Showing 39001 words to 42000 words out of 224143 words
Chapter 14 - DAN MACE COMPLETED Romantic Book .txt
da tari bare su iya bashi hak'uri ya barni na kwana zuwa da safe,,a cikin wannan daren na sake barin unguwar duk da kasancewata y'a mace na kama hanyar Sardauna crescent,na sauka a k'ofar gidan around 12am har da mintuna na bawa mai napep kud'insa na bud'e get na shiga na kulle,na k'araso bakin entrance nayi knocking,still tak'i zuwa ta bud'e,,na yi magana nayi bagging d'inta amma bata yi niyyar zuwa ta bud'e ba,na yi shimfid'a na zauna ina tunanin rayuwa a haka muka ga wayewar gari,da safe ma still na koma nayi magana amma bata kula ba bare ta bud'e,na tafi orphanage da ta fad'a min zata kaika da niyyar na karb'o ka,zuciyata da tunanin hakan zai sa idan Allah ya taimake ni ta ganka ta yarda abunda na fad'a mata gaskiya ne,,na sha wahala sosai a wannan yinin ranar kafin hukumar gidan marayun su yarda su bani kai,muka dawo gida na koma ta can baya wajen window da nufin yi mata magana ina rik'e da kai kana bacci,har lokacin tana zaune inda na barta,nayi ta rok'onta har dare shiru,na hak'ura nace "shi kenan za mu jira duk tsayin lokaci,muna nan tare dake ba zamu barki ba,kinga yaronki ma na karb'o miki shi.."
Daga haka ban sake magana ba na koma inda nayi shimfid'a na zauna ina ci gaba da tunani,ban san me ya faruba dana barta a d'aki ba,bayan wani lokaci tazo ta bud'e k'ofar tana lek'owa,na d'aga kaina muka kalli juna da ita,jikina a sanyaye nayi murmushi nace "kin gani ko,bamu tafi ba muna nan muna ta jira mu zo gurinki."
Bata yi murmushi ba sai gesturing fuskarta da take yawan yi kamar wacce ke jin wani abu na mata yawo a jiki,kusan mintuna uku muna kallon-kallo ta koma ta bar k'ofar a bud'e,na tattara y'an kayana na bita a baya ina rik'e da kai a hannu d'aya d'ayan muka kayanmu,,,zuwa na gidan na iske abubuwa da dama,wasu masu dad'i wasu kishiyarsa sai dai mafi yawa daga ciki sune marasa dad'in,rashin lafiyar Hauwa ba k'aramin gigita min tunani yaso yi ba,a wannan hali rashin fahimta daya shafi tunaninta,muka yi ta yawon zuwa hospital,daga karshe muka samu wani likita ya bani shawaran mu gwada zuwa psychiatry,saboda duk binciken da likitoci suka yi sun tabbatar kwakwalwarta ce ta fara tab'uwa,tun daga ranar da likitan nan ya fad'a min hakan bamu sake komawa ko wane irin hospital ba sai psychiatry,munyi yawo akan neman lafiyarta har ban san adadi ba,a nan Kano munje² har ban san adadin yawon mu ba,muka shafe tsayin shekaru biyar muna yawo tsakanin *DAWANAU* da gida,sai dai kullum muna nan tsaye guri guda tana dai under medication ne,naga lamari babu ci gaba na tattaro ta muka dawo gida,sati uku da fitowarta daga dawanau muka nufi birnin ikko (lagos),can d'inma dai yawon muka yi ta fama da shi,ita sun rik'eta a asylum mu kuma muka kama haya,a can ne saboda kasancewar baka gama primary ba na samu damar mayar da kai shool,har ka gama makarantar primary ka tafi secondary muna zaune a can,bamu da kowa a garin ni nake kaika makaranta ni nake d'auko ka,idan na dawo na ji da aikin gida da zuwa duba ta,har zuwa lokacin da kayi wayo kana