Showing 36001 words to 38424 words out of 38424 words
Chapter 13 - Surbajo Book Complete document by Zahra Muhammad Mahmud .txt
kika sake bin mijinmu wlh semun sauya miki halitta tsinanniya kawai,"
Al-ameen ne ya katsesu dacewa, "Haba ku kuwa yanzu abinda kukayi kunyi adalci kenan?yazaayi kukama y'ar mutane kuyi mata irin wannan izayar wannan ay zalincine ina laifin kuyi mata warning da baki amma shine harda irin wannan azabtarwa,"Aisha ce takatseshi dacewa,
"wato abinda mukayi munyi laifi ko ?sabida munmata hukuncin daya dace da ita shine har Kake cewa bamu kyauta ba to wlh semun mata wanda yafi wannan muddin takuma kallon mijinmu,"Surbajo tace,
"ke kika tsaya ma yimasa bayani wlh Aunty kawai kijawo mana ita muci gaba da cin uwarta inyaso seya zab'a ko mu ko ita," tana gama fad'in haka ta finciko Aji dad'i dake b'oye abayanshi suka ci gaba da shirgarta harseda suka karyata a k'afa duk yadda yaso ya amsheta yakasa seda suka gaji dan kansu suka kyaleta, suka wuce d'akin Aisha suna dariya suka barshi tsaye akan Aji dad'i wacce ko numfashi batayi, kiran driver dinshi yayi yabashi kud'i da shot note yace yakaita asibitin sojoji kinkimarta driver yayi yanufi asibitin da ita wanda yake mallakin sojojinne me suna 44 kuma babu nisa tsakaninsu da asibitin.
koda aka kaita asibitin seda tayi kwana goma sannan ta ji sauk'i sallamarta akayi yayinda k'afarta dasuka karyata kuma akayimata D'ori aka bata sandar dogarawa,ta koma Abuja cike da danasanin sanin Al-ameen datayi arayuwarta tabbas tunda take bata tab'a danasanin karuwancin datakeyiba se yanzu dan haka had'a yanata yanata tayi takoma gaban iyayenta tanemesu gafara.
Shiko Al-ameen gaba ya d'aura da matan nashi inda sukuma suka maidashi mahaukaci,
inyashigo gidan suyi masa dariya inze fita su kwashe da dariya sunde maidashi kamar tab'ab'b'e abin yafara damunshi dan har tsarguwa yakeyi in suna dariyar se yad'auka wani abun suka gani ajikinshi suke dariyar har gaban mirror yasha tsayawa yana k'arewa kanshi kallo dan yaga mesuke wa dariyar.
Rannande ritsasu yayi afalon suna masa dariyar Surbajo ya damk'o yace,
"Yaza'ayi kumaidani mahaukaci kusani agaba kunamin dariya to wlh yau sekun ciremin abinda kukewa dariyar,"yafad'a rai ab'ace, dariyar suka sake tuntsirewa da ita suna nunashi sakin Surbajon yayi yakama dube dube ajikinshi, da gudu suka bar falon kowa ta gudu d'akinta tasa key,murmushin takaici yayi yawuce nasa d'akin yaganosu wato gasashi sukeyi dan yanuna b'acin ranshi akan abinda suka yiwa Aji dad'i.A ranshi yace, "to fita harkarku zanyi ko kunamin dariyar".
