Showing 9001 words to 12000 words out of 24314 words

Chapter 4 - SAURAYINA BOOK COMPLETE DOCUMENT BY Mrs Sadauki .txt

10 Jan 2025

2213

à 09:02] MRS SADAUKI 👑: *SAURAYINA*💅🏻💅🏻💅🏻




LoVe and HoRrOr story💔☠️




```MRS SADAUKI```✍🏻
Dedicated to Autar Manya👑
*FCWA*☀️
____________________________________________________________________________________________________






Page 5




Cikin second uku na ƙara ƙarewa Ali kallo, kyakkyawan namiji ne son kowa don bai da makusa amma sam ni dai bai min ba.
“Ya jikin naki?” muryarsa ta ƙatse min tunani,ban iya buɗe baki ba sai idona na ɗan juya sai na ga ya saki murmushi kamar a mafarki sai jin na yi ya shafi gefen fuskata,ƙurrr idon Mubashar kanmu wanda ya dawo shi da docter tuni yanayinsa ya canza zan iya hango tsantsar takaici a ƙwayar idonsa.


Dr ya zo kai gare ni ya fara min tambayoyi abin da nake ji yanzu,na girgiza masa kai kawai alamun ban jin komai.Sai kawai ya fita,Ya Mustapha ne ya tambayi ba'asi Mama ta ce “a bar zancen kawai tun da dai mun samu ta farfaɗo ”
“Shi kuma ɗan banzan yaron can fa? Haka kuka bar shi ya tafi? ”
Sai da Mama ta kalle ni kafin ta ce “am... Alamu dai sun nuna kamar Mubashar ya ji masa ciwo a hannu shi ne...shi ne na ce ya biyo mu asibitin a dubasa shi ma”
Wannan karon Ali ne yayi magana “dole na ɗauki mataki akai! Amma yanzu dai ba wannan ne gabana ba,fatana ta warware tun da ina son a gama komai na aurenmu tun da mission zan zan je Kamaru”




Da mamaki a fuskar Mama,amma sai ta shanye shi sanin Ali abokin Mustapha ne gun aikinsu guda.
Mubashar dai ne ɗan faɗi ba a sa ka ba ya ce “wane aure kuma?”
Sai a lokacin Ali ya juyo ya dube shi,sai kuma ya maida dubansa ga Ya Mustapha ya ce “abokina ba ka yi masu bayani ba?”
“Mu je sergent na kirana ” Ya Mustapha ɗin ya faɗa ya na mai duba wayarsa,Ali ya fiddo kuɗi ya ajiye gefen kaina suka fice Mubashar ya bisa da mugun kallo kafin ya maido hankalinsa kaina.
“Mi kike ji yanzu?” ya jefo min tambayar a dake,ban basa amsa ba sai harara da turo baki gaba.
“Ba ta jin komai ,ƙila da ƙarin ruwan sun ida gida za mu je” Mama ta faɗa ta na murmushi, Mubashar ya sauke ajiyar zuciya ya na mai ci gaba da kallona,tsabar takaici na lumshe ido ina tunanin Fahad ɗina ina tsoron Ya Mustapha da baƙin abokinsa Ali su yi masa wani abun.Tuna irin dukan da Mubashar yayi masa ya saka na ƙara jin ɗaci a raina har ban san lokacin da na ce “Mugu!” sai kuma na fashe da kuka wiwi.
“Ke lafiyar ki?” Mama ta yi saurin tambaya ta.
Cikin kuka na ce “Mama ina son ganin Had don Allah a kai ni ɗakinsa”
“Tuni an sallame an ɗora shi malama don haka ki nutsu bai asibitin nan” Mubashar ya faɗa ya na mai ƙaraso wa kusa da ni ya riƙe min hannun da aka saka wa ƙarin ruwa,cike da takaicinsa na kai bakina na gantsara masa cizo.
Tamkar wata mahaukaciya haka na dinga cizon duk inda na samu a jikinsa hatta ƙirjinsa,duk yadda ya so kuma na tsaya na nutsu kamar yadda na lura amma na ƙi ba sa haɗin kai har sai da na cire robar ƙarin ruwan.




