Showing 57001 words to 60000 words out of 224143 words

Chapter 20 - DAN MACE COMPLETED Romantic Book .txt

i won't do it,but when za ka ci gaba.!?" ya jinjina kai yace "until we have time again." Tayi murmushi tace "shortly if we come out again.!?"
Yayi saurin kallonta,itama shi take kallo ya girgiza mata kai yace "No.! Not today" tayi saurin cewa "tomorrow to.!" Ya kalleta lokacin da Bareerah ta bud'e musu k'ofa tana musu sannu,ya amsa yana shigewa ta biyo bayansa da sauri tace "u still haven't said anything.!"
Ya tsaya yana kallonta ta matso inda yake tsaye da sauri tana marairaicewa,a hankali yace "okay.!" Tayi masa murmushi tace "Thanks" ya gyad'a mata kai ya wuce zai nufi hanyar kitchen tace ya bata ta kai,ya ajiye ledojin hannunsan sannan ya wuce bedroom d'insa,wucewa tayi itama ta nufi hanyar d'akinsu ita da Annie bayan sun gama shirya komai,wanka ta fara yi ta d'auro alwala,sai da ta fara shafa mai a jikinta sannan ta saka kaya ta fita,a parlor ta tarar da su shi da Bareerah tayi musu sallama Bareerah ta fara amsawa sannan shi da hankalinsa fiye da rabi yake kan computer,ta nemi guri ta zauna tana kalle² can ta daure ta kalli Bareerah tace "Ina Annie.!?" Cikin muryar damuwa,ya d'ago a hankali ya kalleta yaga fuskarta ta bayyana damuwa ya ci gaba da kallonta,Bareerah tayi murmushi tace ta shiga duba Aunty,ta rausayar da kai,shiru² tana jira taga ta fito taga har lokacin bata fito ba a hankali ta juya tana kallon k'ofar d'akin data shiga,kansa a kan computer yana clicking yace "Ki je mana" tayi saurin kallonsa taga hankalinsa baya kanta,ba tayi zaton da ita yake ba,a hankali ta sake juyawa tana kallon d'akin,ya d'ago idanunsa "don't u want to go.!?"
Tayi saurin sake juyowa taga ita yake kallo,ya gyad'a mata kai alamun tambaya,a hankali ta mik'e ta fara tafiya,har ta je bakin k'ofa ta waiwayo taga ya ci gaba da aikinsa,tayi knocking sannan ta tura k'ofar ta shiga da sallama,a zaune ta ganta bayanta jingine da pillow,ta tsaya kallonta taga itama ta d'ago tana kallonta kamar ta santa,Annie ta waiwaya ta kalli Nusrah tace "A'a daughter shigo mana kika tsaya a nan" a hankali ta fara d'aga k'afarta tana tafiya,Hauwa ta zuba mata idanu tana kallonta har ta tsaya a kusa da su,tace "Annie sannu da aiki,ya mai jiki.!?" Annie tana mik'a mata spoon data deb'o abinci tace "Yawwa! Daughter,mai jiki Alhamdulillah gata ta fara samuwa" ta kalleta taga ita take kallo har lokacin tace "Allah ya bata lafiya" Annie ta amsa "Ameen daughter",hannu Hauwa ta mik'a tana tab'a Nusrah,a hankali ta sake matsawa taje kusa da ita tana yi mata murmushi,tana ta kallonta kusan mintuna uku ta juya ta kalli Annie data zuba musu ido,a hankali ta bud'e bakinta "Wannan baby'n ki ce.!?"
Mamaki Nusrah tayi da taji tayi magana,ta d'ago da sauri ta kalli Annie,murmushi Annie tayi mata ta juya tana kallon Hauwa tace "Ehh! Babyna ce,kina son ta ne.!?" ta shafa fusakar Nusrah tace "Tana da kyau,,i like her,za ki bani ita.?"
Ta gyad'a mata kai tace "ai kema baby'n ki ce" tayi dariya kad'an tace "What's her name to." Annie tace "Sunanta *NUSRAH"*
Lolly ta tab'e baki irin yadda Nuraz yake yi idan yaji abu bai masa ba tace "can i call her with Angel"
Annie ta sake yin murmushi tace "call her with every name u want,,kada ki damu it's ur daughter" ta sake rik'o hannunta tana ta kallonta,a haka Annie ta ci gaba da bata abincin har ta gama Nusrah bata fita ba tana cikin d'akin a zaune a d'aya gefen nata,tana ta kallonta da tausayawa musamman idan ta tuna labarinsu yayi kama da juna sai taji zuciyarta ta karye,tana son yin kuka ko zata ji sauk'i amma idon Annie ya hana ta,haka tayi ta daurewa har Annie ta tattara kayan zata fita Nusrah tace "Annie kawo na kai" ta mik'e da sauri zata karb'a Lolly ta b'ata rai tana kallon Annie kamar za tayi kuka,Annie tayi murmushi tana kallon Nusrah tace "Barshi daughter zan kai,ki zauna tare da ita zanje na dawo" tana fad'a ta fita da kayan Nusrah ta koma ta zauna inda ta tashi,Hauwa ta ci gaba da kallonta.....








