Showing 1 words to 3000 words out of 24314 words

Chapter 1 - SAURAYINA BOOK COMPLETE DOCUMENT BY Mrs Sadauki .txt

10 Jan 2025

2219

[17/04 à 16:40] MRS SADAUKI 👑: *SAURAYINA*💅🏻💅🏻💅🏻




LoVe and HoRrOr story💔☠️




```MRS SADAUKI```✍🏻
Dedicated to Autar Manya👑
*FCWA*☀️
____________________________________________________________________________________________________






Page 1




Duk illahirin Musulmin Nijar sai hada-hadar jajibirin ƙaramar sallah suke,ƴan mata sai kitso da lalle suke yayin da ni kuma zuciyata take cike da tsoro, fargaba da zullumi suka raunata ruhina wanda ba komai ya haifar da haka ba sai baƙin alƙawarin da na ɗaukar wa Saurayina wanda duk duniya babu wanda nake so sama da shi.Ido na rumtse gam ina addu'ar da ba za ta guje ba,don in ba yau ba ne gobe sai ya tabbata.
A karo na biyu Mama ta jefo min tambayar “ke Sharifa ba za ki je ƙumshin ba?” yanayin yadda ta min maganar a tsawace ya saka ni saurin buɗe idon tare da miƙewa daga kwancen da nake,raunatacen maƙoshina mai cike da ƙishi na daidaita kafin na ce “Mama babu tabbas fa ganin wata a yau! ”


Sosai Mama ta ƙure ni da idonta masu matuƙar razana ni,“Sharifa mine ne ke damun ki ? Yau ke ce kike gudun kwalliyar sallah?”
Na sunkuyar da kaina zuciyata na ɗan bugawa ,domin muddin na ci gaba da kallon idon Mama tabbas za ta fahimci wani abu.
“Tambayar ki nake! Ko Fahad ya ce bai son ki?”
Furucinta har ya fi damuwar da ke damuna zama tashin hankali a wurina,tuni idona suka ciko da ƙwalla ban san na lokacin da na furta “gwara na ga mutuwata da wannan ranar,Mama Fahad shi ne rayuwata in babu shi babu ni ”
Tsuki ta ja ta na amsa sallamar Papa da ya shigo ,a bayansa kuma yaransa ne ɗauke da ledodi.
Kallo ɗaya na yi masa na sunne kai ina wasa da yatsuna,“wa ya taɓa ki?” Papa ya faɗa,ba tare da na kalle shi ba na ce “ba komai !”
“Mi kika yi mata take kuka? ”
“Ƙumshi kawai na ce ta je ta yi fa ”Mama ta faɗa don kare kanta,don duk yadda take da tsanani a kanmu Papa na yi mata katsalandan don bai son ana takura mu.
“Tun da ba ta so ai shikenan mine ne na takura ta?”




Saurin barin wurin na yi na koma can ɗakina,tun kafin na isa nake jin tsuwar wayata ta na ringing ɗin waƙar *Zan rayu da kai zan mutu da kai* iya Fahad kawai na sawa shi na musamman.
Wayar na cire daga caji ,a nan wani kiran ya kuma shigowa hannu na rawa na ɗaga .Ina jin lokacin da ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce “babyna ina kika aje wayar ki? Sama da kira goma fa na yi ko ki na salon ne ana ƙawata min ke?”
Kamar ya na ganina na girgiza kai tare da cewa “a'a ban je ba”
“Kamar ya ba ki je ba? ”
“Had ba fa lalle gobe sallah ba,yau duk ban jin daɗin jikina ” na furta murya na ɗan rawa don na fahimci kamar ransa ya ɓace wanda kuma hakan barazana ce gare ni.
“Sharifa ban son iskanci da rainin hankali,wato ba ki son cika alkawarin da kika yi min shi ne za ki kawo wani banzan tunanin ki .Tun da aka haife ki kin taɓa ganin inda aka yi azumi talatin?”
“Had wallahi ba haka nak...” saurin katse ni yayi ta hanyar cewa “ya isa haka Malama! Dama na san ba sona kike ba shi yasa kika ƙi bari mu zama abu ɗaya! ”
“Innalillihi! Had ni ce ban son ka? ”
“Eh mana Rifa! In ba haka ba miye a ciki don kin bani kan ki? Ni fa zan aure ki ba wani ba kuma na faɗa miki zan saka kwararon roba gudun shigar ciki”




Shaaa! Haka hawaye ke min shatata a kumatu,Allah ne shaida ta ina mahaukacin son Fahad wanda shi kuma ko rabinsa bai yi min.Inda kuma aka samu akasi mugun tsoronsa da nake ji,yadda nake shakkarsa ko Mama albarka.
