Showing 3001 words to 6000 words out of 24314 words

Chapter 2 - SAURAYINA BOOK COMPLETE DOCUMENT BY Mrs Sadauki .txt

10 Jan 2025

2216

na koma na kama wa anty aikin.












MUBASHAR




Tun ranar farko da ya zo gidan ya ƙyallara ido ya ga Sharifa ya ji Allah ya jarabce shi da muguwar kaunar ta ,sai dai abu guda ya lura da shi kanta na rawa ba ta tsoron kowa gidan daga babban yayansu sai Mama.Hakan kuma ya samo asali ne daga Papa wanda shi ne ke sangarta ta duk abin da take so shi za a yi sam bai son ana takura ta.
Duk abin da Sharifa ke yi Mubashar na ankare da ita, ya sani sarai ta na zuwa gidan rawa don ya sha bin ta a ɓoye amma abun na basa mamaki yadda Papa bai ɗauki hakan wata matsala ba tun da a gabansa take fita ɗin.


Yau lokacin da Mama ta sanar da shi zai kai ta gidan anty Maimuna tun da safen nan sam sai ya ji hankalinsa bai kwanta ba.Wannan yasa ya tsaya sai da ya tabbatar ta shiga gidan sannan ya dawo,a saman hanya ne ya lura ta manta ledarta bai yi saurin komawa ba ya bari ne sai an ɗauki lokaci ya je ya kai mata ashe rabon ya je ya ga abin takaici.


Madubin idonsa babu abin da suka nuna masa sai fuskar Fahad wanda babu abin da ya fi shi da shi na dangin kyau sai hasken fata.Mubashar ya bugi sitiyarin mota ya na jin wani baƙin ciki na daɗa rufe shi,a haka har ya isa gida.Dakyar yayi wanka ya shirya cikin farar shadda wacce Papa ne ya basa ita sabuwa dal a leda,bai saka hulla ba haka ya fito ya zauna zaman jiran mai gidan nasa wanda a tare za su je sallar idi.






Papa ya fito cikin shirinsa sai baza ƙamshi yake,fuskarsa cike da annuri ya ce “mu je ko?”
Miƙewa Mubashar ɗin yayi ya shiga ya zauna mazaunin direba,Papa na gefensa tun da suka ɗauki hanya suke kabbara har suka isa.Bayan sun dawo kuwa har falo Papa ya ja shi suka je don cin abinci amma fafur Mubashar ya ƙi sai zubo masa nasa aka yi ya je ɗakinsa,ba don an haramta yin azumi ranar sallah ba to da tabbas azumi ya miƙe da shi tsabar yadda zuciyarsa ke cike da ƙunci.Kishin Sharifa kuwa ya rufe masa ido musamman yadda ta bar sumarta ta buzaye a buɗe sai kaɗawa take,ya rumtse ido a can ƙasan zuciyarsa ya ce ‘ Allah kaɗai ya san iyakar mazan da suka gan ta a haka ɗin’








A can bangaren Fahad kuwa ya na isa gida da kashin awaki ya fara cin karo da shi wanda ƙanwarsa ke ta faman tattara shi wuri guda.Ya ja tsuki,don a kullum ya na takaicin kasancewar shi ɗan nan gidan ya so ace gidan masu kuɗi aka haife shi.Ɗakinsa ya wuce wanda ko ƙyaure bai da sai labulen wani koɗaɗen yadi,maimakon ya fara shirin zuwa sallar idi kamar yadda kowanne matashi musulmi yake a'a kawai sai yayi kwanciyarsa kan cakusasar katifa ya ɓingire baccin da bai yi ba a jiya ya na tunanin yadda zai yaga mutumci Sharifa.Ba shi ya farka ba sai ƙarfe ɗayan yara,ko wanka bai yi ba ya je ya buɗe tukunyar da ke kan murhu dafa duka ya gani ta macaroni ya ja tsuki ya ce “tsabar baƙin ciki ko nama babu sunan wai nan sallah ake yi”
Mahaifinsa wanda ke can gefe ya na sauraren rediyo ya ce “saboda ba ka kawo ba shi yasa ba a saka ba”
Fahad ya taɓe baki kawai har zai zuba abincin ya ci ,Umma mahaifiyarsa ta ce “ka ga wani abinci nan da aka kawo gidan maƙwabta zo ka ci jar miya ce da naman kaza”


