Showing 27001 words to 30000 words out of 224143 words
Chapter 10 - DAN MACE COMPLETED Romantic Book .txt
tuba."
"Baka ga komai ba Rafeek,me zai kaika saurin neman yafiya.? Mu laifin me ma kayi mana da zaka nemi gafarar mu,mu da muka yi laifi mu yafi kamata mu nemi yafiyarka saboda mun yanke hukunci ba tare da tunanin abunda gaba zata haifar ba,da ace tun farko mun tsaya munyi tunani da haka duk bata faru ba,amma tunda kai muka yiwa ba dai² ba kayi hak'uri ka gafarce mu,in sha Allah hakan ba zai sake faruwa ba."
Tana kaiwa nan ta sauko daga saman kujera tayi tsugune akan k'afafunta tana kallonsa tace "Muna fata zaka yafe mana laifukan da muka yi maka,muna sane da wanda ma bama sane."
Wani irin kunya ce ta dabaibayeshi ya kasa kwakwkwaran motsi a gurin bare yayi magana,Hajiya cikin fusata ta banka masa harara tace
"Da kai nake isashshe uban mutane,,idan ma banda rashin kunya irin taka Rafeek har kana da idon da zaka kallemu.? Bayan tarin kunyar daka samu ji yanzun ka d'auko jiki mu yafe maka.. Idan munce mun yafe sai kuma ayi yaya.?"
Shiru yayi bai yi magana ba,Hajiya taci gaba da fad'a son ranta ta inda ta shiga ba tanan take fita ba,Hauwa tunda ya shigo take jin gabanta na fad'uwa ta kalle su duka a hankali ta sunkuya ta d'auke y'an kayanta ta bar parlor'n,Hajiya ta bita da kallon tausayi bayan ta dawo da kanta kan Rafeek da yayi wani irin kicin² tace
"Sai ka wuce ai kaga yaron,ka kuma tabbatar ka bata hakur'in abubuwan da suka faru a bayan,yanzun kam kayi kad'an kace yaron nan ba jikinka bane.."
A karon farko ya d'ago yana kallon Hajiya data had'e girar sama dana k'asa yace
"Hajiya ni kuma me zai had'a ni da yaro.!?"
Yatsunta ta ware tana zaginsa tace "Zaka tashi kaje ko sai na sab'ar maka,kuji min futsararren yaro,to dan ubanka idan baka sani ba abunda kowa yake hangowa a fuskar yaron nake son ka gani da idanunka,,kuma bari ma kaji na sake fad'a maka kamar yadda kowa ya gani ya tabbatar yaron nan jininka ne yake gudu a jikinsa,kaf fad'in duniyar nan banga wanda za'a kira da ubansa bayan kai ba,tashi ka wuce ka bani guri,idan kak'i kuma salin alin maza wuce ka bar min gida.."
Ta karasa maganar tana nuna masa hanya,girgiza kai yayi cikin bayyanannen b'acin rai zai yi magana ta sake tarar numfashinsa
"Ka wuce nace ka gansu,ni ban b'ukaci jin komai daga bakinka ba.!"
Bisa dole ya tashi yabi bayan Hauwa cikin bin umarnin mahaifiyarsa,shi kam ba don plans d'insa na son raba Hauwa da gidan daya k'ullo da baya so yayi ruining d'insa da baiga abunda zaisa yaje ba,wannan shi ne dalilin da yayi masa jagoranci zuwa d'akin Hajiya inda yake tsammanin nan ta shiga,a saman bed d'in mahaifiyar tasa ya hango ta zaune ta zubawa guri d'aya ido ko k'iftawa bata yi,kana gefenta a kwance kana bacci cikin kwanciyar hankali,da ganinta kasan tana cikin tsananin damuwa but bata san wane ne ya kamata ta fito ta fad'awa ba,har ya k'araci kallonta bata sani ba,sai daya shigo cikin room d'in kafin ta farga ta san wane ne a kusa da ita,saurin mik'ewa tayi tsaye tana ja da baya like taga abun cutarwa kusa da ita,kad'an ya kalleta ya d'auke kansa a kanta,yaci gaba da takawa har ya k'arasa inda take tsaye kamar wacce ke jiran ace kyat ta zura a guje,ta ci gaba da matsawa tana saita entrance da zai kaita waje,still ya sake tab'e baki ba tare daya sake kallonta ba ya fara magana
"Me yasa kike da tsananin taurin kai ne.!? Bayan duk maganganun da muka yi dake a bayan,nayi tsammanin zuwa yanzun da kika tabbatarwa kanki nan d'in ba gidan mahaifinki bane zanzo na iske kin koma naku gidan... But sai naga ashe baki yi zuciya ba kina nan still.!"
