Showing 1 words to 3000 words out of 21708 words

Chapter 1 - CELEBRITY FARASHIN TASIRI Book Complete by Mrs Sadauki .txt

10 Jan 2025

2188

[30/08 à 21:47] MRS SADAUKI 💫: 🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽
*FARASHIN TASIRI*🪺
```celebrity```🌬️
🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽
*Gajeren labari*🕊️


MRS SADAUKI 💫✍️


FCWA ☀️


Special gift fo my VIA FANS 🪷


❌Don Allah duk mai so ya fara daga farko,in kuma kin karanta ki yi share domin wasu su amfana




Page 1




“Ban...gane ka na asibiti ba? Mike faruwa? ”


“Na ce miki Sadiq Allah ya karɓi ransa ya riga mu gidan gaskiya ,yanzu haka ana ƙoƙarin yi wa gawarsa wanka”


Tamkar wacce aka buga wa ƙaton dutse haka na ji saukar furincinsa,ban san lokacin da na saki wayar ba na yi faɗuwar ƴan bori.Abu na farko da ya fara faɗo min a rai shi ne yadda yayi ta sambatuna a daren jiya ya na shaida min ni ce macce ta farko da ya taɓa kusanta a rayuwarsa .




Hawaye masu mugun zafi suka zubo min a kumatu,na sani ni karuwa ce duk abin da nake domin na samu kuɗi nake yinsa amma Sadiq shi na daban ne,ya so ni tsakani da Allah tun a lokacin da nake tallaka.Muguwar rayuwar da na saka kaina bai sa ya daina sona ba.
“Ki na da kyau! Wannan sana'a ba ta dace da ke ba.Zan so Allah ya nuna min ranar da zan aure ki,komai naki ya zama mallakina ni ɗaya” shine furincinsa na jiya bayan na ci galaba a kansa har ya kwanta da ni.




Ringing ɗin wayata shi ya maido da ni daga halin alhinin da ruhina ya lula.
“Alhaji Nera” shine sunan da ke yawo,da sauri na goge hawayen ina mai ɗaga wa.
“Baby na shigo gari ina son ganin ki a central hotel,a ɗakin da mu ka saba haɗuwa” shi ne abin da ya faɗa .
“Ban cikin yanayi wlh ,rasuwa aka yi mana” na faɗa kamar zan yi kuka.
“Subahanallah! Wa rasu?”
“Wani saurayina ne!” na basa amsa kai tsaye.
“Hhh! Wata sabuwa in ji ƴan caca! Meelat yau ke ce ke kuka akan namiji? Hum! Kar fa ki manta ke Cele ce wannan ba girman ki ba ne damuwa da wani can banza”




Cikin wata marainiyar murya na ce “Sadiq ne fa!”
“Sadiq? Talakan saurayin ki wanda ke ƙin karɓar kuɗin kin nan?”
“Shi fa dai” na furta wasu hawayen na zubo min shaaa.
“Allah jiƙansa! Amma Baby please ki ƙoƙarta ki zo ,na yi miki tanadi mai kyau” Alhaji Nera ya faɗa ya na mai yin dariyarsa ta shaƙiyanci.




Jin furincinsa ya saka na ji ɗan ƙwarin gwiwa,wayar na ajiye bisanin na shiga ban ɗaki na feso wanka.Kalolin turaruruka na shafe jikina da su sannan na fesa na baki bisanin na saka riga da wando jeans tare da ɗora hullar gashin doki.




Ban yi kwalliya ba hakan ya saka farin fuskata fita da kyau.Man leɓe na shafa bisanin na ɗauki key ɗin motata bayan na saka takalmi masu tsini.
Ina tafe ina rausaya kamar bishiya,mai gadi na ganina ya ruga ya buɗe gate.
Baƙar motata na shige na yi mata key, ina tafe ina sauraren kiɗa.


Wayata ta ɗau ringing,na ja uban tsuki ina masifa “jarababbe ni fa ban son jarr...” maganar ce ta gintse ganin sunan Heelat.
Ina ɗaga wa ta ce “Meelat ki na ina ne har yanzu ba ki ƙara so ba?” ta faɗa.
“Ban ƙara so ina ba?” na tambaye ta.
Ina jin mamaki a maganarta lokacin da yake ce min “ki na nufin ba ki san Sadiq ya rasu ba?”
“Na sani mana” na bata amsa.
“To mi kike jira da har yanzu ba ki zo ba? Kin ganmu nan fa duk abokanmu kowa ya zo”
Na ɗan taɓe baki na ce “zan zo ni ma,akwai wurin da zan je mai muhimmanci”
“Meelat duk uwar sadaukarwar da Sadiq yayi a kan ki har akwai abin da ke da muhimmanci da ya wuce ki hallarci zana'dar shi?”




“Heelat!” na furta cikin wani salo daidai nan na kawo hotel ɗin.
“Okay!” ta furta tare da kashe kiran.


Fitowa na yi bayan na gama parking,motar Alhaji Nera na gani a parker.Na saki murmushi tare da kutsa kai ciki,direct sama na hau inda ya saba kama mana ɗaki.
Knowking na yi,ya zo ya buɗe ƙofar.Uban tumbinsa na ƙurawq ido ina jin takaici,amma kasancewar mayyar kuɗi ce ni na share.
“Ya na ga ka na min wani kallo?”
“Kyau kika ƙara Babyna!” Alhaji Nera ya faɗa ya na washe baki.