Fahad ya washe baki ya je ya karɓa,ba wanke hannu ko Bismillah ya shiga kwasar girki.Can ƙasan zuciyarsa kuwa cewa yake ‘yo in ba don ina son saya wa kaina mutumci wurin babyna ba ai da gidansu zan je na ci ɗuwawun kaji har sai na gaji! ’ sai kuma ya ja tsuki a fili.
Umma ta ce “lafiyar ka kuwa?”
“Wallahi Umma wani banza ne kawai ya firgita min Sharifa ”
Umma ta washe baki ta ce “wai ni kam sai yaushe za ka kawo min ita na gan ta? Ko za ta zo ta gaishe ni ga sallar nan?”
Fahad ya ƙyalƙyace da dariya ya ce “haba Umma a wannan gidan ne zan gayyaci Sharifa? Kin san kuwa waye mahaifinta? Shararren mai kuɗi ne fa irin manyan buzayen nan ne wanda Nera ta kwanta”
“To in ba da abun ka ba Fahad mi yake? Ai ba a canza wa tuwo suna,ka sani in ta zo ta taimaka mana da kuɗin da za mu gyara gidanmu?”
“Umma har yanzu fa ɗaliba ce ba ta gama karatu ba,ina za ta samu kuɗi?”
“Mahaifinta za ta yi wa magana mana”
“Hum! ” shi kawai Fahad ya yi,don duk yadda suka kwashe shekara biyu suna soyayya ko da wasa bai taɓa nuna wa Sharifa ya na son dalar ta ba,gani yake tsoronsa da take ji duk zai zube in ta fara basa kuɗi.Sannan yanayin yadda yake shigar tsadadun kaya ko ita ba za ta yi tunanin talaucinsu ya kai har haka ba.
Ya na gama cin abincin ya je ya ɗibi ruwa ga randa ya je yayi wanka,shiri yayi mai kyau ya fesa turare bai zarce ko ina ba sai majalissar su ta ƴan zaman banza,a sha shayi a zagi mutane masu wucewa da hirar ƴan mata da duk wani dangin shiririta.








SHARIFA




A gidan Anty Maimuna na yi wunin sallah mun ci mun sha mun yi hotuna ni da ita,lokacin da mijinta ya zo shi da wani abokinsa suka zo mai suna Ali mai mayen kallo da makirin murmushi.Duk yadda na so guje masa amma sai da ya karɓi lambata kafin su tafi.
Bayan sallar magrib muka yi waya da Mama ta sanar da ni Mubashar na kan hanya zai zo ya ɗauke ni.Haka kawai na ji zuciyata na buga wa,ina nan zaune kuwa sai ga shi ya shigo da sallama kasancewar dama ya san Anty Maimuna in ta je gida shi ke maido ta nan ɗin.
A mutumce suke gaisawa tare da yi wa juna barka da Sallah kafin mu ɗunguma mu fito,ban sani ba hira ce ta yi daɗi ko me kawai dai na samu kaina da buɗe gidan gaba na zauna sam ban farga ba har sai da ya soma tuƙi na ji numfashinmu na garwaya.




A hankali na ɗan saci kallonsa,tuƙi yake a hankali kamar bai son yin gudu sai bin ƙira'a Sudais yake yi.Wayarsa ta ɗau ruri wacce ya jona da motar, ya ɗaga ba tare da ya cire ta a bluetooth ɗin ba.
“Assalamu aleykum yaron albarka” na ji muryar wata mata ta furta.
Sai da ya saki murmushi mai sauti kafin ya amsa a shagwaɓe,ni abun ma dariya ya ban.
“Wa'aleykum Salam Ya Ammy kin wuni lafiya?”
“Alhamdullah! Lafiya lau ɗazu mun tafi gidan gaisu ne na zo na tarar da wani kiran naka.Am... muna magana ka ce ka samu matar aure ,fatan dai mai tarbiyya ce Malama kamar dai kai,ta iya girkin gargajiya ne irin miyar kuɓewa da ta ganye?”


Wani murmushin ya kuma yi ya na mai kallona sai muka haɗa ido,ba tare da ya janyen idonsa kaina ba ya ce “Ammy ina tuƙi in na sauka zan kira ki” ƙittt ya kashe.