A karon farko ta d'ago ta kalleshi bata ce masa komai ba ta d'auke kanta daga gare shi,harararta yayi yana tab'e baki
"Hakan yayi miki kyau,but kamar yadda kika ga na dawo a yanzun ina so ki sawa ranki lokacin barinki gidan nan ne yayi,cos ni banga amfanin zaman ki a k'ark'ashin inuwar mahaifana ba,ko muna da wata alak'a ne kuma bayan waccan ta baya.!?"
Sake d'aga kai tayi ta kalleshi suka had'a ido yana jifanta da mugun kallo,juyawa tayi tana kallon baby'nta da yake motsawa alamun yana son tashi,dakatawa shima Rafeek yayi da zancen da yake har sai da yaga yaron bai tashi ba sannan ya juya zai fice daga d'akin muryar Hauwa ta dakatar da shi
"Duk abunda kace naji but har yanzun maganar kawai kake yi babu evidence,,idan dan kana ganin bazan iya barin muku gida bane kake tunani ina so ka cire wannan a ranka,in sha Allah zan tafi cos ba'a binne kurwata a nan ba bare kace na zaune muku a gida.."
Wani irin juyowa yayi yana murmushi da gefen bakinsa ya tako ya dawo gabanta
"Kika ce mene ne.!? Ba'a binne ruhinki ba.? Idan ba shi d'in aka rufe a gidan mu ba zaman mene ne kika ci gaba da yi daga lokacin dana furta cewa na yanke alak'ar dake tsakanin mu.!? Why don't u leave us.!?"
Ya k'arashe yana zare ido da d'agawar sauti,murmushi tayi mai ciwo
"Wannan kuma ba ruwanka bane,zama na ko tafiyata duk basu shafi mutum ba.."
"Sun shafe ni,,cos nan gidan mu ne kuma gidan mahaifina na asali,me zai sa ke baza ki gwada komawa naki asalin ba.!?"
Kallonsa ta sake yi ya d'aga mata gira d'aya "Yeah I mean it.! Ki gwada mana.."
Sauke kai tayi k'asa bata ce komai ba sai dai taji k'irjinta ya fara zafi,Rafeek cikin wani irin murya yace
"I knew baza ki tab'a iyawa ba,wannan gidan naku dai mai kama da village's graveyard babu yadda za'ayi na yarda zaki iya komawa cikinsa.."
Yayi mata murmushi yana shafa sumar kansa,a d'an fusace ta kalleshi
"Kada ka sake ko da wasa ka zagarmin asali na,,gidan mu it's for us ni da y'an uwana da shi muke alfahari,haka kuma naku it's urs,so kowa ya zauna iya matsayinsa,ni bance ka zagarmin asali ba,kuma naga ai nan d'in da kake magana bani na zaunar da kaina ba.."
"Wane ne ya zaunar dake idan ba son duniya ba.? Gidanku a yanzun baza ki iya rayuwa cikinsa ba,saboda kinga duniya kin shiga inda yafi naku,me zai sa ki koma can ko ba haka bane.!?"
"Ba haka bane,amma idan amsar kake nema kana iya zuwa gurin mahaifiyarka ka tambaye ta dalilin da yasa na kasa tafiya,har yanzun nake zaune muku a gida.."
A fusace tana kaiwa nan ta juya tayi hanyar fita,da sauri ya rik'o hannunta,kamar wacce aka dannawa pause ta k'ame a gurin da mugun mamakinsa
"Baki isa ki fad'a min wannan maganar na bari ki fita ba,dake nake yi so ba ruwan Hajiya ta a ciki,tunda ke kika fara dole ke zaki k'arasa."
