Showing 36001 words to 39000 words out of 224143 words

Chapter 13 - DAN MACE COMPLETED Romantic Book .txt

wannan shi ne zuwanta na k'arshe,but ta gwammace zuwan da ace ciwo ya yi ajalinta ita kad'ai a gurin da babu wani cikin ahalinta,cikin y'an watannin ta yi wani irin ramewa ta yi duhu kamar ba ita ba,duk wanda ya santa idan ya ganta a wannan tak'aitaccen lokacin na tabbata zai yi wahala lokaci d'aya yayi saurin ganeta,ta kamo hanyar K'ofar Na'isa a karo na biyu cike da fargaba,but data tashi zuwa wannan lokacin sai bata yi k'ok'arin shiga gida ba ko nema na,ta sake aiko min wasik'a,ina zaune cikin d'aki jigum sak'on ta ya riske ni,na karanta naga fiye da rabin maganarta akan na nema mata yafiya ne a gurin Baba,sai sauran mutanen da nasan wani mu'amala ya tab'a had'a su,ina kuka ina karamtawa har na zo inda take barmin wasiyya tana sanar min ta jima ba ta da lafiya na taimaketa na nema mata alfarma gurin Baba na zo na ganta ko da sau d'aya ne kafin ta Allah ta kasance mata,a wannan wasik'ar nayi gamo da tsananin tashin hankalin da ya wuce tunani na
_"Kiyi hak'uri y'ar uwata.! Babu yadda zanyi,ya zame min wajibi na sanar miki,duk da na san kema ba laifinki bane da kika kasa zuwa inda muke,,a halin da nake ciki,bayan dawiwa ta ciwo ya ci k'arfina,ina jin kamar ba zan rayu ba,idan haka ya kasance ina rok'on za ki nema min alfarma a gurin Baba,idan ya barki ko da a shek'ara sau d'aya ne zan yi alfahari da hakan,kema ina fatan za ki je ki duba min yarona,ban san yadda rayuwa ta zata kasance ba,shi yasa na yanke shawaran sanar da ke tun yanzun,zan kai Nuraz orphanage,idan kin samu dama dan Allah Yaya ina rok'on ki kije ki ganshi,na san Yarona ba zai yi maraici ba idan kina raye,na san yana da wata mahaifiyar kamar ki kuma za ki kula da shi fiye da yadda zanyi masa,ni dai tawa ta zo k'arshe sai dai ina yi mana fatan mu kasance tare har a aljannah,idan na yi miki wani laifi ina neman afuwar tun daga yarinta har zuwa girma na,ki yafe min y'ar uwata... Allah ya k'addara saduwarmu.. BISSALAAM.!"_
Daga k'anwar ki mai k'aunar k'i har abada *HAUWA BABA MUHAMMAD...*
Tsananin firgici da tsoro na shiga lokacin dana gama karanta sak'on ta,ba tare da na jira neman izinin fita a gurin Baba ba na fito daga gida kamar zararriya nabi hanya ko zan ganta,ina tafiya ina tambayar mutanen unguwa ko sun ganta.!? Sai ace min yanzun babu jimawa ta wuce,da sauri nake wucewa na bar wajen na yi gaba,ina tafe ina sake tambaya,amma abun takaici har na fito titi na gama dubawa ko mai kama da ita ban samu ba,na koma gida cikin firgici na tarar Baba ya dawo,ina kuka na sake zuwa gurinsa da wasik'a ko zai tausaya min ya bari naje,still Baba ya sawa idanunsa toka kamar waccan ranar,ya nuna min sam baya ko son yin maganar,dana takura akan ya barni naje yace idan na sake na fita bada izinin sa ba Allah ya isa bai yafe min ba.
Tsoro da tashin hankali suka sake shigata,rashin sanin matsayin Allah ya isa da Baba yayi min,da tsoron halin da y'ar uwata take ciki suka sa na kasa ko magana,ina ji ina gani ga address d'in inda take amma zuwa na dubata ya gagare ni,ban san mene ne zai faru ba idan na fita ba da izininsa Bana ba,sannan mene ne makomata idan na sab'awa umarninsa,,sati guda da zuwanta kullum da ciwon kai nake yini saboda damuwa ga yawan mafarkai da nake yi marasa dad'i,zuciyata kullum cikin yi min khud'ubar naje na duba ku take,na daure na ci gaba da zama ina jiran tsammani,,a cikin satin wani abu daya faru ya sake sawa jiki na yayi sanyi,ko wane lokaci na kwanta bacci da rana ko dare mafarkin Hauwa nake yi,a ko wane lokaci da zan ganta tana kuka tana sake rok'ona kada na manta da kai na kula mata da kai,,kwana biyu tsakani na sake yin mafarki da Innarmu,tun bayan rasuwarta da nayi ta mafarkai da ita,na jima sosai ban sake ganinta ba,ranar na kwanta bacci kenan tazo min cikin wani irin fuska mai ban tsoro,ina murna na nufi inda take zaune da niyyar na rik'e ta sai na ga ta yi tafiyarta,na dunga binta ina rok'on ta tsaya amma bata sake waiwayowa ba,sai dana gaji na fad'i a k'asa,ina kuka ina kiranta da rok'on ta tsaya,sannan naga ta juyo tana kallona tana kuka,hankali na a tashe nace "Inna mene ne ya saki kuka.??" Bud'ar bakinta tace "Ban san haka za kuyi min ba Maryam.. Ke da mahaifinki kun tozarta ni,kun wulakanta ni.. Laifin me nayi muku haka.!?"


