Showing 33001 words to 36000 words out of 46437 words
Chapter 12 - MIJIN MARAINIYA Book Complete BY Fadeela Lamido.txt
kuma ai munfi kusa da ummi.
muryar abduljalal taji yana fadi safna tunanin me kike?
yaya tunanin kairat nakeyi mun barta ita kadai. yace karki damu idan muka gama cin amarcin mu zan dauko ta tadawo nan da zama gaba daya.
safna tace yaya ummi ko zata bari?
da sauri yace safna bar wannan maganar kisan tunanin me nakeyi .
gargiza kai tayi yasake cewa ina tunanin gashi kin haifi yaro me kama dani.
Safna tace nidai yariya nakeso.
nima inaso safna amman nafiso ki fara da namiji dan nasa mishi sunan daddy.
safna tace toh yaya in mace ce wani suna za,a sama ta. bude baki yayi ahankali yace na baki zafi.
safna ta sake cewa baza,a samata sunan ummi ba?
mikewa yayi yace taso muje muci abinci. safna ta lura yaya ko sunan ummi beson yaji ta Kira
suna cikin cin abin cin ne wayar abduljalal tayi kara ya dauka yasa akunne sa, yana fadin ina kwana anty.
anty bata amsa gai suwan shiba ta shiga yimai fada jalal me bilkusu tayi maka ka mareta har fuskarta ta kunbura haka?
anty zuwa tayi muna barci taita buga kofar, safna duk tabi ta firge
da sauri anty tace lallai jalal safnar yariyar goye ce da zakace wani an firgita ta, har yanzun dai kanan da bakar zuciyar ka , ita kuma safna tana kallo kamari yariyar muta ne ko, toh shike nan idan ka kuma ganin bilkisu agidan ka kasa bulala ka zaneta ba mari ba yana kukarin yin magana ta kashe wayar.
ture abincin yayi gefe ya sake kiran ta bata dauka ba mikewa yayi ya shige dakin sa.
safna binshi tayi da kallo domin bata fahimci abin da suke fada ba, ta fara kwashe kayan da suka bata takai kitchen saida ta wanke su sannan ta fito har lokacin jalal be fito ba, wuce wa tayi dakin ta tayi wanka kwalliya ta tsaya tayi sosai sannan ta nufi dakin jalal tana tura kofar tajita bude sallama tayi . jalal dake ciki ya amsa , tana saka kai ta ganshi tsaye ga dukkan alamu wanka yayi dan daga shi sai gajeran wando ga dogon wando a hannun sa yan kokarin sakawa.
safna naganin haka ta juya baya , murmushi jalal yayi ya aje wandon hannun shi ya iso gare ta jin shi kawai tayi ya rogumeta, ta baya yana kaimata kiss ta ko ina kamar zai hadiye ta, zuwa cen yadan dakata ya leko da kansa zuwa daidai fuskar ta dan jalal dogo ne sosai, yace har kinyi wanka, Allah yasa dai yauma ba haka kikayi wankan ba sabulu ba.
safna na rugume jikin jalal tace ai na samu wani sabulu acikin akwati na bashi da wari sosai.
jalal yace jinan safna in kinji abu namiki wari ki daina cewa yana wari cewa zakiyi bana son kamshin shi, dan kinsan Allah idan kika kara cewa ina wari saina fasa miki baki.
kallon shi tayi da mamaki tace yaya yanzo nan kai sai ka dake ni.
me zai hana na dake ki ,kiyi abin dokan kigani.
haba nina san bazaka dakeni ba in kuma zaka iya bismillah. jalal yace ai baki min komai ba yanzun.
dan tureshi tayi kadan ta rike hancin ta tace yaya jalal wari yake.
murmushi kawai yayi yace Ina binki bashin duka idan kika haihu zan miki.
a,a ni ban yadda ba yanzun nake so.
matso wa yayi ya riketa yace daidai ina zan daka.
safna cikin ta, tanuna tace ka daki nan
dariya jalal yayi yace lallai safna ke muguwa ce ,toh naki.
haka zaman su yaci gaba da kasan cewa
cikin farin ciki da kwanciyar hankali jalal yana nuna mata so daidai gwargwado har wani cika su kayi suka kara haske sukan leka gidan hajiya da daddare gidan ummi kuwa tunda suka tare ko jalal be leka ba bare safna, amman bata san cewa jalal baya zuwa ba gashi har sun kwashe sati uku da tarewa
alhaji kuwa tun washe garin ranar da ya raka jalal gidanshi yabar garin ko sallama bema ummi ba.
