Showing 12001 words to 15000 words out of 24314 words

Chapter 5 - SAURAYINA BOOK COMPLETE DOCUMENT BY Mrs Sadauki .txt

10 Jan 2025

2215

SADAUKI 👑: *SAURAYINA*💅🏻💅🏻💅🏻




LoVe and HoRrOr story💔☠️




```MRS SADAUKI```✍🏻
Dedicated to Autar Manya👑
*FCWA*☀️
____________________________________________________________________________________________________






Page 6




Ɓangaren mata Mubshar ya kai ni ya na mai yi min magana cikin taushin murya “ki nutsu ki yi sallah in kin gama ki jira ni a nan cikin masjid zan zo na neme ki kar ki je ko ina kin ji ko?”
Tsakiyar idonsa na kalla ina mai jinjina masa kai,kamar wata ƙaramar yarinya da ya juya zai tafi na tsayar da shi .“Ya Mub...shar don Allah kar ka jima ban san kowa ba a nan” ya sakar min murmushi kafin ya tafi .Toilet na shiga na ɗauro alwala sannan na shiga masjid ɗin mai cike da mata duk sun sha manyan hijabai har ƙasa.Na shiga sahu na yi tsaye har aka tada sallar,bayan an gama da ɗaiɗaya duk suka fita na yi saura ni ɗaya kawai sai faman zuba wa ƙofa ido nake ina jiran shigowar shi.
An ɗauki lokaci mai ɗan tsayi kafin ya shigo,da mugun sauri na miƙe wani irin abu nake ji kamar ƙaramin yaro mai neman rarrashin uwa.Wannan yasa saura ƙiris na faɗa jikinsa yayi saurin tare ni da dukkan hannuwansa,murya a sanyayye ya ce “mu je na kai ki gida”


Idona ya ciko da ƙwalla,ba haka na so ba ! Na yi tunanin zai tambaye ni dalilin zuwana a nan ɗin amma haka na bi bayansa har muka isa parking special.Wata haɗaɗiyar mota Benz na ga ya buɗe min gidan gaba,haka na shiga na zauna kafin shi ma ya shiga ya tuƙa mu.






“Ya jikin ki?” na ji ya furta ƙasan maƙoshi kamar ba shi ne yayi maganar ba sai yanzu na tuna ma da kaina na ciwo.Murya na ɗan rawa na ce “babu sauƙi!” ƙuuuu ya ja ya tsaya,da idonsa ya kafe ni kafin ya ce “mine ne ainahin abin da ke damun ki?” kuka na fashe masa da shi kafin na ce “aure za su min Yayaaaa!”
Bai ce komai ba sai ya ci gaba da tuƙi,sai da ya ɗauki lokaci kafin ya ce “ba ki na son shi ba ?”
“A'a ni kawai burge ni yake yi, amma zuciyata Fah....” ko kafin na ida ya buga min tsawa “ya isa! Kar na sake jin kin furta sunansa domin ba mutumin kirki ba ne bai son ki”
“Ya na sona kawai dai bai da kuɗi ne,ina da tabbacin in ya samu kuɗi sai ya fi faranta min rai da su fiye da kowa” na furta ina jin wani abu na tsira min a zuciya.


“Saboda ki faɗa min ki na son shi ne kika zo wurina?”


“A'a gidan anty Maimuna za ka kai ni kuma ka ban wayata ”


“Ba zan bayar ba!” ya furta hankali kwance daga nan bai sake furta komai ba har muka isa ƙofar gidan,sai a lokacin na tambaye shi “motar wace ce wannan?”
Ya ban amsa kai tsaye “ta Sheikh ce”
“Mine ne ya faɗa maka to? Wace magana kuka yi da ya ce ya na son ganin ka?”


“In ji tsoron Allah in girmama wacce nake so kar na yi amfani da so wurin cutar da ita,sai kuma ya ce na mayar da ke gida” ya bani amsar ya na kallona,na ɗan haɗiye yawu kafin na ce “Ya Mubshar har yanzu ba ka taɓa nuna min budurwar ka ba ko a hoto ne”
Ya ce “mine ne amfanin nuna wa mutum kansa?”
“Ban gane ba?”
“Wuce ki shiga ciki muna da darasi zan koma makaranta”
“Amma Yaya don Allah ka sanar da ni ya budurwar nan ta yi bayan ta gano ta na ɗauke da ciki?”
“Ƙawarta ta fara sanar ma,ta bata shawarar a zubar ta ƙi.A ƙarshe dai tun ta na ɓoyo har iyayenta suka sani,ba su jinkirta zuwa gidan su saurayin ba amma fafur suka ƙi amincewa da zancen suka ce ƙazafi ne ta yi wa ɗansu tun da kowa ya san ustaz ne”
“Kenan cikin ta zubar?”
“A'a barin gidan iyayenta ta yi ta je can wani gari ta raini cikinta har ta haifu”


“To amma ya labarin su har yanzu su na raye ita da ɗanta?”na tambaya ina jin tausayin su,sai da ya yi min wani kallo mai wuyar fassarawa kafin ya ce “ga yaron da aka haifa zaune tare da ke!” kallon ban gane ba na fara binsa da shi kafin na waro ido na ce “wai kai? Kai ne aka haifa? Ka na nufin labarin Ammy ka ban?”




