Showing 3001 words to 6000 words out of 24835 words
Chapter 2 - ZUCIYAR MACE Book Complete By Sadiya Abdul.txt
ɗauki tata wayar ta kunna data, sai ta ga Ramla ba ta online, ta sauke ajiyar zuciya, amma har lokacin tana fargaba, ta rasa ya za ta yi ya daina janyo mata abun kunya irin haka, ana fara sallar isha'i ya tashi zai fice, yana cewa Salim"Sai na dawo".
Salim ya ce"Daddy ina za ka tafi? Don Allah ka zauna yau kar ka fita".
Ya yi dariya yana ɗaga Amir sama ya ce"Ai dole na fita, idan na zauna a gidan me zan yi Salim? Zuwa zan yi na gyara wasu abubuwa".
Salim kuwa da surutu ya ce"Wani abu?"
Ya ce"Kai yaro ne Salim, ina zuwa kar ka yi bacci ka ji?"
Ya gyaɗa masa kai, Nura ya fice yana kiran waya, idan ya yi irin wannan fitar sai ya kai sha biyu har ƙarfe ɗaya, kullum sai ta yi bacci yake dawowa.
Zuwa takwas da rabi yaran sun yi bacci, ta yi musu shimfiɗa a falo, ta yi musu addu'a, sannan ta rufe falon ta shige ɗaki, ƙofar gidan dama kodayaushe a rufe take, sai dai idan ya dawo ya saka mukulli ya buɗe, dayake tana da nauyin bacci ba kullum ba take jin dawowar tasa ba.
Ta sauke Aiman daga bayanta ta kwantar, ta yi masa addu'a, sannan ita ma ta yi, babu jimawa bacci ya ɗauke ta, haka take yi kafin ƙarfe tara ta yi bacci, saboda babu ɗan fira.
Yayin da Hasana ta saki baki take sharara bacci, shi kuwa Nura yana fita masallaci ya tafi sallar isha'i, bayan an idar ya hau babur ɗinsa ya tafi gidan su wata Hafsa, wacce ya karɓi lambarta tun shekaran jiya da ta zo shagonsa siyan kayan kwalliya, tun a ranar ya so zuwa, amma yana da wasu alƙawuran, sai yau layi ya zo kanta, Ramla ma ya je ganin gidansu ne kawai amma sai zuwa jibi zai koma. Fira sosai suka yi da Hafsa, wacce bai ɓoye mata yana da mata da ƴaƴa uku ba, sai dai ya faɗa mata sam bai yi dacen mace ba, Hafsa ta ce"Ikon Allah, amma dai auren wuri ka yi, wallahi ban yi zaton kana da aure ba".
Ya yi wani murmushin ƙasaita ya ce"Wallahi da aurena, kawai dai tsabar tsafta ne da kula da kai, sannan kin san idan mutum yana cin guminsa yadda ya kamata ya ci mai kyau ya sha mai kyau, dole za a gan shi tsaf".
Hafsa ta ce"Hakane" Don ita ta tsani kishiya, ba za ta iya auren mai mata ba, ta yi soyayya da masu mata wajen su uku, duk mammaƙo gare su, ba sa ɓarin kuɗi saboda hidimar gidansu ma ta ishe su, sai dai shi wannan ta ji yana zancen yana cin mai kyau.
Nura ya ce"Wallahi Hafsa a hakan ma da kika ganni don ma dai ina da matsala ne a gidana, ban yi dace da mace ba, kin san ita rayuwa idan ka yi dacen mace ta gari wacce ta haɗa komai kamar dai ke ɗin nan, to fa har wata ƙiba kake yi".
Hafsa ta ce"Kuna samun matsala da ita kenan".
Ya ce"Idan kin ji matsala ɗaya kenan, matsaloli ne da yarinyar nan birjik wallahi, kin ga dai irin kayan kwalliyar da nake siyarwa, amma wallahi sai na yi wata ban ga hoda a fuskarta ba, kuma duk order da na yi sai na dara kai mata ta zaɓi kaya kafin na kasa a kasuwa, ɗinki duk wata sai na yi mata ita da yara, amma indai kin ga ta saka sabon kaya to fita za ta yi, nama a firji sai dai wani ya tarar da wani, amma idan ta kwaɓa girkin kare ma ba zai ci ba, gaskiya mata kuna da matsala, yawanci ku ne kuke saka mazanku ƙara aure".
