Showing 39001 words to 42000 words out of 46437 words
Chapter 14 - MIJIN MARAINIYA Book Complete BY Fadeela Lamido.txt
babu kwari jalal ya mike yace daddy mutuwa tayi.
a,a jalal tana nan daran ta haihuwa ce amman jalal kayi ta mata andu,a Allah ya rabasu lfy .
jalal be yadda da abinda daddy ya fada ba dan haka ya fara share hawaye.
alhaji yakira anty nusaiba yagaya mata halin ta suke ciki nan da nan saiga su ita da matar baba salisu suna rike da kayan baby ganin ummi agurin abin ya basu mamaki.
2:46pm sukaji safna tayi kara mikewa jalal yayi zai shiga anty ta rike shi ta bude baki zatayi magana suka sake jin wani ihun, wannan karon sai da alhaji yasa hannu suka iya tare shi, yana fadi daddy kuka fah takeyi haka sukai ta bashi baki juyawa yayi ya fita yasamu wani dan dutse ya zauna yata share hawaye.
yana zaune agurin anty ta fito da gudu tana dariya jalal albishirin ka.
mikewa yayi yana kokarin share hawayen shi yace anty ta haihu ne?
Jalal mu godewa Allah safna ta sauka lfy mun samu yan biyu.
jalal ya zaro ido yace anty da gaske cikin sauri ya nufi ciki ya same su alhaji sai dariya suke alhaji ya dafa jalal yace jalal kuka ya kare ko?
kunya ce ta kama jalal yayi kasa dakai yana murmushi yace daddy wai da gaske yan biyu ne?
alhaji yace 'yan buyu ne jalal mace da namiji kana mamaki ko, ikon Allah kenan.
bayan angama gyara jarirai aka basu damar shiga ummi ce kan gaba tana shiga ta sauke idanun ta akan safna da sauri ta rintse ido gurin ta ta nufa takira sunan ta taji shiru, alhaji yace zaliha kirabu da ita kila bacci takeyi daidai lokacin nusaiba ta dauki macen takalle ta sannan tamikawa alhaji tace yaya ga matar ka ta juya zata dauki dayan ta ganshi hannun matar baba salisu haka suka taro suna kallon yaran gwanin ban Sha,awa.
Shiko jalal gurin gurin matar sa yake son zuwa amman ummi tana jikin gadon dan haka ya kasa zuwa wajen.
alhaji ne yace jalal yanaga ka koma gefe kazo kaga yaran mana.
sosa kai yayi ya kalli safna yace daddy ina zuwa.
alhaji ya fahimce shi yace kazo ka gansu mana safna ai bacci take.
da saurin sa yace daddy ba bacci take ba idon ta biyu.
sai da alhaji ya kalli safna sannan yace zaliha fito daga nan gurin.
cikin sauri ummi ta fito daga gurin duk arude take so take kawai safna ta tashi .
Jalal yana isa gurin ya duka yanawa safna magana cikin kunne zuwa can ta fara magana ahankali cikin kuka, jin safna na kuka yasa duk suka maida hakali gurin su, amman basajin me suke fadi, jalal ya dago hankalin shi atashe ya kalli ummi ya hada rai.
ummi ta tsargu tace jalal me safna tace maka.
yi yayi kamar beji ba ya mikawa alhaji hannu ya bashi yaran ya kure su da ido.
lokacin da aka sallame su ,alhaji yace awuce da ita gidan hajiya motan jalal ta shiga su anty nusai ba ma haka.
hajiya ta tare su da murna nusaiba ta mika mata yaran ta kalle su tace ikon Allah ga jalal ga safna , hajiya fatima ta shigo rike da safna ta zaunar da ita akan kujera jalal ma ya shigo dauke da kaya ya ajiye agefe hajiya ta kalli jalal tace yaya haka kuma jalal menene haka kaida ka samu karuwa kuma menene naka na hada rai, ta kalli safna tace au kema kuka kikeyi toh abin naku bana lfy bane
anty tace jalal nima nakula akwai abun da yake faru har anty zaliha ma akwai abun da yake damun ta ko kallon yaran batayi ba
hajiya tace tunda sunki mgn ku kiramin alhajin har zalihar ,wannan ai iskanci ne Allah yayi muku kyauta kuzo kuna tur bune mana fuska.
suna cikin haka alhaji ya shigo ummi na bishi abaya hannu ta rike da wanan huton.
bayan sun zauna hajiya tace nifa kun sani aduhu wai me yake faruwa ne?
alhaji yace hajiya wani babban al,mari ne yake shirin faruwa ya karbi huton ahannu zaliha ya mikawa hajiya yace wannan haton safna ta gani kawai sai gani sukayi ta fadi shine muke tunanin ko ta sansu ne .
