Showing 21001 words to 24000 words out of 29328 words
naji dadin yadda ka auri Rukayya Allah yabayaka,kozaka zo muje gidan gwaggon naka ne? Muje sallama sukayi sunkama hanyan *FAWARI*sunata hira Sosai ma tana zaune suka shigo cikin gidan waye"?nine gwoggo Nura kaida waye kodai Rukayya ce aa mahaifin tane toh ganinan zuwa Bissimillah aa kyari yaushe rabon kada kazo gidan nan "tun lokacin da ina yaro banwuce shekaru sha biyu ba a duniya " a ina kasan nura "shine mahaifin Rukayya " wani razanta,d?datayi,"wannan yayar mamata ce dakake ganin ta nima itace ta rauneni
[25/05, 07:35] Maman Khairat: 🅿️6️⃣8️⃣⏭️6️⃣9️⃣____________Bangane tare kuke dashiba? "Wannan k'anwar mahaifina ne" nikuma uwata ce "tayaya kenan?ta inda kasani "bantab'a jin kin haihuba yaya nura yazama d'anki?
Kamar yadda kaji yafad'a nine mahaifiyar shi ,kunwatsar da zumunci kyari " bansan kodan kunyi kud'inne ba shiyasa .
Wannan yaro shine bango Abun jingina shine madubin da nake haskawa koda mutuwa nayi na,umarci dangina subashi gadona dan banida kowa sai shi "nina tsince shi ,a k'ofar gidana anzo anjefar dashi nayi mishi karatu tundaga primary har nagaba nakuma aurar da shi da jikana,guda d'aya .
A ina kuka had'u ne? Wannan shine Baban Rukayya " aa kagayamun gaskiya Nura da gaske nake "kai kyari taya kasamu yarnan " Gwoggo kibari kawai labarin ne dayawa,tashi Nura yayi dan bayason yaji mezasuce karya zama sirrin cikin gida ne "kagayamun " sharrin shed'an ne komai yagaya mata"kagani ko Allah kenan dakace bakaso yanzu Kuwa tana cikin jerin yaranka da kakeso toh kabi duniya a hankali marayu suma sunada rana Sosai akan kowani irin abu daka d'auka zaka gudu ne kagodewa Allah "shiyasa Nura yace bazai tab'a auren yar asali ba sai Wanda itama ciwon dayasame shi ,itama yasame ta"
Kawani zuba manyan kaya kaman na Allah kadaiji tsoron rabbi dan duniyan nan wallahi in har baka bita, a hankaliba akwai babban matsala Sosai
Surutu tatayi tana ganin kyari tatina da d'an uwanta duniya kenan Allah yamusu rahama Amin "zamukoma Allah yakiyaye hanya " Nura kacewa Rukayya gobe tazo ,toh zangaya mata ,lokacin da suka fita "Nura kaga wani ikon rabbi ko haka Allah yake hikimar shi kaduba a gidan k'anwar mahaifina katashi ,ita kuma Rukayya ta rayu a gidan marayu Allah kenan mai kyauta da k'ari.
" hakane Baba yanzu yaushe zaku tashi? Sai nayi magana da Gwoggo na duk abunda tace ,babu komai duk yadda kukayi dai dai ne Allah dai yayi muku Albarka Amin..
Hawaye ne,yazubo ta idon Nura yanzu haka rayuwar zata ,wuce batare da naga iyaye naba.,kafad'an shi Baba kyari yadafa "zanzame maka gata kuma uba babu ,Wanda zai maka gorin mahaifa " nagode bari ,in mayar dakai gida "ka,iya mota ne na,iya kad'auki motar da ,aka kawo maka kayi amfani da shi nagode har k'ofar gidan a,ka kaishi,
Yana shiga Rukayya " Rukayya meyafaru ,kai zan tambaya naga jikinka yayi sanyi"kinsan Babanki d'an yayan Gwoggo ne"bangane ba toh nikam yadai haka,duk Abun in katab'a sai kaji an had'a dangan taka..