“Za a ga wata a yau in sha Allah! Ki je a yi miki ƙunshi kin san ai ya na burge ni sosai.Ina so gobe na sha yatsun ki fiye da na kullum.Babyna don Allah ki cika min muradina wallahi ke ɗaya nake so nake kuma sha'awa ke ma ai shaida ce” Fahad ke faɗa cikin zaƙin muryarsa mai kamar busar sarewa.
Ban iya cewa komai ba sai kuka marar sauti,ya ci gaba da cewa “babyna har fa na samo mana inda za mu huta,ɗaki mai kyau har da AC dakyar abokina ya ban auro duk don ina son nuna miki irin yadda nake maitar son ki”
Furucinsa na ƙarshe yasa na ɗan ji sanyi ,kamar wacce aka yi wa dole na tambaye shi “Had da gaske ka na sona sosai?” sai da yayi murmushi mai sauti sannan ya ce min “fiye da so!” nan fuskata ta cika da annuri kan kace wani abu mun fake da hirar soyayya wacce babu wani abun albarka a ciki sai yadda za mu kasance a gobe.




Bayan ya kashe wayar ne na nufi toilet cike don yi ɗahara saboda yanayin da na tsinci kaina.Bayan na fito na shirya tsab na fito domin zuwa gun ƙunshi,kuɗi Mama ta bani kafin direba ya kai ni.
Ko da na isa gidan cike yake da jama'a,ta na ganina ta miƙe ta zo ta rungume ni ta na ihu tare da cewa “na zata ba za ki zo ba”
Na ɗan ture ta ina hararen ta na ce “kar ki wani nuna kin damu tun da ban ga kin kira ni ba”
“Hankalina ne ya ɗauku! Zauna in na ida ma wannan sai na yi miki ” ta faɗa tare da jawo min kujera,a haka muke yin hira ta tsokana.Har ta zo ta soma yi min wanda iya yatsun hannu ne dama nake yi wa lalle a ƙafa kuwa daidai suwu ne ake yi wa kwalliya amma duk da haka da zan tafiya sai da na aje mata kuɗi wanda ita kanta Ramlah ɗin ba ta sani ba.








A cikin wannan wunin tunanina ya rabu biyu,na ganin wata da kuma abin da zai faru a gobe.A cikin wannan zullumin muka sha ruwa har muka tafi sallah muka dawo,kamar marar lafiya haka na kwanta a doguwar kujera na ƙurawa tv ido ina jiran jin labaru.Yayuna maza kuwa sai ciye-ciye suke su na hira da Mama,ina jin su suna tambayar Lafiya yau Auta ta kasa cin komai amma Mama ta share su.


Ana sanarwa an ga wata na ji duk illahirin hankalina ya tashi,sam na kasa ɓoye damuwata har sai da na fiddota fili “innalillahi shikenan gobe sallah!”
“Ka ji min zancen banza! Ganin watan ne ke innalillahi? ” Ya Mustapha ya tambaya a tsawace wanda shigowarsa kenan,na yunƙura na tashi hakan yayi daidai da shigowar kiran Fahad.Hannu na rawa na ɗaga kiran,
“Ya tabbata gobe sallah!” shi ne abin da Fahad ɗin ya faɗa cike da murna wacce nake da yaƙinin ba wai don saboda sallah ba ne sai kawai don zai karɓi budurcina ne a goben kamar yadda na masa alƙawari.
A sanyayye na furta “ni ma yanzu nake gani a télé Sahel ”
“Lafiya na ji duk kin yi sanyi ?”
“Gajiya ce kawai,azumin yau ya ɗan wahalar da ni kuma na fita na yi ƙunshi” na furta tare da ɓoye masa damuwata don gudun ɓacin ransa.
“Gobe da ƙarfe nawa za ki zo?” ya tambaye ni cike,“zan zo kar ka damu” na furta cikin salon kwantar masa da hankali da basa tabbaci .Mun yi hira sosai kafin ya min sallama,waigowar ga da zan yi sai na ga kamar innuwar mutum ta yi saurin barin ƙofar ɗakina.Na basar tare da shiga toilet na sakarwa sumar kaina da ke tsefe ruwa,sai faman lumshe ido nake ina nazarin ‘anya zan amince na bayar da kyautar abu mafi muhimmanci a rayuwata? Shin in ma na yarda Mama za ta iya ganewa? ’ sai kuma na cije leɓena na ƙasa kafin na ɗauro towel na fito.