“Ok na gode sosai!” na faɗa ina mai zama bakin gado.
Kusa da ni ya zauna ya fara shafata,sai dai ban biye masa ba saboda furincin Heelat da ke ta min yawo a kwanya.
“Baby don Allah ki cire mutuwar nan a ranki,shi fa ya riga da ya mutu to tunanin mi za ki yi?” Alhaji Nera ya faɗa ya na ƙoƙarin raba ni da kayan jikina.
Ban hana shi ba,haka kuma shawarar shi ta yi aiki kaina na ba da kai bori ya hau.
Bayan komai ya lafa ne yake ce min “kin ƙara zama ta musamman mene ne sirrin?” ya faɗa tare da kashe min ido ɗaya.
Ban basa amsa ba na tashi na shiga toilet na yi wanka,ina fitowa na mayar da kayana.
Ina tsaka da ɗaura igiyar takalmina ya miƙo min waya Android iPhone tare da wani turare wanda zai kai darajar dubu ɗari.
Na karɓa ba tare da na gode ba na miƙe tsaye,“zan tafi”
Yayi min kiss a goshi bisanin na fito.




Cikin aljihun mota na saka wayar da turaren bisanin na maida akalar motata hanyar gidansu Sadiq.
A daidai lokacin da nake fitowa daga mota,a kuma daidai wannan lokacin ne aka ɗauko gawar Sadiq za a saka a mota.
Ga dai duk jinkinsa rufe da likafani amma hakan bai hana ni ganin idonsa ba ya na fitar hawaye.Kukan jini Sadiq yake,yayin da kuma nake jin amon muryarsa ya na cewa “Meelat mi na yi miki har haka da za ki sayar da ruhina?”


Na zabura tare da yin ƴar ƙara jin an taɓa ni.Heelat ce,“lafiyar ki? Mene ne na gan ki cikin ruɗani? ”
“Ba komai !” na faɗa,ina mai sake kallon motar da tuni an shigar da gawar Sadiq wanda kuma ke yi min magana cikin ɗaga murya “Meelat ki cece ni kar ki bari a tafi da ni,ban mutu ba” motar na bi da kallo har suka ɓacewa gani na.




“Meelat ki rasa kayan da za ki zo da su gidan makoki sai wannan?” Heelat ta faɗa,na ɗan dube ta .
“Wai lafiya kike? Ya na gan ki wata iri? Ai ban yi tunanin mutuwar Sadiq ta shige ki har haka ba” Heelat ta sake faɗa.
Yayin da kuma sauran ƙawayenmu suka ƙara so ,gidansu Sadiq yayi ƙaramtar da ba zai ɗauki mutane sosai ba wannan ya saka duk suka tsaya waje.




“Gida zan koma!” na faɗa ina shirin tafiya Heelat ta riƙe ni,“ki jira mu yi ta'aziya mana .Yanzu za mu shiga amma don Allah bari na ba ki kallabina ki yafa ”
Ta faɗa tare da ciro kallabinta da ke ƙasan hijabi ta bani.
Karɓa na yi don kaf cikinmu ni ɗaya ce mai shigar banza duk da akwai uwanda ba su saka hijabin ba.


Ciki mu ka shiga don babu laifi mutane wasu sun ragu.Kamar wacce aka ce ma ga wadda ta kashe ɗanki haka Mamar Sadiq ke kallona da jajayen idonta ta kafe ni da su ko ƙyaftawa ba ta yi .
Da sauri na sunne kai ina jin zuciyata na mugun bugawa,lamurran da suka faru da ni a waje sai yawo suke min a kwanya.Har yanzu ban gaskata cewa abin da Sadiq ya faɗa min gaskiya ne ba.




Heelat Malama ce wannan ya saka ta wakilce mu ta fara jero addu'a'o'i mu kuma mu na amsawa da Amen .Duk da kaina a sunne yake amma har yanzu ina jin idon mahaifiyar Sadiq su na yawo a jikina.Na ɗan ɗago domin tabbatar wa,karaf mu ka haɗa ido da mugun sauri na mayar da su na sunne.




Wayata ce ta fara rigingin na katse kiran da sauri,sai dai yadda wani kiran ke ta shigo wa fiye da goma ya saka ni ɗaga wa,cikin ikon Allah daidai nan Heelat ta gama addu'a duk muka fitowa.


“Hello!” na furta,cikin ƙaraji yake min masifa tare da yi min furinci da ya kusa saka bugun zuciyata bugawa.
Tsabar kaɗuwa ya saka na riƙe Heelat gam ina mai sake tambayar Alhaji Nera “meeemm..me ka ce?”


“Ki sakar min gabana wanda kika sa yake ta fitar da jini,wato Meelat a kaina za ki gwada tsafi? Kin san wane ne ni ? Kin zata ni ɗin kanwar lasa ne?”
“Gaba kuma?” na sake tambayarsa a lokacin tuni injin da ke kula da ganina ya fara yin ƙasa.
Cikin gwanjin kuka,ban sani ba ko ya fahimci ban ma san abin da yake son sanar da ni ba yake cewa “Meelat ki yi wa Allah ki sakar min gabana ke ce kawai na yi amfani da ita duk yau,ki taimaka ki bar min abat1 wlh sabon aure zan yi.....”








*is not for free*😮‍💨
[31/08 à 11:01] MRS SADAUKI 💫: 🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽
*FARASHIN TASIRI*🪺
```celebrity```🌬️
🪽🪽🪽🪽🪽🪽🪽
*Gajeren labari*🕊️


