Showing 9001 words to 12000 words out of 46437 words

Chapter 4 - MIJIN MARAINIYA Book Complete BY Fadeela Lamido.txt

Advertisement

10 Jan 2025

9495

porum_
*kuna burgeni😘*


22-24


Akan wani dalili kika mare shi ?
ciki sanyi murya ummi tace alhj mun shirya zamu fita da safna har nashiga mota amman jalal yasa hannun shi yarike safna wai bazata shiga ba dan ya raina ni.
Jalal ya bude baki yace ai shigar da tayi ne be kamata ta fita dashi ba.


Cikin fada ummi tace kasan shigan da tayi be dace bane kai kasa hannun ka ka taba ta, ko muharramar kace ita.
shiru yayi ya juyar da kansa gefe



alhj yace to ya isa ke zaliha daga yau karki kara dukan jalal, inbanda ma abinki ya za,ai ki mareshi gaban safna, kanwar sace fah.

haushi ya bani alhj.
to shikenan kisan yanzun me zai faru, daga yau kar safna ta kara fita gidan nan inhar ba makaranta zata ba, ya juya yace jalal magana ta kare ko ?


shiru jalal yayi alhj ya sake cewa ko akwai saura ne halal


eh daddy, da sauri ummi ta harareshi dan haka yayi shiru.
sai da alhj yasake cewa ina jinka abduljalal meye kuma?


daddy kuma fa har samari zuwa gurin safna suke kuma ai karatu take.


alhaji dariya yayi yace abduljalal kai duk matsalan ka agurin safna take, toh jalal kodai son safna kake ne?


sai da ya kalli ummi san nan yace a,a.
itama ummi kallon sa take.


alhj yace ya hausan a,a jalal karfa kai kwauron baki wani yama kafa ya sake yin dariya, san nan yace ke zaliha kina fah shige mana hanci, kuma daga yau kar safna ta kara fita wajen wani.


haba alhj wai me yasa kakeyin haka jalal ne zai rinka juyamu agidan nan duk abinda ya fada kawai sai ka yan ke hukunci.


murmushi yayi yace naga kamar yana son ya fiki hankali ne, be jira me ummi zata ceba ya fita adakin itama bayansa tabi.




************


suna fita yaji zuciyar sa tamai fes tare da mamakin ya akai daddy ya dago shi ai lokaci beyi ba, ba yan zun ya kamata su sani ba sai ya samu soyayar safna neman zazzabin yayi ya rasa.


washe gari ana kiran sallan subahi ummi ta nufi dakin jalal yana kwance yana bacci ummi ta fara tashin shi yaro tashi kayi sallah, tashi yayi ya zauna, ummi tace yajiki ko asibiti zamu, da saurin sa yace naji sauki ummi nama warke.


bayan ya dawo daga masallaci be koma barci ba kamar yadda yake yi ada sai ya fara shirye shiyen fita kananan kaya ya saka yayi kyau matuka ya fito falo ya zauna babu kowa afalon ya nan zaune safna ta fito da gudu bata san cewa da mutun afalon ba taci karo da kafar jalal har ta fadin kasa kara ta sake dan taji zafi sosai.


da sauri jalal yamike yazo gaban ta ya tsuguna yace
sorry safna kawo na duba miki.
cikin kuka tace bana so bakai bane kasamin kafa, badu baki yayi cikin mamki yace yazanyi nasa miki kafa bake kika fito da gudu ba, be jira me zata ceba ya kama kafar ya matsa, fashewa tayi da kuka sai da su ummi da alhj suka fito suna fadin lfy.


ganin jalal sukayi rike da kafar safna itoko kuka take cikin daga murya ummi tace me ya faru?
Jalal yace faduwa tayi ina tunani kamar buguwa tayi .
ummi tace alhj wai wannan ne kake cewa yana da hankali ji inda ya ke taba ta .
mikewa yayi yana fadin ummi wani irin magana kikeyi, safna tashi muje asibiti


ummi bata so jalal yakai safna asibiti ba, domin bata son sultan yagan su tare dan suyi da hajiya baturiya yau zasu turo mata makudan kudi, tayiwa safna sayayya duk da cewa hajiya baturiya tasan halin danta ba aure ne agaban saba, amman duk yarinyar da ya nuna yana so sai taita kashe kudi dan ta faran ta mai rai.


