Showing 6001 words to 9000 words out of 24314 words

Chapter 3 - SAURAYINA BOOK COMPLETE DOCUMENT BY Mrs Sadauki .txt

10 Jan 2025

2214

ɗan shagwaɓe fuska na ce “Mama don me Saude ba za ta yi ba?”
“Ke nake so ki yi! ” ta na gama faɗa ta fice.Toilet na shiga na yi wanka na kimtsa kafin na fita falo,babu kowa sai ƙaton tv da ke ta magana shi ɗaya.Table na nufa na haɗa tea na sha kafin na wuce kitchen,tuni Saude ta fara gyaran kayan miya da taimakon ta na yi komai.






A ɓangaren Mama kuwa ta dai ce Mubashar ya kai ta wani wuri ba tare da ta yi masa bayani ba har suka isa.
A tare suka shiga har babban falon kamar yadda ta buƙata,su na ta gaisawa da mutanen gidan kafin Sheikh Muhammad ya fito cikin shigarsa ta kamala dogo ne fari tasss ya ɗora gemunsa ka na ganinsa ka ga ahali sunnah.




Bayan sun gaisa ne Mama ta ce “wannan ne dama nake yi maka zance a jiya,ya na hadda alƙur'ani sai dai na Warshi ne irin na ƴan allo to Yaya ina son ya koma kamar dai kai haka a koya masa karatun litattafan Musulunci ”


“Ai duk ɗaya ne karatun Warshi da Habsi,amma in sha Allah za mu yi abin da ya dace.Ya sunan ka?” cewar Sheikh Mohammed.
Mubashar da sai yanzu ne ya san dalilin zuwan nasu wato gata Mama za ta yi masa kenan ya basa amsa da “Mubashar ne sunana”
Nan ya fara yi masa tambayoyi game da makarantar da yayi,kamar yadda ya shaida wa Mama haka ya maimaita yanzun ma ba tare da ya ɓoye komai ba.
“A Borno na yi karatu,a can ne kuma aka koyar da mu wasu laƙanin,wanda da farko muna dai taya malaminmu ne in an kawo masa aikin tsibo daga haka yayi ta koyar da mu amma ban taɓa gwada wa ba sai sau ɗaya a can Tilabery da wani ya ce ya na son wata na masa aiki kuma ya ci.A ranar da ya zo yi min godiya ne Ammyna ta fahimci al'amarin da ke faruwa shine ta ƙone duk kayan aikin sannan ta hane ni da juya ilimina domin sana'a, wannan dalilin yasa ma na fito neman aiki har Allah ya haɗa ni da Hajiya Mama”




Sheikh Muhammad ya jinjina kai bayan ya gama sauraren shi kafin ya ce “Allah yafe mana baki ɗaya ka ci gaba da yin istigfar.Gobe za ka fara zuwa makarantarmu ban sani ba ko ka taɓa jin ana cewa Imam Malik ba? To sunanta kenan.Makaranta ce mai koyi da sunnah da kaucewa duk wani abu da ya saɓa ma koyarwar manzonmu” sosai Sheikh Mohammed yayi masa bayani yadda zai fahimta,kasancewar Mubashar bai da girman kai haka ya tsaya ya saurare shi.
Da za su koma haka ya basa wasu littattafan,a hanya ya na zuba wa Mama godiya har da yin kukan farin ciki.Su na isa gida Mama ta wuce can ciki,shi kuma Mubashar ƙarƙashin innuwar mangoro da ke tsakar gidan ya je ya zauna tare da danna kiran Ammy.
Bayan sun gaisa ta ce “jiya ina ta jira ka maido shiru,ba ka bani amsa ba na ce yarinyar....” yayi saurin katse ta ya na mai cewa “Ammy akwai abun murnar da nake son sanar da ke fa”
“Wanda ya fi wannan?” ta tambaya.
“Eh Ammy! Hajiyar da suka ɗauke ni aiki ce ta biya min makaranta irin ta ƴan gayu,gobe zan fara” nan ya yi mata bayani,sai ga Ammy ta na kukan murna “Alhamdullah! Allah na gode ma dama ya ce in ka yarda da shi zai maka ni'ima ta inda ba ka zato.Ka bani lambar Hajiyar na kira na yi mata godiya, Mubashar ka je hankali ka yi karatu Imam Malik duk Nijar babu makarantar da kai ta,domin har Larabawa ke da kwai cikin masu karantarwar”
“In sha Allah Ammy! Zan sake kiran ki” sai ya kashe tare da nufar ɗakinsa.Ɗan ƙaramin akwatinsa na ƙarfe ya buɗe ya zaro wata sarƙa wacce suke shige da wacce ya bai wa Ammy a shekaran jiya.Sai da ya ɗan juya ta kafin yayi Bismillah ya buɗe lular tsakiya,garin magani ne a ciki wanda Allah kaɗai ya san surkullen da aka yi masa.
“Daga yau ba zan sake yin imani da duk wani abu da ya shafi abu kamar haka ba” ya furta tare da sauke ajiyar zuciya sai ya je ya ƙone su daga ƙarshe.