Bai bani amsa ba kawai dai ya jingina ga kujera haɗi da lumshe ido,daga inda nake ina jin yadda zuciyarsa ke mugun bugawa.Cikin wata irin murya ya ce “ wannan dalilin yasa nake jin takaici in na ga budurwa na haukan saurayi musamman irin FAHAD wanda kullum burinsa ya kusance ki.Ifa na rantse da Allah da ace na yi dogon karatun boko da tabbas zan fito alƙalin mata ne,duk wanda na samu da laifi kwatankwacin hakan da Allah kawai ya san hukuncin da zan yi masa”




“Ka yi haƙuri!” na furta dakyar,ya buɗe idonsa ya watso min su kamar daga sama ya jefo min tambayar “ki na sona?” ji na yi kamar ya buga min guduma,ban basa amsa ba kawai na ɓalle murfin mota na fita da gudu na shiga gidan ina jin wani iri a jikina.








MUBASHAR




Ya bi bayanta da kallo ya na jin wani irin takaicin kansa ,da ya kasa riƙe sirrin zucinsa har ya sanar da ita ya na sonta.Dakyar ya iya jan mota ya koma makaranta,ya na isa ya wuce aji don ya san tuni Sheikh Muhammad na ciki.
Murya kamar ta maras lafiya yayi sallama a bakin ƙofar aji, Sheikh ya juyo ya dube shi kafin ya amsa tare da basa izinin shigowa.Mubashar ya je ya zauna mazauninsa,sam hankalinsa bai wurin ballantana har ya fahimci abin da ake a haka har aka gama darasin.Ya miƙe ya nufi Sheikh da ke zaune ya na duba system ɗinsa,“ga key ɗin motar” ya faɗa cikin sanyi.
“Ka riƙe shi gun ka” Sheikh ya basa amsa ba tare da ya ɗago ya dube shi ba.
“Na kai gida?”
“Ka tafi da ita ka dinga hawa” ya faɗa wannan karon ya na mai ɗagowa ya kalle shi,da sauri Mubashar ɗin ya sunne kai.
“Lafiya ? ”
“Alhamdullah!” ya faɗa domin ɓoye sirrinsa.
“Okay ka tafi”
“Na gode” ya faɗa kafin ya fice,yau dai ga shi an basa mota special don ya dinga hawa amma sam bai jin murna.Dakyar ya isa gida,nan ya ƙara tarar da wani sabon tashin hankalin yadda mutane suka cika tsakar gidan ga kuma akwatina jere ras.
“Innalillahi wa'inna ileyhi raji'un !” Mubashar ya motsa laɓansa,kasa fita yayi daga cikin mota haka ya zauna ya na kallon yadda komai ke wakana.Can mata suka fito daga ɗaki su na rangaɗa buɗa wacce ta kusa tarwatsa zuciyarsa, Mubashar ba shi ya fito daga cikin mota ba sai da ƴan kawo lefe suka watse.Ya na fitowa kuma ana kiran sallar magrib.Sashensa ya nufa ya je ya yi wanka ko zai ji sanyi kafin ya ɗaura alwala ya wuce masjid,bayan an gama sallah ne ya wuce can ciki ya gaishe da su Mama.
Papa ne ya sanar da shi zancen kawo lefen,ya yi jarumtar yaɓo murmushi a fuskarsa ya yi doguwar addu'a kafin ya miƙe zai tafi Mama ta tsayar da shi “ka zauna ka ci abinci tukuna,yau ya aka yi kuka taso da wuri na zata sai an yi sallar isha'i za ka dawo”
“Dama ina tsayawa ne don ƙara bibiyar abin da aka yi mana” ya bata amsa,Mama ta ce “au! Shi yasa zo zauna na zuba mana”
“A'a ban jin yunwa! Yanzu ma fita nake son yi”
“Ok in ka dawo sai ka ci”




Da haka Mubashar ya fita,mota ya shiga ya duba yawan petur ya ga kusan ma tankin cike yake.Kawai ya ɗauki hanyar Tilabery,gudu kawai yake shaɗaɗawa sai ya ɗauki wajen awa uku kafin ya isa.
Ammy na kwance ta na jan casbi yayin da Fadila ke yi mata matsa ƙafa kawai sai jin tsayuwar mota suka yi.Babu jimawa kuma Mubashar ya shigo,gaban Ammy ya zube wacce tuni ta tashi zaune kasancewar akwai hasken lantarki ta gane shi.
“Subahanallah! Yaron kirki mine ne haka?” bai iya cewa komai ba kawai ya kwanta ya ɗora kansa kan cinyarta kafin ya ɗora hannunsa saitin zuciyarsa ya na fitar da wani huci.
