Showing 1 words to 3000 words out of 24835 words

Chapter 1 - ZUCIYAR MACE Book Complete By Sadiya Abdul.txt

26 Dec 2024

5655

[11/16, 6:31 PM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE*




BY
SADIYA ABDULRAZAƘ




*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATOIN*




PAGE 1




"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Ihu jama'a, a kawo ɗauki!".Hayaniya da ihun mutanen gidansu ya ta tashe ta daga baccin safenta mai ɗan karen daɗi, ta ja dogon tsaki tana jan yaƙunannen bargonta don ta rufe fuskarta, wai ko za ta samu damar rage tasirin hayaniyar, gidansu gidan yawa ne, mai cike da hargitsi, sun saba da hayagaga mara dalili, sai dai ta yanzu ta fara zargin da dalilin, duba da yadda yara da manya suke ihun babu ƙaƙƙaunatawa, "Yekuwa jama'a! Salamatu ta faɗa a rijiya, ku kawo mana ɗauki!." Maganar Mama Karime ta daskarar da duk wata na'ura ta jikinta ta dakata da aiki na wucin gadi, a hankali ta juyo da kanta ta yi wa idanunta matsuguni a gefen shimfiɗar Mamanta, da fatan Allah Ya sa ba ita Salamatun ake nufi ba, duk da ta san babu wata a gidan mai irin sunata, nan ta ga wayam babu kowa a kai, ta tashi a firgice daidai sanda Nusaiba ta bankaɗo ɗakin da take tana haki tana cewa"Ke Nuratu, tashi babarku ta faɗa a rijiya!".


Da wani irin hanzari ta fice a guje har sai da ta yi fatali da Nusaiban da ta kawo mita rahoto, maƙota har sun fara shigowa ana ta salati, ta yi tsalle da nufin faɗawa rijiyar don ta ceci Mama, ganin an tsaya kame-kamen yadda za a yi, kamar ba su ɗauki ran nata a bakin komai ba, Baba ban da salati ba ya yunƙurin taɓuka komai, aka cafe ta ana ba ta haƙuri, ta ɓarke da kuka tana kiran sunanta cikin fitar hayyaci, "Maaamaa!" Tsayin mintuna kafin Malam Haruna ya zo, wanda masani ne sosai a kan harkar haƙan rijiya, su biyu suka shiga, aka samu nasarar ciro ta, aka shimfiɗa tabarma aka zube ta aka shiga ba ta taimakon gaggawa, sai dai ta ƙi numfasawa, Baba ya ƙarasa ya kasa kunnensa a saitin zuciyarsa, sai ya ɗago ya ɗora hannu a ka yana cewa"Ƙalu inna lillahi wa inna ilaihir raji'un, Salamatu ta tafi, ta tafi ta bar mu, an yi mana mutuwa ni da Nuratu!". Nuratu ta yi kanta a guje, tana jijjigata haɗe da gunjin kuka, amma ko motsi ba ta yi ba.


Gabaɗaya gidan aka hau salati, wasu suna cewa ba ta mutu ba, a tafi asibiti, Baba ya hau faɗa yana cewa"To wane asibiti ana zaune ƙalau? Ni ƙaramin yaro ne da ban san mutuwa ba? Na binne uwata na binne ubana, na binne matata, na binne ƴaƴana huɗu sannan a ce ban san mutuwa ba, aradu Salame ko ba ta mutu ba na tabbata ba za ta tashi ba sai ta ƙarasa".


Nan aka yi masa ca, ana nuna masa muhimmancin zuwa asibitin, abin takaici Baba sai ya zaro aljihun rigarsa duka biyun yana kaɗewa yake cewa"To wai da shekaruna zan kai ta asibiti? Ga shi dai ko ƙarfanfana babu a aljihuna".


Ta sake fashewa da sabon kuka, nan wani maƙocinsu ya sunkuci Mama ya fice da ita, sannan Baba da sauran mutane suka mara masa baya, haka ita ma ta bi su ko ɗankwali babu a kanta, sai ƙanwarta ce ta cire hijjabin jikinta ta saka mata, ta bi su titi a guje, ta tari adaidaita sahu ta shiga, ya bi bayan nasu, a tare suka shiga asibitin ko ta kan kuɗin mai adaidaitan ba ta bi ba, shi ma bai tambaya ba ganin halin da take ciki.