FAHAD


Abokansa suka haɗa wasa a wani gidan gona ,sanin Sharifa ta na cikin period kuma ba zai samun yadda yake so ba yasa shi fara kiran ƴan matansa uwanda sun fi goma a haka yayi ta nema har ya samu wacce ta yarda su je su watse ɗin.Lokacin da Sharifa ke ta gwada kiransa shi kam bai da lokacinta ,sai dai ya na da niyyar kiranta a gobe .
A gajiye ya buɗe idonsa saboda sam bai rumtsa ba ya samu ƴar mutane ya na ta hole wa da ita,tun dare har asubah abu ɗaya suke.
Fahad ya jawo wayarsa da ke can gefe ya duba,saƙon Sharifa ya gani «Had gobe ka zo gida Mama na son ganin ka,da dukkan alamu lokacin aurenmu ne ya zo» ya na gama karanta saƙon ya ida ture budurwa da ke kan ƙirjinsa ta na sharar bacci.Kayan jikinsa ya fara nema a cikin kayan da ke zube na abokan shiriritar tasa.Ya na gama kimtsa wa ya fice ko ta kanta bai bi ba,babur ɗinsa ya hau ya na tafe ya na gwada kiran lambar sharifa amma ba ta shiga a haka har ya isa unguwarsu inda ya tarar da cincirindon mutane a ƙofar gidansu.Bai kai ga tambaya ba ya hangi motar ƴan sanda ga Umma a zaune ta na sharar ƙwalla.....
[21/04 à 09:07] MRS SADAUKI 👑: *SAURAYINA*💅🏻💅🏻💅🏻