iya zuwa da kanka ka dawo,,a takaice dai muka sake shafe tsayin shekaru sha biyu a Lagos gurin neman magani ba tare da samun nasara ba,,nasarar da zan iya cewa mun samu a wannan fannin duk abunda yake faruwa da ita bata duka,but idan abun ya haura mata za kaga tana yi kamar zata fita aguje tana surutai,bayan wannan babu wani abu makamancinsa sai dai ko shirun data koma yi daga baya,idan ka yi o magana baza ta amsa ba,haka ma surutai ta daina yi,,daga lagos al'amari yak'i a lokacin ka kammala secondary school muka sake dawowa Kano,dawowarmu babu jimawa idan baka manta ba shi ne farkon lokacin dana nema maka admission a U.K a jami'ar Oxford,after then na sake neman kasuwancin da zai rik'e mu na fara saboda dukiya idan ba'a juya ta tabbas wata rana dole ta k'are,bare mu da muka d'auki shekaru muna yawo,,mun shekara uku ina yawon kasuwanci komai dana san ana amfanin yau da kullum ina siyarwa,Alhamdulillah ubangiji shi ne komai,ya sawa mutane son kayan da muke kasuwancin su,Allah cikin ikonsa ya sake dafa mana kasuwanci ya karb'u,a da mu muke siyarwa cikin k'ank'anin lokaci ya juya al'amarin ya zama mun koma wholesaling sai dai mu shigo da kaya mu raba su ga retail's,Alhamdullah ba zan gaji da fad'a ba a tsakanin shekaru bakwai da dawowarmu kasuwancin mu ya tsaya da k'afafunsa mun samu wadata fiye da baya,Alhamdulillah alaa kulli halin,ba mu da wani damuwa daya wuce lafiyar mahaifiyarka,kullum rayuwarmu cikin haske take but a kullum na kasance mai addu'ar hasken da zai tunkaromu nan gaba ya kasance mafi girma daga cikin hasken da muka samu a baya... Wannan shi ne tak'aicce cikin labarin rayuwar mu..!"
*BACK TO STORY...*
Dogon ajiyar numfashi suka yi a tare Nuraz ya kalli Annie a hankali idanunsa sunyi ja hawaye suna zuba yasa handkey yayi whipping d'insu yace "Annie me yasa bayan rasuwar mijinki baki yi wani auren ba!?"
Murmushi tayi wanda iya kacinsa saman lips tace "Habibiiy.! Shin ta yaya ne ni da nake da patient zanyi wani aure,sannan kai kuma na kai ka ina.!? Kada ka manta ba ko wane namiji ne yake son rik'on d'an da ba nasa ba.. Besides ma ko da ace zanyi aure a wannan lokacin ko wane ne yazo da niyyar aurena ba zai tab'a yarda da aure ni ba."
Yace "Me yasa to Annie.!?" Tace "Ka manta a baya na fad'a maka korata babanmu yayi kamar yadda ya yiwa Hauwa.!? Saboda haka ka ga babu namijin da zai yarda ya auri wacce take *KORARRIYA*,bcos zai ta zargin me tayi haka mai muni iyayenta suka rabu da ita.!? Ka ga kenan rayuwar aurenta kawai dai zai kasance ne ta yi auren amma baza su tab'a samun nutsuwar zuciya ba,,sannan a duk ranar da aka samu sab'ani zai iya goranta mata,hakan kuma zai iya kaisu ga rabuwa.."
Gyad'a kai yayi yace "Na fahimci uzurinki Annie.."
D'an murmushin yak'e tayi ta goge fuskarta,a hankali tana kallonsa cikin salon son ta canja hiran ganin ya yi shiru yana tunani tace "Yaushe zaka koma ne.!?"
Ya d'ago kansa da sauri dake k'asa yana tunanin irin hukuncin da zai yiwa mutane biyu da suka canja tarihin mahaifiyarsa yace "Ina kenan Annie.!?"
Tace "School nake tambayar ka.!"
Ajiyar zuciya yayi yace "Maybe sai wani satin."