Yau kuma su Ruky ne suka dira agidan bayan bak'ar wahalar dasukasha kamin su gane kwatancen da'aka musu,dakyar megadi yabarsu suka shiga,, afalo suka sami Aishan a zaune tana wasa da Hanif da Yusuf, da sallamarsu suka shiga falon mamakinsu ne k'arara a idon Aisha kallon tsana da k'iyayya take binsu dashi har suka zauna. Suna zama carab Zuly tace cabd'i Jan kice kece kika koma nani d'in yaransu ken...... bata gama fad'in abinda tai niyya ba Aisha ta kifeta da Wani lafiyayyan mari tasake k'ara mata wani, mamakine yahanasu yin wani yunk'uri, d'aga murya Aisha tayi tace,
"Sister ki fito munada bak'i Wanda yadace ayimusu sanitation a brain d'insu,"da sauri Surbajo tafito daga kitchen hannunta d'auke da muciya guda biyu dan tun ranar dasuka daki Aji dad'i suka yi meeting akan duk sanda d'aya yaji d'aya yakirashi akan suzo suyi sanitation to abun dukane yasamu dan haka Surbajo harda d'amararta tana zuwa falon tamik'awa Aisha muciya guda d'aya ayko batare da b'ata lokaciba suka rufesu da duka ta ko ina k'arar hayaniyarsuce ta tashi Al-ameen a bacci da gudu yafito falon ganin yak'in da akeyi afalon ba k'aramin mamaki yabashiba,dakyar yak'arasa gurin ya rabasu da kyar su Ruky se kuka sukeyi sabida dukan dasuka sha,Aisha tace,
"matsiyata marasa kunya wato har kuna da idon dazaku sake kallona da Sunan k'awance to daga yanzu bani baku kunyimin illar da har na mutu bazan manta dakuba kuma wlh bazan yafe mukuba kufice daga gidannan yanzu wlh,"jiki asanyaye suka fice a gidan ran Zuly yafi na Ruky b'aci sabida bata samu damar ida nufintaba.
shiko Al-ameen masifa yarufesu dashi dacewa,
"Wlh maganar dakuke d'aukomin tafara isata ace gidana yazama filin dambe ay dana sani tun farko anginamin filin wrestling agidan dannaga alamar Roman reigns and Dean Ambrose ne agidan yakamata agina muku filin dambe,"ko kallonshi basuyiba suka wuce d'akinsu
ππππππππ
*SURBAJO*
ππππππππ
Zahra Muhammad Mahmud
Kuyimin afuwa masoyana wlh raina ne yab'aci Shiyasa na kula.Amman Namuku alkawari bazan sake kulasuba kugafarceniπππ
*Dedicated to, faty axland,rufaida umar, sadnaf,seemaluv,ummu yusura,maryam s bello,duka members na pml this page is yours love you all with all my heartπππππ*
*pure moment of life writers*
*p.m.l*
*page 91-95*
Al-ameen binsu yayi d'aki dukansu kowacce yay mata fad'a,yaja musu kunne sosai yanuna musu b'acin ranshi,hak'uri sukai ta bashi dakyar ya hak'ura suka koma zamansu kamar da.
Yau Surbajo ce da girki dan haka tun safe take ayki sabida sunk'i yarda ad'aukomusu me ayki ba yarda beyi dasuba amman fafur sunk'i yarda, se azahar tasamu tagama kintsa komai,da sauri tashiga wanka tafito ta shirya acikin wasu shegun kaya tayi kyau ba kad'anba,d'akin Al-ameen tanufa sabida yakira ta yace mata yadawo.tana shiga da gudu taje tarungumeshi takaimishi kiss, rungumota shima yayi yana Murmushi yace,
"Haba Baby wannan runguma haka ay Seki karyani,koda yake John cena ce ke bakyawa mutum dukan rashin imani",yafad'i yana dariya duka takaimishi sannan tasa kukan ahagwaba tace,
."Wlh bazan yardaba nice John cenar?,kai shikenan kafi son mukyale su suzo su wargaza mana gida, muna zaman lfy su kunno mana bala'i wlh k'aryarsu dole mud'au mataki",tafad'i tana murgud'a masa baki .
Dariya abun yabasa Dan haka rungumota yayi suka fad'a gado yana fad'in,
"Da kyau tawan Shiyasa nake sonki bakya d'aukar non sense, dan haka nima bari nad'au mataki anan, "romance d'inta ya shigayi kota ina tun tana tureshi harde Itama tabi yarima akasha kid'a.
Seda komai yalafa sannan suka sake wani wankan suka shirya suka fito zuwa dinning inda Aisha Itama fitowarta kenan, d'auke da Hanif d'ayan hannun rik'e da hannun Yusuf,cin abinci sukayi cike daso da k'aunar junansu.