LoVe and HoRrOr story💔☠️




```MRS SADAUKI```✍🏻
Dedicated to Autar Manya👑
*FCWA*☀️
____________________________________________________________________________________________________






Page 4




Da azama Fahad ya nufi motar ƴan sandar,sai dai kafin yayi magana ya ji muryar Nana na cewa “yawwa Maman ga shi nan ya zo” inda sautin ya fito ya duba,sai yayi tozali da Nana hannunta riƙe da jinjirin yaro sabuwar haihuwa.Gabansa ne ya faɗi ras ,ya haɗiye wasu yawun tsoro kafin ya ce “ uwar mi kike nema a gidanmu?”
Mahaifiyarta ce ta basa amsa da “uwar abin da ka shuka ta zo miƙa ma tsiyar ka.Ke miƙa masa shegen ɗansa,miƙa masa na ce!” ta ƙarashe faɗa cikin ƙaraji hakan ya janyo hankalin dukkan mutanen da ba su hankalta ba.




Umma ta fito daga mota ta na kallon Fahad wanda ya rungume jaririn,sai rarraba ido yake ya rasa mi zai cewa Ummar.Nana da mahaifiyarta kuwa tuni sun bar gun su da motar ƴan sanda,“ka kyauta kuma na gode” cewar Umma ta na mai shigewa cikin gidansu na laka.




Cike da kunyar jama'a Fahad ya ratsa su ya bi bayan Umma,bai taɓa tunanin akwai ranar tonon asirinsa ba sai yau.
“Umma don Allah ki yi haƙuri wallahi tsautsayi ne kuma ba ni ɗaya ba na kusance ta...” ko kafin ya dire zancensa Umma ta zuba masa yatsunta biyar kan kunci .
“Ban son jin komai! Ka san tun yaushe ake neman ka? Tun jiya zuwan da suka yi ya fi cikon casbi,duk tunanin su na ɓoye ka ne shi yasa yau suka zo da motar ƴan sanda ta yadda asirinmu zai tonu ana zunɗenmu a unguwa.Dama ka san ba aurenta ba za ka yi shi ne har da wani bani labarin ta?”


Fahad ya ajiye jaririn da sai baccinsa yake kafin ya ce “wannan fa ba Sharifa ba ce! Dama ƴar iska ce kawai don ban son tsiyar gumi shi yasa na karɓi yaron nan amma ki bar ta da ni take zancen”
Umma ta jefe shi da kallon masheƙan aya ta ce “ko makaho ya dubi jaririn nan ya san ɗan ka ne,abin da nake so da kai dai shi ne ka bar yawon banza ka san ciwon kanka don na ji labarin jiya wasa kuka shirya shi yasa ma ba ka kwana gida ba”




“Umma ni fa ban son yaron nan...” bai ƙarasa faɗa ba sai ga abokinsa Kb ya shigo gidan hankalin tashe don ko sallama bai yi ba .
“Abokina yanzu aka kira ni aka ce babu lafiya,na zo kuma na ga kamar hankalin ka kwance ” cewa Kb.
Umma ta yi caraf ta ce “eh mi zai sa ya tada hankalinsa tun da ita ƙaddara ta san ɗakin kowa ,kuma ai ba gare shi farau ba ballantana ya ƙare kansa” daidai nan jinjirin ya fara canyara kuka,Kb sam bai damu da zantukan Umma ba don tun ba yau ba ya san da ba ta son taren shi da ɗanta Fahad sai dai babu yadda zai yi Allah ya haɗa jinin su.




Fahad ya girgiza kai kawai kafin ya buɗe ɗakinsa ya ce wa kb ya wuce ciki,yayin da Umma ta ɗauki ɗan ta na ririga shi “Fahad ya kamata fa ka nemo madarar da za a basa ya sha”
“Banda ko sisi aljihuna ki ara min in na samu sai na baki” ya bata amsa.
Kb ya ce “akwai a wurina bari na je na siyo” sai ya fasa shiga ɗakin ya fice .
Fahad ya dubi mahaifiyarsa ya ce “ Umma don Allah ki bar nuna zallar ƙiyayyar ki ga Kabiru shi ɗin...”
“Ya isa haka! Wuce ka yi wanka dubi yadda fuskarka take a yamutse” Umma ta faɗa ta na bai wa jaririn ruwa.
Bokiti ya cika da ruwa ya je yayi wankan,ya na fitowa shi kuma Kb na shigo wa.
Madarar gwangwani ce sai biberon inda za a dinga kaɗa madarar,sai da ya nuna wa Umma yadda ake haɗa wa sannan ya wuce ɗakin abokin nasa.












“Fahad ka ga abin da nake guje maka ko? Wannan rayuwar da ka ɗaukar wa kan ka sam ba ta da tabbas” Kb ya faɗa cikin rashin jin daɗi.
Fahad ya ja numfashi kawai,sai da ya gama shirya wa cikin ƙananan kaya sannan ya ce “sau ɗayan wahala ne kawai ka ji abokina”