Mama na tarar zaune bakin gadona hannunta riƙe da wata sarƙa mai shegen kyau sai juya ta take.


“Zo nan ki gwada na gani in za ta yi miki ” na ji furucinta daga sama ,kusa da ita na matsa tare da karɓa na duƙa na ɗaura sarƙar ƙafar na saka ta tsakiyar biyun srkoƙin da ke ƙafar haguna.Wani abu mai kamar shock ɗin lantarki na ji ya ɗan kama ni,sai kuma na ji kamar ƙafar ta yi min nauyi amma duk da haka bai hana ni bayyana murnata ba ganin farar ƙafar tawa ta ƙara yin kyau .
“Na gode Mama!” na furta ina shafa sarƙar,ba tare da ta ce komai ba ta tashi ta fita na bi bayanta da kallo ina tambayar zuci ‘ lafiya mike damun Mama?’ ba yau ba ne ta fara bani kyauta irin wannan ba,hasali ma duk ita ta bani sarƙoƙin da ke ƙafata kasancewar saka ta ya zama kamar al'adarmu ce Buzaye.




A gaggauce na shirya cikin rigar bacci na haye bed,lambar Anty Maimuna Yayata wacce na bi ma na kira bayan mun gaisa na marairaice murya na ce “anty don Allah ki kira Mama ki ce ki na so na zo na taya ki aikin abincin sallah,wallahi duk Ya Mustapha ya takura ni ina tsoron ya dake ni ”
“Ai kuwa dama ina da niyyar yin haka sai dai sanin halin ki na ƙiwa shi yasa ban roƙi alfarmar ba” ta faɗa ta na dariya,ni ma dariyar na yi kafin na kashe .
Ina nan kwance ina tunani har bacci ya ɗauke ni,sai sallar asubah da na tashi.Ina zaune kan tapis Mama ta shigo,ko gaishe ta ban yi ba saboda ta wani haɗe fuska ta ce “ki tashi ki shirya direba zai kai ki gidan Maimuna ”




“Wajen mi kuma yau sallah?” na yi tambayar ina ɓoye murna ta kamar ba ni na shirya plan ɗin ba.
“Sharifa umarni na baki in kin je kin ga abin da za ki yi ɗin” ta na gama faɗa ta fice .
Har da tsallen murna na yi kafin na shirya cikin wasu arnan ƙanana kaya sai na saka doguwar riga sama.Ɗinkin sallana na saka a leda kafin na fito ina kumbure-kumbure irin ban son zuwa,haka na yi wa Mama sallama bayan ta kawo ni bakin mota ta shaidawa direba in da zai kai ni.
Gidan baya na zauna na hakimce tare da tsara text na tura wa Fahad,ina ɗago idona suka sarƙe da na Mubashar direbana.Na tamke fuska ba tare da na ce masa uffan ba,a haka dai ya kai ni har ƙofar gidan Anty Maimuna,da na fita daga mota ƙin tafiya yayi hakan na ja tsuki ƙasa-ƙasa tare da tura ƙofa na shiga na yi tsaye ban fito ba sai da na ji ƙarar mota.
Bayan layi na nufa inda muka aje magana da Fahad zai tsaya jirana,ai kuwa ya na zaune kan tsohon mashin roba-roba.Ina haɗa ido da shi na ji sanyi ya ratsa ni,da ya sakar min makirin murmushinsa kuwa ji na yi kamar na some don daɗi .A shagwaɓe na ƙarasa shi kuma ya wani jawo ni kaina ya bugu da ƙirjinsa,“babyna!” ya furta cikin wani salon tayar da hankali ya na jan numfashi,ban kai ga amsawa ba ya fara shafa yatsuna da suka sha lalle.
“Zo ki hau yau ke za ki tuƙa mu ” ya furta ya na daɗa jawo ni,da murna na hau babur ɗin ya na bayana na lula da mu a direction ɗin da yake nuna min.Hannuwansa biyu sarkaye da cikina,haɓarsa kan kafaɗata haka nake tuƙin ba tare da mun ishi kowa kallo ba kasancewar muna cikin babban birnin Niamey har muka isa wani haɗaɗen gida.Fahad ya saka babur ɗin ciki ni kuma ina take masa baya har cikin falon ɗakin,tun a nan wasa ya fara zalamarsa ta fito ƙarara musamman da na cire abayar sama .
Rawa ta kai rawa har muka zube kan doguwar kujera,a yadda na ga Fahad ya fita hayyacinsa na gansa kuma a zahiri babu sutura jikinsa ya tado min tsohuwar fargaba da tsoron da na binne tun gida ........
[18/04 à 09:34] MRS SADAUKI 👑: *SAURAYINA*💅🏻💅🏻💅🏻




LoVe and HoRrOr story💔☠️




