Showing 3001 words to 6000 words out of 46437 words

Chapter 2 - MIJIN MARAINIYA Book Complete BY Fadeela Lamido.txt

Advertisement

10 Jan 2025

9493

naje na dawo , haka banzayen kakannin ki sukama uwarki har ta mutu bata kara saka su a idon taba.
[2:05PM, 11/24/2016] Fadeela lamido: 💘💍💍MIJIN MARAINIYA💍💍💘




Story
&
Written
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed


7-9


Itako safna bata fahimci me goggo ke nufe ba dan bata da wannan labarin , haka tai ta zaman jiran goggo har ta gaji tun tana ganin wucewan mutane daidai har ta daina gani dan haka tsoro ya shige ta, mikiwa tayi tabi hanyar da goggo tabi , tana tafiya tana dubawa ko Allah zai sa su hadu da goggo.


wata mota ce ta shigo layin tun daga nesa motar ke hasko ta, dan haka ta tsora ta , motar na zuwa kusa da ita ta tsaya, wani dake cikin motar yace yace ke ina zaki da daddaren nan, kisan ko karfe nawa kuwa?
cikin kuka me ban tau sayi ta girgiza kai wanda ke mazauni direba yace kabir ina ruwan ka da ita ne kasani ko aljana ce yanzun 12:15 pm fah ,yace yarinyar ar zikice za aganta a waje awannan lokaci, kabir yace kuma fah haka ne aboki na, motar su kaja suka mike layin.


Safna ko babu abin da take ban da kuka, gaba tayi kadan ta samu wani dan dutse ta zauna sautin kukan ta kawai kake ji awajan wasu samari ne suka zo wucewa su uku irin yan shaye shayen nanne sun sha sun bugu daya daga cikin su yace kai kunga wata baby danya, da sauri suka isa wajen ta suka fara ja mata dan karamin hijjabin dake jikin ta safna ko kuka take tana kokarin guduwa amman Ina sun riga sun rike ta dukkan su ukun har sun yaga mata riga dama bawani kwari ke gare suba suna kokawan kwance mata zani .


wan,nan motar ta dazun ce ta sake dawo ,mutun daya ne acikin ta sabani dazun da suke su biyu jin uhun yariyar yasa shi tsayawa ya haska su da fitalan motar yaga abinda ke faruwa da sauri ya fito yafara takawa zuwa wajen yana musu tsawa cikin fada ya daga murya sosai .


daya daga cikin su yace kai kuzo mu gudu yaya abduljalal ne da gudu suka kwasa abduljalal ya matso kusa da ita ya tsoguna ya dauko hajjabin ta ya mika mata ta karba ta saka kuka kawai take abduljalal yace yanzun ina zaki?


tace goggo nace tabar agun wata bishiya tace na jirata kuma naga ta dade bata dawo ba, sheni na biyo hanya ko zan ganta.
cikin mama jalal yace kina nufin mahaifiyar ki kece abarki a titi.

a,a kishiyar mama tace.
yace to ke ina mamar ki?
cikin kuka tace suyi hatsari har baba na sun rasu.
Jalal ya tausaya mata sai dai har yanzun be gama yar da, da yarinyar ba yana ganin kamar dai ta fito yawo ne, ya juya yace Ina yan uwan ku suke,
tace nibasan kowa daga cikin dangin muba kakata kawai na sani itama ta rasu jiya akayi bakwai, shine akace ma goggona takaini gun dangin kakata, shine ta barni tace najira ta tadawo.


hankalin jalal ya tashi ya rasa yan zun ya zai yi da yariyar nan gashi dare na dadayi , zuwa yayi yabude motar sa ya shiga da gudu safna ta biyo shi tana fadin dan Allah karkabar ni anan.
ai bazan barki a nan ba ya bude dayan gefen yace shiga mutafi , bayan tashiga ta zauna jalal yace ya sunan ki?
tace sunana safna.