hajiya kallon huton tayi tace wannan ai musa ne.
alhaji yace hajiya wani musa kuma ?
tace musan iya mana ko kana nufin baka gane shi bane.
alhaji kallon huton yayi sosai yace innalillahi wa,inna ilaihir raju,un
Safna na daga gefe kuka kawai take murya hajiya taji tana fadin safna kinsan musa ne?
cikin dashewar murya tace babana ne.
hajiya ta zaro ido a,a safna ko dai kama suka miki wannan fa dan yayata ce uwar mu daya uban mu daya, yanzun nan kina nufin ke jikar iya ce.
cin kuka tace eh.
kowa afalon gumi ne yake karyo mishi itako ummi hankalin ta yafi na barawo tashi.
hajiya ta share zufan da ya karyo mata tace ke zaliha Ina kika samu wannan huton ?
jalal najin anyi ma ummi wannan tambayan ya fita afalon dan yanajin kunyar abin da ummi tayi.
cikin kuka tace hajiya wannan matar itace kanwa ta da nake baki labari, zaro ido safna tayi ta mike tace ummi kina nufin kece yar mahaifiyata, ina wlh wlh bazai wuyo ba gara naga mutuwa ta da naga wannan ranar😭😭😭😭
[8:57PM, 12/22/2016] Fadeela lamido: 💘💍💍MIJIN MARAINIYA💍💍💘
Story
&
Written by
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed📝
1013-1016
Anty nusaiba ta kama safna ta zaunar da ita tana fadin safna ki natsu mana baki san jikin ki babu kwari ba ne.
safna tace anty ni ki sakeni tafiya zanyi wlh bazan zauna ba.
kowa afalon share hawaye yake sautin kukan ummi kawai kake ji.
alhaji yayi gyaran murya yace safna zo ki zauna, batayi musu ba kusa da hajiya ta zauna , hajiya ta kalli safna tace tabbas biri yayi kama da mutun lokacin da hanne tazo gidan nan zaliha ta tambeye ta amman sai tace ba, ita ba ce, kuma nima na tambaye ta ina yar da kishiyar ta tabari sai tace min tana gurin dangin mamar ta , hajiya ta nisa takara cewa toh me hanne take nufi da haka.
alhaji ne ya dago yace hajiya ga dalilin ta nan bata san inda yarinyar take ba kame kame take tunda su tace musu tana gun dangin baban ta ke kuma ga abinda tace miki.
hawaye ne yake zuba afuskar hajiya tace amma ko indai haka ne ni kaina naci amana, dan tun lokaci da aka ma iya aure da baban musa dangin mu duk suka guje ta saboda mijin da ta aura bame karfi bane babu me zuwa inda take sai ni dama mu biyu ne mata sai yayyen mu maza guda uku haka in naje iya zatai ta min korafin ita ba me zuwa gurin ta, nice me lallashin ta har sai naga hankalin ta ya kwanta, ana cikin haka nima aka aurer dani, tun daga lokacin ban sake zuwa garin ba sai da iya ta haifi musa mijinta dakan shi yazo ya fada balefi dagi sunje tun daga sunan musa ban sake zuwa ba sai dai ita tana zuwa gida na akai akai dan haka ban cika damuwa ba ,dan bata rufe wata bata zoba haka muka ci gaba da tafiya sai dai rashin lafiya ko wani babban abu muke zuwa gurin ta duk da cewa ita ko da yaushe tafe take, kuma duk wani Sha,ani sai dai in bataji ba, ko koma bata da lfy bana mantawa zuwan ta na karshe gidan nan nasiha tai tamin akan zumunci ko sati daya ba,ayi ba mukaji lbrn rasuwan ta kuka ne yaci karfin hajiya ta jawo safna tana fadin naci amanar iya.
safna lafewa tayi jikin hajiya tana kuka hajiya ta dafa kan safna hawayen ta na diga jikin safna tace safna ki yafe min nina saka ki a halin da kike ciki da ace sanda nazo gaisuwar iya na dauke ki da haka be faru ba, ninayi tunanin hanne zata hada da nata tarike, sai nake ga kamar idan idan aka dauke ki zata ce annuna mata banban ci , bansan cewa bakin hali gareta ba.
safna kara rugume hajiya tayi dan ita duk wani abu da yashafi iya gir mamashi take kuma ai tun haduwan ta da hajiya na farko bata nuna mata tsana ba, kuma bata taba nuna mata babbaci tsakanin ta da jalal da yake jikan ta ba, dan haka hajiya da 'ya'yata sun gama mata komai tun da sun sota alokacin da basu san waye ita ba, dan haka ta dago ta fara sharewa hajiya hawaye da hijjabin ta.
ummi ko tana cen gefe uwa kazar da aka tsamo ta daga cikin ruwa.
anty nusaiba ce ta katse musu shirun ni dama tunda naga safna sai da naji ta a raina, take naji son ta ya kamani ashema 'yata ce.
alhaji yace ai irin abin da nake gayawa zaliha kenan yazun gashi inda abu ya koma, yanzon me zakice wa yarki safna.
