Showing 45001 words to 48000 words out of 48742 words

Chapter 16 - INA ZAN GANSHI Complete Book By Xahra Bukar.txt

14 Jan 2025

2383

Batul ta zama tsoro take tamai magana ya gwaleta, tanai jiyo dariyar su apalo cike da annushuwa, kasa jurewa tayi tadau pilo ta rufawa kunnuwanta.
Da dare, wanka tayi ta sanya riga bacci riga da wando, zama tayi bakin mirrow tanai kallon kanta cike da tausayi, shigowa dakin Mardiyya tayi hade da Sallama, amsawa tayi fuska ba yabo ba fallasa, duk yadda take jin kishin Mardiyya bazata iya share taba sakamakon hallarci datai mata, alheri dankone bai zubewa kasa banza.
Mikewa tayi tana fadin "Sister Mardy kin shigo" karasawa gado tayi zata kwanta, Madiyya tayi saurin dakatar da ita da cewa "bacci nakeji, kwanciya xanyi, Sweetie na jiranki kije ki tayashi hira"
Galala Batul tayi tanai kallonta, aranta tace kingama dashi dole ki mikomin saura, afili tace "nima bacci nakeji" hannuta tasa tana kakabe gadon.
Dariya Mardiyya Tayi tace "you are joking, kinsan dai ba yadda zaai kishiyoyi su kwana guri daya, shi kuma mijin dawa xai kwana"
Takaici ne ya kama Batul danta lura sodai take taje gurun prince alhalin kuma ba damuwa yayi da ita ba, hamman karya ta kirkiro tana fadin "Sister y not ki kwana can, ni saina kwanta nan"
Harara takai mata cikin sigar wasa tace "naki wayon, yau kece da prince charming dinki, idan kinaso har gobe ma, jibi sai kiyi hand over".
Ganin dagaske Mardiyya take yasa ta amice zataje akan gobe bazata koma ba.
"As you wish" Mardiyya ta fadi tanai dariya.
Jiki sanyaye tadau hijab tasaka, tsoron zuwa take karya korota, kallonta Mardiyya tayi hade da daga gira tace "princess kina bukatan escort"
Kunya Batul taji, tayi azaman bude kofar ta fita.


Ahankali ta bude kofar tashiga, zaune ta iske shi kan sofa yanai dannan lapton dinsa, bata iya cewa uffan ba ta karasa can karshe gadon hade da kwanciya ba tare data cire hijab dinta ba, sosai ta takure kanta guri guda idanuwanta na kansa tanai kallon kyakyawar fuskar shi, sosai take bukatar sa ajikinta saidai haka bazai yuyuba ayadda taklga fuskarsa tamau ko annuri babu.
2 hours yayi yana danna dannansa daga bisani kuma ya mike ya kashe wuta, hawa gadon yayi ya kwanta can gefe da ita hade da bata baya, idanuwan ta kulle saidai ba bacci take ba, budesu tayi taga uban tazarar dake tsakanin su, babban takaicin ta shine yadda ya juya mata baya uwa baisan da halittar ta gurin ba, kukane ya kufce mata tayi saurin rufe bakinta da Hannu hade da juya mai baya, kuka sosai take ba kagauta, tunani take wace irin kiyayaya Rmd ke mata....
[10:01PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: đź’– *INA ZAN GANSHI*đź’–
Rubutawa
Xarah Bukar


®NWA


xarahbukar.wordpress.com



*Wannan Shafin naku ne Miss xoxo, Aunty Maijidda, Sady Jegal, Mom Fatu, Dota Waliyya, khadija Tsafe, Baby Nurse, Bady Social Sophie, Ummu A'sad, Momikky, Bilikisu Baraya, thanks so much for the love & Support, Princess na tare daku*
*ILYSM*❤❤


