Showing 27001 words to 29328 words out of 29328 words
Rafi,atu har tasamu ciki dan balaulayi takeyi ba ,tana samun kulawa daga mai gidan ta,karatu kuwa yinshi takeyi Sosai bakama k'afan yaro babu wani abunda yake damun ta Rukayya tak'ara samun ciki ,ita da maryam cikin karannan yakan basu wahala bana kad'an ba dan sauran su wata biyu sugama Nura wata d'aya sun maida hankalin su ,a kan karatu..
Sumsumma
"Maman sadiya " tunda yanzu kinsamu tallafi kodai zaki dawo da yaran nan ne? Inna najefa sunce aa wai masu bada taimakon na d'an wani lokaci ne zasuzo sudai na,inyi hak'uri "yara sukuma sunki" toh babu komai Allah yayi mana kekkewan k'arshe Amin ya rabbi
Manyan mutane ne, suka raba gadon Gwoggo gashi tabar wasiyya Harda rubutu ,akan Nura shizai cigadon ta,dan tare dashi suka nemi kud'in filinta biyu da shanu da gida anyi rabon musulunci Sosai
[25/05, 07:36] Maman Khairat: 8️⃣9️⃣⏭️9️⃣0️⃣
Maman Faruq "jiya naje gidan marayu sunbani duk wani bayani da,nake nema gameda ke" suncemun abunda zaifi inje gidan da,aka kawoki a tambaya koza,a dace a akwai wani Wanda yasan ,iyayen ki.
"Amma kuwa da zanfi kowa jin dadi gameda haka,"yanzu yakenan ?"munje danida faruq jiya,munyi kwatancen iyayen naki,amma ance mana akwai wata mata zulfa,u wai suna yawan shiri dan gidan ta kad'ai mahaifiyarki take shiga ance tayi tafiya..
Gobe zata dawo in sha Allahu!
"Sai jibi sai muje dake, sannan Wanda suka kawoki ,lokacin da abun yafaru yayi magana,yace akwai wani Wanda abokin babanki ne, daga baya yazo dubaki,sukace an kaiki gidan marayu..
Nayi farin ciki Sosai dajin wannan labari" hak'ik'a samun miji irin ku, a duniya babban sa,a ce "kinfi k'arfin haka a guna ina yimiki so na, tsakani da Allah ne Shiyasa nake sonki a raina
SUMSUMMA
" Sulaiman ina so muyi wata magana dakai ,toh Malam Sulaiman "dan Allah inaso kafahimce ni"in da hali tunda *Sayyada* tagama Secondary schools gashi tanada ilimi inaso tunda shekarunta sha tara yanzu inaso in har bakubawa wani ba zan aure ta" inaso kubani ita ..
Amma malam kaifa d'an gatane taya,kana malami mai ilimi zaka auri y'ar fulani Mara gata ,Wanda rayuwar su ciketake da,abubuwa kala,kala.
"Aure babu ruwan sa,da duk abunda ka lissafa d'innan " ni, dinnan daka gani ni maraya ne gaba. da baya ,a ranan da,aka haifeni ,a ranan barayi suka shiga gidan mu,suka kashemun iyayena iyayena ba,anan sukeba sudin y'an libiya ne ,aiki ne yakawo su Nigeria nasamu wannan labarin a gun wani tsoho makwabcin mu,shiyake bani labari lokacin ina d'an shekara goma,nasha kwana,a waje saboda rashin gata nifari ne ,nayi bara nayi dako dashi nake biyawa kaina buk'atuna,nayi duk kan wahalan rayuwa fiye da,naka "makwabcin mune yake kuladani gashi ,abunda zaici ma,gagaran mu yakeyi zanyi faskare ,in zubar da bola inyi duk wani aikin wahala ,amma bai hanani karatu ba,,ana cikin haka Wanda yarik'eni yarasu
Nasha wahalan rayuwa gani da ilimi Sosai ai Allah yasoni ina primary nasamu scholarship natafi karatu ,a kasar waje wani a cikin mayan an mutanen yayimun komai bandawo ba sai da nayi doctoring kafun nadawo Nigeria
Ina dawowa in da zanzauna shima aiki ne Allah yasa Wanda suka turamu a cikin su yasamamun aiki ..
Nafara aiki a cikin polytechnic watana hudu ,shida iyalansa sukayi hatsari suka rasu gaba d'ayan su yaro d'aya ne yarage daga baya yarasu shima ..
" gaskiya malam kaga rayuwa kam "Shiyasa baka k'in mutane ,nayi mamaki da har kake iya mu,amala tare damu ko nuna damuwa ,a hakan haka..
" in tanine nabaka duniya wa lahira,nasan kasan matsayin mu"amma baka ganin Sayyada bata dace dakai ba"haba Sulaiman yanzu fa nayi maka bayanin koni waye ne,taya zakace haka..