“Fadila ɗebo min ruwa masu sanyi a randa ” cewar Ammy,ta yi saurin miƙe wa hankali tashe ta ciko moɗa ta kawo Ammy ta karɓa ta yi tofi ciki kafin ta soma yayafa masa su a jiki a ƙarshe ta buɗe bakinsa ta fara basa ya na sha.Ajiyar zuciya kawai yake saukewa,“ɗauko min fanka ki kunna” Ammy ta ƙara faɗa,Fadila ta sake miƙewa ta je ta ɗauko ta kunna.Iska mai sanyi ya soma fita,Mubashar ya lumshe ido kawai tun ya na jin muryar Ammynsa na yi masa addu'o'i har bacci ya ɗauke shi.








A daren dai babu wanda ya rumtsa,Fadila baiwar Allah sai faman zubar da hawaye take yayin da Ammy ke ta jan casbi.Wuraren ƙarfe biyun dare Mubashar ya farka,sai da yayi ɗan jimmm kafin ya fahimci inda yake.Ya tashi zaune kafin kuma ya miƙe ya je yayi alwala,sallar isha'i yayi sannan ya zo gaban Ammy ya ce “ina wuni Ammy na same ku lafiya?”
“Alhamdullah! Tashi ga shimfiɗa can ka shiga ka kwanta” ta nuna masa gidan sauro wanda tuni an ɗaura shi,bai musa ba ya je ya shige.Lamo yayi ya na tunanin yanzu Sharifa aure za ta yi ta bar shi? Ita kuwa Ammy jan Fadila ta yi su ma suka je suka kwanta.








A can Niamey kuwa sai dare ne Sheikh Muhammad ya samu labarin zancen kawo lefen Sharifa.Hankalinsa in yayi dubu to ya watse,duk yadda ya so kiran Mubashar kuma wayar ba ta shiga.Da ya kira Mama kuma ta tabbatar masa tun da ya fita bai dawo ba,tsohon hawan jininsa ne ya ji ya na son tashi.Tasbihi kawai yake yi amma ya kasa nutsuwa,matarsa Hajiya Balkis tambayar duniya ta yi masa amma ya ƙi sanar da ita damuwarsa.Ya jingina jikin kujera ya na roƙon Allah a zuci ‘ Ya Rabb kar ka jarabce ni da abin da ba zan iya ɗauka ba,a baya na rasa farin cikina ina tsaka da maraici ka jefo min gudan jinina tsokata wanda nake jin ko cinaka ban so ya cije shi ballantana wani abu ya same shi.Allah ka tausaya min ka tsare Mubashar a duk inda yake,ka sassauta masa wannan jarabawar’ haka yayi ta yi sanfarorin addu'o'i har garin Allah ya waye.




Ƙarfe bakwai na safe Hajiya Balkis ta shaida masa zuwan Mama,ya bada izinin ta shigo.
Ta shigo ta zauna gabansa,ta rasa ta ina za ta soma faɗa wa Yayan nata har yanzu fa Mubashar bai dawo ba don bai kwana gidan ba.




“Amma ai kin san ya na son Sharifa ko? Shi ne kika yarda wani ya kawo sadakinsa har aka ɗaura auren duk a jiya....” Sheikh Muhammad ya faɗa ya na jan zuciyarsa da ke barazanar faso ƙirjinsa ta faɗo,Mama da ba ta fahimci abin da yake nufi ba kawai ta zuba masa ido.
“Karo na biyu kin ruguza farin cikina! Kin kasa kulawa da amanar da na damƙa miki kin kyauta Aghaisha!” ya faɗa ya na ɗan yin tari haɗi da dafe ƙirji.




“Yaya wallahi ban taɓa sanin Mubashar na son Sharifa ba! Sannan tun kafin na gano ɗan Hawa Kulu ne na ƙudirta a raina zan aura masa Sharifa. A ranar da na je ɗakinsa zan nemi ra'ayinsa akan auren a ranar ne kuma na ga hotunan Hawa Kulu, wannan dalilin yasa na ɓoye saboda muddin ya san ni ce silar barin mahaifiyarsa garin nan zai iya tsana ta ma”




“Wannan duk ba hujja ba ce Aghaisha,a ranar da kika sanar da ni ina ce dai a tare muka yi alƙawarin nema masa duk wani farin cikin rayuwa ta yadda ko da ya san mu ahalinsa ne ba zai guje mu ba,amma yanzu mi kika yi? Farin cikinsa wacce nake hango ita ce nutsuwar shi kika ɗauka kika bai wa wani bare”




Cikin kuka Mama ta girgiza kai ta na mai cewa “ wallahi ba da sa hannuna aka yi auren nan ba ,komai Mustapha ya tsara shi da mahaifinsa kuma...” da sauri katse ta ya na cewa “ya isa haka! Ki tashi ki tafi ban son jin komai da ace ki na son Mubashar ɗin ya aure ta ai kin sanar da ni zancen kawo lefen amma kika ƙi har sai da aka ɗaura” sai kawai Sheikh Muhammad ya soma tari jini ya soma zubo wa ta bakinsa,hankali tashe Mama ta fita ta sanar nan yaran da suke karatu gidansa suka zo suka ciciɓe shi aka kai shi asibiti.




Cikin ikon Allah dai aka samu aka daidaita igiyar numfashinsa,sai dai an hana kowa shiga ɗakin da yake.Mama kuwa sai gwada kiran Mubashar take amma wayar a kashe ,haka ta yi ta yi har Allah yasa ta same shi bayan ya kunna wayar.Cikin kuka ta sanar da shi Sheikh bai da lafiya,ya kuma shaida mata zai zo.








