Showing 21001 words to 24000 words out of 24314 words

Chapter 8 - SAURAYINA BOOK COMPLETE DOCUMENT BY Mrs Sadauki .txt

10 Jan 2025

2221

na zo Ali ya ce ki na wanka,abinci ne Mama ta ce na kawo” Ramlah ta faɗa ta na ajiye gorar ruwa da kofi kusan Ali.
“Ashe ki na hanya ,ya kike ya Mama ɗin ta na lafiya?”
“Lafiyar ta lau.Sai yau fa zan koma gida,don haka sai an jima sauri nake”
“Ki jira mu fita tare” na faɗa tare da buɗe kwanon abincin na ce “ zo mu ci ko?”
“A'a na ci a gida ”




Plate na samo na zuba couscous ɗin da miya na ci na ƙoshi,bayan duk mun gama ne muka fito.Ina gaba Ramlah na baya,Ali na tuƙi sai wani iya yi yake ya na kamo hannuna.Duk da akwai nisa amma sai da ya kai Ramlah gidansu,da za ta sauka kuma ya bata kuɗi masu yawa.Daga nan asibiti muka wuce,bayan yayi musu bayani aka haɗa mu da likitar mata ta duba ni ta kuma tabbatar da lafiyata lau ƙila rashin kwantar da hankalina ne da ban yi ba saboda tsoro yasa bai ga hanyar ba .




Godiya Ali yayi mata kafin mu baro asibitin,a kan hanya ya saya min sabuwar waya sannan ya je gidan layi aka min copy nawa . Sosai na yi murna ina ta zuba masa godiya.








★MISIRA




Jirgin su Sheikh ya sauka lafiya,kasancewar sananne ne tun a nan wasu ke ta masa gaisuwar girma.Su na nan zaune aka zo aka ɗauke su,a hanya Mubashar ke ƙarewa garin kallo yadda ya haɗu sosai.A haka suka sauka masaukinsu,wani ɗan madaidaicin gida ne mai shuke-shuke.Sheikh ya nuna wa Mubashar part ɗin da zai zauna,ya wuce ciki sanyin ƙamshi ne ya tarbe shi har sai da ya lumshe ido.Babu ce kawai a babu a ɗakin, toilet ya wuce yayi wanka ya na fito wa ya ga kaya ajiye kan bed.Ɗauka yayi ya saka kafin ya fito falo,Sheikh ya sakar masa murmushi ya ce “yanzu nake shirin cewa Khalid ya kira ka”
Mubashar ya saki murmushi kawai,Khalid shi ne matashin da ya je ya ɗauko su Balarabe ne bai jin Hausa sai English.




Shayi ya zauna suka sha kafin a gabatar masu da wani kalar abinci mai shegen daɗi.Mubashar sai ƙoƙarin watsar da tunanin Sharifa yake,haka shi ma Sheikh sai jansa yake da hira.Bayan sun dawo daga sallar isha'i ne duk kowa ya shiga part ɗinsa domin hutawa.




Mubashar ya jawo wayar Sharifa,sai yau ne kawai ya binciki abin da ke ciki.Sosai hankalinsa ya tashi ganin irin ƙazaman kalaman da suka yi masaya ita da Fahad.Ya shiga gallery yadda ya ga hotunan su manne da juna saura ƙiris zuciyarsa ta buga ,wasu ma a gidan rawa aka ɗauke su .Idonsa ya kaɗa yayi ja ganin Sharifa zaune raɗam kan cinyar ƙato, addu'a ya soma yi ya na karanto sunayen Allah a haka bacci ya ɗauke shi.Ba shi ya farka ba sai ƙarfe ukun dare,ya je yayi wanka da alwala ya zo ya tada sallar nafila kusan rabin addu'o'in da yayi duk Sharifa ya yi wa su.
Da ya ji ana kiran sallar asubahi ya fito, Sheikh ya fito sai suka dugunzuma suka wuce masjid.