Haka kawai na ji haushi da ban ji amsar da ya bata ba,sai kuma na taɓe baki kafin na mayar da hankalina kan hanya a haka har muka isa gida ina shirin fita ya rufe ƙofofin duka.....
[19/04 à 13:33] MRS SADAUKI 👑: *SAURAYINA*💅🏻💅🏻💅🏻




LoVe and HoRrOr story💔☠️




```MRS SADAUKI```✍🏻
Dedicated to Autar Manya👑
*FCWA*☀️
____________________________________________________________________________________________________






Page 3




“Wane iskanci ne wannan?” na furta a harzuƙe ina kallonsa raina a ɓace,akwai haske hakan yasa na ga lokacin da annurin fuskarsa ya ɗauke ya maye gurbinsa da haɗe rai.Muƙut! Na haɗiye wasu yawu,amma da yake ina da ƙarfin hali da ji da kai sai cewa na yi “ kar fa ka manta a karkashin innuwata kake aiki?”
“Sai aka yi me?” ya tambaya a dake.
“Sai ka girmama ni ” na basa amsa haɗi da murguɗa baki.
“Kin manta abin da na faɗa miki ɗazu ko sai mun je gun Mama na sake jaddada miki?”


“Yi haƙuri don Allah ka ji Mubshar!” na yi saurin faɗa cikin rawar murya.
Ya saki wani makirin murmushi ya ce “ki kiyaye ni bari ganin ki na auta zan ɓaɓalla ki ne kuma ba za a min komai ba tun da amanar ki aka ban ”
“To na ji ka buɗe na fita”
“Yawwa kuma abu na gaba kar na sake jin ƙazamin bakin ki ya ambaci tsarkaken sunana”


Idona ne ya ciko da ƙwalla na ce “ni ce ƙazama?”


Bai bani amsa ba sai motar da ya buɗe ya fice ya bar ni nan zaune,dakyar na iya fiddo ƙafafuwana waje na ja su zuwa babban falonmu.Ina shiga da Ya Mustapha na fara cin karo ya sha shiri kamar wani ango,har zan wuce na ji muryarsa “keee?”
Jiki na ɓari na dawo na yi tsaye gabansa “Yaya ina wuni?”
Bai amsa ba sai umarni da ya bani,“je ki gyara fruits su na kitchen ki saka su a frigo su yi sanyi kafin na dawo,sannan ki nutsu in kika kuskura kika yi min ɗan banzan shirmen ki jikin ki zai faɗa miki ”


Yadda yake maganar cike da iko ya ƙara tunzura zuciyata,tuni wani baƙin cikin ya rufe ni.Ido na tsiyayar ruwa na wuce kitchen ɗin.Wata uwar leda ce cike da kayan marmari haka na zauna na gyara su na saka a frigo kamar yadda ya ce ɗin kafin na wuce ɗakina.Kan bed na haye na fashe da kuka,na ɗauki lokaci mai tsayi kafin na bai wa kaina haƙuri na tashi na yi wanka.Ina tsaka da shafa mai Mama ta shigo,“Sharifa zo ki gaida antyn ki ga ta nan a falo ” ta furta fuskarta cike da annuri.
Na turo baki gaba na ce “ai dama na san ita ce za ta zo tun da ya jido fruits sai ka ce ɗiyar gwal sai wani jiji da kai yake ”
Mama ta min tsawa “zan ci mutumci ki! Babban yayan naku kike faɗa ma haka? Maza ki saka kaya ki fito” ta na gama faɗa ta fice ,a gagguce na kimtsa na fita falon.
A hakimce na gan ta a zaune ta wani sunne kai su na hira da Mama shi kuma gogan ya kafe ta da ido ya na sakin murmushi.




Sanin halinsa yasa na daure na yi sallama,kafin na gaishe ta “anty Nafi ina wuni?”
Sai a lokacin ta ɗago fuskarta wacce ke ɗauke da simple make-up ta yi kyau sosai duk da ta na baƙar mace,“lafiya lau my lil sis fatan kin yi sallah lafiya?”
“Lafiya lau ya gida?” na faɗa ina ƙirƙiro murmushin dole don ni Allah na gani ba ta kwanta min ba tun farkon kawo ta gidanmu ,lokacin da aka kai lefe kamar na yi hauka haka na ji.