"Sake min hannu..!"
"Bazan saki ba sai kin fad'a min abunda nake son ji.."
"Rafeek ka sake min hannu..!"
"Bazan saki ba."
"Na ce ka saki." Ya maimaita "bazan saki ba" bai k'arasa fad'a ba tana juyowa ta wanke shi da lafiyayyen mari idanunta cike taf da hawayen k'unci but sai ta kasa furta ko 'A',shi kansa a bazata yaji marin ya sauka saman kyakykyawar fuskarsa cikin wani irin b'acin rai yana kallonta yace "ni kika mara.!?"
Bata d'ago ta kalle shi ba ta juya da sauri ta d'auki d'anta tasa a kafad'arta zata fice a d'akin yayi saurin sake tare ta
"Ni kika mara Hauwa."
Still bata d'ago ba zuwa lokacin hawaye sun fara sakko mata,cikin wani irin mutuwar zuciya dana gangar jiki tace
"Ka bani hanya na wuce.."
"Ki wuce zuwa ina.!?"
Bata tanka masa ba ta d'auke kai tana goge hawayenta,hak'oransa ya datse muryarsa a k'asa ya fara mata magana cikin kaushin murya
"Though banzo da niyyar zama k'asar nan ba,dole na ne a yanzun na rabaki da asali na kafin ki gurbatamin su,,ke idan banda kaddara mai zai had'o mu da ku.? Ki duba irin bambancin dake tsakaninmu mana,sam bamu yi deserve da juna ba,har yau ina tunanin dalilin da yasa iyayena suke sonki,and ban san mene ne Abba ya gano na musamman a tattare dake ba,,amma tunda Allah ya raba mu,kije can kiyi rayuwarki,sai dai ina sake jaddada miki mari na da kikai sai ya saki shiga masifar da baki tab'a tunanin zata same ki ba,,,and then matuk'ar baki yi niyyar komawa gidanku ba,ina tabbatar miki saina wulak'anta rayuwarki,wulak'anci irin wanda baki tab'a tunanin wani bil'adam zaiyi miki shi a tsayin rayuwarki ba.."
*#Yah Allah save dis innocent soul..😢 Rafeek ya k'ullo makirci..*
#Share.
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*
*'DAN MACE..*
(Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://my.w.tt/29u2S26SG2
Pᴀɢᴇ 9.
#Eᴠɪᴄᴛ
*Am back again.. Babu abunda yafi dad'i a duniya sama da samun masoyin gaskiya,,as u requested me to apologize to u my special friends,na yi hak'uri da yardar Allah,and if God please permits i'll continue sending u as usual,sai dai not really anywhere saboda wasu uzurori nawa,hope u people will help me in sharing,but by Allah's favor if such a problem arises again God knows the truth ba za ku sake jina ba,sai dai for those of us who are on the Wattpad software,then daga lokacin kuma i'll be out of any group,ku sani when ever i leave the group there's no coming back..Chanjin da kuka fad'a daga yanzun ya kamata na fara ganinsa if i don't see any changes kuma i will fill my trouser with air..🏃*
💕
Yana gama fad'a ya barta nan tsaye cikin halin damuwa da fargabar maganganunsa,a zahirin gaskiya tunda ya fita ya barta ita kanta ta fara tunanin komawa gida,to amma wace hanya zata bi ta sanar da su Hajiyarsa abunda ke damunta ba tare da sunyi saurin gano dalilin zuwan Rafeek ne take son tafiya ba.? Har ga Allah maganganunsa sun duki zuciyarta shi yasa tun da wuri ta fara tunanin tafiya ba tare data bari wani ya fahimci nufinta ba,but idan ta tuna Hajiya kuma sai tace "To ni yaya zanyi ne na bar gidan nan bata sani ba.?" Ko kuma "Anya idan na tafi babanmu zai kyaleni na zauna tare da su.?" Irin wad'annan tunanukan da tambayoyin sune suka fi damun zuciyarta,a gefe guda kuma tunanin kalamansa bayan muguwar damuwar da take tare da ita kafin lokacin,cikin y'an kwanaki da zuwan Rafeek gidan,a hankali al'amura suka fara sauyawa idan yana gida gaba d'aya Hauwa bata da sukuni,tun Hajiya na yi mata fad'an ta daina sa damuwa a ranta tayi hak'uri da duk abunda ya faru har ta hak'ura ta kyaleta,a b'angaren Rafeek tunda ya fahimci idan yana guri bata da sakewa sai ya maida zaman gidan kamar ibada,idan ya fita baya jimawa yake dawowa,yayin da a gefe guda b'angarensa da mahaifansa babu wanda ya san yaya suka k'are ta da su tun bayan d'an fushin da suka yi na kwanaki,lokaci guda aka wayi gari aka ga sun gyaro alak'arsu har zaman hira suke,su yi wasa da dariya abunsu kamar da,wannan dalilin yasa damuwar da Hauwa take ciki ta sake yin yawa gashi babu mai d'an shiga gurinta yanzun ya d'auke mata kewa.