Bayan jira na ɗan lokaci aka tabbatar musu da rasuwar Mama Salamatu, Nuratu ta zauna a ƙasa dirshan tana gursheƙen kuka, ana ta ba ta baki, don Mama Karime ma ta ƙaraso asibitin, nan aka ja lissafin kuɗin asibiti da na ɗaukar gawa, wanda Baba ya ce ba shi da shi, sai karo-karo aka yi aka ɗauki gawar zuwa gida, sai ta shiga ɗaki ta zauna ta zama kamar mutum-mutumi sai hawaye da ta kasa dakatar da su, da ƙyar ƴan'uwan Mama suka ja ta zuwa kan gawar bayan an gama yi mata sutura, suka ce ta yi mata addu'a, kuka ta fashe da shi, da ƙyar ta iya buɗe baki cikin in'ina ta ce"Ma...Mama, Allah Ya yi miki rahma, Allah, Allah Ya sa can ya fi nan". Sai ta rushe da kuka, wata zuciyar tana raya mata Mama ba ta farinciki da addu'ar nan tata, saboda ta mutu tana tsananin fushi da ita, da ƙyar aka ja ta a ka mayar gefe, tana kallo aka fice da gawar, zuciyarta na tururi tana yi wa mahaifiyarta kallon ƙarshe.


Ƙullin wainar siyarwar da Mama take yi, na yau sai ya zama na sadakar mutuwarta, Nuratu ta tuna jiya da daddare sanda take haɗawa, ko markaɗe da kanta ta kai, saboda tana fushi da ita, dama haka take yi idan ta yi mata laifi ba ta yarda ta taya ta aiki.


Zuwa azhar ƴan'uwa sun cika gida, har an gama kuka an shiga hada-hadar rabon abinci, wanda Alhaji Hashimu ne ya kawo, ƴan gidansu har da masu faɗa a kan abinci, yayin da Nuratu kuma yawun bakinta ma ya yi mata ɗaci. Mutuwa ta yi mata yankan ƙauna, Mama ta tafi ta bar ta a gaɓar da take ƙishi da yunwar kasancewa da ita, a lokacin da ta fi buƙatar taimakonta da samun kusanci da ita, ta rasu tana fushi da ita, ba ta tsaya ta fahimci uzurinta ba, ba ta yarda da hujjojinta ba, idan aka ce baƙin cikin abin da ta aikata ne ya yi silar mutuwarta ba za ta yi musu ba, domin kuwa tun shekaran jiya da ta sanar da ita ƙaddarar da ta faɗa mata take cikin tashin hankali da ɗimauta, tana yin komai ne da ƙarfin hali, sannan a yadda Mama Karime ta ba da labarin yadda ta faɗa rijiyar ta san ba ta cikin hayyacinta ne, sannan Mama da asuba take fara suyar waina, amma a yau ɗin har gari ya waye ƙullin yana ɗaki ba ta fara ba, ita kuma sai wani shegen bacci ne mai daɗi yau ya ɗauke ta, cikin bargon da take kwance zazzaɓi yana nuƙurƙusarta, ta kai hannu ta dafa mararta tana tunanin yadda zan yi idan abun ɓoye ya fito fili, da wane ido za ta kalli duniya idan ta fahimci da ciki a jikinta na watanni biyu? Mahaifiyarta ma ba ta fahimce ta ba ballantana kuma duniya? Sai ta saki siririn kuka, don zuwa lokacin muryarta ta dashe sosai.


Ƴan'uwan Mama da suke ɗakin sun yi iya yin su ta ci abinci ta ƙi, can bayan la'asar mata duk ana zazzaune, wasu suna shirin ɗora tuwon dare, sai ga Baba ya shigo, fuskar nan a dagule ya kalli Inna Asabe yayar Mama ya ce"Asabe yaya na ga ana shirin kunna wuta?"


Ta ce"E abincin dare za a ɗora".