[25/05, 07:35] Maman Khairat: 🅿️7️⃣0️⃣
Wannan nekuma bansani ba mubarwa Allah komai shizaifi dan abun yabani tsoro gaskiya kiduba"sun watsar da Gwoggo na ko nemanta basayi tunda d'an uwanta yarasu wato kakanki shikenan "yanzu " kowani maraya bashida y'ancin kanshi kenan gaskiya rayuwan tazama wani kala"duk fad'i tashin da Gwoggo tadinga yidani kaman batada dangi "a she ita y'ar babban gida ne..
" banaso kana zubar da hawayen ka ,akan wasu dalilai "ina Alfahari da kasancewa ta,a haka gashi Allah yamun baiwar miji nagari.
Rukayya yanzu babu abunda nake nema ,a duniya fiye da sanin suwaye ,iyayena" amma duk yadda ,akayi Wanda suka yasar dani "na tabbata sunsan Gwoggo zata kula danine shiya sa..
Toh ka godewa Allah !!
Hakan zaifi maka," Baba yace in d'auki mota in yi amfani da shi ,yakika gani "ka d'auka tunda shiya baka gashi yace kayi amfani da shi .
Washe gari da safe a gidan Gwoggo suka k'arya Mohammad a gidan A kayi mishi wanka " Rukayya kyari shine mahaifin ki "E Gwoggo " ki d'auki wannan a matsayin K'addara kinji banaso ki d'aga hankalin ki, "karkuma kice dan d'an uwana ne, " babu komai Gwoggo nad'auki komai ,a matsayin k'addarata babu komai Allah yarufa asiri Amin
Nasiha mai ratsa zuciya Gwoggo tayi muku duk kansu, sai dare sukatafi gida ,Rukayya batason taga Baban ta dan wani kunyan shi takeji Sosai.
"Inna ta rungumi yaranta basuda wata matsala ,amma har yanzu suna wanki da aika ce,aikacen da sukeyi Sayyada batafasa Zuwa aikin taba yanzu kud'in natane bana kowa ba..
[25/05, 07:35] Maman Khairat: 🅿️7️⃣1️⃣⏭️7️⃣2️⃣
Manyan gidan marayu duk an sanar musu,akan cewa Yau zasuje suyi fad'a a Rafi,atu dan haka kowa cikin shiri yake har mama Salamatu.
Ma,aikatan gidan marayu ne su, biyar sunkawo ziyara ,a Rafi,atu anyi sa,a kuwa Abba Faruq yazo Suwaiba,itama tana gari bata sauk'a a gidan Ummi Aisha ba.
Duk Kansu a cikin babban parlour suke sunzauna ,Director ne yafara magana"Ke Rafi,atu inaso kibude kunnan ki da kyau kijini "a cikin tarbiyar da muka baki, wannan halayya baya d'aya daga cikin abunda muka koya miki", a ina kika koyo ,bamu sanki da rashin kunyaba ,meyasa bazaki d'auki k'addaran data zomiki ba,kiduba rayuwar wasu ,abun tausayi kekin samu shine kike haka,kiji tsoron Allah yazama, dole kiyiwa ,iyayen ki biyayya kinsan matsayin iyaye kuwa,wannan abun da yafaru duk yana cikin k'addaran ki,baki,isa ki kaucewa k'addaran ba.
" wani tunda yafad'o duniya yaketa had'uwa da jarabawa ,kala kala,ke ,a cikin jarabawa wanne kika gani?
Abba Faruq ne yayi Magaña "tunda tace bazata zauna ,a gidan nan ba, tafad'i duk in datake so sai tazauna" babu in dazataje muddin tana girmama,mu yazama dole a gareta tazauna shine manufa dan babu wanda yasan meyake faruwa kuma babu gudu babu jabaya ,a batuna ,sannan babu ruwana dake Rafi,atu .
"Mama Salamatu kiyi hak'uri kece uwar da in tayi fishi dani in ke shiga damuwa, ,zanyi duk abunda kukace babu,abunda bazanyi ba yanzu yawuce " amma ya matsayin yaron nan "shima gidan ubanshi ne, zaiyi rayuwa irin nakowa ,babu abunda zaifaru dan haka,ganan mahaifiyar ki,kinemi ta yafe miki shine gatanki ,sannan kidinga tauna Magaña kafun ki furta,kinji Allah yamiki Albarka,.