Jalal kuwa tundaga ranar ya kasa ya tsare safna bata fita ko ina dan ummi na tsoron mijinta kwarai.
jalal ko jan safna yake ajiki sosai harta fara sakin jiki dashi kullum daddare zai aika kairat takira safna suyi ta hira suna dariya.


ummi na kwance adakin ta taji sai dariyar jalal da safna take ji ta daga kai ta kalli agogo 11:38 gaban ta ya fadi karfa ace jallal soyayya yake da yarinyar nan wani bangare na zuciyar ta nacewa ai kwanakin baya baban sa ya tambaye shi yace a,a to amma kuma wannan wani irin sabon salon ne, koma dai menene bazata taba bari jalal ya aure safna ba, yarinyar da sultan yayi soyayya da ita kilama yanzun tana dauke da cuta da wannan tunani ta zabura, tana fadi baza ta sabu ba


cikin sauri ta fito jalal naganin ta yace ummi bakiyi bacci ba.
eh banyi ba, tashi ka wuce daki tun daga ranar ummi ta hana safna fitowa hira jalal na zuwa falo saidai yaga ummi har tsawo sati daya besa safna a idon saba hankalin jalal ya tashi, itama safna kewan jalal take sosai.
washe gari da safe jalal ya fito cikin shirin shi na tafiya office bayan ya gaida ummi yamike ya nufe dakin safna, ummi ta kirashi ya dawo ina kuma zaka, inace office zaka tafi?
eh fita zanyi amman ina son naga safna kafin na fita.
Me zaka mata?
ummi na dade bansa ta a idona na ba fah ,ganinta kawai zanyi na wuce
wai yaro ni zaka munafunta karka mance kamin alkawarin bazaka aure safna ba inma ka fara tunanin aure ne sai kaje gida yayata ka auri yarta aliya dan tun tana karamar ta take sonka.
toh ummi naji munyi waya da daddy yace yau zai dawo inya dawo sai muyi maganar
adawo lfy, jalal yasake cewa ummi naje naganta kona minti biyu ne?
Kiri kiri ummi ta hana haka ya tafi jiki babu kwari


yamma likis jalal ya nufu gida yana shiga falon yaje jikin alhaji ya kwanta ummi bata gurin sai safna da kairat dan alhaji fira yake sosai da su safna ta juya takalli jalal taga yayi dare dare jikin daddy ta kwashe da dariya tace daddy kace ya daina hawa maka jiki karya karya ka.
daddy ma dariya yayi yace safna ai ke bakiga komi ba sai in beda lafiya zakiga har kuka yakeyi.
Kairat da safna sukara saka dariya.
jalal yatashi ya zauna yakali safna yaga sai dariya take yace ke ya isheki, daddy kaga zakasa suraina ni.
suna cikin haka ummi ta fito tana fadin ai jalal ya girma ne besan ya girma ba dazun nace mai yaje gurin aliya su daidai ta.
alhj yace wacce aliya yar wajan Rabi?
eh ita kuwa ashe baka manta suba.
au yanzun kuma kintuna dasu, inace zuwan su gidan nan nawa kina musu korar kare, to waima bari na tambaye ki, kisan inda su baffa suke yanzun,


ummi mikewa tayi zata bar wajan, alhaji yace dan dakata zaliha na samar wa jalal yarinyar da zai aura safna ma na mata miji.
Jalal zabura yayi yamike ya rike kafan daddy yace daddy karka min haka dan Allah 😭😭
[9:11PM, 11/29/2016] Fadeela lamido: 💘💍💍MIJIN MARAINIYA💍💍💘




Story
&
Written by
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed📝




25-27


Alhaji ya kalli jalal yace jalal ko kana da wacce kake so ne?
jalal ya bude baki zai yi magana ummi tace babu wata wace yake so alhaji haka yayi daidai.


safna mike wa tayi tana kuka ta shige dakin su, alhj yabi ta da kallo, ya juyo ya kalli jalal dake tsugune agaban sa, yace jalal in kana da magana kayi mana.
amman jalal da zaran ya daga kai zai yi magana sai ya kalli ummi ya dukar da Kai.
alhaji ya lura da haka yace jalal tashi ka zauna an jima kasame ni dakina sai muyi magana.