Nace "Inna laifin me muka yi miki ne.!? Ban gane abunda kike magana ba.!"

Ta share hawaye tace "Saboda kunga bana raye kuka wulakanta min y'ata.! Me yasa sai da kuka bari na tafi sannan za ku wofantar da ita.!?"
Ina kuka ina bawa Inna hak'uri,bata saurare ni ba ta juya ta ci gaba da tafiya tana cewa "Idan har baki nemi inda y'ar uwarki take kin zauna tare da ita ba,kada ki sake kira na mahaifiyarki,ni ba mahaifiyarki bace,a kullum ina jin bak'in ciki na haifi y'a irin ki.."


Nace "Inna ki yi hak'uri dan Allah,nima fa duka ba laifi na bane,ki yarda dani,babanmu ya hana ni zuwa na dubasu."
Ta juyo ta kalle ni tana goge hawaye tace "Shi kenan,tunda kin yarda ya raba muku zumunci ki zauna tare da mahaifinki,in sha Allah ubangijin daya hallice mu ba zai tab'a barin Hauwa'u tayi maraici ba.. Daga yau ba zaki sake gani na ba,ki je ki zauna da mahaifinki.."
Tana gama fad'ar haka ta juya da sauri,ina kuka ina kiranta amma bata sake waiwayowa ba,jan jiki naci gaba da yi ina son bin hanyar da ta bi,saboda lokacin dana fad'i na ji ciwo sosai a k'afata,na kasa tashi na bita ina nan kwance ina kuka da kiranta har ta b'acewa ganina,cikin k'araji na kwalla kiran Inna,,a firgice na tashi ina dube²,na bud'e ido naga y'an uwanmu mata zagaye da ni sai kallona suke yi suna jiran su ji abunda ya faru na ke zabgaga ihu a farkon dare,na daure na juya ban yiwa kowa magana ba duk tarin tambayoyin da suke min,da suka ga ba ni da niyyar amsa musu kowacce ta juya ta kwanta,,a wannan daren ni dai ban samu damar komawa bacci ba har gari ya waye.
Misalin k'arfe 10am lokacin babanmu ya fita na shirya cikin damuwa,ba tare da sanin kowa ba na d'auki takardata na fita daga gida,na samu mai napep na fad'a masa inda zai kaini,yace na shiga ya san gurin,na shiga muka d'auki hanya,mintuna kusan talatin suka d'auke mu saboda baya wani sauri sosai muka k'araso,ya tsaya a dai² block d'in dana fad'a masa,ina ta tunanin halin da zan tarar da ita yace min "Hajiya mun k'araso."
Na kalli gurin da muke nace "Ka tabbata nan ne kuwa.!?"
Yace "Hajiya ai number za ki duba,ke kika fad'a min fa,ga gidan nan ki sake dubawa mana"
