Showing 42001 words to 45000 words out of 224143 words

Chapter 15 - DAN MACE COMPLETED Romantic Book .txt

tak'aitaccen page d'in,but duk wanda yake tare da ni yana cikin wannan sak'on,rabbi ya bar min ku mu ci gaba da kasancewa tare har aljannah. Really heart u dearies..*💕


Pᴀɢᴇ 13.
#Eᴠɪʟ ꜱᴘɪʀɪᴛ


Ya jima tsaye da tunanin za ta gaji ta bashi hanya,but sai ya ga ba ta da niyyar yin hakan,shi kuma duka a time d'in fitowar ne baya son yi,ya duba cikin motan bai samu umbrella ba,yana tsoron ruwan ya tab'a shi,,shahada yayi at last ya bud'e motar da kyar ya fito,sai daya fara sako kafarsa waje dake sanye cikin longo men's loafers slip shoe bak'i,kafin ya karasa fito da sauran gangar jikisa,sanye yake cikin V-neck double breasted waistcoat mai launin gray sai long sleeve mai launin sky blue,a saman kwantaccen sumar kansa ruwan ya fara sprinkling,kamar ko da yaushe da askin nan nasa da ya san yana k'ara masa kyau,undercut with long side swept,ya fito ya rufe motar da sauri har yana had'awa da sassarfa duk dan gudun kada ruwa ya jik'a shi sosai ya nufi inda take tsaye,kafin ya k'araso ya d'an tsaya da sassarfan da yake ya ci gaba da takowa a hankali har ya k'araso,taku bai fi koma ba a tsakaninsu ya kalleta sosai within a minutes ya tsaneta tsaf,daga ita sai gown na wani plain cotton material mai sauk'in colours da yabi jikinta ya lafe saboda ruwan da yayi mata mugun duka,sumar kanta sakaye cikin turban cap yellow colour,daga haka babu komai jikinta apart of gyale ko hijab,ya tab'e baki kad'an ya juya ya kallo inda ya baro motarsa yace "Sannu ko.!" Yaji bata amsa ba,ya sake kallonta kad'an not minded da shirunta yace "idan ba zaki damu ba,dan Allah ki d'an bani hanya ina sauri zan wuce."
Still bata yi tari ba bare ta tanka masa,sai kallonsa kad'ai take ta zuba masa manyan idanunta,fara ce amma ba can ba,duk da dare ne and duhun da garin yayi a sanadiyyar hadarin da har lokacin bai gama washewa ba but ana iya gane hakan,duk wani suffar kyau da ake buk'ata a gurin cikakkiyar mace sun bayyana a tare ita,she's just the definition of beauty musaman da take cikin jik'ak'k'un kayanta,irin kallon da take masa yayi saurin kawar da kansa gefe da tunanin ko dai bata jin hausa ne.!?
Tab'e baki yayi a ransa yace "maybe ma haka ne" cikin tsadadden turancinsa ya canja harshe,ya maimaita same abunda ya fad'a,abun mamakin yadda tayi da farko haka ta sake yi masa,sam babu alamun tana magana,tab'e baki ya sake yi da yaga alamar ba lallai tana gane abunda yake nufi ba ya juya a hankali ya fara tafiya coz shi dai bai san me zai ce ba kuma,har ya fara tafiya wani zuciyar tace "Shin yanzun idan ka barta a wannan yanayin fa.!? Ka san mene ne zai faru da ita a wannan daren.!?"
Dakatawa yayi a inda yake ya waiwayo kad'an yace "Come" ya yafito ta da hannu,ta sake yin kasak'e tana ta kallonsa,mamaki ne ya kamashi sosai,cikin abunda bai wuce mintuna uku ba yayi mata kallon nutsuwa,zuciyarsa banda bugawa babu abunda take after her physical reality exists only because of the mind's awareness da yayi,ya dawo gefen da take yana sake kallonta cikin son tabbatar da zarginsa akanta,aka yi sa'a lokacin yana kan nazartar halin da take ciki wani irin lightning yayi crossing,after then thunderstorm mai tsananin razanarwa