Duk wani saurin ƙarfina na tattara na ture shi baya,cikin rashin sa'a kuma ni ma sai na biyo shi na faɗi kan ƙirjinsa kaina ya bugu da kansa.Mubashar kuwa da mugun sauri ya rumtse ido jin azaba ta ratsa kwanyayarsa don buguwa yayi da ƙarfen gado.




Na yunƙura dakyar na tashi zaune kan ruwan cikinsa,“aiii!” ya saki ƙara da sauri na dire na zauna ƙasa ina kallon yadda goshinsa ke zubar da jini.Mama da likita suka shigo a tare hankali tashe,sai yanzu na lura ashe Mama ta fita.




“Innalillahi ta jima ciwo ko? Likita duba min kwanyarta kar ace ta taɓu” Mama ta faɗa ta na mai nufar Mubashar wanda tuni ya tashi zaune.




“Ni lafiyata lau kuma gida nake son zuwa” na furta cikin kuka.


Sai da aka yi wa goshinsa bandeji ni ma likita ya duba ni kafin mu dawo gida.A falo na zube ina ta zuba wa Papa shagwaɓa sai dai ba ta je ko ina ba na ji ya na jadadda maganar Ya Mustapha “Yayan ki ya ce min abokinsa na son ki kuma da aure don haka zan baku dama ta biyu ke da Fahad ko ya kawo kuɗin auren ki ko kuma shi Ali ɗin ya kawo.Za a ɗaura aure in Allah ya so bayan kin gama karatu sai ki tare”


“Papa Ya Mustapha ya hana Had ya shigo gidan nan fa,ɗazu ma sai da suka yi ta yin rikici da mai gadi” na faɗa kamar zan yi kuka.
Papa ya ce “zan yi wa mai gadin magana”
Tashi na yi na koma ɗaki,na kira Fahad bugu biyu ya ɗaga “Had don Allah ka yi haƙuri abin da ya faru,Papa kuma ya ce na sanar da kai ya amince da aurenmu don haka ka kawo duk abin da kafi ƙarfi a ɗaura mana aure in na gama karatu kuma sai in tare”
“Ban shirya aure yanzu ba! A ƙara min lokaci ni da kaina zan tsara yadda auren zai kasance ba ƴan gidanku ba” ya na gama faɗa min haka ƙittt ya yanke kiran.Wani takaici ne ya rufe ni,ban san mine ne Fahad ke taƙama da shi ba duk wata hanyar tsiranmu sai ya daƙile ta na yi tunanin zai yi murna da hakan amma girman kansa da gadarar shi sun sa ya watsa min ƙasa a ido .Karon farko kenan da na ji na tsani soyayyarmu,tun ba yau ba na fahimci na fi sonsa fiye da yadda yake sona.Na ja wata ajiyar zuciya ina jin wani abu na min yawo a jiki yayin da kuma zuciyata ke raya min wani matakin da na tabbatar zan cutu amma ƙila hakan ne kawai zai sa Fahad ya shiga hankalinsa .








FAHAD


Ba ƙaramar jibga ya samu daga hannun Mubashar ba, wannan yasa ya kasa tuƙa babur ɗinsa.Ana cikin haka ne kuma Ramlah ta rugo da gudu ta na sanar da su Sharifa ta suma,duk a tare suka dugunzuma har da shi.Wurin ciciɓar ta ne ma ya fahimci kamar ya goce a hannu don har sai da ya saki ƙara,Mama ce ta basa umarnin ya biyo bayansu hakan yasa a asibiti aka duba hannun nasa bai wani jima ba kuma ya kira Kb ya zo ya ɗauke shi.Babur ɗinsa ma ya na can gidansu Sharifa, lokacin da ya zo ba ƙaramin tashin hankali Umma ta shiga ba.Ga jaririn da suka maƙala wa sunan Jamilu mai shegen kuka ne duk sai Umma ta ida rikicewa.Tambayar duniya ta yi wa Fahad amma ya ƙi sanar da ita gaskiya,a doli ta haƙura ta dai shimfiɗa masa tabarma tare da nemo masa lemu mai sayin.A gabanta ya ɗauki kiran Sharifa a yanzu,ya na kashe wa ya dubi Umma ya ce “ina son na yi kuɗi ko don na nuna wa iyayen Sharifa ba su suka baiwa kansu ba.Kin ji wani rainin hankali wai su za su tsara yadda aurenmu zai kasance,to na ƙi na je ɗin kuma wallahi sai sun san ni suka wulaƙanta”
Umma ta ce “a'a kar ka yi haka! Tun da dai ku na son junan ku ai shi ne abu mafi muhimmanci...” ya tari numfashinta ya na mai cewa “wallahi tallahi ba su ga komai ba sai yanzu ma ne zai fara wahalar da Sharifa,sai sun yi da na sani sun zo su na bani haƙuri”
“Mi za ka yi mata?” Umma ta tambaya da tsoro a fuskarta.