Tayi saurin kallonsa tana had'e rai tace "Kai bana son shashanci,da karatun yazo k'arshe saura baifi one month ba shi ne zaka fara delaying wajen komawa,,thought cewa kayi k'arshen satin nan zaka tafi.!?"
Ya gyad'a kai yana marairaicewa "please Annie ki bari na zauna sai wani satin.?"
Kafin ya kai aya tace "Bafa zan bari ka zauna ba,,gara ka wuce,da can me yasa baka tab'a zaman ba tsayin shekaru bakwai sai yau ne zaka fara min shirme.!?"
B'ata fuskarsa yayi yayi kicin² a tunaninsa zata ce ya zauna sai yaga ta tab'e baki ta mik'e tsaye,d'auke kansa yayi gefe,Annie ta kalleshi tace "Za kayi kuma zaka gama,,in dai nice ka san maganata d'aya nake bana biyu.. Komawa ne babu fashi k'arshen sati idan Allah ya nuna mana zaka tafi da yardarsa.."
Tana gama fad'a ta wuce kitchen tana yiwa Bareerah magana,yayi ajiyar zuciya bayan tafiyarta,lokaci guda fuskarsa ta rikid'e zuwa yanayin damuwa,,a hankali kwakwalwarsa ke masa reversing labarin data gama bashi,mik'ewa yayi tsam a gurin yayi hanyar d'akin da take,zaune ya ganta unlike d'azun,ta tasa bowl da kallo,Dr Waseem yana zaune saman table yana ta aikace²,abinci ya bata ta ci tun tashinta,but sama da hour guda tak'i sai kalle² take,idan taga kamar zai juyo sai ta firgita,shi kuma har lokacin bai san me take ba yana y'an rubuce²,sai da Nuraz ya shigo ya d'ago yana niyyar yi masa magana yaga ta zabura za ta sauka a gadon,kallonta yayi ya kalli bowl d'in yaga yadda ya bata haka nan yake,da mamaki a fuskarsa yace "Me kike jira baki ci ba.!?"
Saurin kallonsa tayi tana rarraba idanu,ya had'e rai yace "tambayar ki nake yi fa.!?"
Ta sosa kanta ta sake kafe shi da idanunta,tasowa yayi daga inda yake ya ajiye aikin yace "tunda ba zaki amsa ba yau allura saba'in zanyi miki kafin na tafi,anjima idan na dawo kika k'i ci nayi miki wasu.."
Kallon Nuraz tayi saurin yi kamar za tayi magana ta kuma kallon Dr Waseem,a hankali ta fara girgiza masa kai hawaye na sakkowa saman fuskarta,yace "idan ba kya so maza kici abincin ki,nima zan fasa yi miki allura.."
K'urii tayi masa da ido ta kasa d'aukan spoon d'in ta ci,Nuraz ya tako kusa da ita yayi d'an murmushi da gefen lips yace "Dr kullum haka muke yi da ita sai dai a bata,amma idan ba haka ba bana tunanin za ta yarda taci da kanta."
Dr Waseem yayi murmushi yace "Ai naga alama Dr kun maida ita y'ar gata,kusan kullum haka muke fama,but nafi so ne ko yaya ta dunga gwada ci da kanta,idan ba haka ba nan gaba fa akwai rigima.."
Murmushi suka yi tare,Nuraz ya zauna kusa da ita ya d'auki spoon d'in yace "lemme help" ya deb'o ya mik'a mata,bud'e baki tayi ta karb'a a hankali tana waiwayen inda Dr Waseem yake tsaye yana kallonsu,ya dunga bata tana karb'a har ta ci da yawa,Dr Waseem ya koma ya k'arasa aikinsa,suna gamawa Nuraz ya d'auki kayan ya fita da su ya dawo,allurai Dr Waseem yayi mata babu jimawa ta sake komawa duniyar bacci,suka fita suna d'an tab'a hira but mafi yawa daga ciki akan abunda ya shafi lafiyarta,basu yi taking long time ba tare Dr Waseem yace zai tafi,Nuraz ya raka shi har bakin motarsa suka yi sallama,yace zuwa dare zai dawo,bayan tafiyar Dr Waseem ya dawo cikin gida ya kwanta,tunanin yadda al'amura suka faru a baya yasa shi tashi ya zauna a hankali kwakwalwarsa take sake masa highlighting pictures d'in yadda suka dunga faruwa kamar yanzun ne suke occurring.
