka
yau cikin nishadi yabiya bukatarsa inda besauraramataba se
asuba nace Kai alameen batausayi
wanka yayi yafice masallaci Tana kuka tamike tashiga toilet
tayi wankan tazo tayi sallah sabida kafin yatafi masallaci seda
yamata worning akan ta tabvatar kamin yadawo tahada break
fast sannan tayi gyaran gida tayi wanka tayi kwalliya idan
yadawo yaga batayi daya acikiba zatasani
shiyasa tamike tafarayi jiri nadaukarta sabida rashin bacci ga
jikinta dake mata ciwo ahaka tadaure tayi komai kamar yadda
yabukata har girkinma tayi duk da ba wani dadi yayiba amma
yafi babu
dayadawo abun yaburgeshi har wani nishadi yakeji amma idan
yatuno tilastata yayi seyaji duk ranshi yabaci
maman Yusuf
[3/18, 11:27] Zahra muhd mahmudπ: ππππ
πππππ
*BALLAGAZA*
πππππππππ
Zahra Muhammad mahmud
*pls yanuwa Dan Allah ina barar adduarku yaron Aunty nane
jariri bashida Lfy Dan Allah kusashi cikin adduarku a sallah
ππππππ*
*page 8*
Tundaga wannan rana Aisha take tsoron Alameen Dan ko fita
bata sakeyiba sosai take jin maganarshi
Bangaren rayuwar aurema ko tanaso ko bataso inde shi
yanaso anwuce gurin
Yau alameen ze koma bakin ayki inda yakafamata dokoki
yakuma ce muddun ta karya daya takuka da kanta
Har airport Tamushi rakiya kamar gaske
Ay tundaga airport dinnan bata wuce gidaba kaitsaye gidansu
Ruky tasauka kamar fadi Tana zama Sega zuly tazo nan suka
shiga hirar yaushe gamo daga karshe Aisha tabasu labarin
abinda alameen yamata
Dariya suka samata harda hawaye
Zuly tace dankari amma wlh Aisha kinbada mata yanzu
tsayawa kikayi yadakeki tabdi ayko inde baki dauki matakiba
wlh kinzama filin training dinshi
Ruky taamsa ay yana cewa zedokeki gabansa zaki rike iya
karfinki inyaji zemutu wlh zedena ko ki dunga ajiye wuka
agefenki dazaran yamiki wani wargi kinuna zaki masa kachiya
wlh denawa zeyi amma taya zaki sakarmasa jiki yadunga labta
wlh kin rikito
nande sukasata agaba suna huremata kunne basu bartaba
seda suka tabbatar shawararsu taamsu agurinta Dan har
haushin kanta tadunga ji amma bata baciba tasha alwashin
inyadawo zegane kurensa.
*Photacot*
Alameen ne zaune a office dinshi shida amininshi Usman fira
suke gameda rayuwar duniya ananne alameen yashaida mishi
labarinshi da Aisha harda dukan dayamata
Major Usman ne yace haba abokina meyakaika dukanta
gaskiya baka kyautaba aysu mata insuna iskanci irin wannan
akwai dukan daake musu yasasu haukacema gaba daya
dasauri alameen yamatso yace Kai haba abokina
wlh yabashi amsa
to wanne irine shi dukan alameen yabukata
ka kara aure shine mafita
ajiyar zuciya yayi sannan yace major kafi kowa sanin raayin
mace daya ne Dani arayuwata so gashi nakuma Aura
bandaceba baka tunanin yin wani auran ze Kara daga
hankalinane
haba abokina wancan auran dakayi aurene bana soyayyaba
maana aurene natausayi so yanzu inzaka sake wani wacce
kakeso takesonka zaka Aura wlh inde kadace sekayimin
godiyar shawarar Dana baka amma taya zaka tsaya mace
tana gasaka bakadauki matakiba aywasu matan zumane seda
wuta
dariya sukayi gabadaya suka tafa inda daga karshe alameen
yace zeyi nazari akan zancan Usman
haka kwanaki sukai ta tafiya har Allah yadawo da alameen
gida koda yazo yaga Aisha tayi fatali da dokokinshi be
kulataba
anata bangaren tayi shirin ko ta kwana Amman ga mamakinta
setaga ko kallo bata isheshiba
hakan bemata dadiba taso yakulata tace zata masa kaciya
shiko bawan Allah bata ita yakeyiba
.