MRS SADAUKI 💫✍️


FCWA ☀️


Special gift fo my VIA FANS 🪷




Page 2




Yadda Alhaji Nera ke gwanjin kuka a waya ya tabbatar min da gaskiya ce abin da yake faɗa.
Ina jin muryar wata na cewa “wannan ai baƙin ciki ne,ta ya za ki saka babban mutum cikin wannan mawuyacin hali? Ki taimaka ki saki kurwarsa kar jininsa ya ida.”
Na lumshe ido yayin da wasu zafafan hawaye kuma suka soma yi min zuba,key ɗin motata na baiwa Heelat na ce “mu je ki sauke ni gida don Allah ba zan iya yin driving ba.
“Mike faruwa Meelat? ”
“Mu je zan sanar da ke ” wayata ce ta ƙara yin ringing style Alhaji Nera ne.Ƙin ɗaga wa na yi ,a ƙarshe kuma na kashe wayar.
Heelat ce ta yi driving ɗina zuwa gida,sai dai tun kafin mu ƙarasa na ga motar ƴan sanda da kuma Hajiya Turai matar Alhaji Nera .


Yadda suka yi wa motata ƙawanya na san ban da wata mafita,“Meelat ƴan sanda ! Lafiya laifin mi kika yi?” Heelat ta faɗa a ɗan rikice ta na mai saurin taka burki.


Ban bata amsa ba na fita,daidai nan Hajiya Turai ta nuna ni ta na mai cewa “ga ta nan ku damƙeta ita ce ta kame kurwar mijina”
Ba su yi wani jira ba suka haɗe hannuwana tare da saka min akwa tare da jefa ni a motar su .




Heelat ta fara kuka ta na kiran sunana amma haka mu ka tafi mu ka barta nan tsaye.
A harabar asibiti motar ƴan sandar suka yi parking kafin a fito da ni.Ciki mu ka shiga har ɗakin da aka kwantar da Alhaji Nera ,har yanzu likitoci na kansa su na bakin ƙoƙarinsu.
Yadda al'aurar Alhaji Nera ke ta zubar da jini abun ya ƙara ɗaga min hankali,yayin da furicin likita kuma ya jefa ruhina cikin cakwakiyar fargaba .
“Zai iya mutuwa idan jinin bai tsaya ba nan da minti ɗaya”


Hajiya Turai ta min wani uban dundu ta na mai “don ubanki ki ƙetara shi ko kurwarsa ta dawo jikinsa,don wlh in kika bari mijina ya mutu da hannuna zan kashe ki”


“Meelat kin cuce ni,kin ci amanata...” Alhaji Nera ne ya soma magana sai kuma ya kasa ida wa sai gurnani da yake na fitar rai.
“Ya mutu!” wannan furincin na likita yayi daidai da tsayarwa igiyar da ke tafe da numfashina,ban ƙara sanin abin da ya faru ba sai tashi na yi na tsinci kaina a gadon asibiti.