Jiki babu kwari jalal ya mike be zauna afalon ba dakin shi ya shiga.
ummi ko abin nema ya samu dawowa tayi ta zauna alhaji a ina kasamo wa jalal yarinya?
Yar wani amini na ce yarinyar akwai hankali idai mukai sa,a jalal na santa toh gaskiya munyi dacen sirika.
ai alhaji ba biye musu zakayi ba daga shi har safna.
a,a zaliha ai ko zamanin mu ba,amana auren dole ba bare yanxun, kina ganin jalal aka hadashi da yarinyar da baya so akwai zaman lfy ne, ai gara ma safna ina ganin ko bata so zata zauna dan naga yarinyar akwai hankali, amman jalal ai rikitatce ne.

amman alhaji gaski indai zaka dauki shawara ta karka saurari kowa acikin su.
alhji saida ya kaikaice yace zaliha ban hankalinki, ina son kicire hannuki cikin wannan maganar, ni akwai abinda na shirya kibarni dasu in nagama magana dasu zan gaya miki.


amman dai alhaji bakayi min adalci ba, in ba azayi shawara daniba akan auran safna ai kayi dani akan na jalal, saboda ina da hakki akansa kuma nina san zafin sa.
cikin fada da hargagi alhaji yace nikuma bansan zafinsa ba saboda roroshi nayi ko?
a,a nidai ban ce ba gadai rorarriyar ce wacce ba,asan asalinta ba, wlh alhaji idai kana son naci gaba da zama gidan nan sai safna ta bar gidan nan, yau din nan.


toh dama dai akwai wani abu azuciyar ki akan safna meta miki, me yakawo maganar safna toh safna bazata bar gidan nan ba in kinga zaki tafi kitafi inzaki zauna ki zauna wannan ruwan ki, baki isa ki juya ni agidan nan ba, dan kinga inasonki yasa kikemin abinda kikaga dama, gashi ina ji ina gani yan uwana basa zuwa gidana saboda sungaji da bakin halin ki.



*******




ummi cikin zafin zuciya ta mike to alhaji nagode tunda idon ka ya rufe akan tsintaciyar mage zakamin rashin mutunci
alhaji ma zafi ya dauka yana magana da karfi ai bakiga rashin mutunci ba sai kinci gaba da mayar min magana zaki gane koni Waye.
Suna cikin haka jalal ya shigo yana share hawaye yace daddy dan Allah kuyi hakuri ku bari.
alhaji kunyace ta kamashi ya manta yaran suna cikin gidan, yace bakomai jalal jeka abin ka, kasa tafiya yayi ya nemi guri ya zauna dan haka alhaji ya shige dakinsa, ummi ma tashi tayi ta shige nata dakin.


tun daga ranar gidan ya rikice kowa zuciya babu dadi ana cikin haka alhaji ya gama kwanakin sa ya koma, safna ko duk abinda yafaru ta sani har azuciyar ta take tunanin itako me tama ummi ta tsane ta, jalal kuwa jira yake yaga daddyn sa sun shirya da ummi ya gaya masa shifa safna yake so.


wata rana ummi na zaune afalo saiga wata kawarta tazo ummi ta mike suka rungumi juna janta tayi suka zauna ummi tace madina kinga yadda kika koma kowa.
dafa ummi tayi tace ke kowa ina gidan mijina hankalina kwance bani da matsalan komi, ummi tariya tayi tace hmm madina kenan, madina kar kacewa tayi tace akwai matsala ne zaliha?
ummi bata boyewa madina komi ba, har rikicin su da alhaji.
madina fada ta farawa ummi ke ko sai kace wata karamar yarinya meye naki na fada da miji, baki iya kissa bane har zaki zauna kina bata ran ki, shima jalal ai be kamata ki nuna mai baki son yariyar ba tunda kinyi sake ya fara sonta, yanzun kina nuna baki sonta sai ya juya miki baya , madina ta ciza yatsa Allah baya ba me wuka nama da nice da tuni na wargaza su, haka madina taita ma ummi fanfu da shawar wari iri iri , madina batabar gidan ba saida tasa ummi ta kira alhaji tabashi hakuri.
alhaji yaji dadi sosai dan bashi da roko kuma yana son matar sa, bayan kwana uku alhaji ya dawo, tabbas yaga canji agurin ummi iri iri , da daddare ummi takaiwa alhaji abincin sa har dakinsa suna cikin cin abinci jalal ya buga kofar alhaji yayi mai umarni ya shigo ganin ummi a dakin abin yabashi mama yanai mi guri daga gefe ya zauna, alhaji ya kalleshi yayi murmushi yace zaliha sai naga kamar jalal ya rame, ummi kallon jalal kawai tayi yake dan tasan kome ke damun sa.
Jalal yace daddy nazone muyi magana ba kwanaki kace zamuyi magana ba?
eh hakane jalal maganar auren ku ko?
jalal bece komi ba ya kalli ummi yace daddy ko mubari sai gobe ne?
a,a ke zaliha bamu guri zamuyi magana.
dariya tayi tace haba jalal yanzun nice bazaka iya magana gaba na ba, kuyi maganarku babu ruwana nina kosa ma naji wacece sirikar tawa.
alhaji yaji dadin maganar ummi dan haka yace jalal wacce yariyar kake so?
jalal ya dokar dakai yace safna.
alhaji daure fuska yayi yace jalal lokaci ya kure nariga na bada safna , saida na tambaye ka da farko kace basanta kake ba.
[7:29PM, 11/30/2016] Fadeela lamido: 💘💍💍MIJIN MARAINIYA💍💍💘