Jalal ya sake maimaita sunan safna da sauri yafara neman fitilan motar haske ya baiyana yace safna bake bace shekarun baya na saya rake wajen ki, dama ke ma rainiyace.
cikin kuka tace eh.
Yace to kibar kuka safna insha Allahu zakiji dadin rayuwan ki , jan mutan yayi ya fara tafiya yana tunani yadda zasu kwashe da ummin sa.


lokacin da ya isa gida me gadi yabude mai ya shiga yarasa yadda zaiyi da safna dan yasan yanzun ummi batayi bacci ba saitaga dawowan shi , kilama yanzun tana kallon shi, dan haka dibara tafado mai yace safna inazuwa bari naje nadawo.
cikin sauri safna ta rokoshi tace dan Allah karka gudu ka barni kaima.


cikin kwatar da murya yace bazan guduba safna yanzun zan dawo ai nan gidan mune da guduwa zanyi ai bazan shigo dake cikin gidan muba, ban so ne ummi na ta ganki daddaren nan saboda kartayi wani tunani daban kuma nasan tananan tana jiran shigowa ta, sabo da haka kijirani yanzun nan zan dawo.
Gyada mishi kai kawai tayi amman bata son ya bar ta anan.


yana shiga ya samu ummi sai zagaye falon take da sauri shi yaje ya rungume ta, hannu ta tasa ta tukude shi.
abinda kuma zaka fara kenan yawon dare Ina ka tsaya har 1:30 shiyasa babanka yake cewa ninake sangarta ka.
tsugunawa yayi ya kama kafar ta yace immi kiyi hakuri kabir ne be fito da motar saba sai da nakaishi gida kuma ummi kisan gidan su da nisa amman ummi dan Allah kiyi hakuri bazan kara ba.
hannun ta tasa ta dago shi ta rungume tace jalal dole hankali na ya tashi kaikadai nake kallo naji farin ciki ya lulubeni nazaci kai kadai ne kwaina a duniya sai daga baya Allah ya kawo mana Kairat alokacin dana cire tsanmani kuma har yanzun baji sonka ya ragu azuciya taba, jalal nakosa naga matarka zataga gatan da babu wacce ta taba samu a gurin sirikar ta, balle kuma naga yaran ka.


dukar dakai yayi yana murmushi , ummi tasake cewa jalal baka fara tunanin aure bane har yanzun.
da da durkusar dakanshi kasa yayi yana sosa keya.
ummi tace yau kuma kunya ta kakeji , hmmm jalal mayan kasan, abin da nake so dakai in katashi nemu mata kasamo mana yar manyan mutane kar ka sake kawo mana yar matsiya ta.




07014197556
[9:30PM, 11/24/2016] Fadeela lamido: 💘💍💍MIJIN MARAINIYA💍💍💘




Story
&
Written
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed


10-12


jalal ya dago ya kalli ummi yace ba komai ummi karki damu, ummi bari naje na kwanta tace to ba damuwa Allah ya tashi mu lfy,mikewa yayi yanufi hanyar dakin shi ummi ta bishi da kallo tana murmushi har ya Kule.


shiko jalal ko dakin shi be shiga ba yabi ta kofar baya ya fita, ya bude murfin mutan yaga safna tayi zuru zuru roko mata hannu yayi suka shiga ciki ya bude dakin shi suka shi , yace kinaji yunwa ne?
tace a,a .
to ga bayi nan kishiga kiyi wanka inki fito kisaka wannan rigar yanuna mata wata karamar rigar shi.
in kin gama ki hau gado ki kwanta da safe zan shigo karki sake ki fito.


futowa yayi falo ya kwanta
washe gari jalal najin kiran sallah subahi ya mike ya shiga dakin ya tashi safna dake bacci akan makeken gadon shi, sannan ya wuce masallaci.


bayan safna ta idar da sallah tana zaune kan darduma, taji anturo kofar da karfi , wata yar yarinya ta gani ba zata wuce shekara biyar ba , tana fadi yaya jalal jiya inata jiranka har nayi bacci baka dawo ba ,waige waige ta fara da safna su kai ido hudu dan haka ta saka kuka ta juya aguje tafita adakin, tana fita sukaci Karo da jalal , yarike ta yana fadin me ya sa meki ?