Bayan sun dawo suka yi karatu,kafin Sheikh ya umarce shi ya je ya shirya za su fita.
Bayan Mubashar yayi wanka Khalid ya kawo masa kayan da zai saka,cikin halshen larabci suka gaisa a nan ya sanar masa breakfast na jiransa.
MUBASHAR ya fito cikin irin shigar larabawa, Sheikh ya ƙure shi da ido ya na murmushi haɗi da yi masa addu'a a can ƙasan zuciyarsa .Abinci suka ci su uku kafin Khalid ya tuƙa su zuwa University ta karatun Alkur'ani ta ƙasar.Sheikh ya rubuta sunan Mubashar sannan aka zagaya da shi ya ga ɓangarorin wurin ,daga nan shopping suka wuce.
Yadda aka kashe uwayen kuɗi yasa Mubashar kasa cewa komai sai hawayen farin ciki,kamar wani ƙaramin yaro haka yayi tsaye gaban Sheikh wanda shi kuma ya tallabe kumatunsa ha na murmushi ya ce “ka fi kyau haka my son,in ka na shagwaɓar nan sai ka dinga tuna min lokacin ina saurayi kamar ka.In kuma na ga ka na murna sai na ji takaicin yadda ban yi ma hidima tun ka na ɗan ƙanƙanen ka sai da ka girma”


Mubashar ya shige cikin ƙirjin Sheikh,soyayyar mahaifi da ya rasa ce yake jin ta na huda fatarsa ta na shiga jijiyoyinsa.Son mahaifi yake yi wa Sheikh,murya na ɗan rawa ya ce “Daddy Allah saka ma da gidan Aljannar firdausi! Ya yafe ma zunuban ka ya luluɓe ka da rahamarsa”




“Amen!” Sheikh ya furta ya na ƙoƙarin mayar da kukan da ke shirin kubce masa.
Khalid da ke tsaye ya na kallonsu shi ma sai da ya goge ƙwalla duk da bai san abin da suke cewa ba.








★A can bangaren FAHAD kuwa tuni sojawa sun sake shi,cikin su ne wani ya basa 10mill ya kuwa karɓe.Da ya isa gida Umma ta gasa masa jiki ,juyin duniya kuma ya ƙi faɗa mata dalilin da yasa aka duke shi don ya na tsoron kar ya sanar da ita azo ta tsani Sharifa wacce bai san ma mugun sonta ya fi sha'awar da yake yi mata yawa ba.Ya lashi takobin ko zai rasa ransa sai ya raba Sharifa da gidan Ali shi kuma ya aure ta.......






My book is only 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA Ecobank,DM +22795045822
[03/05 à 09:18] MRS SADAUKI 👑: *SAURAYINA*💅🏻💅🏻💅🏻