Ummi kuka kawai take ta kasa cewa komai, ana haka jarirain suka soma kuka anty nusaiba tace safna tashi muje kiyi wanka kiba yaran nan nono, kamar jira take ta mike ta shige dakin hajiya.
bayan anty ta gama gasa mata jiki suka fito ta sanya kaya ta haye gadon hajiya ta kwata anty tace safna ba kwanciya zakiyi ba kibari yaran sudan ji dumin jikin ki mana.
anty nifa nagaji bacci nakeji.
ban ga ne kin gaji ba me kike nufi ko kallon yaran nan bakiyi ba fah .
anty ni bana so akai ma ummi ta rike ai su bazata ce basu da dangi ba.
anty kallon safna tayi tace karki haka safna yaran nan basu suka miki laifi ba, zadai kidau hakkin sune kawai, ai irin haka jalal bazaiji dadi ba.
ai ni dama banson yaji dadi duk wani abu da ya shafe ummi ban son shi me sonshi ma bana son gani wani sabon kuka ta saka tace anty dan Allah ku sa shi ya sakeni wlh bana son shi ko ganin shi bana sonyi.
anty tace inalillahi wa,inna ilaihir raju,un kar ya kike safna kina son jalal, kar ki yadda laifin ummin sa ya shafe shi dan baya goyan bayan ta
suna cikin haka hajiya fatima tashigo da yaran ta daura macen jikin safna tace bata nono tasha sai kuka takeyi.
safna kallon yariyar tayi take taji son ta ya kama ta amman tana bakin cikin kallon wani abu da shafi ummi dan haka ta fara kuka, hjy fatima tace safna bata mana.
sukuyar dakai tayi ta rufe ido, anty tace ai tace bazata basu nonon taba.
hajiya fatima ta bude baki zatayi magana su kaga jalal ya shigo bece komai ba illa mika hannu da yayi hjy fatima ta saka mai na mijin ya sake cewa bani dayar batayi musu ba ta daukota ajikin safna tamika mai juyawa yayi ya fita.
yana fitowa ya samu ummi makure taci kuka har ta gaji ya tsuguna ya mikawa ummi yaran yace ummi gasu safna tace bazata basu nonon taba.
cikin tashin hankali ummi ta mike, dakin ta nufa ta samu safna ta kifa kai tana kuka ajeye yaran tayi abayan safna ta tsuguna tarike kafar safna tace safna dan girman Allah kiyi hakuyi kiyafe min, nasan na tafka babban kuskure nayi nadaman abin da na ai kata safna ina cikin wani hali, dan Allah ki tausa yama yaran nan, haka ummi taita magana safna batace ta komai ba ga yaran sai faman kuka suke, gani tayi safna bazatayi magana ba ta mike ta fita zuwacen sai gasu da alhaji .
alhaji na shigowa ya zauna akan wata kujera dake gefe yace safna wannan hukuncin da kika dauka yayi tsauri da yawa ni bance karki nuna fushin ki ba, amman inason fushin ya tsaya akan zaliha ka dai, ya sake cewa safna indai kin daukeni uba agare ki toh na umarceki da ki dauki yaran nan kibasu nono.
cikin sauri tasa hannu ta dauke mace dan ita ke kuka na miji har yagaji yayi bacci, daddy na kallon safna sai ciki cikin rike yarinyar take, yajuya yace zaliha tashi mutafi gida.
suna fita falon alhaji yace nusaiba je ki nuna mata yadda zatayi, alhaji sallama yayi wa hajiya suna fita suka samu jalal awaje ya hada kai da gwuiwa
[9:03PM, 12/23/2016] Fadeela lamido: 💘💍💍MIJIN MARAINIYA💍💍💘
Story
&
Written
Fadeela Lamido
Mmn Yazeed📝
1017-1019
Alhaji yace jalal tashi muje gida, jalal beyi musuba ya tashi ya shiga mota ko acikin mota babu me ma wani magana har suka isa gida, ummi taso suyi magana da alhaji amman yace ta bari sai gobe, haka ta shiga daki badan ran ta yaso ba.