“Alhamdullah!” ta amsa a taƙaice ta na satar Ya Mustapha da wani mayen kallon love.
Na taɓe baki ina shirin tafiya na ji Mama na cewa “ki kawo mata ruwa mana Auta ”




‘ Hum! Dama na sani yau zan koma ƴar aikinta har sai ta tafi kuma!’ na faɗa a zuci na nufin kitchen.Ƙaton tray na ɗauka na jera jus da kofi biyu sannan na ɗauki wanda ake saka fruits na jera su tuni sun yi sanyi kuwa.
‘Tsabar iskanci saboda mutum guda aka sayo duk wannan abun mtws ! Shegiya mayuwanci ƴar talakawa yanzu ta buɗe hanji ta yi ta ci’ shi ne abin da nake faɗa a zuci har na iso falon sam ban lura da Mubashar tsabar yadda idona ya rufe da takaici kawai sai ji na yi na yi tuntuɓe ashe ƙafarsa ce.Nan wani abun mamaki ya faru duk abubuwan da ke kan tray ɗin suka yi sama amma kamar almara sai suka dawo suka zauna a trayn ba tare da sun zube ba.






Na ja wata ajiyar zuciya,sai a sannan na lura ma kan cinyarsa nake zaune dirshen .A kunyace na miƙe na je na ajiye tray ɗin kan table,kusa da Mama na zauna wacce na lura kamar duk falon ita kaɗai ta lura da abin da ya faru.




“Zan koma yalaɓai sai kun fito” Mubashar ya faɗa ya na mai miƙewa,Mama ta ce “kar ka yi nisa dai ka san na ce za mu je wani wuri”
“To Hajiya ! ” ya amsa tare da ficewa.




Mama ta kama hannuna ta ce “auta mu je” miƙewa na yi muka basu wuri.Ya Mustapha kuwa kamar jira yake haka ya miƙe ya koma kusa da Nafi ya soma ciyar da su ya na yi mata hirar soyayya har suka ƙoshi,an ɗauki lokaci mai tsayi mu kuma kafin mu dawo falon hannuna riƙe da ledar da Mama ta jibgo wa anty Nafi kaya.




Har bakin mota na yi mata rakiya sai godiya take zuba wa Mama kafin ta ce “Auta sai yaushe za ki je gidanmu?”
Na ɗan murmusa kawai,Ya Mustapha ya zuba min ido hakan yasa na dubi Mama wacce ke tsaye sai cewa ta yi “zan sa Mubashar ya kai ta jibi sai ta yi miki wuni”
A haka sai suka tafi,na yi tunanin ciki za mu koma amma sai na ji Mama na cewa “za mu je ki yi shopping Auta ” sai kuma ta soma kiran sunan Mubashar,babu jimawa ya fito ya na kaɗa key ɗin mota kamar tasa.




Gidan baya muka zauna,mai gadi ya buɗe get yayin da shi kuma ya cinna hancin motar waje.Sai da muka hau kan titi sannan ta sanar da shi Mall ɗin da za mu je,da muka isa har zai zauna cikin mota amma Mama ta ce mu shiga tare.Turarruka ne na zaɓa,sai pant da bra yayin da ita kuma Mama ke ta zaɓar min wasu kayan daban ga mamakina wai har da hijabai abin da bai sha min kai ba muddin ba sallah zan yi ba.
Mubashar ne ya ɗauko su ya kawo su mota bayan an biya,sai hira Mama ke jansa da ita wacce ta kasance ta ƙauyensu ce da kuma Ammynsa.A nan ne na tsinci cewa shi ɗin malami ne yayi makaranta can Borno zaman tsangaya,don har haddar Alkur'ani gare shi a kai kuma hakan ta faru ne saboda burin mahaifiyarsa ne wacce ke can zaune yanki Tilabery.
Shiru kawai na yi ina nazarin abin da ya faru ɗazu wanda tabbas bai da maraba da tsafi,a zuci na raya ‘kenan malamin tsibo ne ko me?’ sai kuma na ji tsoronsa ya kama ni don a duniya ina tsoron lamarin tsafi ko asiri.Muna isa gida na fice ko kayan ban ɗauka ba,direct sashena na shige ina mai kiran layin Fahad amma ga mamakina sai ji na yi ya na kan layi wato waya yake.