Alhaji Faruq munji kabasu kud'i da wasu abubuwa dan tabbas babu wanda zaici gadon ka,a cikin su Allah ya rufa ,asiri Amín
" kiyi koyi da Rukayya mana,yadda ta fauwalawa Allah komai"
Tashi Rafi,atu tayi tarungumi Suwaiba "ki yafemun na tuba ,akan rashin kunyan da nayi miki ,karkiyi fishi dani dan Allah ,dago Fuskanta tayi yawuce ,in sha Allahu Allah ya miki Albarka Amín
GIDAN ALHAJI MUSA
Bugun k'ofa a keyi matar Alhaji, Musu ce, budewar da Maryam tayi,taganta bangajeta tayi tawuce" ke y'ar shegiya kisani kina yarinya dake ,kinzo kin wani, a sirce mun miji daman haka kuke yaran titi, kisani ni,yar a,salice gaba da baya bana wasa da Asalina ..
Dangin,gidan marayu ,wanda a tanb'ade aka samesu,kunyi munafurci dan kar in gane keba yar halak bañe .toh nagane duk wani munafurcin ku,har zungurin kan Maryam tayi ,Tunda kince mijina zaki aura toh muzuba mugani nidake shege kafasa gayyar gidan k'azanta,tunda tafara Maryam ko d'ago kanta batayi ba,duk abunda tafada Recording tayi,a wayarta har tagama tafita daga gidan ,wani hawaye na bak'in cikin yazubo ,ko nono tagagara bawa yaron saboda bak'in ciki har yamma yadawo taransa tayi komai ta,tanadar mishi sai da yaci abinci yawatsa ruwa yana hutawa "ga wannan kaji ,ina zuwa"meye kai dai kaji mana, tashi tayi daga wajen tatafi kitchen.
Tsaf,yaji duk ranshi yab'aci " maman Faruq "kizo ,gani " kiyi hak'uri kinji bansan yadda zanyi da wannan matar ba,amma karki damu zan d'auki mataki,"banaso kayi hukunci cikin zafi,kabari sai zuciyan ka tayi sanyi kafun dan yanke hukunci cikin zafi yana sawa ,ata aikin dana sani dan haka babu komai ..
Key ya d'auka yafice daga gidan, in ka kalli Alhaji musu kasan yana cikin damuwa"meya kaiki gida na?nikuma eh ke mekikaje yi ,?"bari kisani bazan d'auki rashin sanin darajan d'an Adam ba wallahi kinji na rantse Yau bazaki kwana a gidan nan ba kije gidan Ku, sai kinyi hankali kidawo"nikake kora a kan yar gaba da fatiya lalle ka kyauta nagode.
Sai kinfita daga gidan nan Yau zan nuna miki ni, namijine sannan inada y'anci da kuma doka a gida na tunda ke bakeson zaman lafiya.
Yau a kan mace kace in je gidan mu.
Sai dayaga tafiyan yanta kusan mangariba kafun yadawo gida,bata nufi gidan suba gidan Abba Faruq tanufa tayi sa,a yana nan a gida sai da yadawo daga masallaci kafun suka zauna.
"Meyafaru?karya tafad'a Sosai " kiyi hak'uri dole sai kin ajiye kishin ki,Maryam fa,kamar yar cikin ki,take dole zakiyi hak'uri Sosai dan wallahi,muddin kikace zaki dinga zagar mishi mata toh bazaku shirya ba,kece babba meyasa bazaki ja girman kiba
Muje In mayar dake ,har gida ya mayar da ita yara sai murna sukeyi ,kiran Alhaji musa yayi"kana ina?"ina gida wanne a ciki gidan Maryam "ganinan zuwa ..
[25/05, 07:35] Maman Khairat: 🅿️7️⃣3️⃣⏭️7️⃣4️⃣Meyasa kakori Rashida ?kabari tarainani tazamar dani bawanta,ina matsayin mijinta amma duk abunda yafitoh daga bakinta gayamun take."tace kayi sati bakaje gidan taba"k'arya takeyi bawani jiya nadawo gidan Maryam bari na kunna maka kaji metayi sai da Abban Faruq yaji tsaf kafun yarik'e baki "gaskiya wasu matan shed'anu ne nabugawa a jarida " kasan meta gayamun kuwa "kayi hak'uri yanzu kamayar da ita dan yanzuma namayar da ita gidan ka" banason haka Faruq nafa rantse karkasa kaffara yahau kaina tunda nace bazata kwana ba daka barta..