“Kwantar da hankalin ki ban yi mata komai,kawai zan daina ɗaukar kiran ta kuma ni ma ba zan kira ta ba na san ba za ta juri haka ba”
Sai a lokacin Umma ta samu natsuwa.










A can bangaren Mubashar kuwa da zarar ya lumshe ido hoton Ali yake gani ya na shafa kumatun Sharifa.Ya ja dogon tsaki a fili ya na jin tsanar gayen,sai kuma ya saki murmushi tuna yadda moments ɗinsu ya kasance.Ya kai hannu ya shafi wurin da ya ji ciwo,wanda ba don ya rasa control ɗinsa ba lokacin da jikinsu ya haɗu da na Sharifa ba to da tabbas ba za ta iya ture shi ba.Da wannan tunanin ya ɗan samu sassauci ya na mai roƙon Allah ya nuna masa ranar da zai mallake ta.








★★★


Rana zafi innuwa ƙuna,duk yadda na yi ƙoƙarin share FAHAD na kasa kullum cikin tura masa saƙon soyayya da magiya akan ya zo mu yi aure nake amma a wofi an tsikari kakkausa.Ko kaɗan bai nuna ya ga ma kirana ballantana na san ran zai ɗauka,gefe guda kuma Ali sai baje min kolin na sa salon soyayyar yake.Kullum cikin bazata yake min, kyaututtuka tun ban nuna komai har na fara jin daɗinsu.A duk in ya samu sarari ya kan zo gida mu yi hira,ko kuma ya je can makarantarmu in lokacin shan iska yayi wani sa'in restaurant muke zuwa mu ci abinci in banda ra'ayin ya kawo min komai.A sannu a hankali muka fara shaƙuwa da shi har ta kai in bai zo ba zan ɗauki waya na kira na ji dalili,amma hakan bai sauya son FAHAD a zuciyata ba ya na nan daram.




Muna tsaye ni da Ali ya na bani labarin lokacin da su na sabbi a aikin soja ya ce“ ina faɗa miki Habibaty mun ci kwakwa,abinci fa da zafinsa muke ci kuma ba zaune ake yi ba a'a muna motsa jiki in mutum ya kawo daidai farantin abincin ne ya damtsa ya ci”
Na ƙyalƙyale da dariya na ce “ai kuwa ni ba zan iya aikin soja ba,to ya kake yi ka ƙoshi?”
“Ke da na ga fa za a ƙwaren kawai na dinga zuba abincin a aljihu” ai kuwa nan ma dariya na ƙara yi ɗagowar ga da zan yi muka haɗa ido da Mubashar wanda a yanzu na ɗauke shi tamkar Yayana tsabar yadda Mama ta jawo shi a jiki ,don hatta abinci ma tare da ahalin gida yake ci sam ba za ka ɗauka bare ne ba don tuni an kawo ma wani sabon direba shi bai aikin komai sai zuwa Imam Malik in ya dawo ne yake koya min karatu .






A take nutsuwa ta zo min,murya na ɗan rawa na ce “Ya Mubshar!” ba mu da tazara sosai na san ya ji abin da na ce,kawai sai gani na yi ya lumshe ido kafin kuma ya buɗe su ya ƙure ni da su kafin ya soma takowa har ya iso sallama a bakinsa ya miƙa wa Ali hannu suka yi musafaha tare da gaisuwa.






“Babu karatu ne?” ya tambaye ni bayan ya dubi agogon hannunsa,tabbas na san da an shiga aji amma na ƙi faɗawa Ali don ban so ya tafi saboda in ya na min hira ina mantawa da damuwa ta.
“Eh! A'a ban sani ba” na faɗa a ɗan rikice,Mubashar ya shafi gemunsa wanda a yanzu yake samun gyara kuma ya ƙara fito da kyawunsa sosai.