Ya ce"Au! Wato kenan ku banza ta faɗi, kowa ya samu wajen fakewa ya ci abinci ko? Ɗan abincin sadakar da aka kawo mini don rage raɗaɗi tun da ba fita nema zan yi ba, a zage ni a gari a ce ban zauna karɓar gaisuwa ba, shi ne za ku saka abincin a gaba ku cinye, ku bar mu da tagumi ni da ƴar marainiyar Allah?"


Sai ya zo tsakiyar gidan ya ɗaga murya ya ce"Kowa ya buɗe kunnenaa da kyau ya ji ni! Daga yau an rufe zaman makoki, kowace mace ta shuri takalminta ta tafi gidanta, gaisuwa ce an yi na gode, amma kar wacce ta sake zuwa gidana daga yau!".


Mama Lami wacce ita ma matar Baba ce, ta taso tana cewa "Haba Malam..."


Ya ɗaga mata hannu yana faɗin"Kin ga Lami ki kiyaye ni, ni na gama magana!".


Sannan ya shiga ɗakin mai rasuwa inda aka ajiye kayan abincin ya dinga ɗibowa yana kai wa ɗakinsa, ya rufe da mukulli ya fice, nan mata aka dinga ƙananun maganganu, aka fara silalewa ɗaya bayan ɗaya.


Inna Asabe ta shigo ɗakin tana cewa"Kaico! Amma wallahi wannan Iro an yi mara mutunci, yanzu ban da zub da mutunci a gidan mutuwar ma sai ya nuna halinsa? A kan abinci zai hana zaman makoki?"


Mama Suwaiba ta ce"To ke za ki dinga ci da mutane idan kin ce su daina zuwa? Babu wanda bai san halin Iro ba, don haka wannan ba wani abun damuwa ba ne, ni kin ga tafiyata".


Ta kalli Nuratu ta ce"Nuratu ki yi haƙuri ki bar kuka haka, Allah Ya yi mata rahma Ya zama gatanki". Sai ta gyaɗa mata kai alamar ta ji.


Haka duk aka yoye aka tafi ana yi da Baba, ɗakin ya rage ita kaɗai, ta tuna jiya iyanzu tana kallon Mama zaune a cikin ɗakin, fuskarta cike da damuwa, sai ta fashe da kuka tana cewa"Allah Ya yi miki rahma Mama, amma kin bar baya da ƙura".


Kiran sallar magriba ce ta fito da ita daga ɗakin, har jiri take yi saboda yunwa, ta tarar da Baba ya fito daga banɗaki, yana gyara tazuge, ya ce"Yawwa ke Nuratu, ɗazu Alhaji Hashimu ya zo, duk shi ya kawo kayan abincin nan ma, ya ce anjima zai zo ya yi miki gaisuwa".


"To" Kawai ta ce, ta ɗauki buta ta fara alwala, tana tunanin da wane yaren za ta faɗawa Baba tana ɗauke da ciki a jikinta ya gane abin da take nufi?




*******


Kamar kullum tana idar da sallar asuba, ta fito tsakar gida, ta fara kiciniyar kunna wutar gawayi, shayi ta fara dafawa sannan ta ɗora farar taliya, ta zauna tana ta fifita wutar ta ji kukan Aiman ƙaramin ɗanta ɗan wata biyar ya farka, tsakanin kukan da ƙwalla kiran da mijinta ya yi mata ba ta ma tantance wanda ya riga wani ba"Ke Hasana! Hasana". Ta tafi da sauri, ta shiga ɗakin tana raira ƴar waƙarta"Aiman ya tashi, manya sun tashi".


"Ke dalla can kwashe shi ki fice mini!" Cewar mijin nata, ko a jikinta don inda sabo ta saba da halinsa na masifa, gabaɗaya shi kullum a zabure yake ba shi da lokacin nishaɗi tare da ita sai dai idan yana tare da yaransa ko kuma wayarsa, yaran da sai sun zama mutane yake fara son su, amma yaro indai ba ya tafiya ba ya magana to ba mutum ba ne a wajensa, ko kallo nai ishe shi ba, da safen nan idan tana can tana girki Aiman ya tashi, ta sha zuwa ta tarar ya dawo da shi falo, sauro suna ta cizonsa, idan kuma ta yi magana ya ƙure ta da zagi a gaban ƴaƴanta.