Rayuwa taci gaba da tafiya cigaba ta ko ina zuwa yake musu komai tare yake musu ba banbanci, amman matsayin Surbajo aranshi dabanne yana mata son
dashi kanshi besan
iyakarsa ba, kuma Itama haka ko kad'an bata had'a soyayyarshi data kowa, iyayenta yana ganin darajarsu haka Itama tana ganin darajar nasa iyayen, rushe gidansu yayi a rugar yamusu gini na zamani dede da rayuwarsu,sannan yabasu jari me kyau dansu dunga sana'a, Surbajo har rasa bakin godiya tayi,sede fatan gamawa da duniya lfy data dunga yimasa.
B'angaren Aisha ma rushe gidansu yasa akayi akayi musu gini nagani nafad'a yaba mamanta jari me yawa dan ta dunga juyawa Tana kulawa da yaranta, Wanda hakan yasa Aisha K'ara nadamar abinda ta aykata masa abaya sosai tayi masa godiya har tana kuka.
Surbajo tasake samun wani cikin,Allah sarki Aisha murna takeyi fiye da ma Surbajon, tattali da kulawa daga Aisha har Al-ameen babu irin Wanda basayiwa Surbajo,tun cikin nak'arami Aisha tafara siyan kayan Babies tana tarawa unisex, Surbajo har dariya take mata.
Cikin na wata takwas sukaje scanning akace musu Baby girl ce,Wayyo dad'i rasa inda zasu sa kansu sukayi dan murna.
Siyayya suka shigayi kamar hauka don murnar Baby girl dazasu samu, basu da hira Seta cikin ahaka har Allah yasauketa lfy, tahaifo ta mace me kama da ita sak,babu inda ta barota har gwalo suka dunga yiwa Al-ameen na rashin d'aukoshin da Babyn tayi.
Ranar suna baby taci sunan maman Surbajo, wannan Karon harda Ard'o seda yazo suna jin ansama Babyn sunan masoyiyarsa,suna kiranta da Hanifa.
So da k'aunar da Al-ameen ke nunawa iyalanshi abin koyine ga duk magidanci kud'i basusa yarasa lokacinsuba duk kulawarsa nakansu bashida Lokacin komai senasu da iyayensa.
Lokacin aykin hajji yazo dukansu yabiya musu ta international suka tafi harda yaransu, sunyi addu'oi sosai Akan Allah yaba Aisha haihuwa domin Alfarmar Annabi da Alqur'ani.
Haka ranar tsayuwar arfa ma suka tsaya gurin yin addu'ar,suna kuka Surbajo tafi kowa yiwa Allah kukan yaba Aisha haihuwa domin girmansa.
Lokacin dasukaje d'awafin bankwana da kyar Al-ameen ya b'anb'are Surbajo ajikin Ka'aba tana kuka tana sake rok'on Allah, ahaka har suka dawo gida Nigeria kullum addu'arsu kenan.
Maman Yusuf
πππππππππ
*SURBAJO*
πππππππππ
Zahra Muhammad mahmud
*This page is dedicated to Zahra Muhammad Hausa novels group's nagode da irin soyayyar dakuke nunamin wlh acikin masoyana kune first Allah yasa yadda kuke sona Allah yasa inna mutu ku nunamin irin wannan soyayyar gurin yimin addua ngd banda kamarku yan uwana sonku ajinina yake love you all from the bottom of my inner heart.πππππππ*
Na jinjina muku..
Mrs fawwaz
Anty khady
garkuwa
fareeda
feedyluv
Maman sultan
Zee yabour
hafsey
Momyn janan
Maman ihsan
Kunada yawa wainda kuka dace a jinjinamuku Wanda bankira sunanshiba afuwan abinne da yawa mutuwa tashiga kasuwa,Allah yak'aramuku basira,yakuma d'aukaka pml up up up. p.m.l backward never insha Allahu.