*TeamBatul🤸‍♂*



77


Bata runtsa ba har asubah, tanai jinsa ya tashi ya shiga toilet, alwala ya dauro ya fito ya fice masallaci bayan ya zurawa jikinsa dogowar jallabiya, ajiyar zuciya ta sauke mai dauke da shesheka, wani irin azababban ciwon kai ke damunta, dakyar ta iya mikewa ta shiha bayi alwala sannan ta fito tayi sallah, jirin sosai ke dibanta, adaddafe ta iya karasawa gadon ta kwanta, bacci barawo ya saceta.
Saida gari yayi haske Rmd ya dawo gida, zama yayi parlour hade da Kunna Tv. Wayarsace tayi ruri, dubawa yayi yaga Mom ce da azama ya dauka hade da gaidata aladabce, sun jima suna magana daga bisani yace mata karta damu zaizo gidanta suyi magana, sallama yayi mata sannan ya katse.
Zaman awa kusan hudu yayi gurin babu alamun tashin daya daga cikin su, mikewa yayi ya nufa Dakin Mardiyya, zaune ya iske tanai kokarin sakalawa kunnanta dankune, jikinta sanye da English wears na riga da skirt, gaisawa sukayi cikin so da kauna juna sanya suka fito palo, earring din ya amsa ya sakala mata.
Tace "Sweetie am so sorry, ban hada maku breakfast ba" mikewa tayi zata nufi kitchen yayi saurin rikota hade da zaunar da ita.
Murmushi tayi sunai fuskantar juna yace "don't worry, princess xatayi, kinsan i cnt allow you stay away from me"
Murmushi tayi bata ce uffan ba, mikewa yayi ya shiga dakinsa, guntun tsaki yaja ganin yadda take sharar bacci tamkar matacciya, pillow ya dauka hade da wurga mata.
Atsorace ta farka hade da zuburewa zaune tanai sosa idanu.
Daure fuska yayi yace "tashi kije ki hada mana breakfast"
Dauke kai tayi gefe tace "banice da girki ba Sister Mardy ce".
Kollan mamaki ya bita dashi, if he could remember tunda taxo gidan Diyya ke kirki, jiya kadai ne yaga ta taimaka mata.
"Daga yau kice in charge of kitchen ko ba ranar girkin kiba, Understand ?
Bata iya bashi amsa ba, ficewa yayi ya koma palon.
K'wafa tayi, aranta tanai fadin ta daina kuka daga yau, ko miye xai mata she is ready for him, mikewa tayi ta fice daga dakin, kwance taga Mardiyya yanai mata tausa suna dariya cikin anushuwa, kallo daya tai masu ta dauke kai, daki ta shiga tayo wanka sharp sharp sannan ta nufi kitchen hada breakfast, bayan ta gama nasu ta kai kan dinning, tayi respecting kanta ta zauna a kitchen taci nata.






***


Gidan Mom ya nufa, magiya sosai take mai akan ya tayata baiwa Baba Hakuri da neman gafararsa, tayi nadama ba kadan ba, duk cikin kuka take fadi mai hakan.
Kallon ta da sauraranta yake saudai bai yadda da sudden repentance dinta ba.
Yace "Mom koda ace Baba ya yafe miki, hukuncin Ubangiji na jiranki, you left your marriage for years ba tare da wata hujja ba, kinsan hakki aure ba wasa bane shi Vaba da kika raina aljannar ki na karkashin tafin kafarsa, all those years miyasa baki saduda"
Kuka sosai ta fashe "my boy nasan na tafka babbban kuskure plz help me talk to him"
Nisawa yayi yace.
"I cnt, if you really seek his forgiveness, its better you talk to him, besides ni ba sanin abunda ya hadaku nayi ba, keda kika sani i tink should try clean your dirt"
Hannusa ta riko tace "it all my fault, if you can't talk to him, allow me ta talk to his daughter"
"Oh Mom stop it, plz dont involved princess a problems dinki"
Girgiza kai tayi tace "okay, i'll talk to him, but not now nafison saiya huce, nasan he is very angry with me"
Murmushi yayi, dama abunda yakeson tagane kenan, sun jima suna hira daga bisani kuma yabar gidan.