Kadaiyi hak'uri akwai hanyoyi da yawa Wanda zaka hukuntata,ba sai tawannan wajen ba "sannan kabawa Maryam Hak'uri dan wallahi akwai bacin rai " yanzu kaga wani abu kaduba yaran nan,duk sunga iyayen su ,amma ita har yanzu bata ga iyayen taba duk da ance sunrasu Allah ya had'ata da dangin ta Amin ,konawa zan kashe in har za,aga dangin Maryam..
Allah yasa mudace Amin "tunda kadawo da ita bazance komai ba Amma zan ,kaurace mata har sai tagane tayi laifi kafun Allah ya kyauta Ami
SUMSUMMA
Cikin dare kowa yayi bacci Su Inna sunata bacci sai jin hayaniya sukeyi gobara gobara a razane Inna tatashi ta je da gudu tagayawa su Sulaiman sukafita kafun kace meye wuta yahadu, banda kuka babu abunda sukeyi d'aki guda d'aya gobara tacinye shi ,babu Wanda yasan ta,ina gobaran yake sauran kayan su ya kwone saura d'aki d'aya shid'in ma wutar ta,tab'ashi ,abun duk yabasu mamaki, suda ba wuta ne dasuba tayaya gobaran, yataahi Allah yarufa asiri..
Mutane dayawa sunzo musu gaisuwa da jaje"Inna meyasa masifa suketa bibiyan mune?yazan sani nima bansaniba abunne sai muce akwai wani abu" karkayi magana Sulaiman Garbati bayanan yatafi wani gari magani..
Duk mutumin da yakalli gidan su Sayyada sai ya tausaya musu"Inna kodai zamubar Anguwan nan ne "ina zamuje Sayayda..
" Sadiq kaida Ibrahim kunyi shiru "Allah yashiga cikin lamarin mu..
[25/05, 07:35] Maman Khairat: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸
GIDAN MARAYU
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🅿️7️⃣5️⃣⏭️7️⃣6️⃣
______________Garbati ne yashigo da gudu Sayyada ta,taroshi da kaya acikin bako "sannu da zuwa ya Garbati kaga yadda gidan mu yakama da wuta ..
" nagani Sayyada murmushi yayi "wato tanan suka biyo kenan ,suwaye ?kauda maganan yayi suka gaisa da Inna " Garbati naji kayi wani magana eh Inna "wannan wutan sawa ,akayi bana gaskiya bane dan tunjiya nagani a mafarki " wannan aikin su Haruna ne sakawa sukayi wani yamusu aikin amma babu komai yadda sukasa wuta haka nima zan mayar musu"Garbati kafayi mun Alkawari akan bazaka cutar da kowa ba? eh "Inna nifa inaso kisani " wannan abun dayake faruwa duk su Haruna ne sukesawa,sannan sune sanadin yin komai munyi musu na ruwa shine sukuma sukayi na wuta gidan zan kafe in wani munafiki yazo gidan nan wuta zaigani karfa kid'aga hankalinki dan Allah "bakomai Garbati na yadda " ga wannan zanin Wanda nayi mata aikin maganin k'afa ne tabani zani in kai a mamana gashi "ayya Garbati nagode Sosai niban haifekaba amma sanadin fara maganin ka yanzu na d'aura zani yayi biyar " Inna kece uwata kuma duk wani gata yimunshi kike kinga kuwa babu memun wannan gatan Sai uwa
"gashi na siyo mana kayan miya sannan dubu talatin sukabani ..
Nanuna yayi yawa amma sundage dan sunce sunsha wahala wajen neman magani "Allah yasa Albarka Amin ga dubu ashirin da biyar munemo me gyara yad'an gyara mana .
Kabar shi Garbati nakane kai kasha wahala akai bazamu k'arb'aba " wato Inna baki d'aukeni nida su,Sadiq d'aya mukeba kenan ?