*pure moment of life writers*
*p.m.l*
*last page*
*page 96-100*
Allahu gafurur raheem watansu biyu da dawowa Allah yaba Aisha ciki zokuga Surbajo har azumi tayi na nuna godiyarta ga Allah daya amshi addua'rsu,Al-ameen yayi murna sosai itako Aisha harda kukanta gurin nuna godiyarta ga Allah.
kulawar da Surbajo take bata abin gwanin Sha'awa dole su burgeka duk abinda Aisha takeson ci shizata bata ko menene, dayake cikin Aishan me kwad'ayine abubuwa da dama se anbar kaduna za'a samo mata shi in kwad'ayin abunda ba lokacinshi bane a kadunar ya motsa mata.ko kad'an basa gajiyawa da hidimarta wanda ita godiya kawai take musu da fatan alkhairi.
Cikin Aisha se girma yake wanda girman cikin har tsoro yake ba su Surbajo sabida girmane na sose,gashi lafiyarta k'alau ba
ciwon komai se na kwad'ayi gashi yanzu tazama rumbu cin abinci kamar hauka intaci kuma takasa tashi sesun d'agata.
Watan cikin bakwai suka kwasheta zuwa scanning dan su girman cikin ya tsoratasu,koda sukaje cemusu akayi komai normal kawai de twins ne a cikin.
Wayyo dad'i ππSurbajo sujjada take yi tana k'arawa ga ubangiji shiko Al-ameen duk girman Aisha da cikinta be hanashi d'agata ba yana murna.
Daga gurin scanning kasuwa suka wuce suka barta a mota suka shiga wani boutique na babycare suka shiga jidar kaya kamar hauka,daganan gida suka nufa.
Har walima seda sukayi dan murna inda akai addu'ar Allah ya sauketa lfy.
Watan haihuwarta yatsaya kullum cikin addu'a suke Allah ya raba Lfy, wata jumma'a Aisha ta tashi da ciwon nak'uda da sauri suka d'auketa zuwa asibiti.
Da isarsu labour room akasata, Surbajo kamar zatayi hauka dan tausayin Aisha, addu'a kawai sukeyi dan shima oga hankalinshi atashe yake.
Suna nan tsaye wata nurse tafito tamusu albishir data haihu Lfy ansamu twins duka mata,rungume juna sukayi Surbajo da Al-ameen suna nuna farincikinsu ga Allah.
Bajimawa aka fito da me jego da twins d'inta kyawawa dasu aka kaisu d'akin hutu.Surbajo tunda ta d'auki yaran kasa ajiyesu tayi sabida kyan da Allah yay musu kuma abin mamakin yaran da Surbajo suke kama kowa seda yayi mamakin hakan.
Aisha kallon Surbajo tayi murya araunane tace,
"Sister nagode da addu'ar ki gareni,wlh base kin ce kina k'aunataba inda banyarda ke me sona bace yanzu dole nayarda duba da kammanin da yarannan sukeyi dake, nayi imani inba nagartacciyar soyayya hakan bazata yiwuba,nagode miki sister da addu'ar ki gareni Allah ya rabaki da bak'incikin duniya da Lahira,"tafashe da kuka da sauri Surbajo tamik'awa Al-ameen yaran tarungume Aisha tace,
"Haba Aunty yau ranar murnace agaremu ba kukaba Allah ya amshi addu'ar damuka dad'e munayi danhaka godiya kawai zamuyi masa, kimance da komai Aunty na ni mesonkice."
Koda aka Sallamosu Surbajo ce d'auke da yaran tun kan su k'araso gida gidan yacika da y'an uwa kowa murnar haihuwar su twins yake.
Al-ameen yanajin son yaran har zuciyarshi badan komaiba sedan Kama da Surbajo dasukeyi bame kallonsu yace ba ita ta haifesuba, Allah Kenan.
Ranar Suna Surbajo ba k'aramin mamaki tayiba,
dataji yaran duka sunanta Aisha tace asa musu d'aya Zahra d'aya fatima suna kiransu da mamah da mimah, amman Al-ameen me suna zahran Surbajo yake ce mata yayinda ita kuma yaci gaba da kiranta Babynsa.Surbajo godiya tadunga yiwa Al-ameen da Aisha abisa karar dasuka yimata.
