Showing 21001 words to 21708 words out of 21708 words

Chapter 8 - CELEBRITY FARASHIN TASIRI Book Complete by Mrs Sadauki .txt

10 Jan 2025

2194

za mu tsaya?” na tambayi Heelat ina ƙare wa asibitin kallo.
“Sai shugaban asibitin ya zo,shi ne zai damƙa mu ga ma'aikatan ”




Ina shirin buɗe baki na yi magana sai ga motar Bashir ta shigo,ban kauda idona ba har sai da sai da matar ta fito wanda a gaban idona yayi kissing ɗin goshinta.
Wani ƙaton dutse ne ya zo kan zuciyata ya zauna daram,ji na yi kamar na je na shaƙo shegiya don na fahimci matarsa ce wacce akan ta samu ciki ya fasa aurena don yanzu na fahimci Bashir ba zai aure ni ba.Kimanin sati ɗaya currr nake binsa akan ina son ganinsa ya ƙi,a ƙarshe ya faɗan maganar da har in mutu ban zan manta ba “in na aure ki mine ne za ki ban wanda yanzu ba ki ban ba?” shine furucinsa na ƙarshe a gare ni.






Na rumtse ido lokacin da kyakkyawar matar tasa ta zo wucewa ta gabanmu.
“Ke lafiyar ki?” Heelat ta tambaye ni,ban kai gabata amsa ba wata nurse ta kira mu.
Mu na zuwa sai mu ka tarar da sauran abokan karatun mu ashe tun ɗazu su na ciki.


Da tsiya da jaraba sai da na san yadda na yi na je ɓangaren ƴan awon ciki,nan na samu mata sun yi layi sosai ban sha wuya ba wurin hango matar Bashir .Kamar wacce aka yi wa allurar baƙin ciki haka na shiga mota na je pharmaci na siyo maganin zubar da ciki na dawo.
Cikin ladabi na je ina kamawa matar aiki har aka zo kan matar Bashir ,a gabana ta kwanta Madam nurse ta mata scanning ɗan cikin sai juyi yake .
Bayan an gama aka ce na bata maganin masassara don jikinta na da zafi da kuma wasu sauran magungunuka,cike da dubara na bata na zubar da cikin wanda in ta sha shi da wuya ma in mahaifarta za ta ƙara ɗaukar ciki da wuri.
“Allah raba lafiya” na faɗa ina murmushin ƙeta .


Sai wuraren sallar la'asar mu ka tashi,ni na ɗauki Heelat cikin motata direct gidana mu ka wuce.Tsoro ya bayyana ƙarara kan fuskarta ta ce “Meelat duk yadda nake tunanin ki ashe kin wuce nan?”
Na yi murmushi kawai na wuce kitchen, Heelat kuwa sai dube-dube take kamar baƙauyar da ta shigo birni.


Jus da kayan motsa baki na kawo sannan na kunna kayan kallo,Heelat na ci ta na min wa'azi inda a ƙarshe take cewa “Meelat kan wannan sana'ar da kika sa kan ki tun da kin ce saboda kuɗi kike yi mi zai hana ki buɗe shafin Tik Tok yadda kike da kyawun nan na san za ki samu followers,cikin ƙanƙanen lokaci za ki zama *CELEBRITY* ”


Na yi shiru ina tunanin maganarta,sai na ce “a can zan samu kuɗi?”
“Milliyoyi ma kuwa”
Furincin Heelat ya saka na sauke app ɗin Tik Tok ita ta nuna min yadda ake yi komai ta ce wurin wacce suke kwana ɗaki ɗaya duk ta koya .Kamar da wasa na buɗe shafina da sunan *MEELAT ƳAR FULLO* .
Wanka na yi na saka wata baƙar riga marar hannu tare da wando,Heelat ta min video farko a rayuwata na ɗora.


Sama da awa biyu har Heelat za ta tafiya sai kuma ta ce “Shiga mu ga su wa suka yi like da comments”
Hannuna har rawa yake wurin dubawa,caaa haka na ga an yi min tuni na samu followers da comments na ban mamaki.Daɗi na ji kamar zai kashe ni,mutanen da suka nemi na yi masu video sun fi ɗari.Tun daga lokacin na ji kaina ya fara hayaƙi,buri da muradin zama CELEBRITY ya danne zuciyata.......


*Yanzu ne kawai mu ka shigo labarin mun fita daga shimfiɗa,da sannu za mu ji yadda ta zama CELEBRITY wanda in ba ku manta ba farkon labarin tuni Meelat ta fara biyan FARASHIN TASIRI saurayinta Sadiq ya mutu,ga kuma Alhaji Nera gabansa na fitar da jini.Shin wace ce Meelat bayan ta fara rayuwar Tik Tok? Har mene ne ya jaza mata wannan masifar da duk in ta yi mu'amala da namiji yake mutuwa? Ya za ta yi kenan a yanzu da ake tuhumar ta da ta kashe Alhaji Nera?*


Sai mu haɗe a PAID GROUP,only 300 ne via
3184721842
Bala Maryam Mikailu first bank , shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 ,ƴan Nijar carte airtel ta 300f.




NB: 300 kuɗin shiga group ne,daga lokacin da na kammala shi zai koma 500




5/9/23




MRS SADAUKI NIJAR

6
7
8

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login