ya ratso,jikinta ya d'auki rawa fiye da farko ta k'ank'ame alamun ta tsorata sosai hawaye ya fara bin fuskarta,yana kallonta da wani irin damuwa a fuskarsa yayi unbuttoning waistcoat d'insa duk da yasan ba lallai ta kare mata wani sanyin da take ji ba ya rufa mata a saman jikinta ya juya abunsa da niyyar barin gurin cos he don't know what to do,idan yace zai tafi da ita ma bai san da yaya zai yi hakan ba tunda bata fahimtarsa,har ya kai bakin motarsa yana tunanin rashin maganarta duk da ya fahimci matsalar,kamar wanda aka ce masa ya kalli inda ya barta,yana waigawa kamar jinn yaga bata wajen ta b'ace,fuskarsa da mamaki sosai yayi ta kallon wajen sai dai baiyi magana ba ya bud'e motar ya shiga yana tunanin inda ta shiga kuma,yana zama ya ganta tsaye kusa da motar ta gefensa kamar ghost,lumshe idanunsa yayi ya bud'e ya kalleta cikin zuciyarsa yana addu'ar Allah yasa ba aljana bace,saboda duk da yake namiji ya tsorata da wani irin murya yaji tace "Zan bika.."
Da mamakin yadda aka yi tayi magana sosai akan fuskarsa ya kafeta da kallo kamar yadda tayi masa,yana fito da idanunsa waje yace "Ina za ki bini..!?"
Tayi shiru kamar mai son tunawa tana ta kallonsa,ya sake lumshe idanunsa ya bud'e ya maimaita mata tambayar,wani irin gesturing tayi da idanunta da kanta,looks like ana tsikarinta da abu mai tsini ta sake cewa "Zan bika"
Ya juya ya kalli arean da suke,gaba daya wajen yayi shiru babu kowa hasalima ko ababen hawa babu masu wucewa bare a samu mutum,ya kalli steat d'in kusa da shi ya kalleta yayi jimm yana tunanin anya ya tafi da ita,a hankali ya sauke dogon ajiyar zuciya ya girgiza mata kai yace "Toh taho mu tafi"
Inda yake ta matso unlike ta koma ta d'ayan gefen tana k'ok'arin shiga,ya kalleta yace "ba nan ba,can za ki za kije"
Tayi still tana kallonsa cikin rashin fahimta,a hankali ya fito ganin zasu b'ata lokaci yaje ya bud'e mota yace "Zo ta nan muje" tafiyarta da komai nata a nutse kamar mai cikakken hankali,ya taimaka mata ta shiga ta zauna,ya rufe ya koma mazauninsa ya tada motar suka d'auki hanyar Sardauna crescent,suna tafiya yana sake observing nata,tafiyar mintuna ta kawosu bakin get d'in gidansu,yayi horn get man da suka yi bayan dawowarsa babu jimawa ya bud'e masa ya shige,ya samu gefe yayi parking ya fito,ya bud'e mata k'ofa ta fito sannan ya wuce gaba ta biyo shi a baya tana ci gaba da wannan gesturing d'in da kanta da idanu,a bakin entrance yayi knocking maidservant d'insu Bareerah ta bud'e masa k'ofa,ya wuce ciki yana gaisheta,ta biyo shi a baya tana ta kalle²,ya wuce bedroom d'in Annie da yaga bata parlor da niyyar yayi mata bayani kafin ta sako shi gaba da tambayar wace ce ita.!? Ta sake biyo shi a baya,yaji kamar ana binsa yana juyowa ya ganta ta biyosa ya dakata yace "Koma parlor ki jira ni"
Ta tsaya tayi shiru tana kallonsa,ya juya yaci gaba da tafiya ta sake biyo shi,ya shiga bedroom d'in Annie ya ganta zaune saman pray mat tana addu'ah,ya zauna gefenta ya d'ora kansa a saman shoulder d'inta har ta idar,gogar tana ta tsaye daga bakin k'ofa tana kallonsa ta kasa shigowa,Annie ta shafa kansa tace "HABIBIIY.! Ina ka fita ne naji motsinka babu jimawa.!?"
Ya bud'e lumsassun idanunsa yace "Annie kawai fita nayi amma nima ban san mene ne ma ya fitar da ni ba"