alhaji ko rike hannun jalal yayi suka shiga daki bayan sun zauna alhaji yace jalal ka kwatar da hankalin ka insha Allahu komai zai wuce.
cikin sauri yace daddy naji fah abin da safna take fada wai bata sona har tana cewa wai ace min na sake ta.
alhaji yace ya isa jalal kayi hakuri bacin rai ne ya sata fadan haka, kama ta uzuri yariyar tana da hankali,lallashin ta zakayi zata sakko.
washe gari jalal yana shir yawa ya nufi gidan hajiya yana zuwa ya samu hajiya da anty nusaiba suna hira bayan ya gaida su hajiya tace dama yanzon muka gama mgn akan sunan da za,a sama yaran nace sai asa sunan iyayen ka.
jalal yace a,a hajiya abarsu da sunan su ummi ma bata so asa sunan ta.
hajiya tace ai jiya muyi mgn da ita tace asa ma macen saudatu.
hajiya dan allah ki dai na biyewa ummi kuma ni nafison abar su da sunan su, be sake cewa komai ba ya shige dakin ya sami safna zaune tana cin tuwo hada fuska tayi nema guri yayi ya zauna kusa da ita.
shiru tayi bata ce komai ba, jalal yace safna ba gai suwa.
gani yayi bata da niyar magana yace toh ni bari na gaida ki inakwana ?
ban za tayi dashi ya sake cewa safna fushi kike dani to me na miki?
daga kan ta tayi tace kawai ganin ka ne banaso, sabo da tun da na samu lbrn mahaifiya ta naji na tsani dangin ta, mahaifiya ta tayi rayuwar bakin ciki na rashin iyayen ta har ta koma ga Allah bata gansu ba wannan ya nuna min basa kaunar ta da suna kaunar ta basu manta da ita atiti ba dan haka bana son wani abu ya hadani da dangin ta bana sonsu bana kaunar su.
shiru jalal yayi ya dukar da kai zuwa cen yace safna kinga duk cikin wannan abun ummi ce me laifi tunda ita ce ta bata musu rai har suka manta sun taho da ita.
ciki kuka safna tace bawani bacin rai da zaisa ka mance da danka yan zon Kai zaka dauki dan ka ka,ajeshi atiti kace mai bari kaje kadawo, su mahaukata ne?
jalal yace naga alaman baki da hankali mikewa yayi zaifita safna ta bude baki tace kaine dai baka da hankali.
juyo wa yayi ya dawo yace abin har yakai haka?
eh yama wuce haka tun da kafito ta tsotson ummi.
jalal ji yayi kamar ta caka mishi allura azuciyar shi , yace safna kar ki manta fa ummi mahaifiya tace.
safna bude baki tayi tace jalal ai uwa batafi uwa ba.
tun da suke da safna bata taba kiran shi da sunan shi ba sai yau, kara kule wa yayi yace toh nagane abin naki rashin mutunci ne
toh kisan magar da zata rika fitowa daga bakin ki dan bazan dauki wula kancin ki ba inkuma kina ganin wasa ne kikara fadan wata magana kiga ni wlh mugun duka zan miki.
daidai lokacin su hajiya dake falo suka soma jin hayaniyar su aguje suka shigo daidai lokacin da safna take cewa sai dai mudake juna, jalal kuwa yayi kanta gadan gadan anty ce ta riko shi iya karfin ta amma sai kwacewa yakeyi hajiya ce ta shiga tsakiyan su ta girgiza jalal tana fadin abduljalal dubeni nan me yayi zafi hake, kai da nake yabon ka.
yace hajiya wannan yar karamar yariyar zata duga fadamin mgnr da taga dama ni sa,anta ne?
hajiya tace a,a kayi hakuri fita muje, juyawa yayi ya fita yana huci anty tabi bayan shi.
Hajiya ta kamo hannu safna data manne da bango ta zaunar da ita bakin gado tace safna kintaba jin laifin wani ya shafi wani, shi meye nashi, me lefi daban wanda ake hukun tawa daban, karki kara safna dan Allah kisawa zuciyar ki salama.
safna kuka take sosai tace hajiya toh kice mishi ya sake ni.
cikin fada hajiya tace yazon dai kina nufin babu wanda zaigaya miki mgn kiji ko ?
girgiza kai tayi bahaka bane Hajiya ni cewa nayi ya dai na min magana.
haba safna ban da abinki ta yaya zakice ya daina miki mgn mijin kine fa dan Allah karna kuma jin wannan mgnr abakin ki kuma kije ki bashi hakuri, safna ki daina gayawa jalal munanan mgn akan ummin sa uwa uwa ce safna kuma hannun ka