Sallama sukayi yawuce gida duk abunda malam Sulaiman yagaya mishi yasanar a Inna kowa yabada goyon baya a kan hakan .
"Zanbawa Sulaiman Sayyada koda bansan shiba ya tambayi Sayyada in ta,amince nawa mai Sauk'i ne nabashi dan yataimake mu,a lokacin da muke neman taimako, .
Da,dare yazo yasamu Sayyada sukayi magana ta Amince aka fara cukucukun aure babu wani hidima dan shima malam Sulaiman yayi ginin shi mai kyau na zamani yayi duk abunda akasan za,a nema dan yasan waye ne mutanen da yake tare dasu
An tsaida auren nan da wata biyu masu zuwa ,tunda ga lokacin in Garbati yayi aiki kud'in yake tarawa baya kashewa in badai wani Abu za,a nema ba yasiya mata katifa da babban. Keken d'inki da wasu abubuwan kud'in gadon ta,akayi mata siyayya dayawa
*Amarya Sayyada tofa*
[25/05, 07:36] Maman Khairat: 🅿️9️⃣3️⃣⏭️9️⃣4️⃣
Cikin ikon Allah haka suka gama Exam babu wani matsala dan yanzu hankalin su a kwance dangin maryam sai da sukayi sati biyu kafun suka wuce tare da cemata Yabar gado dayawa dan shago yakeda shi na siyar da kayan abinci ga gida daya gina dan haka tun, lokacin da sukaji labarin yarasu amma matar shi sunhaihu aketa ajiye duk abunda yabari shago kuma k'anin sa ne Sa,idu kekulawa da shi ,tasha kuka wajen rabuwa da nata"a she haka akejin dad'i in kana cikin yan uwanka.
Gashi nayi sa,ar miji Wanda bantab'a samun matsalaba, lokacin da yaji banida a sali ya rungumeni bai tab'a mun gorin iyaye ba kok'adan ..
Aisha "inaso in yi aure a karo na biyu" in babu damuwa kinemamun gudun fitina"karka damu zaka,iya nema da kanka sannan zaka samu"sai dai fatana ina rok'on Allah yasa duk wacce zaka aura yasamun sonta a raina ba k'iyayya ba "Aisha bazan tab'a wakak'anta kiba kome nazama" Kufa maza ba,a iya muku kokad'an "amma akwai wata yarinya a gidan marayu Siyama", itakam iyayen tane suka rasu ,haka Rafu,atu tagayamun kodai zaka jarraba mugani dan agun mama salamatun su take da zama kaga Su Rafi,atu kowani Saturday suna zuwa ,sannan sunyaba da halinta,tunda kanace akan cewa sai sai irin sukakeso"
Bazaki gane bane shiyasa ,kinsan kuwa "rik'e irin wannan mutanen muddin bakaci zalinsu ba" toh mudai jarraba mugani sai kaga andace gaskiya kam ..
Bawani tsoro babu komai yanufi gidan marayu yayi musu bayani sunkuma yadda da komai dan yanzu sundaina yadda da kowa sai anyi gwaji kafun siyama ta,amince ta yadda daman Rafi,atu sundade suna jan ra,ayin ta shiyasa mama Salamatu batasha wahala wajen nuna mata wannan abun akwai Alkairi a ciki ba ba,adau lokacin mai tsayiba aka tsaida ranan aure wata d'aya babu yawa.
Siyama tanada girman jiki tafi, su Rafi,atu komai shiyasa mutane sukanyi mata kallon babba ce ma.
BAYAN WATA D'AYA
A wani ranan jumma,a ne aka d'aura auren siyama da Abba Faruq babu hidima dayawa dan yace shiba yaro bane babu Wanda Ummi Aisha tagayawa sai Mabaruka, itan mayazama dole shiyasa tafad'a dan zirga zirganta ,a kai akai tanaganin tunda auren ta yamutu ko Abba Faruq zai amince ya aure ta in zatazo da kwalliya take suwa Sosai in Ummi Aisha ta kalleta sai tayi dariya
Tunda ,a kayi bikin Sayyada babu wani tashin hankali da kad'an kad'an Malam Sulaiman yake siyan wasu kayan ,a duk lokacin da yatina ,ina zainemi dangin shi sai yaji wani iri a ranshi "yazama dole ya nemi hanyar da zai sadashi da y'an uwanshi babu abunda yarage na shedan samun yan uwanshi
I
[25/05, 07:36] Maman Khairat: 🅿️9️⃣1️⃣⏭️9️⃣2️⃣
Alhaji musa ne yakira Nura "kaje gida kacewa Maryam tashirya kakawo ta tsamiyan lilo"lafiya kuwa? E batun dangin natanne ,nikuma ina office " ganinan zuwa.