shurun dayamatane yasa tasake Mike kafa ita adole taci dubu
se Ceto kawayenta nakara zugata
*RUGAR YALLI*
wata rugace ta fulani agarin makarfi ta jahar kaduna jamaa
dayawa basu San rugarba sabida Tana cikin dajine sosai ko
yan garin se tsofaffin zamane sukasan da rugar sabida rugar
gida ukune kawai acikinta gidan alhaji babba dagidan alhaji
jume se gidan ardon rugar wato gidan alhaji yalli
duka gidajen Manyan gidajene sabida kowa dashi da zuriarshi
yake zaune agurin
zahrau wacce akafi saninta da surbajo "ya ce agurin alhaji
yalli wato ardon garin Wanda aynihin sunanshi muhammadu
Mahmuda asalinsu yangarin gwangolane dayake su fulanin
tashine shine suka dawo wannan guri dazama
matanshi biyu sumaye wacce itace uwargida se amina wacce
itace Amarya
yaranshi takwas inda sumaye takeda guda bakwai duka
Mazda ita Kumar amina takeda guda daya wato zahrau
amina asalinta yar garin kadunace awata anguwa mesuna
tudun wada layin kosai anan aka haifeta kaddarar aurece
takaita ga auren ardo dakuma rabo danginta Sam basason
aurannata dashi kasancewarta marainiya shiyasa tunda
taaureshi danginta suka tsameta acikinsu
bayan haihuwar zahraune da shekara biyar Allah yama amina
rasuwa ardo yayi kuka kamr ranshi zefita
yanuwantama dasuka sami labarin rasuwarta sunyi kukan
rashinta dasuka zo gaisuwa suka bukaci ardo yabasu zahrau
sutafi da ita fafur ardo yahanasu yace meze dunga kallo
amatsayin amina idan yabasu ita
ransu besoba amma yafisu iko da ita haka suka tafi suna
danasanin watsi da aminan dasukayi
Maman Yusuf
πππππππππ
*SURBAJO*
πππππππππ
Zahra Muhammad mahmud
*page 9*
Zahrau ta taso cikin tsana da tsangwama irinna kishiyar Uwa
Sumaye ganamata azaba takeyi tun tana karama aka fara sata
zuwa kiwo zuwa yanzu taiya sosai dama ga aladar gidan
insun fita kiwo dare yamusu to acan suke kwana ingari
yawaye su cigaba da kiwon sede laasar nayi zasu komo gida
Shiyasa inzasu tafi suke tafiya da kanzo Wanda aka daka da
gishiri da yaji da man shanu da tukunya sabida koda dare
yamusu acan sugirka suci
Kokadan zahrau batajin dadin zaman gidan inde mahaifinta
bayanan sabida inyananan bame dukanta sosai yake jida ita
kuma gata sunan mahaifiyarshi yasamata shiyasa ake kiranta
da surbajo
Yauma kamar kullum surbajo tafita kiwo ita da ya'u yayantane
Suna zuwa rafi suka hadu da arera yar gidan alhaji jume
itama tafito kiwon itada yaynta saidu
Suna ganin juna suka rungume juna ita da areran sabida
murnar ganin juna guri suka samu suka zauna suna hira
surbajo ayko inada wani albishir dazan miki inji arera
dagaske wanne irin albishir ne wannan kekuwa arera inji
surbajo
Aradu dama jae ne dan gidan alhaji Babba jiya yazo gurin
yayana zubairu danaganshi muka gaisa shine yace wai ince
miki yana gaisheki
ihu surbajo tasa sannan tarungume arera tace
kai madallah aradun Allah naji dadin wannan albishir
Aydama nasan zakiji dadin shiyasa nafadamiki
Ranar agurin kiwo wuni surbajo tayi tanajin dadi Dan harga
Allah sakon gaisuwar da jae ya ayko mata ta sanyaya