Ta kalleshi tace "Allah ya kyauta"


Yayi saurin tashi daga jikinta ya zauna sosai,yana niyyar yi mata bayani yace "Annie.!" Kalmomin suka mak'ale a saman lips,ya k'urawa ind take tsaye kallo,saurin tashi yayi ya nufi inda take yace "Ba sai da nace ki jira ni a parlor ba.!?"
Cikin had'e rai ya k'arasa,tayi saurin kallonsa,Annie ta kallesu duka kafin ta tashi itama tana fad'in "A'ah.! Habibiiy bak'uwa muka yi.!?"


Ya juyo fuskarsa da damuwa yace "Annie bayani fa zan yi miki ta wani biyo ni."


Annie tayi murmushi tace "to mene ne dan ta biyo ka.!? Ce ta shigo"


Ya kalleta ya zabga mata harara yana had'e rai,bai yi magana ba ya juya gurin Annie ya barta a tsaye a inda take,duk yadda al'amarin ya faru daya fita ya fad'awa Annie ta d'aga kai tana kallonta da tausayawa dan ko itama daga zuwansu ta fahimci kamar ba lafiya yarinyar take ba,ta kalleshi tace "To yanzun habibiiy yaya za'ayi kenan.!?"
Yace "Annie nima dai ban sani ba,amma na taho da ita ne saboda ina so na gwada na gani ko Allah zai sa na iya taimakawa akan matsalar ta,da na yi tunanin barinta a inda na ganta but sai nayi tunanin idan ta had'u da wasu suka cutar da ita fa.!?"


Annie ta jinjina kai tace "Ka yi tunani mai kyau,in sha Allah babu damuwa sai ta zauna tare da mu zuwa lokacin da zata samu lafiya,,ubangiji yayi maka kyakykyawan jagoranci akan niyyar ka ta alkhairi"


Yace "Ameen Annie,bari na barta a nan ko,zanyi wanka but zan dawo"