"Anty Maryam ina wuni"kadai nacemun Anty "yazama dole in gayamiki kefa matar Babana ne taya bazan gayamiki Anty ba" Baba ne yace in daukeki ,in kaiki Anguwar tsamiyan lilo zai samoki a wajen "bari nashirya sai mutafi " ina Rukayya ?tana gida lafiyanta
A nutse yakejan motar, har suka, iso sunsamu Alhaji Faruq yana jiransu, zulfa,u itama tazo Nura yana,ajiye su yawuce gi da Alhaji Faruq yatsaya "sannun Ku kushigo mana duk an zauna " munaso muji labari akan maimuna da Yusuf"
"Kamar yadda mukayi zaman mutunci " tacemun ita yar Bauchi ne an hanasu ance bazasu yi aure ba shine suka gudo dan iyayen su basusan in dasuke ba sunzo nan damaturu wani babban malami malam Ibrahim ya daura musu aure ,akan wata budurwar shi tabiyo shi shima ,sannan tayi mishi fariya muddin bai aureta ba zata,iya had'a gobara duk su mutu ,da sunzauna a pamfamari ,daga baya suka dawo da tsamiyan lilo,tacemun sun rabu akan wancen budurwar tasa .suka rabu a lokacin tanada ciki amma suna zaune daga baya suka dawo da auren su tayimun kwatancen anguwan su a bauchi.
Har address d'in gidan tabani lokacin danaje, bauchi naje har gidansu naje sannan nace musu tarasu bamusan waye tazo tasaka wuta a d'akin ba "dan haka ke y'ar halak ne bata hanyar banza ,aka sameki ba ko yau zanbaku number wayan da suka bani",
Kowa nawajen hamdala yayi ,babu wanda yakai Maryam murna zataga kakanun ta da dangin mahaifin ta,basu number tayi sukayi mata in sani sosai.
*Washe gari*
Da safe suka shirya dan zuwa bauchi,tayi mamaki da yadda taga kakanun ta sunada ilimin addini taya suka bada k'ofa wajen ruguza rayuwar Yaransu sunyi madama bak'adan ba sunsha kuka kukan da babu amfani
Hak'uri suka bayar tare da had'asu da mutum d'aya dan yaga inda suke zaune har wani jiki maryam tayi ranan Rukayya da Rafu,atu sunje tayata murna " kinji dad'inki yanzu kam Allah dai yasa mudace"kekam rayuwarki da Sauk'i "banaso kunasa kanku damuwa duk Allah ne ya halicce mu bakuga yadda Allah yatsara abun shiba.
BAYAN SATI BIYU
A cikin satin ,aka d'aura auren Sayyada da malam sulaiman babu wani hidima da,akayi dan mutum ne mara sakewa da jama,a shiyasa bashida Abokai nai Sosai sai nagun aikin su.
Ansha hidima Inna bata gayyaci mutane dayawa ba, dan auren ma,a masallacin jumma,a aka d'aura auren .
Maryam da Rukayya sunhaihu a satin da suka haihu a satin sukafara jarabawar gama makaranta Exam sukeyi sun maida hankalin su suna karatu dangin Maryam sunzo dayawa dan Ranan sunan duk kansu suna Exam
Matan Baban Rukayya susuka zo dan zauna mata a satin Ummi Aisha tayi rawan gani wajen taimakawa Rukayya da shawarwari Sosai
[25/05, 07:36] Maman Khairat: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸
GIDAN MARAYU
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
STORY AND WRITING BY AMINA. MA,AJI (MAMAN KHAIRAT )
TRUE LIFE STORY
PAID BOOK 200
9️⃣5️⃣⏭️9️⃣6️⃣
Inna cikin kwanciyan hankali take babu wani sauran damuwa a tattare da,ita dan yanzu itama har taimakawa Almajirai takeyi in sunshigo bara kowani wata Malam Sulaiman yakan siyamusu shinkafa rabin buhu da wasu abubuwa daya sauwak'a .
Watansu hudu zakace sunyi shek'ara da aure " maman sadiya yanzu rayuwar tayi musu dad'i Sosai babu wani sauran damuwa, inda Sulaiman yanuna yanason Sadiya da aure haka, akaturashi k'auye wajen nema mishi auren ,anyi sa,a anbashi yayi murna saboda hankalin sadiya yanuna ra,ayin shi a kanta..
Alhaji Kyari"Rukayya yanzu nasan dukkanku kungama nasama muku duka aiki kuci gaba da tafiyar da rayuwar Ku,wannan aikin zaitaimake ki keda yaranki koda bayan babu raina.
Dan shi duniyan nan y'ar hak'uri ce nasan nawadata ki da komai banrageki da komai ba "naso mutanan da suka rayu dake, basu barki kinyi kukan rashin ,asali ba..