Life goes On, zamantakewar gidan bai canxa ba, tuni Batul tayi catching head one side, tsakanin ta da Rmd sai gaisuwa, ranar kwananta adakin sa ba abunda ya canxa, kowa zaman you're on your own suke ma juna su, ba abunda yafi kona mata zuciya kaman yadda yake zuwa dauka Mardiyya ranar girkinta, dakan shi zai shigo dakin daukaera tamkar wata sabuwar amarya, tayi ta zuba mai shagwaba yanai biyeta.
Saidai zamansu da Mardiyya ba yabo ba fallasa, sosai take girmamata da darajata, ko da wasa bata taba mata kallon baccin rai ko haushin abunda takeyi ba, iya kaci ta bita da murmushin dayafi kuka ciwo.
Sati Biyu kenan zani bai canxa dauri ba, jira kadai Batul take taga ranar dazai waiwaye ta, ta nunamai ita ba kanwar lasa bace.
Bangaran Mom kuwa ta kasa samun courage din zuwa gurin Baba, kullum cikin saka da warwara take.


***


Kamar Kullum shigowa dakinsu yayi, sanye yake da nite gown riga da wando.
Zaune ya iske Mardiyya gaban dressing mirrow Batul tanai mata oiling gashin kanta, ganinsa yasa tayi azaman ajiye comb dake hannuta, juyawa tayi ta shiga Toilet kafin su daura mata hawan jini.
Bayan Mardiyya ya karaso yanai shafar gashin kanta hade da kallonta ta mirrow.
"Alway late, yauma saida kika bari nazo daukan ki ko?
Ya fadi yanai murmusa.
Kallon mamaki tamai daga cikin mirro tace "Sweetie where are we going by these time".
"My room" ya fadi murya kasa kasa.
Juyowa tayi tanai kallonsa sannan tace "let sleep here"
Dariya yayi yace
"Idan muka kwana nan, wacen yarinyar fa, ina zata kwana"
Ware idanu Mardiyya tayi tace "na manta shataf, ashe Altine ke kwana anan"
Kallonta yayi aranshi yana tausayinta, she is totally confused, dagota yayi hade da rikota suka fita daga dakin tanai fadin "Altine nada kirki sosai, dazu har ruwa taban nasha"
"Eh hakane" ya fadi, karasa shiga dakinsa sukayi ya rufo kofar.
Fitowa Batul tayi daga toilet cike da mamakin maganganu Mardiyya data jiyo, "kodai Sister Mardy bata da lapia ne" ta fadin aranta, kwana biyun nan ta lura kaman akwai abunda ke damunta saidai ta kasa ganowa, zama tayi kan gado hade da sauke ajiyar zuciya, fayus take jin zuciyanta, wani haushi da kishin Mardiyya duk sai taji babu shi aranta, hannu ta daga tanai godewa Allah daya cireta mata kishinta, Mardiyya is too good ace ta sanyata a zuciya, addua sosai Batul tahau yi akan Allah ya basu zaman lafiya.