Rayuwa taci gaba da tafiya inda Ahalin yanzu Surbajo tagama university d'inta Amman Al-ameen yace bazatayi aykiba,bata musaba ta hak'ura,Aisha nakan nata karatun dan itama tuni takoma makaranta,Yaransu gwanin Sha'awa bame gane wannance Mamana acikinsu sabida duk kulawa d'aya suke basu.
Al-ameen hankalinshi akwance na iyalanshi ma haka so da k'aunar dake tsakaninshi da Surbajo se son barka duk da yana b'oyewa gudun kar ran Aisha ya b'aci,amman son da yakewa Surbajo gagara misaline.
ina labarin su Ruky?
Ruky tunda suka bar gidan Aisha da wata uku tafara jin canje canje ajikinta dan haka ta nufi asibiti gwajin farko aka bata sakamakon HIV,yanke jiki tayi tafad'i sumammiya Gado aka bata a asibitin.Zuly nasamun labari tazo asibitin tagaida Ruky kamar abin arzik'i daga k'arshe se cewa tayi.
" Wannan k'awance namu ina sonshi tunda gashi nayi nasarar saka miki ciwon danake d'auke dashi."daganan takwashe labarin komai tafad'a musu tana dariya, Maman Ruky shak'e Zuly tayi kamar zata kasheta tana yimata Allah ya isa,likitoci sunkasa kwaceta a hannunta dan haka suka kira police sukayi gaba da Zulyn.
Ruky ko kuka take me tsanani tashiga barin wasiyya tace ma mamarta tanemarmata yafiyar Aisha tasan hakkintane yake bibiyarsu don Allah tayafemata,ranar Ruky bata sake kwanan duniyaba tace ga garinku bayan tayi kalmar shahada.Allahu akbar Allah nason masu tuba Allah kasadamu da rahamarka dan darajar Annabi da alqur'ani Ameen.
Zuly ko kotu aka shigar da ita k'ara inda aka yanke mata d'aurin rai da rai agidan kaso,gamida horo me tsanani har iya k'arshen rayuwarta. Duniya kenan shiyasa akace abinda kashuka shi zaka girba Allah yasa mudace Ameen.
Su Aisha dasuka sami labarin mutuwar Ruky har gida sukaje gaisuwa ananne mamar Ruky take sanar da Aishan sak'on Rukyn,kuka Aisha tasa tace,
"Wlh nayafe mata duniya da lahira Allah yajik'anta yakyauta namu zuwan,"
godiya yan uwan Ruky sukai tayiwa Aishan.
To Ruky Allah yajik'anki yasa kin huta ya yafemiki kurakuranki.
Surbajo uwar biyu yanzu haka wani cikinne ajikin Surbajo tsoho yafi na Aisha girma scanning na farko aka shaida musu yan biyu ne duka mace da namiji,fad'in murna da farincikin da Al-ameen da Aisha sukayi page din yayi kad'an se fatan Allah ya sauketa Lfy.
Tahaihu Lfy inda yaran suka ci sunan iyayen Al-ameen. So da k'auna agurin Al-ameen da Surbajo abin fatane ga kowacce mace agidan mijinta.
*Godiya ga Allah subuhanahu wata'ala daya bani ikon kammala wannan littafi nawa me suna Surbajo.ya Allah kuskuran danayi kagafartamin wa'azin dake ciki gamu mata masu zafafa k'iyayyar kishiya Allah yasa mata sund'auki darasin, maza mata masoyana ako ina kuke afad'in duniya me surbajo na k'aunarku harcikin ranta Allah yabarmu damasu son mu ameen wandama baya sonmu Allah ka jarabceshi da sonmu,Allah yazaunar damu cikin aminci. Kubiyoni cikin sabon littafina mesuna CIN AMANA KO FANSA*
NGD
maman Yusuf love you all πππ