Satin Rafeek biyu da zuwa gidan al'amura marasa dad'i suka ci gaba da faruwa tsakaninsa da Hauwa,a gefen iyayensa kullum cikin rufe su yake da kyawawan halayensa yana nuna musu shi d'in na gari ne kamar yadda suka sanshi kuma suke so ya kasance,ko wane lokaci yana kan kyautata musu da faranta musu sab'anin idan sun had'o hanya da Hauwa cin mutunci da muzgunawa had'e da kausassun kalamai ke raba su,a cikin hakan ba tare da sanin kowa ba ko neman shawara cikin irin rufin asirin da Allah yayi masa yayi musu Visa zuwa Saudi Arabia suyi umrah a ransa ya k'udurce daga wannan tafiyar baza su sake dawowa Nigeria ba,tafiyar duka cikin sati guda aka tsara yinta,da yake aikin kud'i ne nan da nan aka yi komai aka gama,tunda maganar tafiyar sun ta bayyana a ranar lokacin ana ta sallama da su,kafin su wuce airport Hajiya ta had'a su duka tayi musu nasiha mai ratsa zuciya,jikinsu yayi sanyi musamman Hauwa da kana kallonta zaka san tana tattare da damuwa,irin wacce da za'a tambayeta tabbas zata ce Hajiya ta fasa zuwa,aka gama sallama da su driver ya wuce da su airport,gida ya dawo daga Hauwa sai Maimunatu,Rafeek da maidservant d'insu sai mai gadi dake can bakin get,,a wannan ranar tun daya kasance babu iyayen Rafeek a k'asar,hankalinsa kwance da dare bayan an idar da sallar isha'a ya shigo gidan ya wuce su a parlor yana murmusawa,Hauwa da ta bishi da kallo haka nan take jin zuciyarta na fad'a mata lallai akwai wani bak'on alamari da zai faru da ita,lokacin bacci ya yi Maimunatu tayi mata sallama ta wuce,har suka shiga d'akin Maimunatu bata sani ba sai data juya zata rufe k'ofa taga Hauwa biye da ita,a tsorace ta bita da wani irin kallon mamaki
"Baki kwanta ba dama.?' Ta tambaya soundly muryarta da alamun tsoro,da kai Hauwa ta amsa mata ta wuce tana niyyar kwanciya a saman gado,Maimunatu tayi saurin matsowa kusa da ita tace
"Me za kiyi min a d'aki kuma yau.? Ke da kika ce d'akin mijinki,daga bayan kuma kika ce kin samu wanda ya fishi,nan ai bai wuce a kirasa kitchen ba,ke da kike da d'akunan bacci da yawa me kuma zai kawo ki nan.?"
Bata tanka ta ba sai da ta kwanta sannan tace
"Nan nayi ra'ayin kwanciya yau,idanma za kiyi shiru to,idan ba zaki iya ba kuma ci gaba,dare dai yayi kuma kin san Hajiya basa nan,idan kika damu masu gidan sa daka ki.. Ni babu ruwana y'ar kallo ce."
Murmushi Maimunatu tayi tace "Allah sawak'e wani ya dake ni yanzun,,ko Abba da Hajiya ta sun ce na girma,bare wani can a gefe yace zai dake ni.. Tabb'.!"