Hafsa ta ce"Wasu matan dai, amma ni yaushe zan samu mijin da zai yi mini komai na ƙi faranta masa?"
Ya ce"To Allah Ya sa kakata ce ta yanke saƙa".
Ta ce"Hmm! Idan da gaske kake ba".
Ya ce"Kamar ya?"
Ta ce"To ai na ga haka kuke masu matar nan, yawancinku kuna zuwa wajen zance ne don ku rage dare ba don aure ba, sai an ce ku fito sai ka ga wani matarsa ta fi ƙarfinsa, wani kuma gidan nasa ma da ƙyar ake cin abinci sau uku a rana, ba shi da halin ƙara auren, ni fa shiyasa ban fiya sauraron mai mata ba".
Nura ya yi wata dariya ya ce"Baby Hafsa kenan, kin sanfa akwai maza, akwai muna maza, wallahi ni kam namiji ne a gidana, na fi ƙarfin gidana, sannan idan da yunwa a gidana a jikina za ki gani".
Hafsa ta ce"A jikin matarka dai, ko tana da matsalar gyara jikinta na san tana cin abinci ta ci ko ba daɗi".
Ya ce"To ni dai ki gwada ni ki gani, na tabbata ba za ki yi nadamar ɓata lokacinki ba".
Ta ce"Zan yi bincike dai".
Haka suka dinga fira, yana ta kushe Hasana, da ƙarairayi, don rabon davya ɗauki hoda ya ba ta kyauta har ta manta, ita yanzu sam babu kwalliyar ma a gabanta tun da ko ta yi ba ya ganin ƙoƙarinta ballantana ya yaba, sai dai idan ta yi wanka ta shafa hodar da man leɓe, don kanta ba dai don miji ba.
Sai ƙarfe goma ya bar wajen Hafsa, ya zarce majalisarsu ta bakin titi, ana ta fita sai sha biyu ya koma gida, ya buɗe ya shiga, ya saka sakata, ya tura ƙofar falon ya shiga, yana haska yaransa, ya gyara musu kwanciya, don ɗaya ya ɗorawa ɗaya ƙafa, sannan ya shiga ɗakin, ya canza kaya ya hau gadon, ya haska Hasana da take ta sharar bacci, Aiman a kusa da ita, ya taɓe baki ya kwanta, a yanzu ba shi da burin da ya wuce ya ƙara aure, yana buƙatar ƴar sawalwala wacce dare yana yi zai ji yana ɗokin dawowa gida su sha soyayya, babu ciki babu goyo babu yaran da za a jira su yi bacci.
*******
Ƙarfe takwas da rabi wayar Nuratu ta fara ƙara, ta duba ta ga lambar ce daga Saudiya, ta san Abdul ne mai kira, don yana aron wayar mutane ya kira ta idan ba ta hau online ba, saboda ba kasafai yake saka kati ba, Abdulmalik mutum ɗaya da take gani a matsayin sanyin idaniyarta bayan mahaifiyarta, ta san bai ji rasuwar da wuri ba shiyasa bai kira ta ba, ta ɗauki wayar da sallama, ya amsa, sannan ya ɗora da faɗin"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!".
Nan ta ji wani sabon rauni ya taso a zuciyarta, ta fara kuka, ya ce"Ashe Mama lokaci ya yi" Sai ta kasa magana.
Ya ce"Ki yi haƙuri Nuratu, duk mai rai mamaci ne dama, Allah da Ya ɗauke ta ya fi mu son ta..."
Cikin kuka ta ce"Yaya Abdul ina buƙatar Mama a rayuwata, ina buƙatar uwa, yanzu da wa zan zauna a wannan bahagon gidan namu mai cike da takaici kala-kala?"
Ya girgiza kai kamar tana ganinsa ya ce"A'a kar ki sake faɗar haka, Mama ba ta yi gaggawa ba, mu ma wataƙil yau ko gobe ne, duk mai rai gawa ne shi a tafe. Sannan Allah Yana sane da yanayin gidanku Ya ɗauke ta ɗin ya bar ki, sai mu bar hakan a matsayin wata jarabawar rayuwa Allah Ya ba mu ikon cinyewa".