itako ummi ranar ta wayi gari daga ita sai kairat acikin gidan tayi tunanin wato jalal fushi yake da ita ko ganin shi baya bari tayi, alhaji kowa abakin kairat taji lbrin ta fiyar sa.
tun tana ganin abi kamar wasa ne har ta fara tsora ta.
kiran alhaji tayi har ta gaji be dauka ba, ta fara tunanin kiran jalal, amman kuma da kunya takira shi bayan tace mai bata son ganin shi, fadi tayi a fili me yake shirin faruwa dani ne, iyayena sunki karbata saboda halina dagin mijina basa sona saboda halina mijina dake takama dashi ya juyamin baya saboda yana kuka da halina, dana dake matukar so shima ya hakura ni ,afili take fadi kamar mahaukaciya zuwacen ta sake kuka haka taita yi babu me rarrashin ta
yau ummi ta tashi da matukar so taga jalal tuni ta lura jalal kwata kwata baya shigowa gidan a lissafin ta sati hudu kena da barin su gida wata zuciya tace kodai tare sukayi tafiyar da alhaji be.
mikewa tayi ta nufi dakin jalal tana tura kofar taji ta bude shiga ciki tayi me zata gani duk wani abu na amfanin jalal babu shi adakin, juyawa tayi gurin da aka aje a kwatunan safna nanma wayam babu komai.
rawar jiki ta fara tana haki take fadin na shiga uku, dakin ta tafada ta dauki gyale drive takira tace zoka kai ni gidan hajiya, rabota da gidan hajiya ta dade.
hajiya na zaune taga ummi tashigo kamar ankwato ta daga bakin kura
07014197556✍
[6:31PM, 12/17/2016] Fadeela lamido: 💘💍💍MIJIN MARAINIYA💍💍💘
Story
&
Written by
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed📝
96-99
Hajiya tsoro ne ya kama ta cikin kidima tace zaliha daga ina haka?
cikin kuka take fadi hajiya nazo neman gafararki dan Allah kiyafemin a yanzun nagane kure na , kuka take sosai.
hajiya tace alhamdulillahi dama haka ake so naji dadi da kika fahimce haka ni daman ban kullace kiba tunda ismail yakawo ki amatsayin matar sa dole nasoki balle kuma ga yara har biyu atsakani.
ummi tace nagode hajiya tana share hawaye.
hajiya tace amman zaliha bayan wannan akwai wani abun da yake damunki ko?
hajiya aini duniyar gaba daya ta cakude min iyayena suki karbata amatsayi yar su saboda lefin da na aikata , nan ta shiga bawa hajiya lbr hajiya tace ikon Allah abin mamaki baya karewa , toh zaliha banda abinki ina kika taba jin mutun yaki iyayen sa, toh ai dole kirasa kwanciyar hankali kadan ma kika gani, ai iyaye ba abin wasa bane, karki kara ai kata nakaman cin wannan, kinji ko?
In Allah ya yarda bazan kara ba nagode hajiya.
hajiya tace tashi kije kitchen ki debi abinci. hajiya bana jin yinwa naci abinci agida.
shiru sukayi nadan wani lokaci sannan hajiya ta kalli zaliha tace megidan fa yaushe zai dawo?
tofah hajiya ta sosa ma ummi inda yake mata kaikayi wani sabon hawaye ne yake fita a idonta tace hajiya aini rabon da naga alhaji sati hudu kenan sanda zaitafi ma ko sallama bemin ba kuma ko kiransa nayi baya dauka jalal ma basan inda yake ba, hawaye take sosai.
hajiya ta tausaya mata tace ya isa haka share hawayen ki, kikace rabon ki dashi sati hudu? eh
hajiya tace toh ai yadawo yayi kwana biyu ya koma, yau kwana biyar da tafiyar sa, kina nufin ba,a gida ya kwana ba kenan,toh ko kin masa wani abune?
shiro tayi tana ta share hawaye.
hajiya tace toh kidaina kuka ai tunda kukayi aure shekara kusan talatin ban taba jin kan kuba, mijiki nasonki yayi hakuri da ke duk da cewa yasan baki son yan uwan sa, ina ganin dai akwai abinda kika masa.
hajiya wayar ta dauka ta shiga daki number alhaji takira bayan ya dauka tace me matar ka ta maka katafi kabar ta babu ko sallama?
alhaji yace lallai zaliha bata da kunya gidan ki tazo shakaran ta nawa batazo gidan ki ba.
hajiya tace nidai ba wannan na tambaye kaba babu ruwanka , koma me tayi maka kayi hakuri bakaga inda ta fita haiyacin taba ta rame tayi baki kai ko kunya bakaji abokan ka su ganta ahaka, ai sai ace wahala take Sha.