A bangaren Ammy ba ta takura Mubashar ba sai ya faɗa mata abin da yake faruwa ba.Kawai dai ta yi masa nasiha mai ratsa jiki,wanda a ƙarshe ya sanar da ita budurwar da yake tsananin so ce aka aurar.Murmushi kawai ta yi nasu na manya ba don wai ba ta ji ɗacin haka ba a'a sai don basa ƙwarin gwiwa tare da nuna masa ba komai ne da kake so ba kake samu.“Dama haka lamarin Allah yake,sai ka so abu wanda shi ɗin ba alkhairi ne gare ka ba in ka yi dace Allah na sonka sai ya kuɓutar da kai daga sharrinsa.Ka yi haƙuri Allah zai baka wacce ta fi ta” Ammy ta faɗa ta na kallon Fadila, Mubashar ma haka ya na shirin magana ne kiran Mama ya shigo ta sanar da shi zancen rashin lafiyar Sheikh.
Da sauri ya miƙe ya ce “Ammy zan koma sai in mun yi waya” har bakin motar suka yi masa rakiya ,ya sosa ƙeya ya ce “sai dai ban kawo muku komai ba”
Ammy ta ce “ai ba mu buƙatar koman ,kwanaki ma an fidda zakka an kawo mana duk kayan abinci kuɗin da ka aiko kuma su na nan ko dala ban kashe ba har ina cewa ko na sayo ma Akuya a kiyaya ma”
Mubashar ya ɗan saki murmushi kawai,nan dai yayi musu sallama kafin ya ɗauki hanyar komawa Niamey.






SHARIFA


Furucin Mubashar abu ne da ban yi tunani ba,ko kaɗan ban taɓa kawo hakan a raina ba wannan yasa kawai na gudu na barsa.Da na shiga ciki kuwa kuka kawai nake yi,anty Maimuna ta yi tunanin na murna hakan yasa ta yi ta buɗa ta na min waƙar amare.Sai da na gaji don kaina sannan na daina,sallah kawai na iya yi amma sam na kasa cin abinci.A gidanta na kwana da tunanin Mubashar,da safe yunwa ta tayar da ni na je na ɗora ruwan zafi na haɗa Lipton da citta da menthe na sha.Ina nan zaune falo Anty Maimuna ta fito ta na sanar da ni Sheikh bai da lafiya,kuma Mubashar bai kwana gida ba.
“Wa ya faɗa miki bai kwana gida ba?” na tambaya hankali tashe.
“Mama ce! Zo mu haɗa abincin da za mu kai daga asibitin sai mu wuce gida na ga lefe”


Na ja tsuki na ce “wai lefe!” anty Maimuna ta saki baki ta na kallona,na ce “ni fa ban shirya aure ba gaskiya karatu ne gabana ”
“Sai ki je ki sanar da Papa,ko kuma bari na kira Ya Mustapha sai ki faɗa masa” ta na gama faɗa ta wuce kitchen,ni kuwa ɗakinta na wuce na ɗauko wayarta kiran lambar Mubashar na yi ta yi amma ya ƙi ɗagawa.Ina nan kwance ina saƙe-saƙe har anty Maimuna ta zo ta sanar da ni na je na shirya .Wanka na yi ta fiddo min doguwar riga fara sol na saka ,hijabin na wurgar na ce “ki ban kallabin rigar mana”
“Ki na matar auren?”
“Don Allah Anty ki ban”


Ta miƙo min na ɗora shi a kai,sannan muka fita ita ke ɗauke da ƙaramin basket ɗin abincin har muka je bakin titi muka samu taxi.
Tun da muka ɗauki hanyar asibitin gabana ke wani irin bugawa,har muka isa.Muna shiga ciki na tsaya cak ina kallonsa ya na mai fitowa daga cikin mota ,anty Maimuna ce ta kira sunansa sai ya juya muka haɗa ido da shi.Ban sani ba ko idona ne amma gani na yi kamar ya rame,ban taɓa ganinsa da uwannan kayan na jikinsa ba duk da ba wasu tsadadi ne ba amma ni dai ya min kyau .
Iskan da ya fara kaɗawa ne ya sa na lumshe idona,sam ban damu ba da kallabina da ya sauka daga kaina ba duk da ina jin gashina na taɓa min fuska alamun iska na kaɗa shi.
“Sai ki buɗe idon don ya tafi” na ji muryar Anty Maimuna,ai kuwa ina buɗe wa babu Mubshar.Takaici na ji,a haka muka ƙarasa ciki inda muka tarar da danginmu an dubiya sai dai fa shi Sheikh ɗin an ɓoye shi.
Ina ƙoƙarin wuce wa don samun wurin zama na take ƙafarsa,wajen na yi sauri na janye sulɓi ya kwashe ni na faɗi ƙasa na buge baki na saki ƙara ina mai ɗagowa na kalli Mubshar da ya ƙi tare ni har na faɗi.......










*Jummah Mubarak*😶‍🌫
[28/04 à 10:15] MRS SADAUKI 👑: *SAURAYINA*💅🏻💅🏻💅🏻




LoVe and HoRrOr story💔☠️