zuciyarta
*JA'E*
dane agurin alhaji babbah Dan kimanin shekara ashirin
kyakkyawane naajin farko dan duk mazan garin bawanda
yakaishi kyau shiyasa kowacce mace take kaunarsa gashida
da kyauta dan inde yace yanasonki to ko zakici soyayyar
gyada da burodi kimore gashi ranar kasuwa kullin kosanki da
yar yau na musammanne
Shiyasa kowacce mace burinta yace yana sonta
to surbajo ma Tana cikin jerin masu sonnasa
yau akwai biki agidan alhaji babba inda yake aurar da yarsa
Safiyya yar kimanin shekaru goma shadaya
Su surbajo sune kawayen Amarya sabida suma shekarunsu
sha dayanne
ga alada ta Fulani akwai wani wasa dasukeyi bayan shadi inda
maza da yanmatane zasu taru suyi layi layin maza dabam
haka namatama zasu fuskanci juna suna wakar
Wayyohoro hirobe gadaibe jadu jande wayyo horo hirobe
gadaibe jadu jande. Seme kalangu yasa kida to matanne daya
bayan daya zasu dunga fitowa su tsaya a tsakiyar filin se
tagama kallon samarin Wanda yamata acikinsu shi zataje ta
yalo da kafarta yin hakan nanufin tanason yafito suyi rawa
kenan kuma yawanci daga wannan rawarne soyayya take
shiga tsakani hartakai ga aure
to wannan bikinma anshirya irin wannan wasan
Danhaka surbajo taruga kowa zuwa gurin sabida tanada gaba
sabida basa son arugasu zaban jae sabida a alada irinta
wasan duk Wanda kika zaba fita zakuyi tsakiyar filin kuchase
sosai to inkuma yaji yanasonki zece kufita afili kusami guri
kuyi mgn
fili yacika bamazanba ba yanmatanba
su kuma mazan kowa burinshi Allah yasa surbajo tazabe shi
Dan itama duk yanmatan garin tafi kowa kyau
anfara waka inda surbajo ce farkon fitowa tashigo filin tafara
rawar Fulani irin wacce ake daga kafa dayannan ana saukewa
sannan takarewa mazan kallo can idonta yasauka akan jae
yanamata murmushi ayko batayi kasa agwuiwaba ta yaloshi
ihu yayi sannan yashigo filin da kwambe suka fara rawa tare
inda me kalangu yadunga wasasu dacewa kyakkyawa se
kyakkyawa
bayan sungamane jae yacewa surbajo Sudan fita afilin ay
sauran yanmatan naganin sunfita kowacce haushi yakamata
inda sukasha alwashin se summa surbajo dukan tsiya akan
yaloshin datayi
hakade yanmata da samarin suka ci gaba dawasansu har suka
gama
itako surbajo tunda jae yace sukebe farinciki yabi yacikata
dantasan yau tafi kowa saa a duniya
koda suka keben juya mishi baya tayi alamun jin kunya
shimade kunyar yakeji Danhaka shima bayan yajuyamata
sannan yafara mgn
wato surbajo nadade inashonki amma nakasa fadamiki
segashi yau Allah yakawo ranar dazan sanar dake danhaka Do
Allah do annabijjo kishe kina shona.nide aradu ina shonki
kunyace da dadi suka rufeta Dan haka ta ranta anakare
takoma gurin arera
gudun datayi shiyabashi tabbacin tanasonshi Danhaka agurin
yafara rawar cin nasara Dan yasan yama mazan garin nisa
maman yusuf
[3/18, 11:54] Zahra muhd mahmudπ: ππππ
πππππ
*SURBAJO*
πππππππππ
Zahra Muhammad mahmud
*fans muna barar adduarku yaron da bashida Lafiya Allah
yamasa rasuwa to kutayamu da addua Allah yajikansa yasa
