Showing 15001 words to 18000 words out of 24835 words

Chapter 6 - ZUCIYAR MACE Book Complete By Sadiya Abdul.txt

26 Dec 2024

6007

bar zancen don kar abun ya yi wa Baba yawa, ya tausaya musu sosai, ya kuma gode Allah da aka gano hakan, bai aure ta ba ya sakawa matansa.


A ranar da daddare ya je ya kai kayan abinci da yawa, sannan ya kai wa Nuratu kayan shayi, da fruit, ya haɗa mata da kuɗi, ya zauna da Baba ya ce masa"Baba haƙiƙa na so na taimaki Nuratu ta hanyar aurenta, to kuma sai aka samu wata ƴar matsala wacce ba zai biyo na ƙara aure nan kusa ba, saboda haka ka yi haƙuri ni na janye zancen auren, idan ta samu miji kawai ka aurar da ita, sannan ina ba ka shawarar indai wannan yaron da ya yi mata abun ya amince zai aure ta, to kar ka ƙi, domin shi ne ya fi cancanta".


Baba jikinsa ya yi sanyi ƙalau, ya ce"Amma Alhaji wannan wace matsala ce?"


Ya ce"Matsalar iyali ce, na yi iya yina na ga abun ba zai yiwu ba, ka yi yadda na ba ka shawara kawai". Ya ɗakko dubu hamsin ya ba shi, ya ce ya ƙara a jarinsa don kula da iyali. Baba ya dinga godiya, har da ƙwallarsa, ya bi Alhaji da kallo cike da jajantawa Nuratu na asarar da ta yi.




08028966015
[11/23, 12:44 PM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE*






BY
SADIYA ABDULRAZAƘ




*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation)


https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY


PAGE 8




Baba yana shiga gida ya shiga ƙwala wa Nuratu kira, ta fito gabanta yana faɗuwa, ya ce"To yau dai burinki ya cika, Alhaji Hashimu ya fasa aurenki, sai ki je ki auri yaron da ba a san ranar dawowarsa ba ma".


Ta ji sanyi a ranta, ba ta ce komai ba, har ya gama faɗansa ya fice.


Tsawon sati ɗaya tana fama da Abdul ya ƙi sauraronta, sai dai ya duba saƙonta ya yi shiru babu amsa, har ta gaji ita ma ta ƙyale shi zuwa sanda zai huce, sai su sasanta. Wasu daga cikin ƴan'uwan Mama sun gane ta yi ɓarin ciki, saboda duk da Baba ya hana zaman makoki, suna zuwa kullum su ga Nuratu, su kuma taho mata da abinci, don haka ba ta ɓoye musu ba, saboda ta san dole zancen ya fita gari, ko ƴan gidansu za su iya fitarwa, ballantana kuma ƴan'uwan Abdul, ƙanwar Baba sai ta gyara mata jiki daidai gwargwado, bayan sun yi mata faɗa da nasiha.


Bayan kwana arba'in da mutuwar Mama, zuwa yanzu har ta fara sarewa da lamarin Abdul, domin kuwa har yau bai saurare ta ba, ta yi nacin da magiya iya iyawrta ta gaji, don haka ta zuba masa ido, a kwana arba'in ɗin nan ita kaɗai ta san halin da take ciki na ƙunci, kullum a ɗaki take wuni, don kunyar fita waje take yi, gani take kowa yana ganinta zai gane ta zubar da ciki, idan an yi abinci ana miƙo mata, wataran duk su biyun su ba ta, wataran mutum ɗaya ta ba ta, wannan duk albarkacin kayan abincin da Alhaji ya kawo ne, don a baya Baba bai damu da cefanen gidansa ba, sai dai kowacce mace ta yi sana'arta, ta ci da ƴaƴanta, shiyasa Mama ma ta kama sana'ar waina kafin rasuwarta, ga shi yanzu har an ɗora Khadija a kai, dama tare suka yi Candy da Nuratu, kuma babu maganar miji, ballantana cigaba da karatu.