```MRS SADAUKI```✍🏻
Dedicated to Autar Manya👑
*FCWA*☀️
____________________________________________________________________________________________________






Page 7






A kunyace na miƙe ina shafar inda na buge ɗin ko zan ga jini amma babu komai.Kowa yayi min sannu amma banda shi,gefen anty na zauna ina satar kallonsa sai wani ƙara haɗe rai yake ya na haɗiyar yawun da ban san ko na mene ba kawai dai ina ganin maƙogoronsa na motsawa.Ya juyo muka haɗa ido sai kuma ya ƙi kauce wa kallona ni ma haka na yi masa ƙur,yadda ya kafe bakina yasa na shafa gun sai na ji ya ɗan kumbura.Na shagwaɓe fuska kamar zan yi kuka ina mai ci gaba da kallonsa,ya kawar da kai gefe.Ana cikin haka ne kawai muka ga an turo Sheikh Muhammad bisa gadon maras lafiya an nufi wani ɗakin da shi duk sai muka tashi muka bi bayan su.
Idonsa biyu sai kllonmu yake ɗaya bayan ɗaya,Mubashar ne ya matsa kusan kansa ya na cewa “Sheikh ya jiki?” bai basa amsa ba sai hannunsa da ya kamo ya na ɗan matsa shi.Mubashar ya buɗe baki zai yi magana Sheikh ya tari

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login