Baba kadai na fad'an haka rubuceccen Al,amari ne munaso bamaso namu k'addaran kenan " Allah yamuku Albarka Amin naji dadi da kukasawa Gwaggo Maisuna dan tasanadiyan Ku nasan darajanta gashi y'ar uwata ce tajini kuwa Allah yayi Albarka Amin
Babu wani sauran kunya yanzu da Rukayya mahaifinta yake shawara bayayin shawara da wani dan yafijin shawaranta a kan nakowa yana son y'arshi Sosai .
Mama Salamatu tana tafiya tafad'i take aka kaita Asibiti numfashi yak'i tsayawa ,ansanar a gidan marayu take Rafi,atu Rukayya Maryam Siyama duk sunji duk suzo banda kuka babu abunda sukeyi ga Siyama da k'aram ciki har kusan tara ,na dare duk suntaru babu Wanda ya,iya magana juyata,anata yumata fifita "Rafi,atu bani ruwa zansha " toh bari na d'agaki duk Kansu suka d'agata tasha Ruwan suka juyamata kai shikenan tafiyan kenan Allah yajik'anta yamata rahama .
"Tayi bacci kuduba babu abunda ke motsi fa," shikenan mama salamatu tabarmu ,babu Wanda baya kukan rashin mama Salamatu ,mata mai kirki ko haihuwa bata tab'ayi ba kowa sai yatausaya musu ,irin kukan datasukeyi koni naji mutuwar ,duk Wanda aka tambaya sai ace yaranta ne dan kowa sai katausaya mata, lalle gidan marayu anyi babban rashi bana kad'an ba...✍
Maman Khairat ce
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
GIDAN MARAYU
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🅿️9️⃣7️⃣⏭️9️⃣8️⃣
🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚
Haka ,aka shirya ta mutane dayawa suntaru kowa Alkairin ta yake fad'a babu Wanda bai fad'i Alkairin mama salamatu ba "Su Rafi,atu duk sunrame babu Wanda mutuwan bai shigeshi ba Yadda suka damu da mama Salamatu basudamu da iyayen Su hakaba Suwaiba tazo gai suwa tare da jajanta musu .
Malam Sulaiman yatafi memo dangin Su cikin sa,a yasamesu da kwatance Allah yahad'ashi da yan uwanshi yayi murna da hakan satin sa biyu yadawo Nigeria tare da musu Alkawari duk ranan da Allah ya Sauk'i Sayyada zai kawota tasaba da yan uwanshi dan suma suna cikin Farin ciki zasu koma Nigeria da zama
Wani kulawa da Abba Faruq yakebawa Siyama kaman bai tab'a aure ba sai a kan Siyama ganin hakan ne yasa Rafi,atu bata yawan zuwa gidan ,badan komai ba sai dan har yanzu kunyan Abba Faruq takeji taki sabawa da shine yahaifeta..
,A wani ranan ,alamis Siyama tahaihu tasamu beby girl yaranya kamar ba jaririya ba zakace tayi wata da haihuwa ,lafiyayya da ita gonin sha,awa.
Anyi Auren Sadiya cikin ikon Allah komai anyishi cikin rufin asiri Garbati shiyazama kaman uba dan duk abunda ,a,kenema babu Wanda yagaza ,yayi wa wani magani yad'auki yarshi yabashi ,Sadiq shikam karatu yakeyi yana polytechnic malam Sulaiman shike d'aukan d'awainiyan shi .
Sayyada taje wuni gidan Inna kafun kace miye tahaihu tasamu yaranta guda biyu duka maza ,sai kiran shi ,a kayi yazo yakaisu gida babu Wanda yasan zata haihu daga shi sai ita.
Garbati karatu ,duk da ya girma amma yasaka Ibrahim karatu dan ya ,dogara da kanshi.,sai dai muyi fatan Alkairi a Inna dan gidan ta yazama gidan Alkairi tarik'e Wanda bajinin taba ta .
Ansha suna y'an uwan Inna duk sunzo tare da na Janbo Anyi abu cikin kwanciyan hanhali.
A hanyar kaduna Abba Faruq sukayi hatsari take ya amsa kiran ubangiji babu Wanda baiyi kukan rashin Abba Faruq ba musamman Siyama ,bayan rasuwan da sati d'aya Ummi Aisha tarasu jama,a sai surutu sukeyi tsakanin Ummi Aisha da Siyama wata shida Allah yamusu rahama,anraba gado
*Tammat Tammat*
Anan Nakawi k'arshen gidan marayu kuskuren dake cikinta Allah ya yafemana Fad'akarwar Allah yabamu ikon amfani dashi
Sai munsake haduwa a littafi nagaba mai abun Al,ajabi