hajaya kirabu da zaliha makirar mata ce, inda kisan halin ta bazaki yarda da tubanta ba, kice mata kawai ta wuce gida saina dawo.
nidai nace ka kira ta, ka kwatar mata da hankali abin ya mata yawa jalal ma kai ka hana shi zuwa gidan kenan, toh yanzun yaya kake son tayi.
alhaji yace shike nan hajiya zankirata.
ummi bata tafi gida ba har dare gashi kuma har yanzun alhaji be Kira taba sai gurin 7:30 taga kiran shi jiki na rawa ta dauka tafara gaida shi be amsa ba yace kina ina ?
cikin sauri tace ina gidan hajiya.
yace toh maza kitattra kayan ki kije gidan iyayen ki sai Nazo, kin shirya wani munafuncin ne dan kirabani da mahaifiya ta, toh baki isa ba, kinyi kadan,maza ki bar gidanan .
hajiya nadaga daki tajiwo ummi tasaka kuka me ban tausayi, fitowa tayi tace zaliha yaya akayi?
ummi ta gayawa hajiya abinda ya faru, ran hajiya ya baci afili tace Ismail kuma abida beyi da kuruciyar shi bane yanzon zaiyi, toh shikenan, ke kuma wannan ya isheki ishara dan yasan baki da gurin zuwa ne shiyasa yace kitafi .
ummi kuka take sosai tace yanzun hajiya yaya zanyi baffa yace idan nakara nufu gidan shi batare da nacika sharadin da yabani ba Allah ya isa.
hajiya nisawa tayi tace kizauna anan kafin yadawo muji abinda yake nufi kuma ko yakiraki awaya karki dauka, ke kima kashe wayar baki daya, dan naga alamar ran shii a bace yake dake kar yazo ya aikata abin da yafi haka . godiya tayima hajiya sosai suna zaune sunyi jugun jigun saiga kairat ta shigo tana kuka ummi shine kika tafi kika barni, kwantar da ita tayi akan ciyarta tana rarrashin ta.
ranar da ummi ta wayi gari agidan ummi, jalal kuma agidan sa ya tashi da matsanan cin mura da zazzabi tun yana daurewa har ya gaji yace safna zoki rufeni, zuwa tayi ta taba jikin shi taji zafi rau tace yaya katashine muje asibiti .
cikin rawar murya yace safna bazan iya tuki ba, bari sai anjima, rufeshi tayi ta fita zuwa kitchen domin karasa girkin da ta daura.
bayan ta gama takoma dakin tasame shi ya ture bargon sai faman kira sunan ummi yakeyi, ta dauka wasa yake saida ta karasa kusa dashi ta gane da gaske yake yi, dariya ta fara tace meye haka yaya saika ce kairat.
ai ko sauraran ta beyiba kiran ummi kawai yake yi zuwa cen ya jawo safna zama tayi agefen gadon ya dago kanshi ya daura aciyar ta sai faman sanbatu yake tun abin nabata dariya har yasoma bata tsoro zuwa cen taga ya fara kuka hawaye shabe shabe, da sauri ta sauke kan jalal daga jikinta karamin hajjab tasa tayi waje.
tana fitowa gate din gidan su gidan dake jikin nasu ta nufa dan taga me gidan suna yawan gaisawa da jalal, gate din gidan ta fara bugawa me gadi yazo ya bode yace lfy ?
safna ta rasa me zatace dan ko sunan mutumin bata sani ba, hango shi tayi rike da hannun matar sa zasu shiga mota hango safna da me gadin su ya hana su shiga karasowa gurin sukayi safna ta gaida mutumin tace ni makociyar kuce anan gidan nake ta nuna gidan su da ahannu ,miji nane bashi da lfy dan Allah ku taimaka min ku kaimu asibiti.
mutumin yace kece matar abduljalal dakai ta amsa, yace toh babu damuwa muje na dubashi, duk suka rankayo har matar sa, suna shiga falon suka tsaya, safna tace muje yana ciki, mijin yace a,a je kigaya mai idan zai iya fitowa yafito inkuma bazai iyaba saina shiga.
safna tana shiga tasame shi yadda tabar shi be daina surutun ba,tasan jalal batashi zaiyi ba tace yaya dan Allah kadaina magana kayi shiru gayinan za,aduba ka, bece komai ba sai kokari riketa yake taje tace wa mutumin yace kashiga.
safna bata koma ba zama tayi kusada matar, ta kalleta tace ki kwatar da hankalin ki in Allah ya yarda zai samu sauki , tasake cewa gashi muna kusa amman bamu sanjuna ba, ya sunanki?
