Showing 15001 words to 18000 words out of 24314 words

Chapter 6 - SAURAYINA BOOK COMPLETE DOCUMENT BY Mrs Sadauki .txt

10 Jan 2025

2218

numfashinsa “alhamdullah ai na samu lafiya! Ya kake ? Ina ka tafi na yi ta kiran wayar ka amma ba ka ɗauka ba ka sa duk hankalina ya tashi?” yadda Sheikh ke magana cike da kulawa yasa tsikar jikin Mubashar tashi sai yake jin ina ma ace wannan ɗin mahaifinsa ne? Rana ɗaya tak da bai ji ɗuriyarsa ba ya ɗaga hankali amma shi mahaifinsa bai taɓa ma nemansa ba duk tsawon rayuwarsa.


Sheikh ya katse masa tunanin da yake ya ce “ kar ka sake yin nisa da ni ! Kai ne na fi jin farin ciki in ina tare da kai kaf cikin yarana ” Mubashar ya lumshe ido,sanin duk yaran da Sheikh ɗin ke magana ba biologique ƴaƴansa ba kawai zumuncin musulunci ne .
“In sha Allah Dadd...am Sheikh ” Mubashar ya furta a rarrabe,saura ƙiris ya kira shi da Daddy amma sai kuma ya canza .
Sheikh ya ɗan murmusa ya ce “ya ammyn naka ta na lafiya ko?”
Ya jinjina kai ya ce “lafiyarta lau”






Da taimakon Mubashar ya tashi zaune sai a lokacin ya fara amsa gaisuwarmu amma banda ta Mama,ina lura kuma da ita sai ta sunne kai.
Hajiya Balkis ce ta shigo sai baza ƙamshi take,direct kusan mijinta ta je ta zauna ta na mai tambayarsa jikinsa ya amsa sama-sama kafin ya dubi Mubashar ya ce “ina son jus!” da to ya amsa kafin ya fita ni ma na take masa baya ina kiran sunansa amma yayi banza da ni haka na koma a kunyace.


A nan bakin asibiti Mubashar ya siyo jus ɗin ya dawo,anty Maimuna ce ta bayar da kofi aka tsiyaya masa ya sha bayan nan ya lumshe ido kafin ya ce “Mubashar kira min likita ya zo ya sallame ni ”
“Wane irin a kira likita ka ga kuwa halin da aka ɗauko ka? Kawai ka bari har ka ƙara samun lafiya” cewar Hajiya Balkis wanda hakan ne ya tsayar da Mubashar, Sheikh ya dube shi kallo irin mi ka tsaya jira shi kuma ya ce “da dai ka ƙara haƙuri zuwa an yamma”
“To Allah kai mu”




Da rana abincin da muka kawo ne aka zuba aka ci,wanda ni sam na kasa ma tantance daɗinsa saboda yadda Mubashar ke wani hura min hanci sai shan ƙamshi yake.Bayan sallar azahar ne muka wuce gida ni da anty Maimuna,a hanya take tambaya abin da ya haɗa mu da Mubashar amma na ƙi bata amsa.Da muka isa gida haka ta yi ta duba kayan da ke ciki ta na yabawa ni dai ina gefe ina kallonta haɗi da tunanin wai yanzu gaske na zama matar Ali.






A can asibiti kuwa yamma na yi likita ya sallame Sheikh Muhammad bayan an yi masa gwaji an ga jikin nasa yayi sauƙi sosai.
A mota Mubashar ne ke tuƙi, Sheikh na zaune gefensa a can baya kuma Mama ce da Hajiya Balkis hira suke kan zancen lefen Sharifa da aka kawo ita Hajiya Balkisun ce ke sanar da Mama ai Ali ɗan ƙawarta ne da dalilin da ya hana ta zuwa wurin kawo lefen.
“Amma Sharifa ta yi dacen miji don Ali babu ruwansa da ƴan mata duk kuwa kuɗinsa” Mama dai ba ta ce komai ba sai murmushin yaƙe,“amma ba da ita zai tafi ba ko? Ko da yake na ji uwarsa na cewa a bari sai Sharifar ta gama karatu ban sani ba ko Ali ya yarda”yadda Hajiya Balkis ta ƙure Mama da ido yasa a doli ta bata amsa da “juma'a mai zuwa za ta tare don ba wani babban...” maganar ce ta yanke sakamakon sakin mota da Mubashar yayi ya na ta ƙoƙarin danne burki amma ya kasa sai da Sheikh ya taimaka masa.Cak motar ta tsaya, Mubashar ya ja wani dogon numfashi kamar ransa zai fita kafin ya aro jarumta ya lalubo nutsuwa ƙira'a ya saka ya ƙure volume kafin ya ci gaba da tuƙin.
Sheikh ya juya ya kalli Mama kafin ya maido dubansa kan titi,lokaci zuwa lokaci kuma ya na ankare da Mubashar har suka isa gida.Da taimakonsa Sheikh ya isa har ɗakinsa,Mubashar zai fita amma ya tsayar da shi ya na mai cewa “ka je ka yi wanka wani zai zo ku tafi wani gun ”
“To bari na je gida”
Sheikh ya rumtse ido tuna har yanzu fa Mubashar gidan Mama yake da zama,“ok ka yi sauri ”




