Showing 42001 words to 45000 words out of 46437 words

Chapter 15 - MIJIN MARAINIYA Book Complete BY Fadeela Lamido.txt

Advertisement

10 Jan 2025

9502

baya rubewa ka yanke kayar , safna yanzon zaliha ta gane kuran ta ya kamata ki yafe mata, tana cikin wani hali ki taimaka mata ta samu ta daidaita da iyayan ta, saboda ayanzon ke da baki da iyayen kin fita kwanciyar hankali dan kin rabo dasu lfy , itako ga iyayen tana kallon su amman ba dama taje gurin su, sabo da suna fushi da ita, toh dan Allah kiyi hakuri ki yafe mata, yanzon anriga an zama daya, ban da matsayin ta na yar mahaifiyar ki, kuma ga jikokin ta nan agaban ki, dan Allah mu yafi juna kwata kwata duniyar ma guda nawa take.
jikin safna yayi sanyi tace shikenan hajiya amma ni abin da yake bani haushi yaya za,ayi mutun ya manta da dan sa.
hajiya tace bar wannan maganan safna kandara ce haka Allah ya so.
tace dama hakane sai mutun yayi abu da gangan yace wai kaddara ce.
hajiya tace safna bar wannan maganan tashi kije kibawa jalal hakuri dan naga yayi fushi sosai .
suna fitowa suka samu anty nusaiba tana rarrashin jalal yana zaune idon shi ja wur kallon safna yayi ya girgiza kai itama kallon shi tayi ta neme guri ta zauna tayi shiru.
anty nusaiba ciki ta shiga hajiya ma barin gurin tayi aka barsu su biyu, cikin sauri jalal ya mike zai fita safna ta tashi ta riko rigar sa, kallonta yayi yaga tayi kasa dakai
bece mata komai ba, ahaka suka tsaya safna na rike da rigar jalal har tsayon minti 15 ba wanda yace wa kowa komai