Haka ta goya yaron, ta tashi sauran yaran Salim da Amir ta shiga yi musu shirin makaranta, sanda ta kammala komai bakwai da rabi har ta yi, don sai ta dafa musu indomi wacce za su tafi da ita makaranta baya sun ci taliya a gida, sai lokacin Nura ya fito cikin shirinsa na fita, ya buga uban wanka ya sha wani yadi daga gani ma yau ya fara saka shi, ya kafa hula, kamar mutumin kirki, irin wankan da ya sace zuciyarta ya yaudare ta da daɗin bakin sama mata rayuwar soyayya mai cike da farinciki, sai ga shi ya kawo ta baƙin gidansa mai cike da ƙunci ya kulle, ba ta da wani amfani a idonsa sai na bautarsa shi da ƴaƴansa, suka karya a tare, ya ɗauki mukullin babur ɗinsa ya haɗa kan yaran za su fita, ta ce"Me za a dafa anjima? Babu kayan miya a gidan".


Ko kallonta bai yi ba, ballantana ta samu amsa, wannan yana ɗaya daga cikin halinsa wanda ta saba da shi, suka fice tana tunawa yaran addu'ar fita daga gida.


Da rana ta dafa shinkafa da wake, sauran yajin nata ma kaɗan ne, ga shi ba ta da ko sisi ballantana ta ƙara barkonon, ƙarfe ɗaya yake ɗakko yaran daga makaranta, sai ya ci abinci ya koma kasuwarsa, wacce babu nisa da gidan nasu, dab da yaran za su dawo ƙawarta Ramla ta zo, ta ce daga kasuwa take shi ne ta biyo, ta zubo mata abinci, suna ta fira cikin nishaɗi.


Tana jin ƙarar babur ɗinsa gabanta ya faɗi, don ba ta son ya shigo gidan tana da baƙi, don kar ya yi mata faɗa a gabansu har a san halin da take ciki, don ma dai ya san Ramla.


Ya shigo da sallama, suka amsa, Hasana ta yi masa sannu, ya amsa idonsa a kan Ramla, wacce take kicikinar mayar da hijjabinta, ya kalli abincin da yake gabanta ya kalli Hasana ya ce"Ke wai Hasana wace irin mace ce mai taurin kai?"


Sai ta sha jinin jikinta ta sunkuyar da kai ƙwalla har ta kawo idonta, ya ce"Sau nawa zan faɗa miki ki daina dafa mai da yaji a cikin gidan nan? Ta ya zan dinga yin cefane mai kyau kina nunawa duniya gidana babu rufin asiri? Nama ya ƙare ba za ki sanar da ni ba?"


Ita dai ta yi shiru cike da takaici, don rabon da ta ga nama tun na babbar sallah.


Ya kalli Ramla ya ce"Wannan ƙawar taki don Allah ki dinga yi mata faɗa, wai idan kana da shi ba ka ci ba me za ka yi?"


Ta ɗan yi murmushi ta ce"Gaskiya kam ba ta kyautawa".


Ya ce"Tsakani da Allah fa! A ce za ka yi baƙuwa ka dafa garau-garau, alhalin ba babu ba ce, Ina zuwa".


Sai ya fice.


Hasana ta sauke ajiyar zuciya, suka cigaba da taɓa fira, kafin ta tashi za ta tafi, ta rako ta tsakar gida, sai ga shi ya dawo da ledoji a hannunsa, ya ce"A'a Ramla kike ko wa? Ba dai tafiya za ki yi ba".


Ta ce"Tafiya zan yi baban Salim".


Sai ya miƙa mata ledojin ya ce"Ga wannan balangu ne da lemo, wallahi mai kaji bai fara gasawa ba, ba zai yiwu a zo gidana a ci garau-garau ba, alhalin Allah Ya hore mini".


Hasana ta san Ramla da kwaɗayi, ai kuwa babu musu ta karɓa har tana rusunawa, ta yi masa godiya.


Ya ce"Maman Salim bari na koma kasuwa, yau ba na jin yunwar ma".