Mubashar na fitowa Mama ta miƙe suka fita ,shi ya tuƙa ta har gida amma babu wanda ya cewa wani komai.
Wanka yayi ya shirya kafin ya koma can gidan Sheikh ɗin,tuni mutumin da za su tare ɗin ya zo.
“Ina katin ɗan ƙasar ka yake?” mutumin ya tambaya, Mubashar ya fiddo ya nuna masa sai suka yi wa Sheikh sallama suka fito.
Shi ke tuƙi Mubashar na gefen shi,sai nasiha yake yi masa har suka isa inda ake paspo ba su wani ɓata lokaci ba aka yi wa Mubashar duk abin da ya dace kafin a sanar da shi nan da kwana biyu ya dawo ya karɓa.




Mutumin ya maido shi gida,sai a lokacin Mubashar ya samu lokacin yin tunanin da bai yi ba .Yadda Sharifa ta bugu ba ƙaramin zafi yayi masa ba amma sanin ta haramta gare shi yasa bai yi yunƙurin tare ta ba.Hawaye suka ciko idonsa ji yake kamar yanzu ne Mama ke cewa juma'a mai zuwa za a kai Sharifa gidan wani ƙato namiji wanda ba shi ba.Rurin wayarsa ne yasa shi dawowa hayyacinsa,Ammy ce da sauri ya ɗaga .
“Ina ta jira ka kira ni amma shiru,ya ne ka sauka lafiya ya mai jikin?”
“Da sauƙi Ammy,har ma mun dawo gida”
“To ka bani shi na yi masa ya jiki”
“To kashe in na shiga bangaren shi sai na kira ki”cewar Mubashar kafin ya fito daga ƙarƙashin innuwar mangoro ya wuce ciki. A zaune ya tarar da Sheikh a falo ya na duba wasu takardu,cikin girmamawa ya sanar da shi Ammy na son magana da shi. Sai da yayi ɗan jimmm kafin ya amince, Mubashar ya kira bayan Ammy ta ɗaga ne ya miƙa masa,“assalamu aleykum ustaz ya gida ya ƙarfin jikin?” sai da Sheikh ya lumshe ido saboda jin muryar da ya jima ya na jin ƙishirwar ta ,“Alhamdullah jiki yayi sauƙi na gode sosai ” ya furta muryarsa na rawa.
Ammy ta ce “ni ke da godiya Alhaji , Allah ƙaro afuwa yasa kaffara ne” ya amsa da “amen Ya Rabb na gode!" Kafin ta miƙa wa Mubashar wayar ba don ya gaji da muryar ba a'a sai don jin wani yanayi wanda ya tunatar da shi ashe har yanzu namiji ne shi.






“Ka tsaya ina son yi magana da kai” Sheikh ya tsayar da Mubashar da ke ƙoƙarin fita “ammy zan kira ki daga baya” bayan ya kashe kiran ya saka wayar aljihu sai ya zo ya zauna gabansa.




“Ina son fitar da kai waje domin ci gaban karatun ka wace ƙasa kake son zuwa?” Sheikh ya tambaye shi .
“Duk wacce ka zaɓa ta yi”
“Zaɓin ka shi ne nawa” Sheikh ɗin ya faɗa ya na tsure shi da ido kafin kuma ya turo masa takarda mai zanen ƙasashen duniya.
Idon Mubashar suka ciko da hawaye,wai yau shi ne ake neman zaɓinsa domin zuwa wani gun da mota ba ta zuwa sai jirgi kamar ba shi ne almajirin nan ba wanda yake kwana bakin titi.