07014197556
[6:58AM, 12/27/2016] Fadeela lamido: 💘💍💍MIJIN MARAINIYA💍💍💘






Story
&
Written by
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed📝




120-122


Gani yayi bata da niyar magana dan haka ya zame rigar shi yayi gaba.
safna naganin ya wuce ta fara kuka, sai da ta gaji da tsayowa ta wuce daki, ta shiga ta samu jarirain sai kuka suke, cikin tausayawa ta dauke su ta sasu acinyar ta.
tana cikin haka taji muryan alhaji da ummi suna gaida hajiya, bayan yaran sun sha nono ta kwantar dasu tamike dan gai da daddy sai da ta saka hajjabi sannan ta fito.
alhaji naganin ta ya washe baki , gwaiwan ta tasa akasa ta gaida shi ya amsa, ta juya barayin ummi kanta akasa ta gaida ta, amsawa tayi cikin farin cikin .
safna mikewa tayi zata bar wajan alhaji ya dakatar da ita.
ahaji yace wata magana nake son muyi me mahimmanci hajiya kisa mana baki dan naga safna har yanzon bata huce ba,
hajiya gyara zama tayi.
alhaji yace yazon daga gidan baffa muke nashiga ni kadai na mai bayani abin da ke faruwa amman kwata kwata yaki saurara ta wai mun shirya karya ne nida zaliha daga karshe cewa yayi indai da gaske ne , toh nakawo mai yarinyar.
alhaji na kaiwa nan yayi shiru
hajiya tace toh amman da naso abari ayi suna tukun, shiru suka yi na dan wani lokaci zawacen hajiya tace, safna tashi ki shirya.
mikewa tayi cikin daure fuska ta shiga daki ,bata jimaba ta fito ,ummi ce tabita da kallo taga bata fito da yaran ba, bata ce komai ba ta mike ta shiga ta kwaso yaran ta fito ganin inda safna ta daure fuska yasa hajiya ta mike tana fadin bari na dauko gyale na, naraka ku.
bayan sun shiga mota hajiya tace ina jalal ya kamata ace tafiyar nan dashi akayi ta.
alhaji yace kwarai kuwa bari na kira shi, daga wayar shi yayi ya kira jalal, yana dauka alhaji yace jalal kayi maza ka same mu gidan baffa gamu ahanya harda safna.
jalal najin an abaci safna yaji ranshi ya baci dan haka yace daddy bani da lafiya ne kaina namin ciwo.
alhaji yace ka daure dai kazo ina jiran ka, bayan ya kashe wayan yace safna halan kunyi rigima da jalal ko?
shiru tayi bata ce ko maiba, sai hajiya dake zaune kusa da safna tace ai kowa dai yau anyi tsiya sosai dan naga jalal ya tun zura
alhaji yace yauwa dan indai kaji jalal na fadin kansa na ciwo toh akwai bayani.
nan dai alhaji ya farawa safna nasiha har suka isa gidan.
bayan sun fito daga motar dukkan su suka shiga cikin gidan safna tun akofar gidan ta fara kuka.
sun shiga da sallama wata dattijiyar mata ta fito daga daki cikin sauri safna tabi da kallo ,cikin sauri ta karaso ta rike safna ta kalli fuskar ta sosai ta juyar da idonta kafar safna cikin kuka ta fara kiran baffa tana mai magana cikin fillanci.
fitowa yayi arude ya nufi safna kafar ta ya kallah shima kuka ya fara yana fadin Allah da girma yake tabas yar saudatu ce kafar su iri daya cikin sauri yace rahane sa mana tabarma.
bayan ta shinfida tabarma kowa ya zauna ummi ko sai rabe rabe takeyi.
Itako safna tunda baffa ya rike hannun ta be sake ba tana zaune kusa dashi, abayan sun gaisa alhaji ya gabatar da mahaifiyar shi agurin baffa da matar sa rahane, baffa dadi yaji sosai sannan ya shiga yi mata godiya akan abinda alhaji yake mai yabon alhaji yayi sosai daga bisani ya shiga saka mishi albarka.
hajiya ma dadi taji sosai ganin inda baffa kesawa danta albarka dan haka tace toh baffan yaudai gaka ga yar saudatu dan haka yanzon sai mu yafi juna dan Allah abar tuna baya dan zaman duniya dan hakuri ne, kuma in mune yau ba mune gobe ba dan Allah ka yafewa zaliha .
sai alokacin baffa ya kula da ummi data makure agefe yace hajiya ina jin bakin ciki idan na tuna rashin mutuncin da yar isakar yariyar cen tamin tasani atashin hankali da bakin ciki badan ina da tsawon kwana ba toh da bakin cikin yariyar nan ya kasheni tun lokacin da aka daura mata aure da alhaji babu wanda yasan gidan sai yayar ta rabi, dan haka da muka ta dade bata zoba na yanke shawaran nadauki mahaifiyar ta da kanwarta muje mugano ta ita da danta har gidan yayarta naje tamin kwatan cen gidan .
bayan mun sauka amota sai muka fara tafiya da kafa dan iya kudin mu kenan kona komawa gida bamu dashi tafiya taki karewa har saudatu ta fara gaji danaga ta gaji sosai gata ba karama ba bare adauke ta , sai muka zauna gindin wata bishiya saudatu na zama ta fara gengyadi ganin yama na karatowa mamarta ta tashe ta amman sai tace bata huta ba dan haka muka barta wajan mukace bari muje mudawo, cikin ikon Allah muka isa gidan tunda me gadin ya fada mata ga baki sai gata rike da hannun jalal yana karami cikin bacin rai tace wai lfy kuwa.
har yau na kasa mance wannan kalmar haka na daure nace naga kusan wata shida baki zo bane nace bari muduba ko fly, cikin sauri tace lfy ta kalau kuje gida inanan zuwa, mahaifiyar ta na kokarin magana tace a,a mama dan Allah kuyi sauri kar kawaye na su fito su ganku zasumin dariya har tana kiran me gadin wai ya bude mana kofa.
haka muka baro gidan cikin bacin mahaifiyar ta ttun anan ta soma kuka haka muka zauna mukayi ta kuka sai yamma likis muka tuna da saudatu saida mukayi tafiya me tsayi muka isa wajen, wayam muka samu gurin babu kowa duk muka duba unguwar bata ba lbrin ta gashi dare yayi ganin haka muka nufi gida akafa ko Allah zaisa gida ta nufa, sai tsakar dare muka isa gida tunda lokacin ban sake samun lfy ba har yau sai dai sauki kowa agurin kuka yakeyi daidai lokacin jalal ya shigo ya same su cikin wannan hali.
ummi mikewa tayi taje gaban baffa ta tsuguna tana neman gafarar shi.
bece mata komaiba yana rike da hannun safna, dan haka hajiya taje har gabasa itama tsunawa tayi tace baffa kaduba girman Allah yafewa yarinyar nan, ganin hajiya da yayi akasa cikin sauri yace Allah ya yafe mana baki daya.
[7:32AM, 12/27/2016] Fadeela lamido: 💘💍💍MIJIN MARAINIYA💍💍💘






