Showing 15001 words to 18000 words out of 48742 words
Chapter 6 - INA ZAN GANSHI Complete Book By Xahra Bukar.txt
da azama ba tare da ta jira cewarta ba.
Sauke numfashi Inna tayi ta mike tsaye tana kai komo adakin, yazamata dole tama Rasheed magana, lokaci yayi dazai fito ya nuna mata shine wanda takeso tun kafin ciwon zuciya ya kamata, yadda taga Batul na kuka ta yadda cewa lailai tayi sanyi kuma ta saduda, dakinta ta nufa tahau lalubar wayarta dan kiran Rasheed.
Babban titin unguwar ta tako tanai sak'a da warwara a zuciyan ta, Iv data gani ya nuna mata a fountain Mansion xaai Dinner saidai kuma batasan gurin ba, amma kuma idan taje ya xatayi, nuna kanta garesa xatati ko miye ?, gigiza kai tayi hakan bazai yuyyba, zataje ne kawai taganshi ido da ido.
Napep data tsada ba wanda ya dauke ta acewarsu gurin district area ne da napep ko achaba basa zuwa, dakyar dai tasamu taxi sukayi ciniki ya kaitaa naira dari shida dan ba karamin nisa ne da inda ya dauke taba, can farkon hanya ya sauketa ta tafara takowa toward the gate, Kasa karasawa tayi bakin gate din, sojijin kusan 20 ke tsaye bakin gate din, sai manyan motoci da suke artawa ciki a guje, daga gurin da take tana jiyo sautin wak'a dake dashi.
Tsuru tsuru tayi, bugun gabanta na tsananta, shahada tayi ta nufa gate din, daya daga cikin soja ya dakatar da ita yana tamvayar ta Iv, ba'a bata ba tace dashi, tuni ya kuma daure fuska, dan kuwa babu mai shiga sai da Iv, dinner din is strictly on invitation.
"Oga dan Allah ka barni na shiga " ta fada amarairace. bai tanka taba saima kallon gefe sa da yake, Mom ke takowa cikin takun kasaita, sanye take cikin tsadaddiyar leshe kanta daure da gele wanda Oshewa beauty suka mata tieing, kallonta Batul tayi aranta tana adduaa Allah sa matar ta barta ta shiga.
Karasowa tayi.
"Julius make sure ku tsaya postion dinku, gasu nan isowa" ta fada tana kallon julius bata ma lura da Batul dake tsaye ba, juyawa tayi zata tafi sai kuma ta juyowa kallon Batul, dauke kai tayi da sauri ta kalli julius tace "miya kawo almajirai gurin nan ?
"Hajiya ayi hajuri, yanxu zata tafi"
Harara takaimai taja tsaki ta wuce.
"Yarinyar kibar gurin nan, kafin nasa a wulla ki titi"
"Dan Allah ka barni na shiga, it very urgent" kuka ta sanya tana magana.
D'ayan soja dake tsaye yace "yunwa take ji, bara atura kodan snack ne abata ta tafi"
Gefe Batul tayi ta tsaya tana sharar kwalla.
Covony na mayan motoci guda ashirin sukayi, motar amarya da ango ne a tsakiya, suka karaso gaban gate din basu shiga ba, duk motocin suka tsaya, Zaune suke a motar babu mai magana tsakanin, jifa jifa ne Mardiyya ke kallonsa ta saki murmushi, shima murmushi yake sakar, gabadaya hankalin sa baya jikin sa, maganar su da Inna a waya kadai ke yawan mai a kai, ita so take ya nunawa Batul kansa, saidai bazai iyaba dan kuwa ba sonta yake kuma bai yadda ta saduda ba, nan gaba tana samu wani oppurtunity halin karyar ta xai dawo, asalima he is planing of sakinta idan Baba ya dawo daga tafiyar kauye da sukayi.
Numfasawa yayi ya jingine kansa cikin seat hade da kawar da kansa gefe yana duban waje da hasken lantarki ya gwauraye, gabansa ne ya fadi ganinta can nesa tsaye tana zubda hawaye, idanuwan na kallon motarsa tasu da tasha decoration, motar kadai take gani banda mutane dake ciki kansancewar tinted glass dinta.