LoVe and HoRrOr story💔☠️




```MRS SADAUKI```✍🏻
Dedicated to Autar Manya👑
*FCWA*☀️
____________________________________________________________________________________________________






Last free page 10






Sama da shekara ɗaya yanzu da aurena amma ko sau ɗaya Ali bai kusance ni ba duk da kuwa ya na gwada sa'ar shi sai kafin ya cimma burinsa lamari ke kwaɓe wa.Abu guda na sa a raina kawai bai da lafiya ne dama,kuma sosai na ji daɗin haka don normal nake karatuna wanda tuni mun gama Finally year rantsar da mu kawai ya yi saura.




A gurguje nake tafiya kasancewar motar gidana ta lalace ba direba ne ya kawo ni ba.Kasuwa na je na yi dukkan siyayyar abin da zan buƙata a taron karrama ɗalibai da za a yi gobe,ina jin tun ɗazu wayata na ringing amma ban fiddo ta ba saboda kar a ƙwace.




Na ja tsuki na ce “yanzu haka Ramlah ce ita da komai na ƙauyawa tak....” magana ta ce ta tsaya sakamakon wata dalleliyar mota da ta kusa kaɗe ni.Na yi ɗan baya da sauri ina zagin matuƙin kafin na yi gaba,abun mamaki har na yi nisa ni na ga motar na bin bayana na tsaya cak.Motar ta zo daidai gabana ta yi parking,kafin a hankali a sauke baƙaƙen maduban,ido cikin ido muke kallon juna.Ban san lokacin da na saki ledodin hannuwana ba sam,jikina tuni ya ɗau rawa zuciyata kuma ta soma buga wa da mugun ƙarfi kamar za ta faɗo.Na lumshe ido ganinsa a tsaye a gabana,ya sha wasu mayun suit baƙaƙe sai baza ƙamshi yake.
“Rifa!” ya kira sunana cikin wani yanayi mai tattare da ma'anoni dayawa,na buɗe idona wanda tuni suka ciko da ƙwalla.
“Na yi kewar ki” ya furta ya na kallona tsakiyar ido.Murya na ɗan rawa na ce “Had! Kai ne? Ko kuwa mafarkin da na saba yi ne? Don Allah ka faɗa min ba bacci ba nake”
“Ni ne da kaina my Rifa ” ya bani tabbaci kawai sai na faɗa jikinsa na saki wani marayan kuka,ina jin yadda zuciyar FAHAD ke wani irin mugun buga wa da ƙarfi .
Ya ja numfashi ya ce “mu je ki shiga mota kin ga mutane sun fara kallonmu” sai ya ni kamar wata ƙaramar yarinya ya zagaya da ni can ɓangaren ya zaunar da ni a gaba.Ina kallonsa ya kwashe ledodina yasa gidan baya kafin ya shigo ya zauna,ido kawai na tsura masa yadda yayi wani mugun kyawu kamar Balarabe fatar jikinsa har wani ƙyalli take baƙar sumar kansa da ta gemu da sajensa kuwa kamar Karaan.






Muna tafe ina ƙare masa kallo,sanyi ac motarsa ma kaɗai ya isa ya nuna ma ya na cikin jin daɗi.Har muka kai wani tantatsetsen gida bai ce min uffan ba sai aukin murmushi,mai gadi ya buɗe ya na wani rusuna masa shi kuma ya Parker motar cikin jerin motocin da ke ajiye sun fi kala biyar.
Da kansa ya buɗe min ,ƙafafuwa tuni sun yi sanyi dakyar na iya fiddo su waje ai kuwa tsayuwa ta gagare ni.Cak ya sungume ni ba tare da na yi zato ba,da sauri na lanƙame wuyansa da hannuna hakan ya ƙara wa fuskokinmu kusanci har ina iya jiyo ƙamshin man da ya shafa a sajensa.
Tafiya ya soma da mu har muka isa bakin wata ƙofa mai kyau,da kanta ta buɗe ya shigar da mu ya aje ni kan luntsuma-luntsuman kujerun da ke zube a falon.
“Barka da zuwa gidan ki” ya furta ya na murmushi kafin ya ƙwala kiran sunan “Sulvi? Sulvi?” da gudu wata matashiyar budurwa ta fito ka na ganinta ka ga inyamura,da Yaren French yayi mata magana ta amsa kafin ta wuce babu jima wa ta dawo da tray hannunta ta aje a gabana.




Na kasa cewa komai sai kallon uwar dukiyar da aka zuba nake,ina son tambayar FAHAD gidansa ne ko kuwa na uban gidansa ne amma dai na yi shiru.
Hijabin jikina ya cire ya na mai zama kusa da ni,da kansa ya zuba min jus na sha haka ma kayan marmari kafin ya ce “taso mu wuce ciki” babu muso haka na bi bayansa muka hau ƙaton benen da zai sada mu a sama mai ɗakuna sama da biyar.
Wani shock na ji lokacin da muka bi ta wani ɗakin mai jar ƙofa,sai da na ji kamar an zuba min ruwan ƙanƙara yayin da kuma sarƙa ƙafata na ji ta na matse ni.