meceton iyayenshine sukuma iyayenshi Allah yabasu hakurin
jure rashin sa ,rest in paradise my baby*
*page 10*
Tundaga wannan lokaci syy me karfi tashiga tsakanin surbajo
da jae ko kadan basa son rabuwa da juna
Yauma kamar kullum jae yazo hira gurin surbajo
Akan wani ice suka zauna yayinda surbajo tajuyamasa baya
sabida kunya
Gyada takawomusu da burodi sunaci suna hirar
Can jae yace surbajo aradu inna aureki nahaye nasan duk
garinnan se andunga hirata saboda na auri sarauniyar mata
Dariya tayi tasake rufe fuskarta sannan tace aynima hakanne
Dan yanzu haka yanmatan garinnan haushina sukeji Dan
rannan munje kiwo nida arera su haulen gidan ku suka tsareni
wai sesunmin duka ayko nida arera muka hadu mukaimusu
dukan tsiya
dariya yayi sannan yace hauka sukeyi nibance inasonkowa
acikinsuba shima Baffa cewa yayi inzabi wacce nakeso inde
agarinnanne ze auramin nikuma nazabeki
Dadine yarufe surbajo harseda sautin dariyarta yafito
hakade suka gama hirar wacce yawancinta cin gyadar yafi
yawa
****************************
Al ameen yanzu yafita harkar Aisha kwatakwata harkar
gabanshi kawai yakeyi yayinda mahaifansa zuwa yanzu
sunfara bashi shawarar yakara aure kuma yabasu tabbacin ze
Kara yana neman wacce yake sone fatan alkhairi suka masa
alameen anturashi wani course kasar amurka inda seda
yakwashe tsawon shekara guda acan yanzu idonshi yakara
budewa ya waye fiye da tunaninku ko maganarshi yanzu
tasauya Alameen Kenan Dan kimanin shekaru arbain da
haihuwa amma babu me ganinshi yayi zaton yakai hakan
Aisha ma yanzu bata da lokacinshi Dan yanzu tazama yar
business Dan haka kasuwancinta yafiyemata komai
Mahaifiyarta tanasane da irin tsiyar da Aishan take tsulawa
agidan miji amma kda wasa bata taba tsawatarmataba sabida
gudun kar abin arzikin da Aishan take kawomata tadena
Su Ruky suma kullum cikin bata munanan shawara suke inda
ahalin yanzu har sata takema alameen din yasan tanamishi
satar Amman ko afuska be nunamataba Dan yafuskanci bata
da wadataccen hankali
***************
surbajo Ankara zama yanmata inda yanzu shekarunta sha biyu
da haihuwa Dankaka yanzu sumaye har tallan nono da fura
take doramata tabi yanmatan rugar sukai cikin garin makarfin
ranar dabata siyarba dukan tsiya take mata shiyasa surbajo
bata dawowa gida da wuri matukar tasan bata siyarda
nononba
Se tara nadare take baro cikin garin kamin tagama keto dajin
ta iso rugarsu goma tayi
haka baffanta zetamata fada itade sede tai tabashi hkr
itakuma sumaye na zugashi da cewa maza tafara bi shiyasa
take dare bata dawoba itade surbajo sede kuka
wasawasa seda kaiwa dare agurin talla yabi jikin surbajo
sabida bata da kan kasuwa Dan wani lokacin setakai laasar
baasiya ko na kwaboba gashi nonon yafi Nakowa yawa acikin
wainda suke zuwa tallan tare
duk sanda ta dawo se baffanta yazaneta sannan yamata fada
akan dolene setayi cinikin inbata siyarba ta dawo mana inya
tambayi sumaye ko itace take cewa surbajo karta dawo seta