```MRS SADAUKI```✍🏻
Dedicated to Autar Manya👑
*FCWA*☀️
____________________________________________________________________________________________________






Page 2




Yadda Fahad ya raba mu kaf da suturar jikinmu yasa na sadaukar na miƙa wuya ,na rumtse ido ina jin wani baƙin ciki na taso min a ƙahon zuciya.Jira kawai nake na ji azaba ta ratsa ni kamar yadda nake ji ƙawayena na faɗa da zafi sex ɗin farin sai dai shurun da na ji yasa na buɗe idona.Fahad na gani a zaune ya kafe jikina da ido kawai,na ɗan yunƙura na tashi zaune ban kai ga tambayarsa ba na ga jini duk ya ɓata gun da na kwanta.
“Jinin mine ne?” na tambaya a ɗan tsorace,sai a lokacin ya kafe ni da mayun idonsa masu saka zuciyata rauni.
“Dama kin san ki na period ba ki faɗa min ba umhum?” ita ce tambayar da yayi min.
Na girgiza kai cike da tsoronsa na ce “ a'a sai fa sha biyu ga wata nake yi ko ka manta?”
“To mi ya kawo shi tara ga wata iyeee?” ya min wata tsawa da tasa duk na firgice har na kasa basa amsa,ya ci gaba da cewa “wato magani kika sha ko?”
“A'a wallahi Had ban sha komai ba sai dai in stress ce ta sa ya zo lokacinsa bai yi ba” na faɗa cikin rawar jiki muryata na rawa.
Wani wawan mari ya ɗauke ni da shi kafin ya ce “kenan baƙin cikin kasancewa da junanmu kike? Sharifa ba ki sona! Yanzu na gane da ba ki sona yayi na gode” ya na gama faɗa ya dire ya nufi wata ƙofa ya shiga can sai na ji ƙarar ruwa alamun wanka yake yi.






Hankalina ne yayi mugun tashi ganin irin fushin da yayi har da ikirarin wai ban sonsa,wanda a duniya in akwai kalmar da na tsana bayan wannan take.Cikin fitar hayyaci na miƙe na bi bayansa, tsaye yake shower na ta shatatar ruwa a kansa,amma farin sanin da na yi masa har na fahimci idonsa ma zubar ruwan suke a haka ya watso min su sun ja kamar nunannen tumatur.Kamar wacce ta zauce na taka gun shi,abin da na yi sam ban yi tunanin zan iya taɓa jikin nasa ba ma amma sai ya wani kwaɓe min hannu ya tura ni na yi tangal-tangal zan faɗa ga madubi yayi saurin caɓko hannuna ya haɗe ni da ƙirjinsa a tare muka saki ajiyar zuciya.


“Had ina son ka don Allah kar ka sake furta haka! Zo ka yi a hakan!” na furta cikin gwanjin kuka ina mai matse damatsan shi irin na ƴan dambe.
Muryarsa na ɗan rawa ya ce “ko na yi ba zan samu yadda nake so ba babyna!” yadda numfashinsa ke fita ma kawai ya tabbatar min ya na cikin tsananin buƙata.