Story
&
Written by
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed📝




123-125




Godiya tayiwa baffa sosai sannan tasa hannu ta daga ummi ta kaita gaban mahaifiyar ta.
mama rahane kin amsawa tayi ta juyar da kanta gefe sai da hajiya tasa baki.
baffa yana rike da safna mama rahane tazo tarike safna tana fadi ya sunanki ne?
safna shiro tayi tana zunbura baki, hajiya tayi murmushi tace sunan ta safna ai fushi take daku tace dama cen baku son saudatu tunda har kuka manta da ita.
baffa yace ayya yarinya barashin so bane akwai yanayi na rashin wayewa ada bakamar yanzon ba, amman munji mun dauka kiyafe mana kaddara ce .
kowa agurin murmushi yayi banda jalal dake tsaye, alhaji yace kai kuma yaya zaka zo katsaya mana akai.
yace daddy inason naje gida ne , bana jin dadi. alhaji yace ka bari muma yanzon zamu tafi, baffa yace alhaji kafin kutafi bari akira mamar ta rabi ta ganta, ya fara kira rahane dauko mayafi kije gidan rabi ki gayo mata, cikin sauri ummi ta mike tace bari naje, kiran jalal tayi suka fita tare.
bayan sun dau hanya ummi tace jalal me ya hadaka da safna?
mamaki ne ya kama jalal dan haka yace ummi wani ne yace miki munyi fada.
hararar shi ummi tayi tace ina tambayar ka kana tambaya na, dan baka da kunya.
bahaka bane ummi ai naga baki cikin gidan ne lokacin.
toh ina sauraron ka me ya hadaka.
ummi rashin kunya take min kwata kwata ta raina ni.
dakatar dashi ummi tayi jalal inason kayi hakuri da duk wani abu da safna zata maka bana son in sake jin ance kunyi rigima kajiko, kuma yan zon kaje ka bata hakuri.
da sauri jalal ya kalli ummi yace inbata hakuri fa kika ce ai ita ce tamin laifi ita ya kamata tabani hakuri.
eh na sani ka dai bata hakuri bana son ganin yariyar cikin bacin rai.
ummi ni gaskiya bazan bata hakuri ba, kin ga inda take gaya min magana ne.
ummi shiru tayi bata sake cewa jalal komai ba har suka isa gidan, yana tsayawa ta bude ta fita bata jima ba sai gata sun fito da yaya rabi har da yarta aliya sai murna suke.
baya suka shiga ummu na gaba suka kama hanya ahanya ne jalal ya kalli aliya yace ummi na dade banga aliya ba tun tana karama , sai kuma naga kamar tana kama da safna.
ummi banza tayi dashi sai yaya rabi ce tace ikon Allah itama zaliha haka tace, nina zaku ma naganta wlh.
jalal ya juya gurin ummi yace ummi lfy kuwa?
banza ta sakeyi dashi, yaya rabi tace zaliha abduljalal na magana kinyi banza dashi. rabu dashi yaya, jalal bashi da kunya ninace mai yayi abu yacemin shi gaskiya bazaiyi ba, kiri kiri.
nan da nan yaya rabi tashiga yiwa jalal fada , har suka isa gidan fada takemai.
suna shiga ta gane safna ta juya barayin ummi tace amman zaliha kin ban mamaki da har kikai zama mai tsayi da safna baki gane taba, hannu tasa ta daga safna, safna ma gani tayi kamar mamarta sunyi kama da mamarta sosai dan haka ta rungume ta tana kuka take taji son yaya rabi ya kama ta jinta take kamar mahaifiyar ta, duk da cewa da kaga yaya rabi kasan tana cikin yanayi na talauci.
aliya tazo ta baya ta tsaya tace anty safna. Cikin sauri ta waigo sukayi arba da juna safna sakin yaya rabi tayi ta rike aliya haka sukaita murnan ganin juna sai gurin la,asar suka fito, safna na rike da aliya wai ita adole sai dai sutafi da ita.
mama rabi tace safna kibari ran suna in munzo sai tazauna tamiki kwana biyu kinga yazon kayan ta duk suyi dauda.
safna tace mama toh basai ta saka nawa ba. ummi tace yaya ai hakuri zakiyi kawai mutafi da ita.
mama rabi tace toh Allah ya tsare sai munzo suna.
bayan sun dauki hanya hajiya tace toh kodai zamuyi gaba daya ne daga nan mu wuce gidan goggo safna cikin murna tace eh Hajiya.
alhaji ne yace toh bari akira jalal agaya mishi dan motar sa daban kar ya wuce gida.
bayan alhaji yagama waya da jalal yace yaran dai zamani basu da kunya kunga wai jalal tunanin yaran shi yake wai cewa yayi za,a kwasar musu iskar mota, dariya sukayi ummi ta kara rufe jariran ta rungume su ajikin ta, suna isa gidan malam musa alhaji da hajiya ne kadai suka sauka amotar suka shiga gidan da sallama, goggo ta fitoh daga daki tana fadin wai wai hajiya kece da kanki sannun ku da zuwa tabarma ta shin fida bayan sun gaisa goggo tace bari naje na sowo muku shinkafa da wake.
hajiya tace a,a ni ba zama nazoba nazone naga jikokina.
cikin fadowan gaba tace aiko basa nan iro yana gun yansan da an kamashi itako salame yanzon ta dauki tallan gyada.
cikin mamaki hajiya tace a,a batayi aure ba?
hawaye ta fara sharewa tace ai ya fasa tunda yagano ciki gare ta.
hajiya ta girgiza kai tace toh kizo ki raka mu gidan da dayar yariyar take naganta.
goggo tace ayya ai sun bar garin nan kwata kwata yanzon bansan inda suke ba.
alhaji yace tohfah mukuma gashi ganinta mukazo ya sunan tane ?
baki na rawa tace safna , suna cikin haka saiga ummi sun shigo da jalal goggo ta zabura tamike tami tana fadin yau na shiga uku karya ta takare dan Allah ku rufamin asiri wlh bansan inda safna take ba, nan da nan tashiga basu lbr tana kuka .
bayan ta gama ne hajiya tace to yanzon meye ribarki?
babu wlh kawai bakin kishi ne ya debeni har na aikata haka gashinan alhakin ta na bibiya ta yara na duk babu nagari kuka goggo taci sosai babu me lallashin ta hajiya fadi take kigama kukan kije ki ne momin jikata dan ba yadda zanyi ba.
Idon goggo duk sun fito waje kuka harda majina.
alhajine yama jalal umarnin ya shigo da matar shi, dan haka ya juya ya shigo da safna safna na shigowa goggo ta kara tsorata , tace dama kunsan safna ne, a Ina kuka same ta, zuwa tayi ta fara duba jikin safna tace ikon Allah safna ce haka kamar yar wani hamshaki , ni inan cikin bakin ciki da tashin hankali muta ne na nunani wasu suce min uwar karuwa wasu sucemin uwar barawo, cikin kuka take maganar ki yafemin safna na tuba bazan kara ba.
hajiya tace kima Kara mana, ina zaki ganta bare ki kara ita da take dakin mijin ta cikin fada tace ku kuma kutashi mutafi, duk mikewa sukayi suka fita safna ko tsayawa tayi tana kokarin daga goggo hajiya tazo ta jata
[10:21AM, 12/28/2016] Fadeela lamido: 💘💍💍MIJIN MARAINIYA💍💍💘