#Share pls.
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©®2020.*


*'DAN MACE..*
(Tʜᴇ ᴘꜱʏᴄʜɪᴀᴛʀɪꜱᴛ)..💥



*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://my.w.tt/29u2S26SG2


Pᴀɢᴇ 18.
#Cᴏɴғᴜꜱɪᴏɴ


Fitar Annie babu jimawa ta gama abunda take,dawowa tayi d'akin ta duba ganin Hauwa ta fara bacci ta kira Nusrah,ta tashi da sauri zata fita tana amsa kiran har ta kai bakin k'ofa Lolly ta farka,tana kallon zata fita ta barta ta b'ata fuska kamar za tayi kuka,Annie tayi shiru tana kallon ikon Allah,a hankali ta shigo ciki ta dafa shoulder d'inta tace "Mene ne.!?"
Ta d'ago kanta a hankali cike da sakarci tace "ki ce ta dawo.."
Annie tace "wace ce zata dawo.!?" A hankali tana kallon Nusrah dake tsaye bakin k'ofa tana kallon su tace "My Angel"
Annie ta juya ta kalli Nusrah tace "zo daughter" Nusra ta taka a hankali ta koma Annie ta kalleta tace "yi hak'uri daughter ki zauna tunda bata so ki tafi,barin kawo miki abincin sai ki ci a nan" Nusrah ta amsa da "toh"
Annie ta fita parlor tana girgiza kai tana murmushi,Nuraz ya d'ago yana kallonta yaga tana murmushi,tab'e baki yayi kad'an yace "Annie.! What makes u laugh.!?"
Ta kalleshi tana d'aukan plate d'in dake ajiye saman dining tana serving tace "Wollahi nida Lolly'nka ne,ta hana Nusrah sam ta matsa,yanzun na lek'a na tarar ta fara bacci,daga na kirata ta zo ta ci abinci ta tashi zata min rikici,na tambayeta tace wai bata so ta tafi,shi ne nace ta bari to na kai mata abincin can sai ta ci,idan ta koma baccin sai ta fito" bai ce komai ba ya jinjina kai yana mamakin al'amarin.