“Daddy ka zaɓa min” ya furta muryarsa na rawa, Sheikh ya saki wani murmushi mai sauti ya na jin zuciyarsa fara sol Mubashar ne farkon wanda ya kira shi da sunan Uba duk da Sheikh yaransa ke kiran shi.
Ya sauka daga kujera ya rungume shi ya na bubuga bayansa “ya isa haka! Yi shiru zan zaɓa ma ai dama haƙi ne na Uba ya aika ɗansa wurin da ya dace da shi”




Hajiya Balkis da ta fito daga kitchen tun ɗazu ta taɓe bakinta kawai kafin ta wuce ɗakinta baƙin ciki fal zuciyarta .
Tsawon lokaci Sheikh ya sake shi suka koma zancen karatu ya na yi masa tambayoyi shi kuma ya na basa amsa.










FAHAD


Ji yake matakin da ya ɗauka shi ne daidai,duk da kuwa ya na cutuwa da rashin Sharifa.Iya romance kawai ke shiga tsakaninsu amma ya fi samun nutsuwa da ita kan sauran ƴan matansa da suke sheƙe ayarsu.
Sannu a hankali soyayyar shegen ɗansa ke ratsa zuciyarsa,har yau ba a yanka masa rago ba sunansa dai Jamilu.Kusan kullum ya na fita aiki don samo kuɗin sayen madara,babur ɗinsa kuwa tuni ya aika abokinsa Kb ya ɗauko masa shi a gidan su Sharifa.


Yau ya na zaune a gida ya na hutawa kwatsam Kb ya aiko masa hoton Sharifa da Ali ga akwatinan aure a tsakiya.Zumbur ya miƙe zuciyarsa na bugun tara-tara,ya mirza ido ya fi sau goma don tabbatar da ko idon ne nasa ke masa gizau amma tabbas Sharifar dai ce .Sam bai taɓa tunanin ko saurayi ta saurara ba ballantana ta kai su da zancen aure.
Karon farko kenan da ya kira ta tun bayan da uban dukan da ya sha,sai da ya jera kira wajen bakwai kafin a ɗaga,FAHAD dama tuni zuciyarsa ta yi rauni kawai sai ya fashe da kuka ya na cewa “Rifa dama akwai ranar da za ki manta soyayya ta har ki amince da auren wani? Wallahi duk duniyar nan babu wanda ya fi son ki sama da ni har su munafukan iyayen naki masu hure miki kunne ki na ji na ko? Don Allah kar ki amince na san tabbas auren doli ne za su miki ni kuma da na bar sauraren ki shine kika amince,to ki yi haƙuri ki fito mu gudu mu....” Mubashar da zuciyarsa ke tafarfasa ya yi saurin katse shi “kai banza ka cika min kunnuwa da shirmen ka,alamu sun nuna ka manta dukan da na yi maka har yasa ka buɗe ƙazamin bakin ka kake wani cewa ta fito ku tsere to tsaya na faɗa maka billahil azim ko ka yi saurin cire wannan banzan tunanin daga kan ka ko kuma haɗuwa ta da kai hummmm” sai kawai kashe kiran.
Fahad ya kalli wayar ya na ƙara jin wani tashin hankalin,hoton ya sake dubawa ya ga dai ba na Mubashar ba ne wannan soja ne.
Babu shiri ya fito ya zuri takalmi kamar wani mahaukaci haka ya ɗau mashin ya nufi gidan su Sharifa.Yayi niyyar ko kirɓin gumba za a yi masa sai ya je,ya na shiga layin ya ga motocin sojawa su ma duk sayen suke da kakin soja wanda babu tantama abokan angon ne.Gefe guda kuma ƙawayen amarya ne kowacce ta ci ado,can ya hango Ramlah wacce yake jin haushinta don ya san babu ta yadda za a yi ace ba ta san an kawo kuɗin auren Sharifa ba ga dukkan alamu ma har an fara shagalin biki.