“An kira ni ne an ce ba ki shiga aji ba ko zan san dalili?” ya sake watso min wata tambayar,sai na ɗan saci kallon Ali wanda da dukkan alamu bai ji daɗi ba.
“Yanzu zan shiga” na faɗa da sauri ina juyawa saboda yadda Mubashar ɗin ya kafe ni da mayun idonsa,ina tafe ƙafafuna na harɗewa kamar zan faɗi har yanzu ina jin idonsa a jikina.






Bayan tafiyar Sharifa, Mubashar ya ɗan yi gyaran murya ya ce “don Allah ka bar zuwa nan saboda hakan zai taɓa karatunta da ƙimar ta musamman in ka dubi kayan jikin ka”
Ali ya dubi kansa,kakin soja ne yake sanye da su .Ya ɗan haɗe rai ya ce “mi kayan nawa suka yi ?”
“Ba su yi komai ba” Mubashar ya faɗa kafin ya shiga cikin makarantar ya bar Ali nan tsaye shaye da mamaki.Direct ajin su ya wuce ya tabbatar ta shiga kafin ya je ya zauna zaman jiran ta,da ya ga lokacin tashi ya kusa ya kira sabon direban ya tabbatar masa ma tuni ya na kan hanya.






Cours ake amma sam hankalina ya kasa nutsuwa,ina tsoron faɗan Ya Mubashar ɗin wanda a yanzu ya kasance malamina mai koya min karatun Addini.Ana gama darasi na fito ina raba ido don yadda zuciyata ke bugawar nan ya tabbatar min ya na nan bai tafi ba.
“Ga ni a nan!” na ji muryarsa a bayana,na ɗan zabura tare da juyowa muka haɗa ido.Muƙur na haɗe yawu kafin na ce “ashe ba ka tafi ba?”
“Um! Ba ki so gani na ba ko?”
“A'a ni ban ce ba”
“Tun yaushe Ali ya zo nan?”
Sai da na sunne kai kafin na ce “bai jima da tafiya ba”
“Ki ɗago ki ban amsa”
Ƙin ɗagowa na yi saboda na san muddin na yi masa ƙarya zai gane in dai muna kallon juna ne,zip ɗin jaka ta na zuge na ciro waya ina ƙoƙarin kiran direba amma ya fige ta hakan yasa na ɗago.A take tsoronsa ya rufe ni ganin idonsa sun yi ja,murya na ɗan rawa na ce “Zan kira direba ne”
“Ga shi a can ya na jiranmu” sai kuma ya soma tafiya,na take masa baya har muka isa ina kallonsa ya miƙawa direban kuɗi ya ce “ka shiga taxi” sai kuma ya karɓi key ya buɗe mota ya zauna.
Jikina ne ya ɗauki rawa,rabon da na hau tuƙinsa an fi wata uku amma banda zaɓi haka na je na zauna a gaba ya figi motar kamar zai tashi sama maimakon ya ɗauki hanyar gida sai kawai na ga ya ɗauki wata.Tuni idona suka ciko da ƙwalla amma ban ce komai ba,kamar yadda shi ma yayi shirun sai hucin da yake fitowa daga ƙasan zuciyarsa.Mun yi tafiya mai ɗan nisa kafin mu isa wani wurin mai ɗauke da itace dayawa,a hankali yayi parking ya fita ya zagayo ya buɗe min.Na fito dakyar,duk ko ina innuwa ce ya nuna min wani dutse ya ce “zauna!” ban musa ba na zauna ɗin.
Murya a ɗan dake ya ce “kin san abin da yasa na kawo ki nan?”