Na kalli house number sosai na duba ta jikin takarda,na ga iri d'aya ce babu bambanci,na sake kallon tsarin gidan na tabbatar nan ne inda ta rubuta,na sauka na biya mai napep kud'insa sannan na juya na kalli gidan,zuciyata har lokacin cike taf da tunanin anya nan d'in ne.!? Ina wannan tunanin na tunkari get d'in gidan,na yi shahada nayi knocking ina tunanin ganin ta inda Hauwa zata b'illo amma sai naji shiru,har kusan mintuna goma ban ji motsin kowa ba bare na ga mutum,nayi tunanin sake kwankwasawa amma wannan karon sai na tab'a entrance d'in,abun mamaki ashe k'ofar a bud'e take duk tsaiwar da nake yi,da mamaki sosai akan fuskata na kalli unguwar da nake jinta shiru sannan na wuce ciki na fara tafiya ina yi ina kallon ikon Allah da mamakin yadda aka yi Rafeek yayi mata kyautar gida kamar wannan,har na k'araso varenda da zata sada ni da parlor,na tsaya ina jin fargaba,a zuciyata ina addu'ar Allah yasa lafiya,na daure nayi knocking door d'in kusan mintuna uku shiru babu wani amsan da na samu,na sake yin knocking abun mamakin babu alamun mutum yana rayuwa a cikin gidan,gabana ya fad'i dana tuno kalamanta na ji hawaye suna k'ok'arin wanke min fuska,na nemi guri na zauna na ci gaba da addu'ar Allah yasa ba mutuwa Hauwa tayi ta barni ba,after 2 hours na goge hawaye idanuna duk sun kumbura,na mik'e da niyyar tafiya jikina duk yayi sanyi,na sakko daga saman varenda na kama hanyar get zan bar gidan,ina tafiya ina waiwaye,na yi nisa cikin hukuncin ubangiji na jiyo kamar sautin tari,da sauri na tsaya ina kalle² da tunanin ta ina sautin yake fitowa,amma kuma sai na rasa ina ne,na dawo da sauri na fara bin windows d'in da suke zagaye da gidan,duk window da na nufa sai na tarar da ita a rufe,idan na lek'a bana iya ganin komai saboda curtains dake zagaye da su duka masu duhu ne,nayi ta zagayawa kasancewar ginin gidan detached house ne da baiyi joining ko wane wall ba,irin ginin nan dai kawai da ake yinsa a tsakiya,na kusa gama zagaye gidan ina neman hanyar da zan shiga,dai² lokacin dana gama fitar da tsammani da samun mafita ubangiji ya taimake ni ya ji k'aina.
Window ne guda d'aya daga can edge na k'arshe na gidan a bud'e,har ina had'awa da gudu na k'arasa jikinsa na tsaya ina addu'ar Allah yasa abunda zuciyata take sanar da ni ya kasance gaskiya,sai dana gama addu'o'i na sannan nayi k'arfin hali na kai hannuna jikin windowpanes d'in ina k'ok'arin bud'ewa,kasancewar da yawa windows dana bari a baya na yi gwada bud'ewa ban samu dama ba,sai wannan da alamu suka nuna a bud'e take,ina janyowa ta bud'e na runtse idanuna cikin fargaba,curtains d'in da suka rufe ba'a ganin komai nasa hannu ina k'ok'arin bud'ewa duka,a nan idanuna suka yi bak'in gani.....