Satin su d'aya da zuwa ya fara attending course daya kawo shi,itama Nusrah Alhamdulillah ta samu admission suna daf da fara lectures sun bata cardiology (b'angaren abunda ya shafi zuciya),,tana kwance a parlor taga ya shigo,ta d'aga kai ta kalleshi bata yi magana ba taga ya wuce hanyar bedroom d'in Annie,a hankali can k'asan ranta tace "ko me ya dawo da shi gida yanzun.!?"
Ta tab'e baki ta yi shiru tana tunani,baifi five minutes ba taji alamun fitowarsa,tayi luf ta bi hanyar da ido,ya zo ya wuce da alama bai ganta ba,tashi tayi bayan fitarsa ta nufi hanyar d'akin da mahaifiyarsa take ciki,ta shiga ta tarar tana bacci,a hankali ta zuba mata ido cikin tausayin yadda rayuwarta ta kasance,wasu irin hawaye suka gangaro mata,ta goge tana kallonta,a fili ta furta "All thanks be to Allah,he who united me with good and helpful people,sun taimake ni a lokacin da basu san wace ce ni ba,ba su san asali na ba,da wane irin abu zan saka musu ban sani ba.! Yah Ubangiji kai ka k'addara min had'uwa da su,dukkanin alkhairinsu gare ni ba zan iya mantawa ba,ya Allah ka sakawa wad'annan bayi naka da mafificin sakamako..!"
Ajiyar zuciya tayi tana ci gaba da tunani a zuci,a hankali wani sashi na zuciyarta ya furta "Ko yanzun da a ina nake.!? am i still alive,dead,ko ina nan cikin hauka.!?"


Ta ji hawaye sun cika mata ido,ta zauna kusa da Lolly daga gefen k'afafunta ta kura mata ido,ta yi ajiyar zuciya mai nauyi a hankali cikin mutuwar jiki ta d'aga kanta kanta sama idanunta a lumshe "O Lord.! Kai ne ubangijin dukkan wani abun halitta,u are the reviver of the dead,and receiver of the healthiest life,richest of all and everything,u have made our destiny be the same,yah Allah grant us the ability to succeed all ur test over us.."
Ta jima sosai a cikin d'akin tana tunani,ganin duk lokacin data d'auka bata farka ba yasa ta fita.

In 2 weeks da zuwansu k'asar ta fara attending skul,cikin nasara da maida hankali akan karatunta da tunanin yadda rayuwarta za tayi idan bata maida hankali ba,a gefe guda kuma zuciyarta a kullum cikin yi mata khud'uba da tunatar da ita take,idan ta bawa wad'annan bayin Allah kunya tak'i tsayawa tayi abunda ya dace yaya za su ji,shi kenan sun yi asarar dukiyar su sun tsaya mata,ita kuma ta basu kunya.? Da wane idon ma zata iya kallonsu idan hakan ya faru.!? Wad'annan tunanukan da take yawan yi su suka sake bata damar nutsuwa,ta fara k'ok'arin manta duk wani damuwarta da abubuwan daya faru da ita a baya,a hankali cikin tak'aitaccen lokaci ta ci gaba da confessing matsalar gabanta..

3 Year's later...


Tana zaune saman study table tana karatu,ta jiyo Annie na kiranta da sauri tasa bookmark ta mik'e ta fita,a parlor ta tarar da su Bareerah tana basu labari suna ta dariya,ta girgiza kai tayi murmushi sannan ta k'arasa kusa da Annie ta zauna tace "Annie ga ni..!"


Lolly dake murmushi ta kalleta tace "Zo Baby ni nake kiranki" ta mik'e a hankali zuwa gurinta ta zauna,lolly ta shafa kanta tace "me kike yi ne a d'aki ke kad'ai.!?"


Tana squeezing face tace "Karatu nake yi Aunty i've a test gobe"


Lolly tace "Ok.! Je kiyi karatun ki kada na takura ki,thought babu abunda kike yi ne ki rakani,but bari muje tare da Bareerah"