Story
&
Written
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed📝






28-34


Dagowa yayi da sauri ya kalli daddy yaga daddy ko ajikin shi, abincin shi ma yaci gaba daci, ya mayar da kanshi kasa,
cikin murna ummi tace jalal kayi kuskure da kasani ka fada da wuri gashi yan zun kama kan ka.
ummi lokaci fa be kure ba sai dai in kun zabi wani akaina, ya miki zai fita alhaji yace kashirya anjima kaje kaga yarinyar, bece komi ba ya fata adakin.



yana fita alhaji yayi dariya yace zaliha kifara tanadi dan baza,a sa da yawa ba, cikin murna zaliha tace ai alhaji shiri zanyi sosai yara biyu fah, jalal yana barin dakin daddyn sa, dakin safna ya shiga ya same ta zaune tayi kuka idonta duk sun kunbura, tana ganin shi ta durkusar dakai, jalal yaje daf da ita ya zauna safna kuka kikayi har idon ki suka kunbura haka , me yake damunki ko kema baki son auren ne?
shiru tayi ta kasa magana bazata iya gayawa jalal cewa shitake soba itama kanta tana ganin lefin zuciyar ta datake son wadda yafi karfinta, jalal ne ya katseta safna nifah bazan bari amin auren dole ba, safana zan tambaye ki amman ina son kimin alkawarin zaki gaya min gaskiya tsakanin ki da Allah .


me zai hana yaya jalal indai na sani zan fadama ka.
safna tsakani da Allah babu wani da kika taba jin kina son ki aura.
hawaye ne suka gangaro mata dan bata zaci wannan tambayar ba ,tace akwai.
jalal yace waye wannan safna?
yaya jalal mubar wannan maganar ai kai ma baka fadamin yarinyar da kake so ba.
Safna ni bani da budurwa saidai ko zakimin hanyar kawar ki sai na aura. tace to aigashin nan daddy yasamar maka.
shi ko jalal so yake yayiwa safna wayau yaji ra,ayinta kuma ya rasa tayaya zai fara kuma yana tsuron karya fada tace bata sonshi, dago kan shi yayi ya kalli safna yace,
ni bana so ta gurin daddy ta gurinki nake so.
wai kai yaya dan Allah da gaske babu wacce kake so?
jalal yace gaskiya akwai safna amman tsoron gayamata nakeji kartace bata sona.
safna mantawa tayi dawa take magana tace , kai👉🏻 yaya jalal wacece zata kalleka tace bata so.
cikin dauki yace da gaske safna,saboda me kikace haka.
yaya wlh babu wacce zata ce bata soka komai kyanta komai kudin gidan su sai dai kawai inbata samu ba, kai baka san ka hadu ba ne, wlh yaya kai kyakyawa ne kana da kyau sosai.
dadi sosai jalal yaji ya kashe murya yace toh safna ko zaki taimaka ne ki aure ni.
Sai alokacin safna tatuna tayi subutar baki ciki tashin hankali ta mike zata fita tana fadin mezaka ci dani?
da sauri jalal yamike ya rike safna yace karki kara cewa haka safna, na dade Ina sonki Ina tunani karkice baki so nane shiyasa ban gaya miki ba,
fashewa tayi da kuka tace me zakayi Dani rorarriya mara dangi bani da kowa fah jalal , kaikuwa dan gata ne ummi da daddy suna matukar sonka.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login