Hawaye mai zafi suka fara tunkuɗo juna daga idonta, Yaya Abdul ɗinta ne kaɗai mai mai da damuwarta tasu su biyu, sai dai wannan ƙaddarar da ta afka a dare ɗaya ta dalilin inganta rayuwarsa, sai dai tana zargin hatta shi Abdul ɗin ba zai iya karɓarta ba, da wane idon za ta kalle shi idan ya gane tana da ciki? Ina zai saka kansa a ranar? Ta fi kowa sanin zafin kishin shi, shiyasa yake tsaye tsayin daka a kan ƙananun buƙatunta wanda ba su gagare shi ba, ko wannan tafiyar da ya yi dominta ne, yana can yana bauta don ya tara kuɗin aurensu, kuma ya samu jarin da zai riƙe su, don su yi rayuwa mai inganci.
Suna cikin waya ta ji muryar Baba yana ƙwalla mata kira, ta yi saurin cewa Abdul"Ina zuwa ka ga Baba yana kira".
Ya ce"To ki yi masa gaisuwa, anjima zan sake kira".
Kafin ta fito Baba har ya bankaɗo labulen yana cewa"Wai uwar me kike yi ne da kika share ni?"
Ta fito jiki ba ƙwari tana cewa "Gani nan Baba".
Ya ce"Ga Alhaji can a zaune, sai ki je ku tattauna".
Ta ce"To".
Ta bi bayan Baba, ta tarar da Alhaji Hashimu tsaye yana danna waya, ta tsaya tana kallon fuskarsa da wayar ta haska, babban mutum ne zai doshi shekara sittin, sati biyu kenan da haɗuwarsu, ya kawow malamin makarantarsu sadaƙar da yake kawowa duk wata, ya ganta, a ranar sai ga Malaminsu wato shuganan makarantar ya zo har gida wai an aiko shi, ya zo neman alfarma, ya faɗa mata Alhajin yana sonta, kuma matansa uku, nauyi da kunyar Malam Isma'il bai hana ta faɗa masa tana da wanda take so ba, don haka Malam ya samu Baba ya faɗa masa, a ranar Baba faɗa kamar zai ari baki, ya ce dole kuwa ta manta da kowa ta aure shi matuƙar da gaske yake, duk kuwa da kafin Abdulmalik ya bar ƙasar nan sai da iyayensa suka zo suka yi magana akan bayan shekara biyu zai dawo sai a yi auren, a lokacin Baba murna ya dinga yi, saboda yana ganin Abdul zai tara arziƙi kafin shekara biyun, amma bayan zuwan Alhaji Baba har yana cewa"Wane shirmen banza ne ki zauna jiran wanda ya tafi Saudiya? Ai sai ya shekara goma bai dawo ba, idan ya dawo ma ya ce kin tsofe ya samu wata ya aura, don haka ba za a yi wannan shashanci da ni ba".
Mama ta yi iya yinta don a bar zancen Alhaji Baba ya kafe, tijarar safe da ban ta dare da ban, har ƙarar Mama ya kai wajen yayyunta tana hurewa ƴarsa kunne, shi ne ta ce kawai Nuratu ta haƙura ta aure shi, to a nan ne fa ta sanar mata zancen cikin jikinta, wanda ta same shi silar taimakon Abdul.
08028966015
[11/18, 1:06 PM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE*
BY
SADIYA ABDULRAZAƘ
*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation)
https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY
PAGE 3
"Barka da fitowa". Muryar Alhaji Hashimu ta dawo da ita nutsuwarta.
Ta ce"Ina wuni".
Ya ce"Lafiya lau, sannu Nuratu ya haƙuri?"
Ta ce"Da godiya".
Ya ce"Allah Ya yi mata rahma Ya sa aljanna makoma, sai ki yi ta haƙuri kin ji ko?"
Ta amsa da amin, suka yi shiru na ɗan lokaci, kafin ya ce"Kin ci abinci dai ko?" Ta yi banza da shi, ya sake cewa"Me kike son ci? Kar damuwa ta saka ki zama da yunwa, sai ya haifar miki da wani ciwon, na zo miki da abinci ki daure ki ci".