“A'a tun ba yau ba kuke tare da Nana ni a tawa shawarar kawai ka aure ta”


“Allah tsare ni da auren ƴar iska!” cewar Fahad ya na haɗe rai.
Kb ya murmusa ya ce “to kai mine ne?”


“Irin ka ne ni ko ka zata ban san ku na holewa kai da Ramlah ba?”


“Ita ɗin wacce zan aura ce kar ka manta haka.Kuma babu abin da ya shiga tsakanina da ita,ranar nan ma da ka gan ta ɗakina wani dalilin ne ƙwaƙwara ya kawo ta”


Sai da Fahad ya sheƙe da dariya ya ce “to a faɗa wa kaji zabi hira suke! Ka ga tashi mu je ka yi min rakiya gidansu Sharifa”


“Ba zan je ba! Ni ma gidan tawa amaryar zan je!”


“Okay!" Ya faɗa ya na mai maƙe kafaɗu.A tare suka fito,Umma sai wanka aka yi wa baby Kb yayi mata sallama maimakon ta amsa sai cewa ta yi “saura kayan sawa na baby ” bai ce da ita komai ba ya zo ya ja motarsa ya wuce gidansu Ramlah wacce ke can ta na jiransa tun ɗazu .
Sai da ya shiga ya gaida iyayenta sannan ya fito ya zauna cikin mota,jim kaɗan ta fito cikin adonta.Yadda ta haɗe rai alamun ta yi fushi yasa shi cewa “sorry Hajiyata ba gani na zo ba?”
Ramlah kamar za ta yi kuka ta ce “saboda Allah mi ya tsayar da kai?”
“Fahad ne mana”
“Ka ce ciwon kan ka” Ramlah ta faɗa ta na taɓe baki.
Kamar suɓul da baka Kb ya ce “ai kuwa yau ma ya kwaso jan aiki,wata yarinya ya yi wa ciki yanzu har ta haihu yau ta kawo masa ɗansa”
Ramlah ta dafe ƙirji “ciki?” ta faɗa da ƙarfi sai a lokacin Kb ya tuna ya yi katoɓara musamman da ya san ita ɗin ƙawar Sharifa ce.




Cikin son kawar da zancen ya ce “wane gida za mu fara zuwa?”
“Duk inda ka kai mu” Ramlah ta faɗa ta na fiddo wayarta ta na dadana wa a haka suka fara ziyar dangi da abokon arziki inda a ƙarshe ta ce ya kai ta gidan su Sharifa.










#Gidan Papa




Muna gama girki ni da Saude muka jera kan table ɗin cin abinci.Wanka na je na sake yi sannan na kunna wayata,saƙon Fahad ya ta gwada kirana aka turo min na lumshe ido ina jin wani irin sanyi na ratsa ni wanda ba komai ya janyo haka ba sai don ganin Fahad ya damu da ni tun da har ya gwada kirana sama da goma sai kuma na wata baƙuwar lamba marar suna.
Simple kwalliya na yi kafin na feshe jikina da turare na fito falo,tuni Yayuna Munir da Sharif sun fito su na ma cin abinci.
Na turo baki gaba na ce “ba a ko jira har na fara ci shine kuka zuba”




“Ke wa?” muryar Ya Mustapha ta katse ni wanda shi ma ya fito cikin shirinsa sai baza ƙamshi yake .
“Yaya wasa fa nake!" Na faɗa cike da shakku.
“Su ɗin sa'anin ki ne?” na girgiza kai idona na cikowa da ƙwalla.
“Na sake jin banzan shirmen nan ki ga ikon Allah.Mi yasa kika kashe wayar ki ne? Ali ya ce yayi ta kiran ki bai samu ba” sai a lokacin na ɗago na dube shi,wato tuni shi ma sun gulmata masa abokin mijin anty Maimuna na sona.




“Wayar ce ta mutu sai yanzu na caza ”
“Yau zai zo sai ki shirya tarbarsa,sannan ki aje hankali ki nutsu da kyau da zarar kun fahimci juna zan basa auren ki”




Tamkar saukar guduma haka na ji furucinsa,babu tsoro sam a idona na kafe shi da su na ce “shi kuma Fahad ɗin fa?”
Ya Mustapha ya ɗaga hannu da niyyar mari na amma Papa ya dakatar da shi.Da gudu na koma ɗakina ina kuka,ban ma san lokacin da Mama ta dawo ba.
Ina cike da ƙuncin nan ƙawata Ramlah ta shigo,“ke lafiyar ki?” shi ne abin da ta faɗa ta na buga bayana.Na tashi zaune ina dubanta da kumburarun idona,ban wani ɓata lokaci ba na koro mata bayani tun da ni da ita ba mu ɓoye wa juna sirrinmu.Maimakon na ga damuwa kan fuskarta sai akasin haka,“ai wallahi gwara ki cire Fahad a ran ki don sam ba ku dace ba,kin ga fa yanzu Kb ke faɗa min ya yi wa wata ciki an kawo masa baby.Yanzu irin wannan mijin za ki aura?”