#Share pls.
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*


*'DAN MACE..*
(Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥



*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://my.w.tt/29u2S26SG2


*Wah! 😍 U people are killing me with ur warmth comments,thank u so very much,thank u all my friends..Bahot² shukhurya..*♥


Pᴀɢᴇ 12.
#Iɴꜱᴀɴɪᴛʏ

Akan Hauwa idanuna suka fara sauka,kwance take amma cikin wani irin yanayi mai ban tsoro da firgitarwa,na koma baya da sauri cikin tsananin tashin hankali har ban san lokacin da na fasa k'ara ba,ta juyo ta kalli inda taji ihun bata ga kowa ba,ta juyar da kanta babu damuwar komai a ranta,nayi kuka sosai har sai da naji na sire bana iya sake yin hawaye,guiwoyina sun yi sanyi bayan na bawa zuciyata hak'uri na sake matsawa jikin window ina ta kallonta a hankali cikin muryar mai kashe jiki na kira sunan ta "Hauwa'u.!"
Ta juyo da sauri ta kallo inda nake,a hankali ta k'uramin ido kamar mai son tuna wace ce ni,na daure duk da hawayen da suke bin fuskata nace "Me ya same ki kika dawo haka.!?"


Ta yi shiru ta ci gaba da kallo na ba tare da ta ce komai ba,ina kuka nace "zo maza ki bud'e min k'ofa,ni ce y'ar uwar ki,ban san haka rayuwarki zata dawo ba,ki gafarce ni y'ar uwata,da na san haka al'amarin nan zai kasance tabbas ba zan tab'a bari kiyi nisa da ni ba,sai dai duk abunda zai faru ya faru,ki yimin afuwa k'anwata,ba a son raina haka ta faru ba.."
Still bata motsa daga inda take ba,ta yi shiru dai ta zuba min idanunta,duk abunda nake fad'a tana saurare na,sai dai alamu sun gwada gaba d'aya bata fahimtar abunda nake cewa,nayi magana nayi begging d'inta amma kusan duka a banza babu wanda ta ji,bare ta aikata.
Yinin ranar ya kasance a nan na yi shi ina yawo tsakanin harabar gidan da window d'in d'akin da take,har dare ya fara gabatowa ban samu damar shiga cikin gidan ba,wajen misalin k'arfe goma saura mintuna na sake komawa inda take,har lokacin tana nan kamar yadda na barta,na tsaya ina kallonta da tausayawa nace "Hauwa.!"
Jin magana yasa tayi sauri ta waiwayo tana kallona,na daure nace "Zanje gida na tattaro kayana,in sha Allah ina nan dawowa ba da jimawa ba kin ji.!?"
Kamar ta fahimci abunda nake nufi ta juyar da kanta ta k'urawa guri d'aya ido,cikin yanayin sanyin jiki na janyo k'afafuna na fito,ta waje na samu cable na d'aure get d'in sannan na kama hanya ina tafe ina gabana sai fad'uwa yake,a haka na fara neman abun hawa,da kyar lokacin 11pm saura mintuna 15 na samu napep,na fad'a masa inda zai kai ni,yace na hau mu tafi,na shiga muka fara tafiya,Allah ya taimake ni na samu irin masu napep d'in zamani,gudun da muka yi a lokacin ni na san ba kadan bane,11:00pm muka tsaya a k'ofar gidanmu,na sauka na sallami mai napep,na wuce cikin gida gabana yana ci gaba da fad'uwa,saboda ban san me zan tarar ba.


***
Abunda ya faru gidan mu kuwa a yinin ranar,bayan fita ta daga gida,ban san wane ne ya fad'awa Baba na fita ba,ya saba baya dawowa da wuri amma ranar after Maghreb Baba ya dawo ya fara jkran yaga ta inda zan b'illo,har 11:00pm saura mintuna bai ganni ba bai kuma samu labarin inda na mak'ale ba,dai² lokacin da agogo ya nuna 11pm Baba ya kira babban yayanmu Abdullahi yace yaje ya rufe masa k'ofar gidansa,yayanmu ya taho da niyyar rufe k'ofa kamar yadda Baba yayi masa umarni muka gamu a zaure,ya kalleni ya wuce ba tare da yace min komai ba,na wuce cikin mutuwar jiki saboda irin kallon da naga yayanmu yayi min na k'araso tsakar gida,nayi sallama babu wanda ya amsa,na kallesu d'aya bayan d'aya naga ni suke kallo,nayi ajiyar zuciya ina k'ok'arin wucewa suka fara gulma a tsakaninsu suna tambayar juna "Ko daga ina take da wannan talatainin daren.." rashin samun amsa yasa kowacce taja bakinta ta tsuke.