Na lumshe idona da nake jin sun yi min nauyi,yayin da kwanyata ta yi balaguro zuwa shekarun baya ta na hasko min ainahin tarihina.








Jameela shi ne sunana na yanka,iyayena tallakawa ne.Mu na rayu a wani ƙauye da ake kira da Takalmawa.Noma da kiyo shi ne aikin mahaifina,yayin da sana'ar sayar da koko ya karɓi Innata.
Raheela ita ce babbar ƙawata,ajinmu guda a makaranta.Tun daga collège har zuwa lycée,bayan mun ci jarabawarmu ta ƙarshe wato BAC sai iyayenmu suka yi ta fafutukar yadda za mu shigo birni mu yi karatun University.




Ban da kowa a birnin Maraɗi sai abokin mahaifina wanda suke cinikin shanu, raƙumi da sauransu wato Alhaji Nera.
A ɓangaren Raheela kuwa ita a cikin hostel take karatunta tun da akwai ɗakuna inda ɗalibai ke kwana.




Tun ranar farko da mu ka fara zuwa makaranta mu ka raina kanmu,yadda ƴan matan birni ke cin uban ado yayin da mu kuma kayan jikinmu duk tsofi ne sannan ba wasu masu yawa ba.




“Jar uba Raheela dube min yadda ake ɗaukar wanka sai kace za a yi zaɓen fidda gwani” shi ne firucina yayin da nake ta ganin ƴan mata da samari na ta shawagi cikin sutura mai kyau.
“Jameela kar ki wani damu da kayan jikinsu,kin manta mu ɗin ƴan baiwa ne Allah ya yi mana ni'imar ilimi? Godiya ya kamata mu yi masa kasancewar mu ma mun shiga tarihi a cikin jerin ƴan matan Takalmawa da suka zo jami'a ”


“Haka ne kam! Su Lauratu ai tuni an yi masu aure ba tare da sun samu ilimi ba” na faɗa ina mai yin gaba,Raheela ta yi ƴar dariya ta ce “ke ma fa da yanzu ki na goyon yaro na biyu”
Na kai mata dundu ina cewa “Allah kiyaye min ,duka shekaruna 21 fa”
“Ƴan sha biyu ma an yi masu aure ballantana ke ƙatuwa? Mu je na gwada miki ɗakina ” cewar Raheela kafin mu wuce wurin kwanan ɗalibai.
Ɗaki ne ɗan madaidaici,mai ɗauke da gadajen ƙarfe biyu .


Bayan na ga ɗakin nata mu ka wuce ajin karatu,nan fa kallo ya dawo kanmu yadda mu ka fita daban da sauran ƴan mata.Bai hana wasu samari yi mana dariya ba ana zunɗenmu, kasancewar ban da haƙuri ya sa ni cewa “uban wa kukawa dariya ihiii? Sheguna masu ƙattan kanu ”
Ban san yanayin maganar ƙauyenmu zai basu dariya ba sai da na ga kusan mutanen na darawa su na “wlh ƴan ƙauye ne”




“Eh su na mi shikai in daga ƙauye na zaka ( na zo)?”
Tamkar abar wasa haka suka dinga tsokanata,a ƙarshe da na fahimci maganar ƴan ƙauyen ce basu dariya na yi banza da su.
Sosai Raheela ta yi ta danna ƙirjina,a haka har malamin da zai koyar da mu ya shigo.Nan ne fa suka raina kansu yadda suka ji ina ta ɓarin ilimi kusan ni da Raheela duk mun fi amsa tambayoyin malam .