Story
&
Written by
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed📝




126-130




Lokacin da suka koma gidan hajiya mangariba tayi dan haka alhaji yana sauke su hajiya da su safna suka wuce gida harda jalal, jalal dai fushi yake da safna sosai dan har suka rabo basuyi magana ba.
suma suna sauke ummi masallaci suka wuce saida sukayi sallar ishsha suka dawo gida.
bayan sunja girki ne jalal ya mike yace daddy bari naje gida.
alhaji yace me zaka je kayi agida bayan matarka batanan kayi zamanka mana anan, koba haka ba zaliha?
ummi tabe baki tayi tace alhaji ni yanzo jalal yafi karfi na. Alhaji yace me kuma ya faru kai jalal dawo nan ka zauna, jalal na zama alhaji yace me yake faruwa, me ka mata?
sunkuyar dakai yayi yace daddy akan maganar safna ne, yanzun kwata kwata ta rainani rashin kunya take min, kuma wai ummi tace wai dole ni zan bata hakuri, daddy ai ni ya kamata taba hakuri, amman yaya za,ayi kuma ace ni zan bata hakuri ai sai taji dadi nan gaba ta kara yimin.
alhaji yace zaliha yaya haka, haka ake hukunci?
alhaji nifa bana son ganin safna cikin bacin rai, dan haka ni dai kawai kaje ya bata hakuri, shi wanene da bazata mai rashin kunya ba, ai nima gashi nan kanamin rashin kunyar, wlh inhar bakaje ka rarrashi yariyar nanba zakaga abin da zan maka.
kallon ummi yayi yace toh shike nan ummi naji, a han zar ce ya bar wajen dakin sa ya nufa.
alhaji yabi jalal da kallo yace zaliha bafa haka akeyi ba kina nufin yanzon kinfi son ganin nashi bacin ran akan na safna?
Alhaji aishi babba ne kuma cewa nayi yayi hakuri yabata hakuri.. Katseta alhaji yayi yace aiko indai haka zaki ringayi bakice su zauna lafiya ba dan zaki samai tsanar ta, ai shi amatsayin shi na namiji baxai so matar sa ta raina shiba, kuma nina tabbata ta bata mai rai ne shiya sa yayi fushi da ita amman yana son matar sa bakuma wai dan jalal yana dana bane na yabe shi, dukkan su yaya nane kuma daidai gwargwado nasan halin su. haka alhaji yayita ma ummi nasiha me ratsa jiki.
zuwa cen ummi ta fara kuka bakin ta yana rawa tace alhaji akwai abin da yake damuna ina tunanin idan kaji mgnr zaka tsora ta dani amman yazama dole na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login