SHARIFA


Tamkar kazar da ƙwai ya fashe wa a ciki haka na koma,duk wani shirye-shirye ƴan gida kawai ke yinsa.Mama ma sam ba ta wani damu da ta yi min gyara ba, babu abin da take ban na sha ballantana gyaran fata.Yau muna ranar Alhamis wacce ita ce jajibir ɗin ranar tarewa wata,anty Maimuna tun safe ta zo ta shafa min dilka a dukkan jikina haka ta dinga haɗa min kayan gyaran fata ina wanka za ta yi min wani.Tuni na yi fresh na yi kyau,da na dubi kaina ga madubi sai da na ji takaicin ina ma gidan Fahad ne za a kai ni ba na Ali ba?




Wuraren ƙarfe biyar na maraice duk ƙawayena suka hallara gidanmu don sai yau ne kawai za su yi réunion su da abokan ango wanda a bakin anty Maimuna ne nake samun labarin shi ma zai shigo gari.
Ina nan zaune cikin dangin Mama da suka zo tun daga Agadas sai ga Ya Mustapha ya shigo,gaishe su yayi kafin ya mayar da hankalinsa kaina ya ce “ki fita zuwa lambu Ali na son ganin ki” kai kawai na jinjina masa amma banda niyyar miƙewa.
Tun da aka kawo lefe ba mu yi magana da shi ba,don Ya Mubashar ya ƙi ban wayata hasali ma ya bar barin hanyarmu ta haɗu da na sanar da Mama kuma ta yi kamar ba ta ji ba dole na barsa da ita.
“Ke ba magana nake yi miki ba?” ya Mustapha ya daka min tsawa,da sauri na miƙe ina gyara zaman sahari na da ke barazanar kwancewa na nufi ƙofa da sauri.




Ina ƙoƙarin bin hanyar da za ta kai ni lambu na kai masa karo na yi baya zan faɗi ya jawo ni na faɗa kan ƙirjinsa.Iya ƙamshin jikinsa kawai na ji na fahimci wane ne,ban san lokacin da na fashe da kuka ba na ce “Ya Mubshar shi ne kake fushi da ƙanwar ka a lokacin da ta fi buƙatar ka.Kai fa malamina ne babu abin da ka koya min na dangane da zaman aure ko da yake ba son shi nake ba” na ida furicin ina mai ɗan ja da baya don na ji tun ɗazu yake kiciniyar raba ni da jikinsa.




Cikin idonsa na kalla wanda suka yi zurfi suka faɗa,ya motsa baki dakyar ya ce “Mijin ki na jiran ki” sai kuma ya kauce ya bar ni nan tsaye ,ban gusa ba sai da ya ɓace wa ganina juyowar ga da zan yi na ga Ali tsaye cikin kakin soja ya harɗe hannuwansa.A tunanina ko ya gan ni jikin Mubashar ne sai na ji kunya na sunne kai,“amarya babu lalle?” na ji muryarsa daga sama.
Na ɗago na dube shi,sai ya sakar min murmushi ya ce “kin yi kyau ma sha Allah,ganin ki kawai ya sa na ji duk fushin da nake yi da ke ya ɓace” sai ya zo kuma yayi hugging ɗina ya na son sumbatata na kauce ai kuwa ya riƙe ni gam ganin in na yi wasa kissing ɗin nawa zai yi kawai na ɓoye fuskata cikin ƙirjinsa ina ce masa “ban so! Ban so!” bai kula ni ba sai kuma na ji wani sabon salo hannunsa kan fatar cikina.Kuka na fashe masa da shi sai ya sake ni,“ina wayar ki kullum ina kiran ki ba ki ɗagawa?” ya tambaye ni.
Na turo baki na ce “ta na hannun shi”
“Wa?”
“Ya Mubshar!”
“Mubashar ɗin ne ya koma Mubshar?”
Na gyaɗa masa kai ya ce “ok koma ciki zan fita waje su na jirana”
“Har yanzu ba su tafi ba?”
“Eh! Amma an kama wurin da za su tattauna ɗin abin da aka tsayar kenan sai su faɗa miki ” na jinjina kai kawai .


Sai da ya kawo ni har bakin ƙofar shiga falo sannan ya fice.
Abun mamaki Mubashar na tarar a zaune cikin dangina sai jansa suke da hira duk da alamu sun nuna shi fa ya matsu ya tafi.Muka haɗa ido da shi na ga ya na ƙare min kallo,can kuma ya miƙe ya fice na bisa da kallo ina juyowa kuma muka haɗa ido da Mama.Ɗakina na wuce na bar gun,na ma rasa abin da ke damuna.Sai can cikin dare ƙawayena suka dawo da uban kaya niƙi-niƙi ,dogayen riguna ne iri ɗaya duk suka sayo uwanda za su saka a gobe kan amarya,kuɗin da aka basu suka nuna min Ramlah ce babbar ƙawa wannan ya saka komai na hannunta.