Kallon ta kawai yake yana mamakin abunda ya kawota gurin nan, Inna tacemai ta fita amma baiyi tsammanin nan tazo ba, gashi yanxu sha daya na dare yayi baisan ma yadda zata koma gida ba dan babu abun haya gurin. Hannu yasa da niyya bude bangaransa xai fito tayi sauri daura hannunta daya sha lalle bisa nasa, kallonta yayi ta sakar mai murmushi, tace 'it time" murmushin dabai kai zuci ba yayi yace "okay'
Fara tafiya motocin sukayi suka shiga ciki.
Bangaran Batul kuwa kuka kawai take ba kagauta, snacks da soja ya kawo mata fir taki karbar, dakyar da sudin koshi tabar gurin bayan Julius ya sama mata lift a motar wata da zata koma gida.
Karshe haduwa Hall din ya hadu, Fadin haduwar Hall din kauyanci ne, jama'a masu hannu da shuni ke zaune gurin, daka ga couple din kasan suna cikin farin cikin, dukda cikin damuwa yadda xata koma gida yake bai hanashi sakin fuska ba.
Budirin kadai ake ana ciye ciye cikin jin dadi da annashuwa, can na hango members na *xarah Bukar novel 1, 2, & 3, Home of novel, Pherty novel, Musha karatu, Qurratul-Ayn Novel, Mom fatu Novel*, mamakin ina suka samo Iv nake, ban gama mamaki ba sai ganin su *Miss xoxo Ummee Agoss, Sadiya Jegal, Mom fatu, Queen Miemee, Rookie kazxx, Ramalurv, Hafsat Rano, Dija Waziri, Waliyyah* hakince nagansu suna kwasar loma, nima baa barni baya ba, ledar dake boye cikin jakata na fiddo na kwashi varieties of abincin dake gurin dan kaiwa kawayena su *Mrx Ay, Naja wali, Faty so, fati Imam, Aysha Gajo, Aisha Magasa*😋😋😋😋
Kusan 3am taro ya watse, kowa ya tattara yayi gida, couple ma suka koma gidansu.
*****
Bayan kwana uku.
Mom ta wuce Abuja huta da gajiya, Zaman Rasheed da mardiyyah ba yabo ba fallasa, sosai Mardiyya ke kokarin faran tamai, ba laifi shima yakan kokarin faranta mata dukda bata gabansa, sunyi waya da Innaa ya yanke shawara zuwa dauko Batul ya dawo da ita gidansa, dukda haushinta yakeji zai yi kokarin sanyata farin ciki dan ya lura her case is critical.
Bayan Sallah Isha Mardiyyah ta taimaka mai yayi shurin sa tsaf cikin kananun kaya daya kara fiddo da azahirin kyau sa, har bakin mota ta rakasa ya fice daga gidan sannan ta koma cikin gida cike da shaukin sanshi.
Kwalliyarta tayi cikin dogowar bakar abaya. Tsakar gidan ta fito rike da empty Ghanar ta tana kakkabewa, Inna dake zaune tayi dariya ganin tabar kukan da takeyi tun safe, jira take Rasheed ya iso taga reaction dinta, gashi kuwa tayi kwalliya abunta tayi kyau, komawa daki Batul tayi tana maida kayanta cikin ghanar sannan ta zuge ta fito rike dashi,
Cike da tsiwa ta tsaya kan Inna "tsohuwa Allah kaddara saduwa, idan jikanki ya dawo ki tabbata ya sakeni, idan ms bai sakeni ba xan dawo dakaina na amshi takarda ta".
Mikewa Inna tayi da azama, tace "Batul ina zaki adaran nan ?
Yake da yafi kuka cuwo tayi, tace "Babu ruwanki, na riga na yake shawarar fita duniya dan cinma burin rayuwata, babu wanda ya isa ya hanani"
Kwantar da murya Inna tayi tace "tabbas ba wanda ya isa ya hanaki, amma dan Allah kiyi hakuri ki tsaya kona minti 20 ne, i promise you won't regret it".