A cikin satin da aka yi arba'in, sai ga Baba ya zo cikin gida da zancen gobe iyayen Abdul za su kawo sadaki a ɗaura aure, zuciyarta ta dinga dokawa, sai ta nemi farinciki ta rasa, ba ta taɓa hasashen aurenta da Abdul zai zo ta wannan yanayin ba. Matan na shi suka tambaye shi za a yi biki ko ita Nuratu za ta yi ƴar walima? Ya ce babu wani taron banza da za a yi, a wannan auren na larura, da an ɗaura aure a masallaci shikenan, shi babu wani gayyata da zai yi ma. Duk da haka sai da suka kira ƴan'uwan babarta da na Baban suka sanar da su, washegari misalin ƙarfe biyu na rana aka ɗaura auren Nuratu da Abdulmalik a kan sadaki naira dubu hamsin, duk da an ce babu taron sai da ƴan'uwa na kusa suka zo, ƴan'uwan babarta suka auno shinkafa kwano biyu aka dafa kowa ya ci, an yi sa'a Baba ya zo ya damƙa mata kuɗin sadakinta, ta ajiye a gefe tana kuka, yayar babarta ta ce"Kawowa za ki yi a adana miki, wannan uban naki tsaf zai biyo ya ce ki bada".


Wata ƴar'uwarta ta ce"Kamata ya yi a dinga juya su, ƙila zuwa sanda zai dawo ta tare su isa a siya mata katifa mai inganci". Duk suka yarda da shawarar.


Nan suka tambaye ta batun lefe,ta ce ita ma ba ta sani ba, suka hau faɗa suna cewa wannan ai rainin wayo ne, babu lefe kuma ya ba da sadaki dubu hamsin? Ai arahar ta yi yawa, ita dai ba ta ce komai ba, domin ta san ita ce ta ja komai, a ganinta Abdul ya yi mata halakci ma da ya yarda zai aure ta, ya kuma ɓatawa kansa suna a duniya, don haka ba ta da ta cewa, zuwa magriba kowa ya kama gabansa. Da daddare sai ga Baba ya shigo yana kiran Nuratu, ta zo ta tsuguna, ya ce"Ina kuɗin sadakin? Ai sai ki kawo gobe a siyo miki katifa".


Ta ce"Baba ai na za ta sai ya dawo".


Ya ce"Au dama nufinku auren kawai aka ɗaura, na siyar da akuya kuma za ta cigaba da cin dangata? To wallahi ba zai yiwu ba, ko dai ya kama miki haya, ko ki tafi can gidan iyayensa ki tare, ni dai tun da na aurar da ke, to ya zama dole na gani a ƙasa, me za ki zauna ki yi a gida, da aurenki? A'a ba za a yi wannan shashancin da ni ba!".


Nuratu jikinta ya yi sanyi, har ta fara hawaye, ta kuma kasa cewa komai.


Baba ya ce"Ni shiga ki fito mini da kuɗin, na kama gabana!".


A raunace ta ce"Ƴan'uwan Mama sun tafi da shi, su ma katifar za su siyo mini yau".


Sai kuwa Baba ya rafka salatin da har mutanen gidan suka fito, ya ce"Yanzu ni na haifi ƴar, babu shegen da ya san cinta da shanta, har ta kawo moro, a ce ni ban kai a yi shawara da ni ba a kan sarrafa sadakinta!? Saboda tsabar rainin hankali! To maza shige mu je ki karɓo su!".


Mama Karime ta ce"A'a Malam, wannnan fa ba wani abun tayar da jijiyar wuya ba ne, ni na tabbata mutanen nan ba za su cinye mata kuɗi ba".


Mama Asabe ta ce"Wannan gaskiya ne, kuma su ma suna da haƙƙi a kanta, bai kamata a ce don an ba su kuɗi ka je ka karɓo ba".


Ya ce"Cikinku nan akwai wacce ta siya mata wani abu na gudunmawa? Ko za ku bayar nan gaba? Ku fita harkar ƴata, babu ruwanku da tsarina!"


Ya kalli Nuratu"Ke wuce mu je!".


Dama da hijjabi a jikinta, sai ta wuce ya bi bayanta, suka tafi, suna zuwa ƙofar gidan ya tsaya, ta shiga a sanyaye, Mama tana ganinta ta ce"Nuratu! Lafiya kuwa cikin daren nan?"