“Ban gane ba ki yi min gwari-gwari!” na faɗa don sam ban fahimce ta ba,sai da Ramlah ta sake maimaita min sannan na gane.
Nan wani sabon kukan ya kubce min,maimakon ta rarrashe ni a'a kawai sai ta yi ta ɓata Fahad ana cikin haka ne kiransa ya shigo.Sanin shi ɗaya ke da irin wannan ringing ɗin yasa na ɗaga kiran ko screen ban kalla ba,“ga ni a ƙofar gidan naku mai gadi ya hana ni shiga” jin muryarsa cikin damuwa sai na ji tawa damuwar na barazanar ɓacewa.Ko kallabi ban tsaya sakawa ba na dire daga bed na fice,a tsakar gida na gamu da Mubashar ina jin ya na tambayata ina zan je ƙafata babu takalmi kuma ba mayafi amma na yi masa banza.




Ina isa bakin get mai gadi ya tare ni ya na cewa “hajiya umarni Oga Mustapha ya bayar kan cewa kar na saki na bari ki fita, sannan wancan ma ya ce kar a bar shi ya shigo”
“Ja ka bani wuri in ba so kake na mare ka ba” na faɗa ba tare da na duba yawan shekarunsa ba,da na ga bai da niyyar ja na yi wani ƙuuu doli ya kauce min na fita.


Fahad na ganina ya sauko daga kan mashin ya nufo ni,ya buɗe baki zai yi magana na wanke shi da mari sai kuma na cakumi kwalar rigarsa ina jijiga shi.Cikin kuka na soma magana “ Had mi na yi maka ne har haka? Don mi? Akan wani dalili za ka je ka yi wa wata ciki ta haifa ma ka ɗa? Ni mi na kashe maka ne? Mi yasa ba ka yi min cikin ba madadin ta? Ka san yadda nake mahaukacin sonka kuwa? Ka san yadda soyayyar ka da kishin ka ke azalzalar zuciyata?” cikin fitar hayyaci nake maganar kafin kuma na shige jikinsa ina wani sabon kuka.


Daga baya na ji an wani fizgo ni,babu zato babu tsammani na ji gau tuni na soma gani dishi-dishi ko kafin na koma normal na ji saukar muryarsa mai kamar aradu “tun da kin haukace ai sai ki je yayi miki ciki,banza wacce ba ta san ciwon kanta ba wuce maza gida” ya ƙarashe faɗa ya na wani hankaɗa ni saura ƙiris kaina ya bugi ƙaton get Allah ya min sa'a Ramlah ta yi saurin taro ni.




Mama wacce hayaniyar su ta fiddo ta waje ta yi tsaye ta na kallon ikon Allah yadda Mubashar ya kama Fahad sai jibgarsa yake kamar wanda Allah ya kawo.
“Mama ki na gani ya na dukansa,ki masa magana kar ya ji masa ciwo” na faɗa ina mai zubewa ƙasa cikin gwanjin kuka,duk yadda Fahad ke mayar da martani da kuma ƙoƙarin kare kansa Mubashar ya fi ƙarfinsa.


Mai gadi ne ya shiga tsakaninsu,Mama kuma ta sa baki sannan kawai ya rabu da shi.Idon Mubashar sun kaɗa sun yi ja kamar garwashin wuta,haka ya zubo min su ya na huci babu shiri na miƙe na nufi ciki ko ta kan Fahad ban bi ba.






A tsakar ɗaki na zauna dirshen,hawayen ma ji na yi sun ɗauke.Na rasa jimamen wane takaici zan yi,na cikin da Fahad ya yi wa wata ba ni ba ko kuwa na Mubashar wanda ya zaƙe a lamarin da bai shafe shi ba.






“Cabbb! Wai da gaske wancan direban gidan ku ne? Ko dai shi ma Soja ne Ya Mustapha yake yi wa aiki ?” Ramlah ta faɗa lokacin da ta shigo,kanzil ban ce mata ba.Ta ci gaba da cewa “ba don an yi mana baiko da Kb ba ai da na shigar da takarduna”
Ganin za ta ƙara min takaici yasa na shige toilet,ruwa na sakarwa kaina ba tare da na cire kaya ba.Tsawon lokaci ina a tsaye idona a lumshe sai hoton abin da ya faru,na kashe pampo na fito daidai nan na ji kaina ya sara ban sake sanin abin da ya faru ba sai tashi na yi na tsince ni a gadon asibiti.
Da Mubashar na fara yin tozali fuskarsa cike da yanayi na tausayi da rashin jin daɗi,“Kin tashi?” na ji muryar Mama kusa da ni sai a lokacin na karkato kaina saitin inda take zaune .
“Bari na kira likita” cewar shi ya na mai fita,daidai nan Ya Mustapha da kuma Ali suka shigo.....
[24/04

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login