siyar munafukar har kuka take sawa tace haba alhaji yazaayi
nacemata haka koban haifeta ba ay yatace kuma nasan
hatsarin dake tattare da hakan da irin wannan kalaman take
Rufe bakinshi
insuka koma daki ita da surbajo tashaketa takuma ce wlh
inkika kuskura kika dawo gidannan baki siyarba yankaki zanyi
itade sede tayi kuka tafadawa Allah
jae yasha yimata juyen nonon yabiya kudin Dan kawai tasamu
taje gida dawuri to yau da gobe tafi wasa
ba koyaushene yake da kudin juyenba seyafara rakata tallan
sui ta yawo agari har su samu asiye haka sukeyi sunfi karfin
wata guda suna zuwa tallan tare kwatsam rannan se sukayi
kwantai basu sayar da wuriba ranar basu dawo gidaba se
goman dare
lokacin Baffa yafito yabi hanya yagani meyasa bata dawo da
wuriba dayake basu San jae narakata tallanba seganinsu yayi
tare suna tahowa tsawa yadaka musu yace daga ina kuke
cikin darennan
tsugunnawa sukayi sannan sukace daga talla wankesu yayi da
Mari duka lokaci daya sannan yace nizaku maidar yaro wato
dama abinda innarki take fadamin akan maza kikebi Ashe da
gaskene to wlh yau zaki gane kurenki kaikuma zanga baffan
nakane wawa kawai kekuma munafuka shige mutafi dagudu
tamike tayi gaba Tana kuka koda isarsu gidan yaba sumaye
labarin abinda yafaru cewa tayi ay gwanda dakagani da
idonka Dan Dana fada baka yardaba aygashinan
ranar seda yama surbajo jinajina inda yakara da fadin
gobema ki kuma kaiwa dare awaje wlh Sena yankaki na huta
kuma tallan nono bazaa Dena doramiki ba sabida aladarmuce
kowacce yarinya tanayi Danhaka yazama dole kema kiyi daga
yanzu in magaruba tamiki awaje ki kuka dakanki
haka taci gaba da Kukanta har zuwa washe gari batayi
bacciba
maman Yusuf
πππππππππ
*SURBAJO*
πππππππππ
Zahra Muhammad mahmud
*page 11-12*
Alameen yadawo hutu inda yasamu labarin anyi rasuwa akano
zasu tafi gaisuwa duka family dinsu
Ayko haka suka rankaya gaba dayansu harda matar kabeer da
yaransa gabadaya ran alameen ne yabaci ganin batashi matar
acikin ayarin
Mota biyu sukayi kabeer ke Jan motar da iyalinshi suke ciki
yayinda alameen kejan wacce iyayensa da kannansa suke ciki
Dan be tafi da excode dinshiba sabida gaisuwa zasu
Sun isa kano Lfy sunyi gaisuwa an karbesu cikin mutunci da
karramawa
Seda laasar suka kamo hanyar dawowa gida Dan ba kwana
zasuyiba
**************
Surbajo yau dawuri ta shirya ta tafi tallan nono Dan Tana
gudun tayi dare kuma tasha alwashin yau intaje talla rokon
mutane zata dungayi akan su siya
Tayi kwalliyarta cikin kayansu na Fulani inda fuskarta tacikata
da digedige duk asunan kwalliya bakinta tacikeshi da bakin
kwalli gaba daya dan Tana tunanin rashin yin Kwalliyar ne
yasa baa siyan kayanta
sallama tayiwa sumayen tadauki kwaryar nonon ta wuce
Koda tazo cikin gari jamaa bame bitakanta bare asiya kota
rokesu basa siya Dan haka kuka tasa taci gaba da bin mutane
akan su siya
haka tadunga bi kwararokwararo akan asiyi nonon mutum
Hudu ne kawai suka siya ga nonon da uban yawa
haduwa tayi da Mari yar rugarsuce ita har ta siyar tambayarta