Lokacin cin abincin yayi,ni da Raheela mu ka je mu ka sayo dambu mu ka zauna mu na ci.
“Assalamu aleykum ” wani matashin saurayi ya faɗa,Raheela ta amsa masa sallamar kafin ya ce.
“Don Allah mi sunan ƙawar ki?”
Sai da Raheela ta kalle ni sannan ta ce “Jameela”




“Su Jameela abun babu Bismillah?” ya tambaye ni haɗi da tsure ni da ido,“Kar ka kuma ambaton sunana”
Na furta ina harerensa zan ci gaba da yin magana na ƙware nan na shiga tari.
Ruwan da ke riƙe da hannunsa ya miƙo min na karɓa na sha ,“yau na ga masifa! Wlh ko maye ne kai kurwata ta fi ƙarfin ka” na faɗa ina goge hawayen da ke min zuba don sosai na ƙware.




Shi da Raheela suka shiga yi min dariya,bisanin ya zauna su na hira.Don dole ni ma na saki jiki aka yi hirar da ni,a nan ne na san sunan shi Sadiq.
Tun daga wannan lokaci mu ka yi sabo da Sadiq wanda bai ɓoye min ba ya nuna min so da ƙauna,don abokinsa Hafiz har tsokanarsa yake da mijin baƙauya.






Adadin watannin da na yi a jami'a iya adadin yadda girman burina ke daɗa ƙaruwa a ruhina.Ina son ganin na yi rayuwa irin ta wayayyun mata,na saka kaya masu kyau,na hau mota mai tsada da kuma zuwa wuraren ƴaƴan masu kuɗi.
Sam ban iya ɓoye muradina,a kullum in mun fita na ga mota mai kyau sai na nuna kwaɗayina akai yayin da Sadiq da Raheela ke iya ƙoƙarin su wurin ganin na cire wannan dogon burin sai dai ina,aka ce wanda yayi nisa ba ya jin kira.






Yau ne aka bamu hutun farko, wannan ya saka mu ka fara shirin zuwa can ƙauye.Hajiya Turai wacce a gidanta nake zaune sai wani ɓata rai take don ba ta so na tafi saboda tun zuwana ni ke yi mata wankin kaya da sauran aikace-aikace.




Bayan na gama shirya komai Alhaji Nera ya ɗauke ni a mota ya kai ni can tasha.Tun kafin na sauka na hangi Raheela zaune ta na zaman jirana,ƴan kuɗin kashi ya bani bisanin ya ce min “in kin je sai ki gaishe da Abban ki”
Da “to” na amsa kafin na fito da ƙullin kayana cikin ɗan buhu gari yayi zafi.
Mu ka rungume juna ni da Raheela bisanin mu je mu shiga mota.




“Babu wuri kujera ɗaya ce ta yi saura,ina ga mu fita mu jira wata” na faɗa ina dubawa ko zan samu wata kujerar .
“Ki zo nan ga wuri nan” cewar wata Hajiya daga can ƙarshen mota,da murna na ce “yawwa Raheela ke zauna nan ni bari na je can”
“To babu damuwa amma na so a ce mun zauna kusa da juna” Raheela ta furta duk yanayin fuskarta ya nuna rashin jin daɗi.




Ni kuwa ƙetara wa na yi,na zauna kusa da matar ina mitar “to tun da ba motar gidanmu ba ce ai dole mu yi haƙuri,nan ina ce in kin ji ina faɗar ina son na yi kuɗi na shiga mota mai kyau ya kwatsa ta kike”


Zama na gyara ina mai rungume buhun kayana,direba ya fara jan mota hajiyar da ke kusana wacce ƙamshin turarenta duk ya cika min hanci ta ce .
“Ƴan mata mi sunan ki?” na dubeta a mamakance,ta ci gaba da cewa “na ji kin ce ki na son ki yi kuɗi shi ne nake son na ji ta bakin ki in ki na son na taimaka miki ”
Jin ta sosa min inda yake min ƙaiƙayi ya sa na washe baki,don kallo guda za ka yi mata ka gane mai kuɗi ce ita irin sosai ɗin nan don hauren Makka biyu ne jere ras a bakinta .
“Hajiya da gaske za ki taimaka min na yi kuɗi?” na tambaye ta.
“Ƙwaran gaske ,yanzu haka ina da yara sa'anin ki masu aiki a ƙarƙashina duk sun yi kuɗi ta dalilina.Ina da motoci sama da biyar,yanzu ma ra'ayi ne ya saka ni shiga motar kasuwa sannan yadda kika san shiga ɗaki haka na mayar da jirgin sama ”
Romon bakan da take yi min suka ƙara zautar da ni,sai ƙasa-ƙasa take da murya ta na bani labarin rayuwarta da ƙasashen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login