waigowa tayi gefen ta tace sunana safna kefa? tace nikuma khadija, suna cikin haka mutumin ya fito yana murmushi yace madam karki damu murace tamai mugun kamu amman dazaran yasha magani zai samu sauki, yajuya barayi matar sa yace khadija zomuje nabaki magani ki kawo mata.
bayan kadija takawo magani tare da yi mata bayani ruwa ta dauka ta nufi dakin ta same shi kwance yadai rage surutun da yakeyi tace sannu yaya tashi kasha magani.
jalal ya bude baki cikin murya kalan na me sambatu yace aini bana shan magani safna ki tambayi ummi kiji.
kalon shi tayi da mamaki tace toh ai ko saika sha yama za,ayi kace wani baka shan magani saikace wani karami yaro.
nidai gaskiya katashi kawai kasha.
jalal ya sake cewa safna ki aje maganin nan ko ganin shi bana son yi.
kuka ta saka da karfi, tana fadi toh ni ya kake son nayi gashi bacci nakeji kaikuma sai faman sambatu kakeyi.
jalal yana kokari jan bargo ya rufe jikin shi saka makon zazzabin da ya dawo mishi yace zoki kwanta na bari.
ni sai kasha maganin zan kwata
yace toh naji kawo nasha. mika mishi tayi ya karba yasa abaki ya karbi kofin ruwa yakai bakin sa, kasa hadiyewa yayi ya fara sheka amai.
safna na rike dashi har ya gama hawaye nata zubo mata gashi itama ba kwari gareta ba haka ta kamashi takai shi bayi ta wanke mai jiki, dakinta ta wuce dashi sannan ta dawo ta gyara wajen tanayi ne tana kuka bayan takoma gurin jalal ta dauki wayar jalal takira alhaji.
yana dauka yace jalal, safna tasaka kuka tace daddy yaya bayi da lfy kuma yaki shan magani, saikiran sunan ummi yakeyi.
alhaji yace toh fah, tashin hankali, ciwon jalal wuya gare shi, to ya isa ki daina kukan, share hawayen ki, bari nusaiba zata zo yanzun
[8:23PM, 12/18/2016] Fadeela lamido: 💘💍💍MIJIN MARAINIYA💍💍💘
Story
&
Written
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed📝
100-102
Bayan ta aje wayar ta zauna ta zuba tagumi zuwa cen taga bacci ya dauki jalal itama kwanciya tayi nan da nan bacci ya dauke ta
lokacin da anty tazo gidan shiru ,tai ta sallama babu amsa zama tayi afalo ta shiga kiran wayar safna, aza bure ta tashi ta nufi wayar tasa akunnen ta, anty tace safna gani afalo, wani sanyi taji azuciyar ta ta nufi falo da sauri
bayan sun gaisa anty tace yaya yace jalal babu lfy ko, yana Ina
safna tace yana kwance ya samu bacci. jeki tasoshi yasha magani
anty ai baya iya tashi bakiga inda ya ragwar gwabe ba.
anty tace muje nagani
Suna shiga anty ta fara tashin jalal yabude ido yafara fadin ummi kaina zai fashi
cikin fada anty tace ya fashe din dan baka da lfy kuma duk sai kabi ka damu mutane da surutu saikace karamin yaro.
jalal yasake cewa safna kira min ummi. safna hannu tasa ta dauki wayar jalal anty nusaiba tace safna ajiye wayar nan baza akirata ba idan kamatsu katashi katafi da kan ka katon banza kawai, haka zaka haifi yara suga ubansu yana wannan tabaran
jalal yace toh naji tashi ki tafi gida. tace babu inda zani tashi zakayi kasha magani dan me shagwaba kan bata nan.
kalon safna yayi yamaida idon shi ya rufe daker anty ta shawo kan jalal yasha magani saida ta dama mai acukali.
bayan yasha be jima ba bacci ya kwasheshi .
washe gari jalal yatashi jikin shi yayi sauki sosai ya shiga bayi yayi al,wala yafito ya fara tashin safna tashi kiyi sallah.
mamaki ne ya kamata ta kasa daurewa tace yaya kaji sauki ne?
daure fuska yayi yace eh.
safna kwashewa tayi da dariya tana fadin Allah yakara sauki.
kara tamke fuska yayi yace to meye abun dariya kuma, juyawa yayi yana tafiya yana fadin bari nadawo zaki sani.
12:42 alhaji ya faka motar sa ahabar gidan jalal awaya yakira shi yace yajiki jalal yace yayi sauki daddy yaushe zaka dawo?
alhaji yace nadawo gani ma akofar gidan ka mikewa yayi cikin sauri ya