tayi Don Allah Mari ina kike kai nono da furarki asiye Dan
Allah kifadamini
Murmushi tamata sannan tace aradu da nisa Dan sekin hau
mota naira dari zaa kaiki a akori kura
Dasauri surbajo tace fadamini Dan Allah aradun Allah zani
Tashar yarine tabata amsa daganan tajata takaita inda zata
hau motar
Godiya sosai surbajo tayi mata tahaye motor akori kuran suka
tafi
**************
Alameen tafiya suke suna hira cikin nishadi sabida daddy
bayason gudu amota shiyasa ahankali yake tafiya sabanin
kabeer Wanda yakusa shiga kaduna Dan cewa yayi baze iya
tafiyar wahainiya ba
suna zuwa tashar yari tayansu Yay faci dole Al ameen yay
parking agefen titi dede wani masallaci gurin akwai jamaa
sosai kamarde kasuwa fitowa yayi Dan yanemi Mesa iska
yasamusu suwuce
agefe yaga Mesa iskar Danhaka yace yazo yasamusu dasauri
Mesa iskar yasakamusu sabida ganin dankareriyar motor
dasuke ciki
1k alameen yabashi mutumin se godiya yake
karaf a kan idon surbajo hakan ta faru Dan haka dasauri
takaraso inda alameen keshirin shiga yatada motor dasauri
tace sannu bawan Allah Don Allah kataimakeni dasauri
alameen yajuyo jin zazzakar murya namishi mgn
arba yayi da surbajo dauke da kwaryar nono akanta
durkusawa tayi tana kuka tace Don Allah kataimakamin
kamar yadda Allah yataimakeka kasiyi nonon nan da fura wlh
inna koma dashi bansiyarba yankani zaayi kuma inna Dade
agurin tallan Baffa yace seya yankani takara rushewa da kuka
alameen mamakine yakamashi to inbanda haukar fillo shi
mezeyi da fura da nono dahar zata ce yasiya motarshi yashige
yana shirin tadawa dagudu surbajo tasha gaban motor tana
kuka tace cikin kuka haba bawan Allah Allah fa nahadaka
dashi kaji tausayinamana Don Allah hankalin daddy ne yakai
gurunta mamakine yakamashi Dan haka dakatar da alameen
yayi sannan yabude kofar motor yakirata karasowa tayi jikinta
har rawa yakeyi
mommy ce tafara mgn dacewa yanmata Lfy cikin harshen
fulatanci kasancewarta mommyn bafulatanace
cikin Yaren fulatancin surbajo tabata amsa dacewa taimako
nake nema akan asiyi nono da fura Dan inna koma gida
yankani zatayi inbansiyarba inkuma najima agurin tallan Baffa
dukana zeyi Don Allah kutaimakamin
tausayintane yakama mommy
bayani tayiwa daddy game da abinda surbajo tace
tambayarta yayi da Hausa yace yarinya meyasa kika ga
muyadace damu taimakeki
share hawaye tayi sannan tace sabida naga kuna da kudi Dan
wancam tanuna alameen da haushi duk yagama cikashi
sabida batamusu lkcn datayi
taci gaba naga yabiya kudin sa iska naira dubu guda
amaimakon naira talatin shiyasa
dariya sukayi harda sumunauwara
daddy yace to tundaga ina kikazo nan tallan tundaga rugar
yalli tabashi amsa
jinjina Kai daddy yayi Dan yasan rugar duk sallah anan ake
siyo shanun dayake rabawa mutane kuma agurin shi yallin
wato ardon
ke yar wanne gidace a rugar daddy yatambaya
ni yar gidan ardoce
mamakine yakamashi yace nasan shi yanzu ke yarsace
washe baki tayi jin ance ansan baffanta tace eh Amman
innata ta rasu
no wonder inji