A can bangaren Mubashar kuwa shi dai haka yake jin ahalin Mama tamkar danginsa yanayin yadda suka ja shi a jiki kamar sun san shi kuma suka nuna ma soyayya ƙarara.Ya lumshe ido a karo na barkatai ya na ƙara shaƙar ƙamshin SHARIFA da har yanzu bai bar jikinsa.Ya na nan zaune saƙo ya shigo wayarta,ya duba ya gani hankalinsa ya tashi ganin lambar FAHAD ce .......




Ga masu son fara payment 500 ne via
2670215530
ZULFAU YAHAYA Ecobank sai ku turo shaidar biya ta WhatsApp +22795045822
[29/04 à 13:12] MRS SADAUKI 👑: *SAURAYINA*💅🏻💅🏻💅🏻




LoVe and HoRrOr story💔☠️




```MRS SADAUKI```✍🏻
Dedicated to Autar Manya👑
*FCWA*☀️
____________________________________________________________________________________________________






Page 8




Jikin Mubashar har rawa yake yi lokacin da ya karanta saƙon.A zuciye ya fara neman layin FAHAD ɗin,ya na ɗaga wa ya fara mayar masa da martani “in ka fasa zuwa sace ta daga tsaye uwarka ta haife ka,zo ka ɗauke ta tun yau ba sai gobe ba” ƙittt ya kashe kiran kwanyarsa na mugun sarawa,wato ya fahimci muddin budurwa ta yi rashin dace da saurayin albarka to tabbas rayuwarta na cikin kwata.A daren sam bai rumtsa ba,da zullumi biyu ya kwana ya rasa wacce yake so ga kuma wani banza na son jefa ta cikin matsala.
Washegari tun asuba ake ta hidima ,Mubashar na dai ta dauriya amma sam ya kasa nutsuwa.Sheikh ma ya zo saboda mahaifiyarsa Mami da ta matsa har yanzu ba ta gansa ba,Mama ta sanar da ita Mubashar ɗan Sheikh ne amma ko kaɗan ba ta yi kuskuren shaida mata wai ya na son Sharifa ba so take abun kar yayi nisa musamman da ta hango mugun son Mubashar a idonta kasancewar shine ɗa tilo gun Sheikh.






Iyayen ango sun zo domin ƙara jadadda godiya,ambaton sunan Ali kawai ana jona shi da na Sharifa tafasa zuciyar Mubashar yake.
A hankali ya matsa kusa da Sheikh ya ce “Daddy yanzu za a iya samun jirgin da zai tashi?”
Bai basa amsa ba sai kawai jansa da yayi suka nufi mota,hakan kuma ba ƙaramin daɗi ya yi wa Mubashar ɗin ba.Direba ne ke jansu su kuma su na baya,ya lumshe ido ya na hango fuskar Sharifa wacce ta sha ado da kayan kwalliya na zinare tamkar wata matar indiya.Waya Sheikh ke yi amma bai tsinci komai a ciki ba,ya dai ji mota ta tsaya sai ya ga suna cikin filin jirgi.Dama komai na cikin mota tun daga paspo har ticket,Mubashar yayi tunanin shi ɗaya zai tafi sai da aka zo shiga jirgin ne ya ga Sheikh ma ashe zai bisa.




A wannan gaɓar ne yake jin wata irin soyayya da ƙaunar Sheikh na ƙara huda ɓargon jikinsa.Ya sa hannunsa cikin nasa ya ce “na gode sosai Daddy ka bani kulawa wacce ko mahaifina ne kai sai haka” murmushi kawai Sheikh yayi gudun kar ya buɗa baki zuciyarsa ta rufe.
Daga nan cikin jirgi Mubashar ya rubuta wa Ali text kamar haka «ina taya ka murnar mallakar ƙaddara mafi daraja a duniya ta,don Allah ka riƙe Ifa amana kar ka cutar da ita sannan ka jona mata tsaro na musamman ta yadda FAHAD ba zai ƙara shiga rayuwarta ba.Ka kula sosai yayi ikirarin zai sace ta a yau wurin kan amarya, wannan dalilin ne yasa ma na ƙi bata wayarta»
Da ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login