Ta amsa masa da "toh" ya tashi ya fita,tana ganin ya fita ya fara tafiya ta bishi,kai tsaye ya wuce bedroom d'insa bai san tana binsa ba sai daya shiga yana k'ok'arin rage kayan jikinsa da niyyar shiga ya watsa ruwa,ya ganta tsaye a wajen study table d'insa,mamakin lokacin data biyo shi bai sani ba yasa shi tsayawa yana ta kallonta,ya sake had'e rai ya cire kayan bai kulata ba,ya wuce bathroom ya barta nan tsaye,tana juyowa taga zai shige tayi tunanin fita zai sake yi tayi sauri ta biyo shi,ya juyo zai rufe k'ofar ya ganta a gabansa ya tsaya yana kallonta fuskatsa a matuk'ar d'aure yace "why are u still following me.!?"
Ta kalleshi tayi shiru,a fusace ya daka mata tsawa yace "ba dake nake magana ba kin kafe ni da ido.!? Za ki daina bina duk inda nayi ko sai na faffalla miki mari.!?"
Nanma tayi shiru tana ta kallonsa,ya fito daga toilet d'in ya kama hannunta ya shiga janta,sai daya kaita gefen bed d'insa ya zaunar da ita idanunsa cike da tsoratarwa yace "Nan za ki zauna,idan kika sake bina sai na zane ki"
Ya k'arasa yana zare mata ido,jikinta ya hau b'ari,tana ta kallonsa bata ce komai ba ya juya ya tafi,sai daya kai bakin k'ofa kamar ance masa turn,ya sake ganinta biye da shi sau da k'afa,ransa a b'ace fiye da karon farko ya tsaya ya rik'e waist,itama ta tsaya a inda take tana ta kallonsa like ta ga sabuwar halitta,ya jinjina kai cike da b'acin rai yace "wato baza ki daina bina ba kenan.!? Ke haukar naki haka ya nuna miki ki yi,toilet d'inma sai kin bini.!?"
Tayi shiru tana kallon bakinsa da yake motsawa,ya daka mata tsawa yace "koma can ki zauna ki jira ni nace"
Annie data shigo d'akin a time d'in tace "A'ah A'ah.! Habibiiy,ya zaka na mata tsawa,ka bita a hankali mana"
Ya d'ago kai ya kalli Annie kamar zai fashe da kuka yace "To Annie fisabilillah sai kawai ta dunga wani bina duk inda nayi,nace ta zauna na fito,har fa mayar da ita nayi ta sake biyo ni"
Annie tayi murmushi tace "To yi hak'uri je kayi wankan bari na tafi da ita"
Ya juya ya banka mata harara ya wuce bathroom ya kulle,ta tsaya a bakin k'ofar tana ta kallo,Annie ta matso inda take ta kama hannunta,ta juya ta kalleta Annie ta sake yi mata murmushi tace "Muje ko daughter.!"
Tayi shiru ta k'ura mata ido,Annie ta fara tafiya tace "muje maza kiyi wanka kema" ta fara binta kamar ta gane abunda Annien take nufi,suna tafiya tana waiwaye har suka fita,Annie ta kaita bedroom d'inta ta zaunar gefen bed tace "maza zauna nan ki jira ni,bari na had'a miki ruwan wanka."
Tana fad'a ta wuce bathroom d'inta ta had'a mata ruwa mai d'umi ta fito,tana shirin yin magana taga wayam babu kowa a gurin ,da mamaki tace "Toh! Ina tayi kuma.!?"
Ta fito tayi following footstep d'inta,ta duba parlor bata sameta ba ta wuce bedroom d'insa,tsaye ta ganta a bakin entrance na bathroom tana waiting fitowarsa,Annie ta girgiza kai taje ta kama hannunta,saurin kallon Annie tayi ta kalli entrance d'in,Annie cikin sanyi ta shafa kanta tace "u don't worry ur self daughter,muje zai zo gurin ki idan ya fito"
Ta k'urawa Annie ido,Annie ta kama hannunta suka fita,har bathroom ta kaita ta rufe mata k'ofa ta waje,almost thirty minutes da shigar da ita wanka ya shigo cikin shirin bacci,Annie ta kalleshi tace "Yanzun ya zamu yi ne da k'anwar taka.!?"


Yayi saurin kallonta yana bud'e idonsa sosai yace "Annie.! K'ANWATA kuma.!?"


Tayi murmushi ta gyad'a masa kai,ya tab'e baki yace "Kiji Annie wai K'ANWATA,daga ganinta yau har ta zama relative d'inmu.!?"


Tayi y'ar dariya tace "sosai ma,tunda bata da kowa yanzun sai mu ai ta zama ahalinmu"


Ya sake tab'e baki yana k'arewa d'akin kallo yace "Annie where's she.!?"

Tace "Na sa mata ruwa tayi wanka"

Yayi murmushi da gefen baki yace "Annie! Wai ita ce za tayi wankan..?"


Tace "Ehh! Mana wani abu ne.!?"

Yace "A'ah! Nothing"