Da dare bayan Dr Waseem ya dawo ya sake dubata ya tafi,basu jima ba shima ya yiwa Annie sallama,tun da Nuraz ya shiga bedroom d'insa ya kasa bacci,tunani duk ya cika zuciyarsa ya tashi ya zauna saman study table d'insa ya fara operating computer ya shiga bincike,har wajen 1am bai tashi a gurin ba,da yaji bacci ya fara zuwa masa ya tashi ya fita,sai daya shiga room d'in da take ya dubata ya gyara mata rufa ya d'auko files d'inta ya kai d'aki,sannan ya sake fita zuwa kitchen yayi making one cup na coffee ya dawo ya sake zama a gaban computer yana sipping yana kallon screen d'in,ya sha kusan half cup ya ajiye yaci gaba,har asubah ya kai yana aiki da rubuce²,yana sake zurfafa bincike akan asalin matsalar,shi kansa sai yanzun a bayan samun asalin labarin su ya gano inda damuwar take duk da result d'inta ya jima da gwada masa asali faruwar komai trauma ne amma bai san yaya girman damuwar yake ba sai a yau,,da asubah Annie ta lek'o saboda bata ji fitarsa ba ta ganshi zaune yana aiki,da mamaki sosai a fuskarta tace "don't tell me u are still awaken.!?"
Ya juya ya kalleta ya gyad'a kai,ta jinjina kai tace "me kake yi baka yi bacci ba.!?"
Yace "ina wani assignment ne,and ina so na gama da shi kafin na tafi."
Ta sake jinjina kai tace "okay.! Allah ya taimaka,,amma dai ka dunga ragewa kanka aiki,kana kwanciya kana hutawa,idan ba haka ba aikin zai fi k'arfinka.."
Ya jinjina kai yace "sure Annie"
Ta juya zata fita tace "ka bar aikin haka nan,kayi sallah ka kwanta,idan na dawo naga baka yi abunda nace ba zan tafi da computer na ajiye a gurina"
Yayi murmushi kad'an da gefen baki yace "zan ma bari Annie" tace "better" sannan ta fita,tattara komai yayi ya ajiye bayan yayi sallah ya bi lafiyar bed,har around 11am yana ta bacci,Annie da tazo taga yana bacci around 7 tayi murmushin jin dad'i ta fita ta rufe masa k'ofa,,a haka kwanakin da suka rage masa suka yi ta zuwa suna wucewa,k'arshen sati ya zagayo,ya nemi ya k'ara ko 2 days ne Annie tace lallai sai ya tafi bata yarda da k'arin kwanaki ba,cikin nuna biyayyarsa gareta yayi shirin komawa.
Tun kafin ya koma these time around his mind were filled with lots of wishes,kasancewar a yanzun yana da sani akan yadda rayuwarsa ta faro da asalin rashin lafiyarta,tun daya dawo sai ya sake nutsuwa ya sake confessing matsalar dake gabansa,a kullum a yanzun babban burinsa shi ne ya kammala doctorate degree d'insa,his next target kuma shi ne ya wuce yayi course na neman zama licensed,he wants to become licensed clinical psychiatrist,duk da ya san it can take him 1-2 years,but a shirye yake yayi koma mene ne wajen ganin ya zama *HASKE* ga mahaifiyarsa.
Kullum idan ya shiga skul yana gama abunda yake zai fad'a laboratory,ba shi zai koma apartment d'insa ba wani lokacin sai dare,idan ya koma d'inma baya zama haka yake kwana aiki,har suka cinye last zangon karantunsu da suka cika shekaru bakwai,sun fara exam cikin nasara da yake shi d'in mai k'wazo ne sosai ya sake bada himma,,after long time da suka d'auka suka k'are,ya fito with a good result a matsayinsa na *CLINICAL PSYCHIATRIST* his first wish were fulfilled saura next target nasa.