Kan sofan dakin ya zaunar da ita sunai fuskanta juna, shuru sukai nadan sakwanni sannan tace
"Sweetie inaso muje muga Doctor Amjad Gobe"
Ajiyar zuciya ya sauke ganin she is back to her senses, yace "Diyyah karki damu, mutuwa ta Allah ce bata Doctor ba, just because yace tun last week yakamata ki shiga final stage dinki that doesn't mean you will die, gashi mun shigo second week you are still kicking, plz don't loose hope"
Murmushi tayi hade da kwanto wa jikinsa, cikin sanyin murya tace "Sweetie"
Murya kasa kasa yace "You should be laying down"
Tace "no, it better we sit and be staring at each other"
Tausayin tane ya cika mai zuciya, yace " i was wrong to deny you the satisfaction of love"
Nisawa tayi tace " i know I'm supposed to be cruel or vicious but i cnt because my heart is full of your love, Am I angry at what you did to me? Yeah,
and I've been living in agony for what you did, marrying princess without telling me, it really hurt"
Hawaye ne ya zubomai yayi saurin sharewa, matse ta yayi jikinsa yace "Am sorry"
Tace "Apology accepted, I wish i knew you were such a romantic guy, I would have played so hard to get you 10 years back"
"Let not speak of regret, the past isnt a story to tell"
Murmushi tayi, tanai kokari sauke numfashin ta dake kokarin dauke wa, cikin wahalalliyar murya tace "you showed me your whole life, and i understood it, i know that princess will alway be around to stand by you"
Yace "Why you telling me this"
Lumshe idanu tayi tace "because I won't be
Around any more to tell you"
Kuka ne ya kufce mai, yayi sauri dauke kai
Hannu takai fuskar sa
Tana fadin " Hey, hey. Look at me. It's going to be okay, i don't like it when you cry" juyo da fuskar sa tayi suna fuskan ta juna.
Saurin janye jikinta tayi sakamakon mugun tari daya tsarke ta, cike da kidema yahau yi mata sannu, amai ne yazo mata tayi saurin rugawa toilet, binta yayi yanai mata sannu, wani irin bakin aman jini take kwararawa cike da tsananin tashin hankali, ruwa ya diba hade da gyara mata jiki sanna suka fito, zaunar da ita yayi kan sofa hade da dauko mata maganinta dake side drawer, balla yayi hade da daukan bottle water dake gurin.
"Diyya plz take it".
Kawar da fuska tayi
Ya kuma fadin "plz Diyya ki sha, it will ease the pain & dull the symptoms"
Dakyar ta yadda ta sha, zama yayi kusa da ita, ta kwanto kanta bisa cinyar sa hade da kwanciya tanai numfashi dakyar.
Hannu yakai yana shafar fuskarta har bacci ya dauke ta, shingide kansa yayi jikin gadon hade da runtse idanu.
Bayan some mintuna bacci ya kwashe sa, kirar sallah asuba ne ya farkar dashi, jin alamun kaman tanai magana yasa yace "Diyyah kin tashi".
Bata iya tanka saba, ta gyara kwanciyar ta, mikewa yayi ya shiga alwala sanana ya fice masallaci, bai jima ba yadawo, kusa gareta ya karasa hade da kwanciya, shuru yaji ba alamun numfashi tattare da ita, mikewa yayi azabure yanai kiran sunanta.
Tab'ata yayi yaji alamun babu rai tattare da ita (Kulli nafsin za'ikatul mauti) mikewa yayi cike da kidima bakinsa na furta salati, kasa komai yayi banda hawaye da yake zubdawa, zani yadau ya rufe mata sannan yadau wayarsa ya kira Numbar Hajiya Safara..
Carbi take ja taji rurin wayarsa, ganin lambar sace yasata faduwan gaba dauka tayi .
Yace "cox of your unknow selfish motive, your daughter is dead, believe me kuma Justice must me serve....." Katse wayar yayi.
Tuni Hajiya safara ta kwalla ihu hade da cilli da wayar, Abba mardiyya dake shigowa dakin ne yahau tambayar ta lafiya.
Kuka take tana fadin "Mardiyya ta rasu...
[10:01PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: đź’– *INA ZAN GANSHI*đź’–
Rubutawa
Xarah Bukar


®NWA


xarahbukar.wordpress.com

*This whole Book is Dedicated to My one & only Cutest Miss Xoxo*



*Last Page*


_Allahumma Innaka Afuwwan Tuhibbul-afwa Fa"afuana_




78 - 80








Ba k'aramin girgiza Alhaji Bello yayi ba, cikin tsananin tashin hankali yake tambayar ba'isin mutuwarta, a iya saninsa kalau diyarsa take, farat daya baza'a cemai ta mutu ba.
Kwantar masa da hankali Hajiya Safara tahau yi tanai karar tunasar dashi Ajali idan yayi kira dole aje koda ciwo ko babu, addua kadai ya daje da mamaci ba kururuwa da neman kauce hanya ba.
Sosai jikinsa yayi sanyi dangana ya sanyawa zuciyar sa.
Ba tare da bata lokaci ba jamaa har sun hallara, sutura da jana'izar ta akayi sannan aka mik'a ta makwancin sa, (kulli nafsin za'ikatul maut, Allah yaji kan musulmai). Jama'a da dama na nesa da kusa duk sunzo ta'aziya da ban hakuri, kowa yaban ta yake sanin ta macen k'warai.
Bangaran Batul kuwa tafi kowa girgiza da mutuwar sister dinta, tsabar tsoro da firgici kasa zama tayi agidan, tuni ta koma gidansu cikin tsananin tashin hankali, dakyar Baba ya barta ta zauna bayan ya kira Rmd ya sheida mata zuwanta.