Ta kalle shi tace "ka fad'a dai idan da matsala"
Ya girgiza mata kai,ta kalleshi sosai ta d'auke kai,ya zauna saman couch yana jira ta fito,kusan mintuna ashirin yana ta zaune yaji shiru ya kalli Annie data fita ta sake shigowa d'akin yana squeezing face,Annie ta kalleshi ta kalli k'ofar bathroom dake rufe har lokacin da mamaki a fuskarta tace "Wai har yanzun bata gama ba.!?"
Ya girgiza kai yace "Ehh",wucewa tayi wajen k'ofar toilet tayi knocking,mintuna biyu sannan ta bud'e ta shiga,tsaye ta ganta sai raba idanu take bata yi wankan ba,ta dunga mamakinta though she knew something was wrong with her brain,lek'owa tayi ta ganshi yana kallon k'ofar kamar yana tunani tayi ajiyar zuciya tace "Habibiiy! Ka jira mu zan mata wanka"
Ya jinjina kai ya tab'e baki kad'an daya tuna abunda ta yi masa,Annie ta koma tayi mata wanka ta wanke mata kanta da yayi datti sannan suka fito tana rik'e da hannunta,ya d'ago kansa a hankali ya kallesu,akan santala² k'afafunta idonsa ya fara sauka,ya dunga d'agowa a hankali har ya kai kan gashinta da yake jik'e,gabansa yayi mugun fad'uwa da suka had'a ido,ya d'auke kansa daga kanta ya kalli Annie a rikice yana mik'ewa tsaye yace "Annie good night"
Ta kalleshi tace "toh Allah ya bamu alkhairi" ya fita yana amsawa,ta bishi da kallo ganin ya fita kamar zata bishi,Annie dake rik'e da hannunta ta kaita saman stool ta zaunar sannan taje ta rufe k'ofa,ita ta yi mata kwalliya ta gyara mata gashinta tayi masa tufka d'aya ya sauka saman shoulder d'inta,ta bud'e closet ta ciro mata wani sleeping gown mara nauyi data siya da jimawa yayi mata kad'an tana ta ajiyarsa,taje ta sake bud'e d'ayan bedroom da take ajiye wasu kayan idan order su yazo,ta zab'a mata inner wears masu kyau,ta dawo ta ganta a tsaye sai kalle² take saboda data fita rufe k'ofa tayi shi yasa bata samu damar fita ba,tayi murmushi sannan ta kamata ta saka mata kayan ta kama hannunta ta kaita saman bed d'inta ta zaunar da ita,abinci taje kitchen ta had'o mata ta dawo,tana bata tana ci tana kallonta har ta k'oshi,Annie tayi mata murmushi sannan ta fita da kayan ta dawo,still a tsaye ta ganta kamar wacce ta had'iye spears (mashi) kama ta tayi ta suka zauna shiru,har to 11 tana zaune,da Annie ta gama abunda za tayi lokacin tana ta hamma cos a time d'in Nuraz ya sake dawowa abunda yazo yi dama kenan ganin da ya yi mata yasa shi fita d'azun babu shiri ya yi mata allurai suka yi sallama da Annie,kamata tayi a hankali ta kwantar da ita ta rufe ta saboda sanyi,ta musu deactivating light ta yi musu addu'ah ta tofa duka edges na d'akin sannan ta kwanta itama.


Da safe Annie ta fita kitchen around 7am ganin tana bacci har lokacin sai bata kulle door ba ta barshi a bud'e,suna ta aiki a kitchen ita da Bareerah,wajen 9am sun gama abunda suke ta dawo da niyyar ta tasheta tayi mata wanka,tana shigowa ta iske gurin data kwanta babu kowa,Annie ta girgiza kai ta juya,bedroom d'insa da take tunanin tana can ta nufa,dai² zata shiga ta jiyo muryarsa cikin fad'a² yana mata masifar zuwa masa d'aki ta tsaya masa akai yana bacci,Annie ta k'arasa da sauri ta kamo hannunta ko magana bata yi masa ba ta wuce da ita bedroom d'inta ta mata wanka ta shiryata cikin wasu English wears riga da skirt,sosai tayi kyau kayan sun zauna mata dai²,ta bata abinci sai da ta k'oshi sannan ta kyale ta,,bayan Nuraz ya fito ya yi break ya dubata sosai,a nan ya tabbatar tana da damuwa sai dai kuma lamarin nata ya shige masa duhu bcos ba hauka take da Allah ya d'ora mata ba kamar na mahaifiyarsa.
Ya kalli Annie da damuwa a fuskarsa yace "Annie matsalar nan fa ina tunanin bana hospital bane"
Annie tayi shiru tana kallonsa har ya gama fad'a mata kan matsalar,ta juya ta kalli inda take kwance tana bacci tace "Yanzun yaya za

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login