Ta fara kuka ta faɗa mata yadda suka yi da Baba, ta ce"Ai dama na san ba zai bar wannan kuɗin ba, ai shikenan dole a bi yadda ya tsara, kunya ce dai za a sha ta daga baya".


Ta ɗakko kuɗin ta ba ta, tana cewa"Ki yi haƙuri da duk abin da za ki gani Nuratu".


Ta karɓa ta fita ta miƙa masa, sai da ya ƙirga su cif sannan ya saka a aljihu suka tafi, a hanya ma yana ta sababi yana cewa zuwa gobe ya ba su, dole su zo su san inda za ta tare.


Ta idar da sallar isha'i ta kasa tashi daga sallayar, gabaɗaya rayuwar ta yi mata zafi, ta rasa inda za ta saka ranta, a gaskiya ba ta son zaman gidansu Abdul, gabaɗaya ɗaki uku ne a gidan, na iyayen ɗaya, na Abdul da ƙannensa maza ɗaya, sai na ƙannensa mata, yanzu a ina za a saka ta kenan? Ba gara ma a bar ta a nan ɗakin babarta ba, idan ya zo ya dinga turo mata da kuɗin abinci. Da shi ya kamata ta yi shawara, amma ya ƙi sauraonta sam, ba ta da mafitar da ta wuce ta sake tuntuɓarsa, don haka ta ɗakko wayarta, ta kunna data, yawanci datarsa a kunne take, sai dai idan ya ji shigowar saƙo ya duba, ta same shi online, ta yi masa sallama, tare da stikar hawaye, ya duba bai ce komai ba, ta yi masa voice ta ce"Assalamu alaikum, Yaya ina wuni? Fatan kana cikin ƙoshin lafiya, a yau burin nan namu na tsawon lokaci ya cika, mun zama mallakin juna, sai dai kuma abun ya zo mana akasin hasashenmu, wannan yana rubuce cikin ƙaddararmu, ya kamata mu karɓe ta, Yaya tun da an cire cikin nan don Allah ka manta da komai, wannan ya zama tarihi, a tunanina soyayayyar da muke yi wa juna ta yi ginuwar da wannan ɗan saɓanin bai kai ya rushe ta ba, ina ƙaunarka har gobe angona".


Ya saurara bai ce komai ba.


Ta sake cewa"Yaya ya ka tsara bayan auren nan? Yanzu zan zauna a nan gidanmu ne, ko haya za ka kama mini?"


Sai ta ga ya fara typing bayan ya saurara, tana ta zumuɗin ganin me zai rubuto, sai ta ga ya ce"Ni na ba wa kura ajiyar nama? Kin san maza sannan kuma na kama miki haya? Mtwsss" Ya ƙarasa da tsaki.


Hawaye ya sakko mata, ta ce"Ko kowa na duniyar nan zai zarge ni, ban taɓa tunanin har da kai ba Yaya, tabbas na yarda a yanzu duniya ba ta da tabbas, na gode da komai, sannan zan ɗauki ƙaddarar zama da kai a duk yadda ka tsara zaman namu".


Sai ma ya kashe data ba tare da ya sake cewa komai ba, sabon kuka ya zo mata, ta rasa da wa kuma za ta yi shawara, wa zai saka Baba ya yarda ta yi zamanta a gidansu? Ta ya za ta fara zama a gidan su Abdul, bayan ko shi kansa bai damu da ita ba, ballantana ya tilasta wa ƴan'uwan shi kula da ita? Ta samu kanta da kiran lambar Yaya Kabir, ya ɗauka suka gaisa, ya ce"Amarya, dama ina da niyyar kiranki, ɗazu Baba ya ce an ɗaura".


Sai ta fara kuka ba tare da ta ba shi amsa ba.


Ya ce"Nuratu, akwai wata matsalar ne?"


Ta ce"E Yaya". Nan ta faɗa masa duk yadda Baba ya tsara, amma ba ta faɗa masa wulaƙancin da Abdul ɗin yake yi mata ba, ta ɗora da faɗin"Don Allah ka cewa Baba gara zamana a gidanmu, can gidan nasu ban ga inda za su ajiye ni ba, kuma ni ba zan iya zama gidan haya ni kaɗai ba".