Na girgiza kai,ya dafe saitin zuciyarsa ya ce “don na baki wani labari ne mai kama da naki wanda ya shuɗe wasu shekaru.Labarin wani kamilin saurayi da wata budurwa ƴar talakawa ”
Ƙurrr na yi masa da ido ina kallonsa kawai,yayin da shi kuma ya ci gaba da cewa “wani saurayi ne suke haukan son juna shi da wata budurwa kullum su na tare in ta na makaranta haka yake bin bayanta,in an aike ta shi ne ɗan rakiya.Iyayenta da iyayensa sam ba sam ba son ganinsu a tare amma suka nace suka biye wa zuciyoyinsu.Ana haka ne shi saurayin mahaifinsa ya shirya masa zuwa ƙasar waje domin yin karatu,hankali tashe ya je kira budurwar ya sanar da ita haka ta kwaso jiki ta zo gidansu kasancewar dama Yayan ƙawarta ne saurayin yasa ta shigo gidan babu wata matsala sai kawai ta yi tsinke ɗakinsa” ya na kawowa nan sai ya tsaya ya na wani lumshe ido,“mugun son da take masa ya rinjaye ta har ta amince da shi yayi sanadiyar rabata da mutumcin ta.Sai bayan komai ya lafa ne suka farga,haka ya taimaka mata dai ta kimtsa ba tare da sanin ashe a wannan daren Allah ya ƙaddarar rabo ya shiga”




“Innalillahi wa'inna ileyhi raji'un ! Cikin shege?” kallona yayi kawai,“tashi mu tafi!” na miƙe da sauri na bi bayansa ina mai cewa “to ya aka yi gaba?” bai ban amsa ba har muka shiga mota.
Kallonsa kawai nake har muka isa gida,da zan fita na ce “Ya Mubshar ka faɗa min mi ya faru mana”
“Sai in an jima zan sanar da ke ,yanzu makaranta an koma akwai jarabawar da zan yi”
Na turo baki kafin na fice,shi kuma ya ja motar ya tsaya bakin get sai da direba ya shiga kafin su wuce.




Ina shiga ciki na zube falo ina faman yi wa Mama ƙorafin na gaji.
“An dai kusa yin auren ki na ga ta rakin kin gaji can ai doli ki girka abinci da kuma aikin gida” cewar Mama.
“Ni dai ban shirya ba sai..” ban kai ƙarshe ba Mama ta ce “in an jima iyayen Ali za su zo ki tashi ki tafi gidan Antyn ki”
Tamkar aradu haka na ji,ko kafin na yi wa Mama tambaya tuni ta tashi.Ni ma ba shiri na wuce ɗakina sai a lokacin na tuna kuma wayata na ga hannun Mubshar.Toilet na faɗa na yi wanka, zuciyata sai matsanancin bugawa take a haka na fito na yi sallah na shirya cikin riga doguwa da hijabinta .Ƴar ƙaramar jaka na ɗauka na fito na yi wa Mama sallama,maimakon na je gidan anty ɗin kawai na cewa mai taxi ya kai ni Imam Malik.
Bayan na biya shi ne na shiga daga ciki,sai kuma na rasa wane ɓangare zan bi tsabar girmanta ina nan ina shawagi a ciki har aka fito sallar Asar nan na ware ido ko Allah yasa na ga Mubshar ɗin sai dai abun takaici duk mazan jallabiya fara ce da su.Tuni idona ya fara kawo ruwa,kamar daga sama na ji an ce “ Ifa ” har ban san lokacin da murmushi ya suɓuce min don shi kaɗai ke kirana a haka.
Ina ɗan waigawa idonmu ya sarƙe cikin na juna,ban taɓa yi masa kallon ƙure ba sai yau dogo ne sosai mai faɗin ƙirji.Ya na da doguwar fuska da dogon hanci,idonsa madadaidaita ne ba su fiya girma ba,bakinsa na ɗauke da laɓa masu kauri baƙaƙe wanda sajensa ya ƙara masa kyawu.Ban san ya iso gare ni ba sai da na ji ya busa min iskan bakinsa,na lumshe ido hakan ya baiwa ƙwallar da ta ciko idona damar saukowa kan kumatuna.Tattausan hannunsa na ji cikin nawa ya na mai cewa “zo nan!” haɗi da jawo ni gefe,sai a lokacin na buɗe ido.
“Mubashar wace ce wannan?” a tare muka juya sai na ga ashe Yayan Mama ne sheik Mohammed.
Gaishe shi na yi sai na ji ya ce “Kamar Sharifa nake gani”
Na ce masa “ni ce!” sai na ga ya kalli hannunmu da ke cikin na juna,sai a lokacin Mubashar ya sake ni.
Sheikh Muhammed yayi tafiyarsa ya na mai cewa “lokacin sallah yayi ta je ɓangaren mata ta yi alwala,in an gama kuma ina son ganin ka a office ɗina”


Na ja wata wawiyar ajiyar zuciya ina saƙa wani abu a raina wanda ban sani ba ko idona ne ba su gane min daidai ba....
[26/04 à 09:57] MRS

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login