"Sai kiyi ai" Batul ta fada tana hararar Inna, juyawa tayi zata fita, Inna tayi saurin rike Ghanar tanai rokonta karta fita, fir Batul taki hakura ganin Inna zata bata mata lokaci yasa ta saka mata Ghanar ta fice waje tanai tsinewa matsiyacin gidan. Da gudu Inna tabita waje amma ina Batul ta riga ta tsare, gudu kadai take batare data waiwayo ba, Hannu Inna ta aza akanta tana fadin "Batul kinwa kanki, opportunity daya rage maki kikai shuri dashi", haushin kanta sosai Inna tayi, da tasan mai hali bazai canxa ba da bata tsaya lallaba Rasheed ya bata chance ba. Komawa tayi gida ttadau waya ta kira Rasheed, driving yake kan titi, kadan ya rage ya karaso unguwar, daukar wayar yayi Inna ta shaida mai abunda ke faruwa cike da damuwa, kwantar mata da hankali yayi yace zasuyi magana idan ya karaso.
Gudu take harta karaso titi, batama ankara da kokarin tsallaka titin da take ba, sai ganin hasken mota tayi ya kusan to da gudu, cike da kidema tayi baya dan kauce mata amma tuni tayi latti motar sa dage dayan lane dince ta faso aguje, wani mugun burki yaja adaidai lokacin da ta kwalla ihu ta fadi kasa sumammiya.
Hankali tashe yayi parking ya fiso, Addua kadai yake Allah yasa bata ji ciwo wa, karasawa yayi gareta yana haska fuskatar, wazai ganni inba Batula ba, wani mugun tsaki yaja cike da tsanarta, ji yake kaman ya barta gurin yayi tafiyarsa saidai bazai iya ba kodan darajan mahaifin ta.
Daukata yayi yasata bayan mota sannan yaja komawa Gidansa da ita, yana parking farfajiyan Mardiyya ta fito da fara'arta, bude motar yaya ya fito da ita kwance bisa hannunsa, da azama Mardiyyah ta nufesa hankali tashe, magana take bai saurare taba banda saurin da yake yaje ya direta, babbab daki mai shegen kyau ya nufa da ita sannan ya kwantar da ita bisa lausassan gado.
"Sweetie wace wanan" Mardiyya ta fadi arude, dan kuwa ta fisa tsorota, atunanin ta macacciya ce.
"Accident tayi, ki kula da ita" ya fadi ya fice daga dakin, dakinsa ya nufa ya zauna cike da taikici sannan kuma ya kunna karamin Tv dake manna a bangon dakin, Tv ne mai dauke da connection footage na gidan gabadaya, part kusan goma na gidan ya nuna, yasa remote yayi zooming part din dakin da ya kwantar da Batul, jira yake kadai ta farka yaga reaction dinta.
Toilet Mardiyya ta shiga ta dibo ruwa a bowl hade da hand towel sannan ta dawo kusa gareta tahau goge mata fuska inda ya kwarzane, bayan ta gama mikewa tayi ta sauka kasa kiran altine ta hada ruwan zafi a flask.
Bayan mintuna biyu Batul ta farka a gigice, tsorata tayi ganin ta a wagegen daki, zaburewa tayi ta mike tana karewa dakin kallo, ina ne nan kadai take tambaya aranta, tasan dai moto ya kusa bige ta ta fadi daganan kuma sai gata anan, "kodai wanda suka kusa kade tane suka kawo ta" ta fadi aranta.
Tsoro da mamaki ne ya kamata, da sauri ta fice daga dakin, bin tangameme stairs din tayi da kallo tana adduaa neman tsari, atunaninta gidan yankan kai aka kawo ta, dago da idanuwanta tayi taga hadaddudun frames mai dauke da picx din Rmd da Matarsa kusan shida anyi decor dasu ajikin bagon, rike baki tayi kam tamkar wace tayi niyyan ihu, jin motsin zaa hawo yasata rugawa dakin da gudu, kwanciyar tayi tana neman mafita, dan kuwa indai gidan Rmd Allah ya kawota bazata fita ba, mafita kawai take nema, can kuma dabara ta fado mata ta saki murmushi hade da runtse idanunta.