Sama da minti talatin ina fafutukar nemansa amma sai hirarsa yake alhalin ina da tabbacin ya na ganin kirana.Tuni zuciyata ta tsinke na rungume matashin kai sai hawaye shaaa,tun ba yau ba na san da cewa Fahad na da ƴan mata dayawa yawanci su suke bibiyar shi wanda na san bai rasa asali da yadda Allah ya yi masa baiwar kyawu.Amma duk da haka ni ta musamman ce soyayyar da yake min ta sha banban da ta sauran.


“Sharifa ga kayan ki nan daga gobe ina son ki fara saka su,kar na ƙara ganin ki cikin matsatsun kaya sannan duk inda za ki je dole Mubashar ne zai kai ki” furicin Mama shi ya ida ruguza laɓuɓuwar zuciyata mai cike da rauni,mai son kuka an jefe shi da kashin awaki mai zai yi? Kawai sai na fashe da kuka wiwi.
Ina jin lokacin da Mama ta hau gado ta jawo ni jikinta,“Autana ki na ji na? Duk abin da nake min ƙauna ce,kuma kowacce uwa haka ya dace ta yi wa ƴarta ta bata kariya.Na ji duk wayar da kika yi da Fahad a jiya,ki sani shi ɗin ba masoyin ki ba ne shekara biyu kenan ku na soyayya an ce ya kawo sadaki ya ƙi ina ce dai ki na ganin duk yadda Papan ku ke son ki sai da ya ɗau matakin hana shi zuwa nan gidan.Duk wanda yake sonka auren ka yake yi ba ya dinga ɗaukar ki ba ku na yawon club-club ba”


Duk da irin ƙuncin da nake ji sam ba zan iya sauraren ana ɓata Fahad ba,hakan yasa na yi saurin cewa “A'a Mama kar ki ce haka wallahi zan iya rantsuwa da Alkur'ani Fahad na mugun sona,maganar aure kuma lokaci ne dole mu jira shi”


Mama ta ɗago haɓata,ido cikin ido muke kallon juna kafin ta ce min “ki na son Fahad?” na gyaɗa mata kai na ce “fiye da kalmar so”
“Kin tabbata ya na son ki zai aure ki ko?”
“Eh Mama!”
“To ki ce ina son ganinsa gobe!” ta na gama faɗa ta kwantar da ni kamar wata ƙaramar yarinya kafin ta fice,na bi bayanta da kallo kafin na ƙoƙarta na rubuta wa Fahad saƙo sai kuma na kashe wayana.








MAMA


Ta na fita ta wuce ɗakin Papa wanda bai jima da dawowa ba,jiki a sanyayye ta zo ta zauna.
Ya ɗan dube ta ya ce “ya dai?”
“Akan auta ne!” Mama ta faɗa dakyar.
“Ina jin ki”
“Alhaji na ce mi zai hana ka sassauta lamarin nan ka ce Fahad ya kawo duk abin da Allah ya sawwaƙe masa ka aura masa ita hankalin kowa ya kwanta”


Papa ya ɗaure fuska ya ce “duka nawa Autar take? 22years ne fa? Sai na yi mata aure ko karatu ba ta gama ba kuma da wancan yaron?”
Mama ta ce “in an yi auren....” yayi saurin katse ta da “ba za a yi ba!”
Cikin jimami Mama ta fito daga ɗakin ta koma nata ta fara saffa da marwa,tun ranar da ta ɗora idonta kan Mubashar ta gamsu da nutsuwar shi, abu na gaba kuma shi ne yadda ya bata laƙanin yadda za ta tsare mutumci ƴarta.Ta ja wani dogon numfashi ta ce “rashin uwa ke sa a yi uwar ɗaki! Da dai in bari Fahad ya ɓata miki rayuwa gwara na bai wa Mubashar auren ki kowa ya huta” daren nan sam Mama ba ta rumtsa ba sai da ta samo wa kanta mafita,ta kira babban Yayanta Sheik Mohammed ta sanar da shi burinta.






Washegari




Wuraren ƙarfe goma na safe ina kwance kan gado Mama ta shigo cikin shirin fita,dakyar na buɗe baki na gaishe ta.
“Zan fita ki shiga kitchen ki ɗora girki”
Na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login