Annie kad'ai taje masa ranar da aka yi convocating d'insu,kwanan ta biyu tare da shi a Oxford suka tattara suka dawo 9ja,tunda ya dawo da yayi kwana biyu yana hutawa ya sake maida hankali kan ainihin matsalar data shafi lafiyar mahaifiyarsan,kullum bashi da lokacin kansa,daga ibada sai aikin kula da ita,bcos tuni bayan dawowarsa suka sallami Dr Waseem bayan sun cikasa da sha taran arzik'i,,after one week Nuraz ya fara nasa aikin cikin k'warewa duk wasu medications da ya san za su taimakawa jikinta ya tanadesu,though ya san za a same su a nan amma bai yarda ya siye su a ko ina ba yayi order su daga U.K ya taho da su,duk da ya san a nan gida 9ja akwai inda zai same su,,Alhamdulillah alaa kulli halin.! Har kullun ubangiji shi ne abun godiya,tunda Nuraz ya fara dorata a kan nasa tsarin within k'ananun lokaci nasara ta fara samuwa,Hasken da suka d'auki shekaru suna nema a lokaci guda ya fara bayyana.
*3 Weeks later...*
Today's weather ya kasance tunda aka tashi garin were darken with some thick clouds,wanda at anytime ake sanya rai da saukar ruwa,but har aka yi zuhur prayer aka yi asr ruwa bai sakko ba,duk da time2time akan samu garin ya d'anyi lighten,,,btwn 5pm to maghreb gari ya sake d'aurewa fiye da farko ko ina yayi duhu sosai,kafin ace 7 yayi ruwa mai k'arfi ya sauka,har around 9pm ruwa bai dakata ba,though it was very light shower of rain ne yake sprinkling,,tsaye yake gefen street d'in cikin wani clean sharp toks 04 pontiac Vibe white colour,ya d'aga kai ya kalli way d'in da zai bi yayi shiru,tunani yake anya ya bi hanyar ko kuma dai zai canza wani.!? Yayi still yana ta kallon yadda kwab'ab'b'en ruwan k'asa yake gudu,siririn tsaki yaja a fili yace
"Wai mene ne ma ya fito da ni by this time around.!?"
A hankali ya sake sakin wani slender crack a karo na sau babu adadi,ya yiwa motar key ya fara tafiya da reverse sanin babu kowa a bayansa,kamar wanda aka ce ya d'aga kai ya kalli mirror ya ganta tsaye a bayansa kamar wacce akayi sculpturing,hasken street lamppost a kanta,horn ya yi mata a tunaninsa hakan zai sa ta matsa,but sai yaga ko gezau tak'i yi,shiru yayi ya zuba mata ido through mirro'n ya jira yaga za ta tafi but still tayi tsaye cikin ruwan,yadda jikinta yake shaking alamu suka gama tabbatar masa ruwan nan dukansa a kanta ya k'are,zuciyarsa ce yaji ta yi skipping yace
"Anya wannan tana da hankali za ta shiga cikin ruwa ta tsaya..??"
Sanin kansa ko shi da yake mai cikakkiyar lafiya baya so ko kad'an ruwa ya tab'a shi bcos in time zai fara sneezing,lokaci guda yaji zuciyarsa ta buga da k'arfi ya fara neman rasa nutsuwarsa.....
*#Wace ce ita.!? And what happen to her mind take tsaye cikin ruwa kamar ba mutum ba.!?*
#Share pls.
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*
*'DAN MACE..*
(Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥
*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://my.w.tt/29u2S26SG2
*My people.! 😍 'DAN MACE FAN'S ina mik'o gaisuwa gareku,zayyana sunanyenku a page kad'ai ba zai wadatar ba,saboda yawan da kuke da shi zai yi wahala na iya rubuta ku a wannan dan