Yaya Kabir ya ce"To zan yi masa magana in sha Allah! Ki daina damuwa".


Suna gama wayar kuwa ya kira Baba, yana jin wannan wata dama ce ta zo masa wacce zai cika muradin da ya daɗe a zuciyarsa, bayan sun gaisa da Baba ya tambaye shi, Nuratu ta tare? Baba ya ce"Ina fa? Babu ma mai zancen tarewar, ni dai zuwa gobe na ba su, ko ba su zo ba zan tura ta, ta tafi can gidan iyayen nashi".


Kabir ya ce"A'a Baba kar ka yi hakan, ni a ganina kamar Nuratu za ta takura a can ɗin, me zai hana ta zo nan gidana ta zauna kafin a tsayar da maganar yadda za a yi?"


Baba ya ce"To indai za ta je ni ai ba ni da wata damuwa, ta tattara ta tafi".


Ya ce"To zuwa gobe zan turo mata kuɗin mota sai ta taho, kamar za ta fi samun nutsuwa a nan ɗin". Suka yi sallama Baba yana ta godiya.


Sannan ya kira Nuratu, ya fala mata yadda suka yi da Baba, ta ce"Amma Yaya har tsawon wane lokaci zan zauna?"


Ya ce"Har sanda zai dawo ƙasar mana".


Ta ce"Amma Yaya babu takura kuwa?"


Ya ce"Wa za ki takurawa? Ni da nake ɗan'uwanki ko matata wacce tun tuni take sha'awar ki dawo gidanta da zama?" Ta yi shiru.


Ya ce"Babu wata matsala, sai dai ko idan kin fi son zaman can gidan nasu, don ban ga alamar Baba zai yarda ki cigaba da zama a nan ba, idan kuwa ya yarda to nan gaba abinci ma sai ya gagare ki, ki dai yi tunani, idan kin amince ki turo account na saka miki kuɗin mota, idan ba ki amince ba sai ki sanar mini, daga haka ya katse wayar.


Nuratu ta zauna shiru tana tunani, ta san matarsa tana da hal mai kyau da son mutane, sai dai kuma wannan fa dogon zama ne, tana tunanin anya kuwa abun zai ɗore ba za ta ƙosa da ita ba? A zuciyarta dai ta ji ta amince, amma a yanzu a ƙarƙashin ikon mijinta take, saboda haka dole ta shawarce shi, ko ma a ce ta nemi izininsa, don haka ta kunna data ta yi masa sallama, ta rubutu ta ce masa"Yaya ina ta magana ka ƙyale ni, Baba ne ta ce bai yarda na zauna a gida da aurena ba, to ni ma ban goyi bayan ka kama mini haya ba, ko don ka samu nutsuwa a zuciyarka, amma na san gidanku babu inda zan zauna, ba wai na raina ba ne, kawai ba zan ji daɗin zaman ba, tun da zan takurawa ƙannenka, to yanzu dai an ce na nemi izininka na koka gidan Yaya Kabir da zama, har zuwa lokacin da za ka dawo. Ka amince?"


"Ki je duk inda za ki je, sai dai ina tunasar da ke, ki ji tsoron Allah!" Amsar da ya ba ta kenan, sai ta tura masa godiya.


Daga nan ta kira yayar babarta a waya, ta sanar mata halin da ake ciki, ta ce mata indai ta ga ana neman kai da ita ta dawo gidan kawun Hadi ta yi zaman ta, shi yayan Mama ne, Nuratu ta ce babu damuwa za ta je ta gwada zaman ta gani, idan da takura za ta dawo, ta yi mata nasiha sosai a kan ta kama kanta ta riƙe mutuncinta, sannan ta mu'amalanci kowa cikin mutunci, ta dinga kamawa Nawwara aikin gidanta.