"Duk d'aya kuke a wajena " bari munemo me gyara ko rufe nan ,ayi munyi magana da Sulaiman yacemun zai kawo me gyara "in yagama Sai ya sallame shi,
Sun nemo me gyara ya gyara wajen da,yacinye da wuta ogan Sulaiman ne yabada jalaf dinda za,ayi ginin dashi,sun gyara wajen yayi kyau ..
Alhaji Kyari yakawo zannuwa da shadda akan su,yi amfani da shi duk bayan kwana biyu zai kirasu yaji yasuke yakuma jikanshi Allah yajarabe shi dason Rukayya Gwoggo taki Amincewa da komawar su ,sabon gida taki, Amince wa, wani rana tace ta yadda sukoma babu komai " Gwoggo inaso kema mukoma tare dake kinga mukad'ai ne gidan yayi mana babba mukad'ai Rukayya kenan "kinga wannan gidan nawa yafimun ko,ina dad'i saboda da gumina na siyeshi" dan haka bazan bar gidan inje ko,ina ba, "mutafi sai kisaka haya a cikin nakin zaifi koya kikagani k'udin zai miki amfani Sosai " Rukayya kinfa nace dayawa zanduba in gani
GIDAN ALHAJI MUSA
Tunda ,aka dawo da Rashida kozuwa baiyi mataba ko, kof'ar gidan baijeba yana zaman shi "dan Allah yaukam kaje musu mana kayi kusan sati a nan ", Maryam ke haryanzu yarinya ce bazaki ganeba " duk da haka kiyi hakuri kibar zancen dan rashida munguwa ce ta,ajin farko "Akwai abunda rashida tayimun Wanda har nakoma ga Wanda ya halicce ni bazan tab'a mantawa da wannan abun ba " d'ana nafari ,matana Tana bacci da jariri lokacin ta haihu ankwanta da shi suna bacci ,aka nemi yaranta aka rasa washe gari uwarshi ta had'iyi zuciya ta mutu babu Wanda yak'ara tambayan yaron nan dagani har dangin mahaifiyar shi ,sai sai dayayi shekara sha takwas ,wani rana kaina yata ciwo na kama sai naji kaman wani Abu yafita daga kaina dana gayamata sai kuma ban k'arajin koda tinanin yaron ba bankuma gayawa kowa ba sai kwanan nan naji,irin abunda naji natafi gun wani babban malami shine yake gayamun Akwai wani babban Al,amari yaron yana raye yazama babban mutum Akwai d'an kamanni a tsakanin. Mu,sannan Asiri a,kayimun ajikin baru yanzuma yarane suka kama barun suka cire masa abunda ke wuyarshi shiyasa..
Toh kinji abunda rashida tayimun ,tun rashida tana amarya taso kar saude ta haihu saude itace uwar gida sai da mukayi shekara bakwai kafun na auri Rashida shine nake ta neman mafuta shiyasa "muci gaba da gayawa Allah in sha Allahu komai zai zama tarihi " nagode Maryam nayi farin ciki da haka kinbani shawara sannan zanyi magana ,a faruq mugani kodai in koma gidan wancen malamin "kafara zuwa gun Abba Faruq kozai nema muku mafita " gaskiya nagode sosai✍
Maman Khairat ce
[25/05, 07:35] Maman Khairat: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸
GIDAN MARAYU
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🅿️7️⃣7️⃣⏭️7️⃣8️⃣
GIDAN ABBA FARUQ
Kisake jikinki Rafi,atu banaso kinasa kanki cikin damuwa ki shayar da yaronki babu wani damuwa shi baisan komai ba "sannan kefa haihuwar taki,danasabar ki cikin gatakike wani ko hakan mabai samuba dan Allah kizama maijuriya kisake jikinki " kiduba Rukayya batada damuwa gashi mahaifinta ya karb'eta hannu biyu dan Allah kisake ranki karatu zaki koma Rukayya itama zata koma inaso kuyi karatun a waje d'aya zansa Alhaji Musa ya nemawa Maryam itama dan tanan nezaku kasance tare ..