Takardu masu dinbin waya Hajiyar Safara ta fiddo daga tsohuwar ma'ajiya, kitchen ta nufa ta baiwa biebee taje bayan gida ta konasu, bata konasu ba tahau karanta abunda ke ciki, fasa konawa tayi ta ajiye su, ganin Alhaji Bello zai fita tayi azama kaimai takardu, karba yayi yahau karanche su cike da tashin hankali, wayar sa ya fiddo ya kira Rmd, sun jima sunai magana daga bisani suka ijiye inda zasu hadu.


Gidan Baba ya nufe ya dauki Batul da tuni tagama Sadudu da rayuwar duniyar, mutuwar mardiyya ba karamin kara mata tsoron Allah yayi azuciyan taba, taso rama Abunda Rmd yay mata saidai bazata iya ba, sai yanxu ma tagano duk abunda yayi hakan ne kadai zaisa mu daman kasancewa da Mardiyya, inda ace bai kula Mardiyya yaba harta mutu, ita kanta she wont forgive herself, guilty conscious kadai ya isheta, tana son Rmd, dole ta tallafe sa balle ma yanxu da yake cikin kunci da tashin hankali.

Tuki yake amma daka ganshi kasan yana cike da damuwa, sosai Batul take tausayinsa, ganin hanyar gidan Mom suka nufa yasata tsorota, rokonsa tahauyi karya kaita gidan, parking yayi yahau bata baki da kwantar mata da hankali, dakyar dai ta hakura bayan ya shaida mata Mom dinsa ta shiryu, koda suka isa gidan faram faram Mom ta amshe su, ganin Batul taki sakin jiki yasata ta neman gafarar ta, sai sannan Batul ta iya sakin jiki, Mom sai lailaya ta take tamkar kwai.


Da yamma Rmd ya shirya suka hadu da Alhaji Bello awani Guest in, takardun Ya mika mai hade da tambayarsa ko yasan da faruwar makamanci haka..
Gigirza kai Rmd yayi cike da kidema ganin takardar mai dauke da shedar siyar da kidney din Mardiyya shekaru ashirin da suka wuce, numfasawa yayi yace "Alhaji yaushe akayi hakan, kuma miye hujjar ku na siyar da kidney dinta a black market"
Ajiyar zuciya Alhaji ya sauke yace "ni kaina bansan da faruwar hakan ba, signature dai ya nuna Hajiya safara ta siyar da kidney dinta batare da sani naba, shiyasa nazo tambayar ka ko kasan wani abu game da hakan ?
Sosai ran Rmd ya baci, yace "banda masaniyan akan komai sai kwanakin baya dana ga takardun treatment dinta, direct gurin Doctor Ajmad na nufa, nan yake fada min Mardiyya nada chronic kidney disease (renal failure) due to improper treatment, the only kidney da take dashi bata taba zuwa ayi mata haemodialysis ba (dialysis to remove waste product from the blood), by the tym da tayi realizing it was too late, left untreated for so long yayi causing mutuwar ta"
Jinjina kai Alhaji yayi kaman yayi kuka yace "bata taba gayamin ba, am sure kuma Safara tasa komai"
"Tabbas tasan komai, cox Mardiyya tafadi min tare suke zuwa asbiti duk wani test result dinta karba take bata bari koda wasa Mardiyya tagani, ciwon yay mata tsananin yasa ta koma ganin Doctor amjad secretly"
"Amma kai hw coms bakasan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login