dakin ka naji neman ka ban gan kaba sai wata aljana nagani .
Jalal dariya yayi sosai sannan yace ba aljana bace anty ki ce na kawo miki amman karki gayawa ummi.
da sauri tace sabo da me baka son ummi ta sani.
saboda bana son ummi ta koreta koke kina son ta kore ta.
a,a to yaya matar kace.
a,a kairat itama kanwa tace kamar yadda kike kanwata , janta yayi suka shiga cikin dakin.
lokacin safna na zaune abakin gado tayi tagumi.


ya dade tsaye akanta bata masan ya shigo ba.
sai da safna ta kwana uku ummi bata san da zuwan ta ba.


ummi ko na lura da jalal baya kwana dakin shi kuma yanzu baya cin abinci sai dai yakai dakin shi , sabanin da yana ci yana sha gwaba, dan haka tace azuciyar ta koma me yake baye mata yau zata gain.


yauma kamar kullum jalal ya dauke abincin shi ya nufi dakin sa ummi na kallon shi, tana nan zaune har ya fito, binshi da kallo kawai take, ya dade zaune ya mike yace ummi sai da safe, to kawai tace dashi.


Yashiga kenan ya zauna yaji anturo kofar , razana yayi ya mike yana fadi ummi lafiya, ummi bata bi ta kansa ba zuwa tayi ta dago safna dake kwance akan gadon jalal tayi wurgi da ita.


jalal ya mike da sauri ya daga ta yasa ta ajikin shi yana rarashin ta dan har ta fita hai yacin ta.


ummi ce ta kara matsowa cike da mamaki tace yaro Ina kasamo yarinya har ka ajeta adakin ka ban sani ba.
kallon shi tayi taga yasa ta a kirjin sa , sai faman rarrashin ta yake, cikin daga murya tace jalal kaine ka kawo min karuwa har cikin gida kasata a kirjin ka agabana dan ka nunamin kai tantirin dan iska ne ko?


cikin sauri ya sake safna yace ba haka bane ummi wlh ummi ban taba zinaba kuma wlh safna ba karuwa bace marainiya ce bata da uwa bata da uba kuma abin da yasa na kasa gayamiki nasan bazaki fahimce ni ba ne.


ummi tace shi yasa ka muna fun ce ni , to maza maza ka tarkata ta ka fitar min da ita agidan nan, dan kaga na kwalfa rai akanka shine zaka neme ka watsa min kasa a ido , kasani sarai bana hada guri da talaka.


abduljalal yace to naji zata fita ummi amman nima bazan xauna ba zan je na nemar mata gurin da zata zauna tunda mu arzikin mu talaka bazai amfana da shiba.


cikin taga murya tace ni kake mayarwa da magana akan wata banzan yarinya, to katafi din in baka tafi ba karai na Allah kuka tasa harda kururuwa yau ga dan ta na cikin ta yana mayar mata da magana, tace indai ko kabi yarinyar nan Allah ya isa nono na ?da kasha.


Jalal ya zaro ido yace ummi abin har yakai haka, to shi kenan ummi na hakura ke safna tashi ki tafi , safna tana kuka ta mike ta fita daga dakin.


Jalal ma tsugunawa yayi ya soma kuka yana fadin ummi,ba ta san kowa ba fa , kuma bata da inda zata ummi marainiya ce fa , ummi ko gezau bayi ba.


suna cikin haka suka ga alhaji mustafa rike ta safna ya shigo har dakin abduljalal, ummi da sauri tace alhaji shine bayi waya kana hanya yau ba sai dai kawai muganka.


jalal mikewa yayi yakoma jikin dady ya kwanta alhaji yace wanan wacece na ganta Waje tana kuka .
cikin sauri ummi tace bamu santa ba.