Baƙinciki ya hana ta cewa komai, ta rufe ƙofar gidan, ta koma ta zauna tana jin zafi a zuciyarta, zuwa yanzu ta fara zargin Nura aljanun son mata gare shi, babu damar ta yi baƙuwa ya ƙyalla ido ya ganta sai ya ruɗe ya yi ta kaiwa da kawowa, yana siyayyar ƙarya wacce ita ba ya yi mata, ƙawayenta sun sha faɗa mata mijinta ya bi su gidansu yana son su daga haɗuwa a gidanta, wasu ma matan aure ne, sai dai idan ya bi su hanya su faɗa masa ba, shiyasa yanzu sam ba ta son ma ta yi baƙuwa mace indai ba ƴar'uwarta ta kusa ba ce, group ɗinta na makaranta duk ta fita saboda yadda ake yi mata habaici a fakaice kowa ya san mijinta na mamajo ne.




08028966015
[11/17, 9:28 AM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE*






BY
SADIYA ABDULRAZAƘ




*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation)




Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY




PAGE 2


Nura ya jima kafin ya dawo, sai da ta shiryar yara suka tafi islamiyya, sai ga shi ya shigo yana haɗe rai, Hasana da zuciyarta take a zafafe bayan ya zauna ta kalle shi ta ce"Baban Salim yanzu haka daga gidan su Ramla kake ko?"


Sai kuwa ya haɗe gira ya fara zabure-zaburen borin kunya yana cewa"Ko kuma uwarta ba! Wai ke Hasana me kika mayar da ni ne? Yanzu rainin naki na lura kullum gaba yake yi ba baya ba!".


Hasana ta ce"Ai na fi kowa sanin halinka shiyasa na faɗa, idan ba haka ba meye na siya mata balangu, bayan rabon mu da nama a gidan nan tun watandar sallah?"


Ya fara jinjina kai, ya ce"Laifina ne, wallahi laifiina ne, saboda na fitar da ke kunyar ƙawarki ko?"


Ta ce"Ka fitar da kanka dai, ko kuma na ce ka shigar da kanka, don na tabbata ko ba daga gidansu kake ba, to za ka je".


Ya ce"Ai ke ba ki da hankali, bai kamata ma na biye miki ba".


Ya juya zai fita, ta ce"Ka tsaya na kawo maka abincinka".


A fusace ya ce"Ba zan ci ba". Ya fice yana ta mita da borin kunya.


Ba ta wani damuwa ba, saboda Nura ya sabarwa da zuciyarta irin wannan ƙuncin, ta ci abinci ta yi wanka ta ɗauku wayarta, tana kunna data ta ga Ramla online, ta ɗaga mata hannu, ta ce"Ya kika je gida?"


Ramla ta ce"Lafiya ƙalau, na gode fa sosai, kin gan ni nan ina cin balanguna hankali kwance".


Hasana ta tura mata stikar dariya. Sannan ta ce"Yau kin samu ɗan rakiya ko?"


Ramla ta ce"Mijinki yana da kirki wallahi, kin ga har gida ya kawo ni fa, ku dai Allah Ya taimake ku, mu ga mu a gida ba karatun ba, ba auren ba, aure mai daɗi wai har faɗa ake miki don nama ya ƙare ba ki sanar ba" Ta haɗa maganar da emojim dariya da mamaki.


Hasana ta ce"Hmm! Ke dai Allah Ya ba ki na gari, auren wuri ba shi ne kwanciyar hankali ba, dace a gidan auren ko da an samu jinkiri shi ne".


Ramla ta ce"Hakane" Sai ta kashe datar, dama ta so ta san Nura ya kai ta har gidansu ne ko a hanya ya ajiye ta, tun da ta ji ya kai ta tana da tabbacin zai koma, sai dai za ta zubawa Ramla ido ta ga za ta kawo mata labari ko za ta karɓi mijin nata, tun da har ga shi tana yabonsa, sannan ta ƙosa da zaman gidan dama, da wannan tunanin ta kai yammaci, sai dab da magriba ta tashi ta dafa farar taliya, don har yanzu bai aiko mata kayan miyan ba. Ana idar da sallah ya shigo, ya ce ta kai masa ruwan wanka, bayan ya gama ya zo falo ya zauna,yana ta faman danna waya, ta kawo masa taliyar, ya buɗe ya yi tsaki, ya fara ci, duk rabin hankalinsa a kan waya yake, haka kawai ta zargi da Ramla yake chart, ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login