Suna gama wayar, ta turawa Yaya Kabir account lambar, nan take ya turo mata dubu goma, ta tura masa godiya. Kabir ya sauke ajiyar zuciya, yana jin wani kaso na nauyin da yake ɗauke da shi a zuciyarsa tun lokacin da ya ji Nuratu tana da ciki, ya ragu, ya ce"Yanzu za a fara yaƙin".






LITTAFIN ZUCIYAR MACE NA KUƊI NE A KAN NAIRA 500 KACAL, ZA KU IYA FARA BIYAN KUƊIN KARATUNKU DAGA YANZU TA NAN


8028966015
Sadiya Abdulrazaƙ opay bank


Shaidar biya ta nan
08028966015
[11/23, 12:45 PM] Sadiya Abdulrazak: *ZUCIYAR MACE*






BY
SADIYA ABDULRAZAƘ




*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS*
(Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation)


https://chat.whatsapp.com/F6SvzSmHfQfJmhV5NN5CDY
PAGE 9





GIDAN NURA




Zuwa yanzu Hasana ta saba da kwana ita kaɗai, ta yi nacin da za ta iya har ta gaji ta watsar, wataran haka za ta je ta ce masa ba ta da lafiya wai ko zai zo ya kwana a ɗakinta, amma bai taɓa yin hakan ba, sai dai ya ba kawo mata magani ya yi tafiyarsa, yanzu ko ta buga masa ƙofar ma ba ya buɗewa, washegari idan ta yi masa maganar sai ya ce shi ya yi bacci a lokacin, alhalin tana kallon shi ta windo. Daga baya sai take kunna datar ita ma, ta dinga tura masa stika ko ƙananun kalmomi irin su i love you, i miss you, sai ya duba ya yi banza da ita, wai ita a nufinta abin da ƴan'matan suke faɗa masa kenan, ita ma sai ta koya ta dinga yi, da haka har ta samu hankalinsa ya dawo kanta, ya ƙyale su, amma daga ƙarshe sai ya kafa mata dokar chart ɗin dare, ya ce duk inda aka idar da sallar isha'i ya ganta online sai ya hana ta chart ɗin ma gabaɗaya. Haka ta zuba masa ido yake ta shagalinsa, a tsawon kwanakin nan sau biyu ya kira ta ɗakin nasa, tana tunawa a farkon aurensu Nura ba ya taɓa kwana uku bai kira ta ba, amma yanzu sai ya yi sati uku har fiye da haka ma bai kira ta ba, to ita kanta ta san a yanzu babu wani gyara da take yi, saboda gani take asarar kuɗi ne, uwa-uba ma ba ta da kuɗin gyaran ne, a da bayan ya yo mata cefanen komai wataran haka kawai idan kasuwa ta yi kyau yakan ɗauki dubu ɗaya ko biyu ya ba ta, amma yanzu ta manta ma rabon da kyautar kuɗi ta shiga tsakaninsu, ko data Husainarta ce take saka mata, da kyautar katin waya.


Sannan zuwa yanzu ta yarda Ramla ita take yi wa habaici, ta gane da gaske mijinta yana soyayya da ita, abun yana yi mata ciwo sosai, indai wata ƙawarta za ta zo, ko kuma ƴan'uwanta to fa sai sun ba ta labarin Nura yana son wata wacce ta sani, ta rasa me yake damunsa, kamar wanda baki yake bibiyarsa. Daga baya ma Ramla sai ta saka a ka mayar da ita group ɗinsu na makaranta, ta yi habaici tana ba da labarin mijin wata ƙawarta ya maƙale mata, a ba ta shawara ya za ta yi da shi? Hasana sai dai ta yi shiru, don ta san ba laifinta ba ne, komai shi ne ya ja mata.Ta taɓa tambayarsa ina Ramla? Ya fara faɗa yana cewa"Wannan wace irin tambaya ce?"


Ta ce"To ai na ji labarin kun jone da ita, kuna soyayya, kuma ita da kanta ta faɗa mini".


Ya ce"To an yi ɗin, Hasana ki ɗauki mataki don Allah!".


Ta ce"Babu wani matakin da zan ɗauka, kawai dai zan ba ka shawara ne, ya kamata ka riƙe mutuncinka, ni ma kuma ka sama miji aji a cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login