Idona na ji kamar za su rufe,na yi saurin kamo hannun FAHAD na riƙe gam.Murmushi kawai ya yi min ,wani ɗaki muka shiga mai kayan ado komai na rayuwa akwai.
Da shigar mu ya umarce ni da na cire duk kayan jikina ko pant bai son gani,tamkar wacce ya rufe wa baki ko gardama ban yi ba na bi umarninsa duk da ba yau ne muka saba keɓe wa ba amma lokutan baya shi ke cire min sutura ai.




Kallona kawai yake yi ya na lumshe ido,ni kuwa duk sai na ji babu daɗi.Ya tako gabana yasa hannu ya cire shushu ɗin da na ƙulle gashina,ai kuwa ya baje kan kafaɗuna.
“Za mu je mu yi wanka” ya ƙara furta min cikin kunne,yadda sautin ya fita ya saka ni saurin lumshe ido.Fahad ya ɗauke ni bai dire ni ba sai cikin ƙaton bahon wanka,shi ma ya cire suturar shi ya shigo ya soma yi mana wanka mai haɗe da romance.Yadda yake kissing ɗina ya sha banban da na Ali,ban sani ba ko ƙila don shi ne nake so nake jin komai normal.Samar da minti talatin muka ɗauka a ciki kafin ya fitar mu muka koma kuma wajen shower,ina gaba shi kuma ya na rungume da ni a baya.A cikin kunnena ya dinga jero min baitocin soyayya masu ratsa ɓargon zuciya,yadda yayi kukan kewata,abin da rashina kusa da shi ya haifar masa.
“Rifa ina mutuwar son ki,babban burina shi ne na mallake ki a matsayin mata.Ki san yadda za ki yi ki rabu da Ali ki zo mu yi aure mu ji daɗin rayuwarmu kin ji?” ya tambaye ni ya kuma hana min damar yin magana sakamakon bakinmu da ya haɗe.






Niyyar kansa ya dawo da mu kan bed ɗinsa ya zuba min salo iri-iri na soyayya .Duk da bai kusance ni ba a yadda ya kula da ni kawai mun gamsu,sosai kuma na yi mamakin yadda ko ƙaƙarin yin sex ɗin bai yi ba.
Da muka ƙara shiga Toilet abu guda na lura da shi,FAHAD bai yi wankan tsarki ba ni kawai na yi muka fito shi da sabulu yayi.
Wani wuri ya buɗe sai ga akwtina sun fi goma,dukkansu manya ne.Ya buɗe ɗaya daga ciki ya zaɓo min wasu kaya riga da wando irin na tura wa ya ce na saka ya na son ganina cikin su,na yi murmushi tare da karɓa na ce “yaushe ka saye su?”
“Sun ɗan jima! Ko na buɗe miki sauran akwatinan ki gani? Kayan lefen ki nake haɗa wa” ya bani amsa tare da taimaka min na sa kayan ai kuwa tamkar wata baturiya haka na fito.




Ɗaya bayan ɗaya haka FAHAD ya buɗe min duk na ga komai,sosai na ji daɗi ina jin ƙaunarsa na ƙara haɓaka.Falo muka wuce,Sulvi ta kawo mana abinci ya fi iri goma ina zaune raɗam kan cinyar shi ita kuma ta na sanar da shi sunayen abincin.
“Zuba min shinkafa da miyar biri,babyna ke mi kike so?”
Da mamaki na dube shi na ce “biri kuma? Yaushe aka halitta mana cin Biri kuma?”
Wani kallo ya min wanda ban san na mine ne ba kawai sai na ji ma kamar na manta tambayar da na yi.
“Zuba mata acake da kifi” ya ba Sulvi umarni,plate biyu ta ɗauka ta zuba wa kowa nasa sai a lokacin na zauna kan kujera.Bayan mun gama ne na ce masa ina son zuwa gida,na saka hijabina muka fito.




A hanya ne yake ce min “na yi tunanin nan za ki zauna sai dare ki koma amma da alamu duk kin damu ki zo baƙin gidan nan”
Na ce “gobe ake karrama mu a makaranta shi yasa”
“Ok amma gobe a gidana za ki kwana”


Na yi shiru ban ce komai ba,“ko ba za ki zo ba?” ya tambaye tare da min shegen kallonsa wanda ban san yaushe ya koye shi ba amma sam bai da daɗi sai nake ganin ma kamar idonsa su na canza wa.
Na haɗiye yawu na ce “zan zo”
“Tun da kin yi alƙawari na yarda,in ma ba ki zo ba da kaina zan shigo har gidan na ɗauke ki” ni dai ban ce komai ba har ya kawo ƙofar gidana,sai da ya min kiss kafin na fice.




Ina shiga na tarar da Ramlah ta cika ta yi fam kamar za ta fashe,na ƙyalƙyace da dariya na ce “fushin na mine?”