Ban da abin cewa kawai sai na shige jikinsa na yi lamo,da ƴan dubarun da muka saba samar wa kanmu nutsuwa a duk lokacin da muka haɗe club muka yi a nan toilet kafin mu fito.




Sai da na goge inda jinin ya ɓata sannan na yi ƙunzugu da kallabina,a haka muka fito ya mayar da ni gidan anty Maimuna.Ina shirin sauka daga babur motar gidanmu na tsayawa,ta glass muka haɗa ido da Mubashar direbanmu wanda ban san uwar mi ya dawo yi ba.






“Had ka tafi” na furta zuciyata na ɗan bugawa yayin da sam na kasa ɗauke idona kan Mubashar wanda alamu yayi suman zaune daga cikin mota.
Fahad ya kamo tsintsiyar hannuna ya ce “wane ne wancan ɗin?”
“Sabon direban gidanmu ne ” na basa amsa ba tare da na maido dubana kansa ba.
“Shi ne kuma duk kika firgice haka? Ko akwai wani abu tsakanin ku?”
Sai a lokacin na kalle shi,na ce “Allah kiyaye min baƙauyen? Mi zan yi da shi?”
“To tsoron mi kike?”
“Kar ya je ya faɗa wa Mama ya ce ya ganmu tare”
“Ki gargaɗe shi mana ai ƙasan ki yake,ki masa barazana in ya faɗa za ki sa Papa ya kore shi” Fahad ya faɗa ya na wani mirza yatsuna.
Na saki murmushi na ce “ina son ka nawa! Je ka kawai sai mun yi waya”
Ya sakar min murmushi ya na mai tuƙa babur ɗinsa,sai a lokacin Mubashar ya fito hannunsa riƙe da leda wacce ita ɗin ta kasance tawa wacce na saka kayan sallana.




Ya zo gabana ya tsaya ƙiƙam kamar wani soja,dogo ne irin sosai don ya fi Fahad zati da faɗin ƙirji damatsa kawai Fahad ɗin zai nuna masa shi ma don ya na ɗaukar ƙarfe ne ya na sport kuma.




Ledar da ya miƙo min na karɓa,har na juya zan tafi na ji maganar shi daga sama “daga ina kuke? Wane ne wancan ɗin? Ina kallabinki yake kika bar gashin ki a buɗe ya na shan iska?”




Takaicin da ya rufe ni a matsayinsa na ƙasƙantace mai aiki gidanmu yasa ni juyo cikin fushi na ce “daga gidan ubank....” ɓarin makauniyar da na ji ne ya hana ni ƙarasa abin da na so faɗa ɗin.


Azaba da raɗaɗin marin yasa na kai hannu na dafe kumcin da ya mara ina mai fashewa da kuka.Dakyar na iya buɗe idona da na ji yanayin ganinsu ya ragu,don buji-buji ma nake ganinsa sai hucinsa da kunnuwana ke jiyo min.
Ya nuna min yatsa ya ce “duk ranar da wannan ƙazamin bakin naki yayi gigin zagina sai na zubar miki da haƙora!” ya na gama faɗa yayi tafiyarsa ya bar ni shaye da mamakinsa.Wai yau ni ce Mubashar ya mara,sai da motar ta ɓace ma ganina sannan na duƙa na ɗauki ledar da ta faɗi na je na shiga gidan anty.




Wanke fuskata na yi da pampon tsakar gida kafin na shiga ciki,daga kitchen ta amsa sallamar da na yi mata .Ni kuwa ɗakin da nake shiga a duk lokacin da na zo gidan na nufa, toilet na shiga na yi wanka bayan na fito ne na je kitchen na gaishe ta tare da roƙonta ta bani auduga.


“Je ki ɗauko a ɗakina,kin san Chéri tun jiya aka kira shi a Company tsabar iskanci wai mission za su je” anty Maimuna ta faɗa ta na juya tukunyar miya.
Na yi ƴar dariya na ce “ai duk wacce ta auri soja ba ta more aure ba,ina dalili ba za ku sha love ba”
Dundu ta min a baya ta ce “ba ki san fa'idar auren soja ba yarinya shi yasa”
“Mi haɗi na da soja dama a bar ni da Had ɗina ɗan Ball ” na faɗa tare da ficewa na je na ɗauko na kimtsa kaina,sai kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login