"Kada ki cika baki Hajiya,gara miki kija bakinki ki b'ame ki kwanta kawai,idan ba haka ba..!"
Sai tayi shiru tana sauke numfashi jin ana tab'a handle d'in k'ofa,a tare suka juya suka kallo gurin Maimunatu ta matsa jikin k'ofar da nufin bud'ewa,Rafeek ta gani tsaye sanye cikin pyjamas d'insa masu matuk'ar kyau,rigar sleeveless sai wando 3quarter farare tas da su,musanyan murmushi suka yi ga juna da d'an mamaki a saman fuskarta tace
"Yah Rafeek did u come to check munyi bacci ko wani abu kake so.!?"
Murmushi ya sake yi yana gyad'a mata kai alamun A'a ga maganarta ta k'arshen,a hankali ta sake yin murmushi tace
"Thank God.! Bayan tafiyar su Hajiya kana kusa da mu,i knew har su dawo babu abunda zai faru damu."
Yana gyad'a kai yace "Sure.!" Sai ya juya da nufin komawa yana fad'in "Good night dear" murmushi tayi tace "Allah tashe mu lafiya",yana tafiya ya amsa mata had'e da sakin wani killer smile,,Hauwa dake k'arshen bed tana sauraren dialogue d'insu kasa fahimtarsa tayi saboda yadda yayi furucin ya nuna kamar akwai abunda yake nufi kuma ba abunda ya kawo shi ba kenan,amma kuma sai ta share bata zurfafa tunaninta akai ba tayi kwanciyarta ta lullub'e jikinta cos tana da nata personal damuwar,dawowar Maimunatu kusa da ita tana kallonta da mamaki tace
"Wai ina kika baro min Yarona ne.? Kinzo kin kwanta min a nan,ya za'ayi na ganki ke kad'ai ne,ina yake.?"
Cikin muryar bacci tace "Yana gurin big sister."
"Ohh! Can zai kwana yau.?"
Tace "Ehh!" Ba tare data d'ago ba,daga haka itama Maimunatu bata sake magana ba ta nemi guri ta kwanta,,a b'angaren Rafeek lokacin da suka yi sallama da Maimunatu kasa tafiya yayi sai daya tabbatar Hauwa tana cikin d'akin sannan ya bar wajen yana sakin wani irin murmushi,tun daga ranar data fara gano nufinsa ta koma kwana a d'akin Maimunatun bcos tana tsoron ta kwanta ita kad'ai wani abu ya faru,kuma tun daga ranar bata sake barinka ka kwana cikin gidan ba,gudun kada idan Rafeek ya kasa samun dama akanta ya dawo kanka tunda yayi furucin kai ba d'ansa bane.
Kwanakin su Hajiya goma da barin k'asar duk wani muguntar daya shirya mata ya fara fito da shi fili,bamu san yaya aka yi ba lokaci guda muka ji gari duka ya d'auki maganar Yaron da Hauwa ta haifa Rafeek yace ba d'ansa bane,duk wata hanya kuma da yasan zata ji babu dad'i yabi ya tozarta ta,hatta maganar rabuwarsu tun kafin ta haifi yaron sai daya tabbatar ya watsata bayan ya nad'e ta da sharri,mutane masu jiran kad'an suka fara zaginta da aibanta ta suna Allah wadai da rayuwarta,a dai² wannan lokacin kuma again sai ga sharrin da y'an gidanmu suka yi mata tun na kafin aurenta da Rafeek d'in ya sake tasowa,mutanen dake mata kallon ta gari suka koma fad'in abunda suka so
"Tabbas biri yayi kama da mutum.. Zata aikata tunda har uban daya kawo ta duniyar ma yayi k'ok'arin bada ta sadaka.. Shi illar mutum mai shiru² kenan mak'etaci ne.. Kaji tsoron mutumin da ya cika nunk'ufirci munafikin kansa ne,ba'a jin cikinsa sai al'amari ya kwab'e.."
Sharri iri² daga bakunan mutane babu wanda ba'a yi mata ba,hatta Babanmu jin irin maganganun da ake ta yad'awa a gari