******Ummi Aisha dakin taimakeni "babu komai Rukayya takirani tace tana zuwa Yau, ita da Maryam Allah yakawosu lafiya Amin kifitoh mushiga kitchen muhad'a musu abunda zasuci toh Ummi " kikawo shi parlour na ya kwanta yayi bacci ..
Sai kusan sha biyu sukazo tare suka shigo"sannun ku da zuwa yauwa Ummi ya aikin da godiya kushiga tana ciki "Rukayya ina Nura yafita wajen aiki ayya Maryam samun waje tayi tazauna," yanaganki cikin damuwa?
Kubari Akwai "Anty Rashida ne take damuna,zuwa tayi tazageni ,bari kuji tsaf,kiyi hakuri kema Allah zai had'aki da dangin ki"yaushe ne kenan?kwanna kusa lokacin da muka,tashi bamuyi zaton zamu samu,iyayen. muba kiduba yadda rayuwar tazomana,nawa tabon har biyu..
Abu na,biyu kuma inason in koma karatu ,,Rukayya nikam Babana yasamamuun,in kuna so kuhad'a ta kaddun Ku in bashi zaifi mungode dan Allah mukaranta abu d'aya,nikuma mukaranta abubuwa daban daban Wanda wataran d'ayan muzai taimakawa d'ayan mu, Rafi,atu yakika gani hakane amma nafison mu,karanta abu d'aya"sannan Babana yasiya mana gida da mota,sannan Gwoggon Nura ita kanwar Babanki Abba Faruq ne"da gaske bai gayamuku ba eh
Wato lamarin mu yanaban mamaki duk abun a cukurkud'e yake kibari Allah dai ya kyauta Amin ya rabbi
Wuni sukayi sunsha hira harda neman mafita daga k'arshe sunbada takaddun su Rukayya zatà tafi Ummi Aisha tayi musu nasiha dukansu
Tunda safe Garbati yaketa wani hade hade duk inna tana kallon shi cen yakece da dariya "Garbati mekakeyi ne kuma kake dariya? Babu ina had'a mana wani magunguna ne Wanda duk wani makiyin mu,bazai tab'a ganin gidan muba, zaiga dubu yaga wuta sannan Wanda sukayi sanadiyan Sawuta suma su d'an d'ana suji " Garbati banason mugunta "Inna kedai kiyi kallo sannan kunsan mutanan nan baduka dukiyar suka bayar ba sun boye karka damu mubarsu da Allah
Inna babu Wanda zaitab'aku yazauna lafiya tunda sosuke suga bayanku ,Sulaiman " Garbati kabarsu duniya ce zata koya musu hankali "Inna jiya malam Sulaiman yabamu kaya sannan yace in baki wannan zanin keda Sayyada gashi wannan yace muk'ara kud'in gyara,wahaye ne suka zubo" meyasa kike kuka?"zanyi kuka Allah yakarbe Janbo yabarmu Ku,dan kutaimakeni gashi ta dalilin Ku ,inata samun Alkairi"bakomai Inna "zan d'auki kayana guda in kai a maman Sadiya jiya tazo gaisheni hijabinta duk a yage sannan kuyi hakuri a cikin kudin in kai mata koda dubu biyar ne kozata siyi wani abu Sulaiman Allah yamuku Albarka Amin
Da safe dakanta Inna takai wa Maman Sadiya " nagode kune mutanen da kuka taimakeni tun lakacin da mukarasa gatan mu,Allah yabiyaku mungode"babu komai ai duk d'aya muke, kema kinyi mana rana,kafun mukai matsayin nan muga abubuwa kala kala yanzu yazama labari kema wataran zai zame muku labari Allah yasa Amin ya rabbi "danace gobe kozaki rakani muje muduba yaran nan a gidan marayun " babu komai Allah yakaimu Amin .
Rakiya tayi mata sukasha hira Sosai na rayuw Inna tabata shawara dayawa sannan ta,amince zatabi duk shawaran Allah ya kyauta Amin✍
Maman Khairat ce
[25/05, 07:35] Maman Khairat: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸
GIDAN MARAYU
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🅿️7️⃣9️⃣⏭️8️⃣0️⃣
GIDAN MARAYU
Maman sadiya da Inna "gun wakukazo