Ya ƙarasa yana miƙa mata babbar ledar da take hannunsa, ba ta karɓa ba, kuma ba ta ce komai ba, sai hawaye da suke ta gudu a fuskarta. Ana haka sai ga sallamar baƙi gidan, suka wuce su a zauren bayan ta gaishe su, sarai ta gane Umma ce mahaifiyar Abdul, tare da abokiyar zamanta, sai ƙanwarsa, su ma kuma sun gane ta, don da fitila a hannunsu suka shigo zauren, gabanta ya dinga faɗuwa, saboda tana fargabar Abdul ya ji labarin an ganta da wani, ga shi mutanen da ba ta isa ta ce masa ƙarya suke yi mata ba ne suka ganta, duk hankalinta ya yi cikin gidan, ta ce masa"Zan shiga gida".
Ya ce"To Allah Ya ƙara afuwa, ga wannan ki karɓa ki ci, da kuɗi a ciki ko za ki yi wata buƙatar, sannan duk abin da kike buƙata don Allah ki sanar mini, babu abin da ba zan ba ki ba, Allah Ya ji ƙan Mama Ya sa ta huta".
Ta amsa da amin, ya ba ta ledar ta karɓa ta yi cikin gidan, ta samu su Umma a tabarmar da ke tsakar gida tare da su Mama Asabe, suna mai da yadda mutuwar ta kasance. Ta duƙa ta sake gaishe su, suka amsa suka yi mata gaisuwa cike da tausayawa, Mama Karime da ta ƙyalla idonta a kan ledar ta ce"Kina zaune ke kaɗai a ɗaki, sai mutuwar ta dawo miki sabuwa ai, ki wuce ɗakina ki kwanta, bari na aika a samo miki ko kunu ne".
Ta ce"To" Ta shiga ɗakin nata.
Sai Zainabu ƙanwar Abdul ta tashi ta bi bayanta, Khadija da Hannatu suna kwance a ɗakin, ta zauna tana ajiye ledar, Zainabu ma ta zauna ta miƙa mata ledar da ke ƙunshe a hijjabinta tana cewa"Yaya Abdul ya ce na kawo miki"
Sai ta ɗakko wayarta ta danna ta kunna mata voice, sai ga muryar Abdul ɗinta ta bayyana, daidai inda yake cewa"Nuratu ga saƙona nan, jikina ya ba ni ba ki ci komai ba wunin yau, na yi nisan da zan ba ki wata kulawar da ta dace, amma ga ƙanwata nan a madadina, idan a baki kike so sai ta ba ki, don Allah ki ci wani abun".
A nan maganar ta ƙare, Zainabu ta miƙa mata ledar, bayan ta ciro yougurt ta buɗe ta matso ta kai mata baki, Nuratu ta yi guntun murmushi ta ce"Wato Zainabu biye masa za ki yi ko?"
Tana dariya ta ce"To ai ni ƴar aike ce".
Nuratu ta karɓa ta fara sha, ta sha kusan rabin jarkar, daidai sanda su Umma suke cewa Zainabu ta fito su tafi, Nuratu ta ji cikina ya fara hautsinawa, yawu ya taru a bakinta, da sauri ta fita tsakar gida ta fara kwarara amai, suna ta yi mata sannu, Zainabu tana cewa daga shan yougurt, Mama Asabe ta ce"Ƙila don ta jima ba ta ci komai ba ne, sannu Nuratu kin ji" Ta gyaɗa kai, ta gyara wajen ta koma ɗaki, su kuma suka yi musu sallama suka tafi.
Tana shiga ta kwanta, a kan sallayar da take wajen, Mama Asabe ta shigo tana yi mata sannu, ta ɗauki yogurt ɗin tana cewa ke ma ai ba za ki sha abu mai sanyi ba yanzu, tun da ƙila rabonki da abinci tun jiya, ta ce da Kadija"Dije tashi ki siyo mata kunu, ko ruwan bunu a wajen Mati mai shayi".
Nuratu ta ce"Gara ruwan bunun Mama".
Khadija tana fita, Mama ta janyo ledar wajen Zainabu, ta ga wani yougurt ɗin ne, da lemuka biyu, sai shawarma guda biyu, ta janyo ta wajen Alhajin, ta fara cin karo da ƴan ɗari biyar biyar a dunƙule, ta faki idonta ta soke su a zani, ta duba sauran kayan, har da kayan shayi, da biredi da manyan biskit ga kuma kaza da lemo babba, ta jinjina kai ta ce"Lallai ana gatale ki Nuratu".