Kai tsaye hanyar d'akin kwananmu na nufa,ina tafiya ina sake tunanin halin da na bar y'ar uwata,na kusa da k'ofar d'aki na jiyo muryar Baba yana daka min tsawa
"Kece.! Maryam ina za ki shiga.!?" Na juya a tsorace na kalleshi jikina sai b'ari yake nace "Baba d'aki zan shiga."
Ya kalle ni sosai yace "Wane d'akin.!?" Nayi shiru na sunkuyar da kaina a k'asa,ya girgiza kai "Ko da wasa kada ki kuskura ki shiga ciki,idan baki jiba kina iya gwadawa,zan nuna miki ni ne na haifeki.."
Nayi shiru ban d'ago ba,zuciyata ta cika da tsoron shi kenan mai afkuwa ta faru,ina nan tsaye Baba ya kalli babban yayanmu "Abdullahi.!" Ya amsa,yace "Maza shiga d'akin can duk abunda kasan na ta ne ka watso min su nan" yayi masa nuni da tsakar gida,ya sake amsawa ya wuce,ina tsaye ina kallon y'an gidanmu gaba d'aya duk wad'anda suke gida suna nan idan aka cire mata na sama da ni da suke gidan aurensu,mutum goma sha uku suna tsaye suna kallon abunda yake faruwa,haka matar Baban namu itama tana tsaye,har Yayanmu ya gama watsar min da kayana ban iya nayi kwakwaran motsi ba,na sunkuya na tattara kayana ina jin zuciyata kamar za ta fashe da tsananin bak'in ciki,ina gamawa Baba ya fito daga d'akinsa ya kallesu duka ya girgiza kai,muryarsa cike da tsoratarwa "Wannan ita ce makomar duk wanda ya ji ba zai iya yi min biyayya ba,a matsayina na mahaifinku ni kad'ai ne gatan ku,shin ina iyayenki suke.!? Duk da suka watsar da ku akwai wanda uwarsa ta tab'a zuwa da sunan ta zo duba shi.!? Ni nake wahala da ku,bai zama dole ku bini ba.!?"
Babu wanda ya iya amsawa,yace "Idan kunji ba zaku iya ba,kuna da zab'in ku tafi kuyi rayuwarku yadda kuka so,,sai dai ku sani daga ranar da muka rabu mun rabu kenan,har abada zan kasance a matsayin ba mahaifinku ba.. Sauran shawara ta rage ga mai hankali."
Jikin kowa yayi sanyi,Baba ya juyo gare ni ya kalle ni "Maryam! Tun da har kin kasance bakya jin magana,ga hanya nan na baki kina da damar kiyi duk abunda kika ga yayi miki kyau,kamar yadda na jima ina tunatar da ke,duk ranar da Allah yasa na ji labarin kin je gurin y'ar uwarki za mu rabu,amma sai baki ji magana ta ba,,shi kenan tunda kin zab'e ta,ki je Allah ya bamu alkhairi.. Dan na cire ku a cikin zuri'ata ba wani abu ne da zai d'aga min hankali ba,Allah ya so ina da wasu y'ay'an.. Ba zan yi bak'in ciki ba,kuma dai Allah ya gani na tsaya akan tarbiyyar ku har na aurar da ku,tsakanin ni da ku idan akwai wanda ya zalunci wani ubangiji ya saka masa.."
Yana fad'a ya wuce d'akinsa yana barwa Yayanmu sak'on "idan ta fita ka rufe min k'ofar gidana.." Duk y'an gidanmu sun yi cirko² kamar zakarun k'auye kowa si bina yake da kallo,nayi godiya ga Allah da irin k'addarar daya zab'a mana,sannan na d'auki jakar kayana nayi sallama da y'an gidanmu,dan na san ba lallai ne ko a hanya mu sake gamuwa ba..


Ba tare da na samu tausaya daga mahaifina ba,duk da kasancewarsa shi ne wanda yayi silar zuwa na duniya,y'an gidanmu ma kuma tun da Baba yace na bar masa gidansa babu wanda yayi ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login