“Ban sani ba tun ɗazu kin samu wuri kin yi zaman ,daga ina kike ma wai?” ta tambaye ni ta na wani kallona,sai da na ja ajiyar zuciya na ce “zan faɗa miki ba yanzu ba” sai kawai na wuce bedroom.Kan gado na haye bayan na cire hijabi,na lumshe ido ina tuna moments ɗinmu.




“Ina kika samu uwannan kayan?” na ji muryar Ramlah daga bayana.Da sauri na tashi zaune muna kallon juna,tambayar ta sake maimaita wa ni kuma ba tare da wani ɓoye mata ba na ce “Had ya saya min”
“Wane Had ɗin?”
“Fahad mana”
“Yaushe suka dawo Nijar?”
“Wallahi ban sani ba ni ma yau dai na haɗu da shi kasuwa”


Ramlah za ta yi magana kenan ,Ali ya shigo bakinsa ɗauke da sallama da sauri ta fita yayin da shi kuma ya tsure ni da ido.Sanin halinsa ba ƙaramin aikinsa ba ne ya nuna min na jaki ba yasa na kawar da kaina,“daga ina kike? ”
“Kasuwa na tafi”na basa amsa .
“Mi kika siyo? ”
“Kayan da zan sa gobe ko?”
“Su na ina?” ya watso min tambaya.
Na yi shiru ina tunani ,tabbas na bar su a motar FAHAD.
“Ba ki ji abin da na ce ba?” ya daka min tsawa ya na ƙara matso wa,bakina na rawa na ce “su na cikin drower” tare da nuna masa da yatsa.




Ali ya je ya buɗe drower nan take ledodi suka faɗo,ya ɗauko su tare da buɗe wa ya na duba wa haɗi da karanta reçu/ receip .Ni kuwa mamaki ne ya kusan kashe ni ganin kayan da na bari a mota ga su kuma a ɗakina.Ya mayar da kayan ya fice,na ja wata wawiyar ajiyar zuciya ina mai cewa “to ya aka yi suka zo nan?” sai kuma na soma tunanin ko na shigo da su ne,ganin zan sawa kaina ciwo kawai na share na soma baccin gajiya.








Ali kuwa ya na fita direct kitchen ya wuce inda yake jin motsin Ramlah.Wani irin finciko ta yayi ya ce “daga yau in na sake jin banzan shirmen ki wallahi ni da ke ne.Kin san aikin da nake yi ne kika taso ni ? Kawai saboda banzan kishin ki a dole so kike mu yi faɗa ni da matata”


Ramlah ta fincike hannunta ta ce“oh matar ka ce? Shi ne ta kasa yi ma komai ina ce ni nake sauƙe duk buƙatun ka sama da shekara ɗaya.Ka na ji Ali wallahi na gaji kawai ka aure ni ko kuma na tona ma asiri” Ramlah ta faɗa ta na jin wata irin da na sani,saboda cin amanar ƙawar ta da take yi ita da mijin ta wanda ba komai ya jawo hakan ba sai yadda SHARIFAr ke bata labarin sirrin aurenta sannan kuma da kwaɗayi da hassadar ƙawarta ta auri wanda ya fi masoyinta Kb.Tun lokacin auren Sharifa bai wuce wata biyu ba Ramlah ke shige da fice har sai da ta ja hankalin Ali,ta yi hakan ne don cin kuɗinsa tun da Sharifa ta tabbatar mata ya na da muguwar sha'awa sai dai fa ko kafin akai ga yin sex komai ke lalace wa.Ta zata za ta ci bulus sai kogo ya juye da Mujiya Ali ya karɓe budurcinta ta mummunar hanya,ta yi kuka har ta gaji a ƙarshe kuma ta shafe idonta da toka suka dinga holewar su kai kace wasu ma'aurata har da ɗaukar maganin tsarin iyali.Burin ta guda a yanzu shi ne Ali ya aureta,shi kuma ya tabbatar mata har abada ba za a yi cin amana da shi ba sai dai in bai auren Sharifa, wannan hujjar ta saka Ramlah a doli sai ta samo laifin da zai sa Ali ya saki Sharifa har wani ta samu wanda zai dinga bin bayan Sharifa duk inda za ta je.






Ali ya dubi Ramlah,kallo irin na ba ki da hankali kafin ya ce “na aure ki? Mi za ki min wanda yanzu ba ki min ba? Ki na ji na ko? Ki buɗe kunnuwan ki babu aure tsakaninmu” ya na gama faɗa ya ficewar shi.








FAHAD


Tun bayan haɗuwarsa da Sharifa yayi dubarar haɗa wani plan kanta ,na kula da duk wani motsin ta da abin da ya shafe ta.Ya na tsaka da driving ya ji ledodi na motsi daga bayansa,kallonsu kawai yayi ya fahimci abin da ke faruwa.Umarni kawai ya basu ya na mai furta wata kalma kawai suka ɓace suka kai kansu cikin drower Sharifa.
Cike da annushuwa ya isa gida,tun bayan rabuwarsa da ita bai taɓa samun nutsuwa ba sai yau kuma da idonsa suka sake tozali

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login