alhaji yace karya kike yi zaliha duk naji abin da ya faru wai kece kike kin talaka dau la yasa kin manta asalin ki, to tun da kin manta bari na tuna miki
[9:07PM, 11/25/2016] Fadeela lamido: 💘💍💍MIJIN MARAINIYA💍💍💘




Story
&
Written
Fadeela Lamido
Mmn yazeed




13-15


ummi kuka ta fara ta fita adakin da sauri ta shige nata dakin.


alhj ya kalli abduljalal yace akan wannan har kake zubar da hawayan ka, meyasa tunda kaji kana son ka tai maketa baka kirani awaya ka gaya min ba, kar ka kara zubar da hawayen ka, bama wannan yariyar ba duk wanda kake son ka tai maka ma kamin magana kabar biyewa ummin ka kaje ko.


jalal kwanciya ya da da yi ajikin daddy yana murmushi.
alhj ya sake cewa jalal zamu zauna tare da yarinyar nan zan sata makaranta zan riketa kamar yarda na hai fa idai har zakai farin ciki da hakan, amma da sharadi guda daya, sai nayi binkece na tabbatar maganar da yarinyar nan ta fada gaskiya ne.

Jalal tsuguna wa yayi yana ma alhj godiya tare da amicewa da maganar alhj.

har alhj ya fita ya dawo ,yace jalal raka yarinyar nan dakin kairat, kar na sake ganinta a barayin ka.
cikin sauri jalal ya amsa , haka yakai safna har dakin kairat ,kairat batayi bacci ba dan haka taji dadin ganin anty safna a dakinta.


bayan alhj ya shiga dakin ummi ya same ta tana zaune bakin gado tana share hawaye, kusa da ita yaje ya zauna ya dafata yace zaliha meye kuma abin kuka.
dole nayi kuka alhj naga kana neman ka tona min asiri agaban dana har da wata bare, wadda bamusan asalinta ba, kuma ni din da kake neman wulakantani ai a gaban iyaye na gaje ka aure ni, kuma duk gorin da zaka min nasan be wuce kace ka ganni ne lokacin da nake kora shanon mahaifina ruga ba har kaji kana sona , ai baza a hada da wannan banzan yarinyar ba, kuma ni abinda yafi damu na kar fa jalal yace son yarinyar nan yake dan nikam ko zanyi yawo tsirara bazan bari yaro ya aure taba.


alhj ya gama sauraran ummi cike da mamaki yace zaliha kina bani mamaki to meye a ciki dan yace yana son ta, ni dai na dauki alkawarin zan riketa kamar sauran yarana, kuma kema inason kireta kamar yar da kika haifa.


ummi tace naji zan riketa amman sai dai in jalal yayi min alkawarin ba aure tsakanin shi da ita.
Hmmm zaliha kinan dai akan bakan ki kenan yanzun kuma amiki magana kice ammiki gori, to shi jalal din da kikace sai yayi miki alkawari bazai ce zai aure ta ba, yasan gaibu ne, be saurari me zata sake cewa ba ya fita adakin afusace.


ummi kasa bacci tayi dan haka washe gari da safe ta nufi dakin jalal ta same shi kwance akan gado ya najin shigowan ta ya miki, kusa dashi taje ta zauna yace ummi dama yanzun nake shirin nazo na ganki nasan kina fushi dani ummi safna abin tausayi ne , tausayin ta ya kamani.
cikin dibara ummi tace na fahimceka jalal komai ya wuce safna zata zauna tare damu amman da sharadin nan gaba baza kace zaka aure taba


dariya sosai jalal keyi cikin dariyar yake fadin haba ummi dama akan haka kike tada hakalin ki , idai wannan ne ki kwantar da hakalin ki , ummi me zanyi da safna ga haddadu babys a gari haba ummi ni wlh ummi kin ma bani mamaki yama za ai haka ta faru.


ummi ji tayi zuciyar ta fes tundaga ranar ta fara jan safna ajikin ta, hakalin safna ya kwan ta ta koma makaranta ita da Kairat suke ta fiya .


akwana atashi gashi yau safna kusan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login