Tayi saurin yin murmushi tace "No.! Aunty muje na raka ki" su Annie suka yi dariya,Lolly tana kallonta taga yadda tayi da fuska,tayi murmushi tace "Je ki gyara fuskarki mu tafi to,tunda kina son fita."
Ta mik'e da sauri ta koma bedroom tana dariya,kaya ta canja zuwa wani simple gown daya sha adon stone's milk colour tasa milk flat shoe ta nad'e kanta da vail d'in rigar,ta feshe jikinta da turaruka masu dad'i ta fito rik'e da wayarta k'irar iPhone8,su Annie duka suka kalleta suka yi murmushi,a yangance ta matso kusa da Lolly tace "Aunty na shirya"
Lolly tayi murmushi ta mik'e tana gyara nad'in vail d'inta tace "Muje ko kada mu b'ata lokaci" suka yiwa su Annie sallama,Annie cike da zolaya tace "Allah yasa ayi min surukai"
Suka kalleta babu wanda yayi magana suka fita,,Ali Jericho Store dake 9 albert street cikin oxford city d'in suka nufa,suna tafe cikin farin ciki,kai da ganinsu kasan suna cikin jin dad'i,babu wanda zai kalli Lolly a yanzun yace ta tab'a yin wani jinya,ko yace tana da saurayin d'a kamar Nuraz mai shekaru 28,yadda tayi kyau tayi y'ar k'iba ta samun lafiya da kwanciyar hankali duk sai girmanta ya b'oye,,sun shigo cikin mall d'in suka wuce Nusrah tana taya ta duba abunda take so,suna yi suna hira cikin nishad'i kamar wasu k'awaye har suka gama d'aukan abunda suke so,suna shirin barin gurin wasu turawa da suka shigo arean da suke suna magana,hankalin Lolly ya kai kansu,su biyu ne sanye da shigar da kana kallonsu zaka tabbatar basu had'a alak'a da musulunci ba,d'ayar tana bawa d'aya labari cikin harshen nasara
"Jenny.! I don't understand what u are saying."


Wacce aka kira da Jenny ta kalli y'ar uwarta tace "Ohh.! Thania don't u recognized his face.!?"


Thania ta gyad'a mata kai tana tab'e baki tace "I don't know him,and i don't think.."

Jenny tayi dariya cikin harshenta tace "k'arya kike yi,kawai dai kice baki gane shi ba.!"

Thania ta tsaya kallonta tace "Kamar yaya.!?"

Jenny ta harareta tace "Ohh No.! Thania.. Don't u know who *SUPERIOR* is.!?"

Thania ta fiddo k'ananun blue eyes d'inta tana rik'e waist,Jenny ta sake yin dariya tace "Shi kika gani yanzun fa za mu shigo.."

Thania tayi dariya tace "Da gaske shi ne wannan,ina guards d'in kuma,naga duk inda za shi a zagaye yake da guards.!?"

Jenny ta gyad'a mata kai tana lumshe idanunta tace "Kin san su manya wani lokacin suna yin b'adda kama su shiga cikin mu",Thania ta fara waiwaye ta marairaice tana rik'o hannun Jenny tace "Please dear,muje na sake ganinsa,i so much love him deadly,kin san na tab'a baki labarin matarsa ta kusa kashesa ko.!?"
Jenny ta gyad'a kai tace "Haka kika fad'a min,ita da boyfriend d'inta ko waye ma.!?"

Thania tace "Yes of course."

Jenny tace "To wai duk ita mene ne ya kaita.!? Ta samu miji kamarsa ta wulak'anta,ai gashi nan yanzun ta yi mana bak'in ciki,yace ba zai sake aure ba,lokacin da akayi hira da shi a news yake fad'a"

Thania ta tab'e baki "Ki bar mahaukaciya,kuma fa wai ashe wannan yaran da ake cewa nasa ne,duk babu nasa kids d'in boyfriend d'inta ne"


Jenny ta zaro ido tace "Hey.! Yaran duka uku babu nasa.!?"

Thania ta gyad'a kai tace "haka ya fad'a ai,kuma kin san DNA suka yi shi ya tabbatar masa babu kid d'insa a ciki"
Da mamaki a fuskar Jenny tace "Ta cuci kanta,yanzun duk wannan expensive life mai cike da alatu ta cuce su ta fitar dasu daga cikinta.."


Thania tayi murmushi tace "I wish za mu had'u ko sau d'aya,da na gwada sa'a ta.."