Nuratu saman ɗakin kawai take kallo, ta yi nisa a duniyar tunani, Mama ta ce"Wai ni kam dama babanki bai raba ki da Abdul ɗin nan ba?"
Nuratu ta ce"Mama ni fa wannan Alhajin dole sai dai ya haƙura".
Mama ta ce"Hmmm! Yaro man kaza, lallai kina da ƙarancin hankali Nuratu".
Ana kawo shayin Mama ta ɗakko kofi ta haɗa mata mai kauri, ta sha, sannan ta ci shawarma guda ɗaya, ta ba su sauran, kayan shayin da biskit kuma ta ɗauka ta tafi ɗakinsu, Mama tana cewa ta kwana a nan ta ce a'a.
Ta shiga ta zauna, kawai sai ta fara kuka, ga ta yau za ta kwana ita kaɗai babu Mama, wayarta ta yi ƙara, ta duba ta ga Abdul ne, ta ɗaga a sanyaye, ko gaisawa ba su yi ba ya ce"Nuratu wane ne wanda kuke tsaye ɗazu?"
Ta sauke numfashi tana lumshe ido, da tunanin ta inda za ta fara yi masa bayani.
Ya ce"Kar ki yi mini ƙarya".
Ta ce"Wani ne, sunan shi Alhaji Hashimu, yana sona ne, ya fara zuwa sati biyu da suka wuce..."
Ya katse ta da faɗin"Innalillahi wa inna ialaihi raji'un!" Sai ya kashe kiran ba tare da ya ce komai ba.
Ta bi wayar da kallo, ta so ya tsaya ta ƙarasa, ta yadda za su fahimci juna, dama ta sani za a yi hakan, ga shi ba ta da katin kiran wata ƙasar, sai ta kunna data, ta kuwa ganshi online, ta yi masa voice ta faɗa masa komai tun farkon haɗuwarsu, ya duba bai ba ta amsa ba, ta yi ta jira har ta gaji, ta kashe data, ta saka sakata a ɗakin ta kwanta, tana jin wani abu mai kama da tsoro tare da kewar mahaifiyarta, sai ta kasa baccin, sai hawaye da suka ƙi tsaya mata.
Haka ta yi bacci rabi da rabi, saboda kewar mahaifiyarta. Da asuba bayan ta idar da sallah ta kunna data, duk yawan saƙonnin da suke tururuwar shigowa na Abdul kawai ta kai hannu ta buɗe, "Ba zan fahimce ki ba Nuratu sai na kammala bincike a kanku. Fatana dai kar ki manta da alƙawarinmu, ke kaɗai ce macen da nake ƙauna da fatan aurenta duk duniya Nuratu, kar ki butulce mini". Abin da ya rubuto mata kenan, a maimakon ta ji daɗi irin yadda ta saba a yau sai zuciyarta ta yi rauni, ta fara hawaye.
Ta koma ta kwanta tana jin yadda gidan nasu ya kaure da hayaniya, da alama har kowa ya cigaba da sana'arsa kenan, kwana ɗaya bayan mutuwar mahaifiyarta, kodayake idan ba su cigaba da nema ba, waye zai ba su abin da za su ci?
Sai a lokacin ta ɗan samu bacci ya ɗauke ta sama-sama, Mama Karime ce ta shigo ta tashe ta, ta tashi zaune tana gaishe ta, Mama ta amsa tana cewa"Sannu Nuratu, kin karya?"
Ta girgiza mata kai alamar a'a. Mama ta ce"Fito ki karɓi koko da fanke ga shi na rage miki".
Ta ce"Idan da ruwan shayi dai zan karɓa". Ta tashi ta bi bayanta, tana jin yadda sanyi yake ratsa ta, saboda zazzaɓin da yake jikinta.
Ƴan'uwa da maƙota ɗaiɗai ana ta shigowa ana yi mata gaisuwa, daidai lokacin Abdul ya kira ta, ta faɗa masa zazzaɓi take yi, ya ce zai turo abokinsa ya ɗauke ta su tafi asibiti, ta ce a'a ya bar shi, ya ce to zai turo Isa ya duba ta, Isa shi ma abokinsa ne, yana da chamest a ƙasan layinsu, ta