Dariya sosai Jenny tasa mata har da kyakyatawa,sanda ta ga Thania ta ji haushi sannan ta dakata tana dafa kafad'arta,cikin rarrashi tace "Sure dear zai so ki kuma,bcos kema ba baya ba ai.. But kin makara dear"


Thania ta washe baki tana kallon Jenny with her blue eyes tace "Ohh.! Thank u dear,,let go."
Shiru tayi saurin yi tana had'e rai,tana kallon Jenny tace "Jenny me kike son cewa ne.!?"

Jenny tayi ajiyar zuciya tana lumshe ido da bud'ewa ta dafa shoulder Thania tace "Dear bafa wani abu bane nake nufi,kawai dai na ce kin makara ne."

Thania ta sake had'e rai tana taune lips d'inta,Jenny ta sake lumshe ido ta fesar da iska mai d'umi za ta sake yin magana Thania ta fizge jikinta ta wuce da sauri zata fita,Jenny ta fara kiranta tana cewa ta dawo ta ji abunda za ta fad'a,bata tsaya ba bare ta dawo,da sauri ita kanta Jenny ta ajiye abunda ta d'auko tabi bayan Thania da d'an gudu duk da tana saman hill shoe ne har suka fice.

A hankali Lolly data bisu da kallo ta juyo tana kallon Nusrah,haka nan taji jikinta ya yi mata wani iri she feels not compatible,ta kama hannun Nusrah da sauri tana jin kanta na sarawa,ta lumshe idonta tana fad'in "Baby let go home"


Nusrah tayi saurin rik'ota da hannu biyu ganin yanayin da take ciki ta fara tambaya
"Aunty are u alright.??"


Ta girgiza mata kai ta d'ago kad'an tana bud'e lumsassun idanunta,yadda tayi wani iri lokaci guda yasa hankalin Nusran ya fara k'ok'arin tashi da sauri tace "Mu tafi to."
Suka kamo hanyan fitowa,sun tsaya sun biya charges e d'in abunda suka siya kafin suka fito,Nusrah na rik'e da hannunta tana mata sannu,ta girgiza mata kai a hankali tace "Thank u Angel",suna fitowa k daga Ali Jericho cab suka tsayar Nusrah ta fad'a masa inda zai kaisu,yace su shiga tana rik'e da hnnun Lolly har lokacin tace "Aunty muje" ta bud'e mata motar tana k'ok'arin taimaka mata ta shiga,kamar ance ta d'aga kai ta hango shi tsaye yana amsa waya,wani muguwar fad'uwa gabanta yayi da suka had'a ido,yadda ta sanshi haka nan dai yake har yanzun babu abunda ya canja,yana nan da kyaunsa,d'an gayu da shi first class,saurin d'auke kanta tayi daga kallonsa ta runtse ido tana karanto addu'o'i,da sauri ta zauna tana juya kanta d'aya side d'in,Nusrah ta shigo ta zauna ta rufe motar,ta yi shiru hawaye suna bin fuskarta,Nusrah ta juya tana kallon yadda jikinta ke tsuma da yadda ta rirrik'eta,ita dai duk ta shiga tunanin abunda ya tada mata hankali,da sauri tace ma drivern ya ja su tafi,baturen ya amsa sannan ya fara k'ok'arin tada mota.


Da wayar a kunnensa tunda suka had'a ido da ita ya kasa ci gaba da magana,suka wuce ta gabansa,,har suka tsaya bakin apartment d'insu jikinta bai daina kyarma ba,Nusrah ta rik'ota suka wuce ciki bayan ta sallami mai cab d'in,suka shiga cikin parlor'n tana rik'e da ita,tana ganin Annie da sauri ta saki Nusrah ta fad'a jikinta tana fashewa da kuka mai tsanani,hankalin Annie a tashe ta kalli Nusrah ta kalleta ta rik'o ta da sauri za tayi magana aka danna doorbell,Annie ta kalli Nusrah ta juya ta kalli entrance tace "Daughter duba ki gani waye.!?"
Ta gyad'a kai a hankali ta wuce jikinta a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login