Kallonta Rmd yake ta Tv, saidai baisan dalilin komawar ta cikin dakin da gudu ba.
Murmushin gefen baki yasaki, yasan definitely she is up to somtin, kashewa yayi ya fice zuwa dakin.
Ahankali Mardiyya ta shigo dakin ta karasa kan gadon ta zauna, bude idanu Batul tayi tana lumshe su kaman wace yanxu ta farfado, mikewa tayi zaune tana kallon mardiyya da itama kallonta take.
"Wace ce ke ? Batul ta tambaya tanai mata kallon rashin sani.
Murnushi mardiyya tayi ta matso da ita tana fadin "ya jikin naki ".
Kallon rashin fahimta Batul tayi mata, "banda lafiya ne ?
"sweetie ya kawo ki dazu, wai kin samu accident"
Tsurewa Batul tayi tahau kuka karya, "accident when n how, i cnt remember anything".
Mardiyya sarkin tsoro, tashin hankaline ya bayyana karara a fuskarta, atunanin ko Batul tayi loosing memories dinta.
Rikota tayi tace "baiwar Allah ya sunanki
"Na manta" batul ta fada cikin muryan kuka.
Cike da tausayi Mardiya tace "plz try to remember wace ce ke, koda ma garin da kika fito ne, kiyi kokari ki tuna"
Shuru batul tayi kaman mai tunani can kuma tace "abu daya na iya tunawa
Mardiyya tace "Gayamin "
"Nasan dai ni yar sarki ce, it seems someone is plotting to kill me" karashe maganar tayi tana juya kanta as if she is trying to recall wasu abubuwan.
"Kill you " mardiyya ta fada in shock.
Yes" abunda na sani kenan, kuka sosai Batul ta fashe dashi hade da fadawa kafadar mardiya, lallashin ta Mardiyya tahau yi.
Duk drama da Batul take akan idonsa, basu lura daya shigo ba, gyarar murya yayi duk suka dago suna kallon sa, mikewa Mardiyya tayi ta karasa garesa, tana fadin "mutune abun tsoro, i wonder mai beautiful princess tayi suke son kasheta" cike da tausayi tayi maganar.
Kasa magana yayi tsananin tsanar Batul da yakeji aransa, kallonta yake, aransa yana fadin "she will never change......
[10:00PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: 💖 *INA ZAN GANSHI*💖
Rubutawa
Xarah Bukar
®NWA
xarahbukar.wordpress.com
46 - 50
Amarairece Mardiyya ke kallonsa, ko alamun tankawa bai yi ba, banda kallo Batul da yake fuska murtuke, murya kasa kasa tace "Sweetie bakace komai ba"
Ficewa yayi daga dakin batare dako kanzir ba, Batul dake kallonsa duk taji ba dadi, mugun kallo dayake mata yasa ta kasa sukuni, tsoronta daya kar ya gano karya ta shirga masu.
Daga inda Mardiyya ke tsaya tace "kar ki damo da looks dinsa, he is nyc magana kuma ba kasafai yake ba"
Girgiza kai tayi kaman zata tayi kuka, Mardiyya tacigaba, "ki kwantar da hankali, you're welcome to stay har ranar da xaki tuna masarautar ku"
Nagode",Batul ta fadi cike da tausayin kanta, deep down aranta murna take abun nema yasamo.
Mardiyya bata bar dakin ba saidai ta kira Altine ta kawo mata komai na bukata sannan tai mata sai da safe ta fice. Dadi sosai Batul taji mikewa tayi tsaye tana tikar rawar murna.
Toilet ya shiga ya sakan wa kansan shawa, mafita kadai yake nema ya rasa, duk hanyar da yabi Batul ce zataci riba, idan ya fito ya bayyana mata kansa gaba takai ta, idan kuma ya sake ta still taci rabi wani guri zata je tacigaba a inda ta tsaya, shawara daya ya yake danci galabarta at her own game.
Karfe takwas na safiya Batul ta farka daga bacci, agurguje ta shiga bayi ta dauro alwawa tayi Sallar asuba, aranta tana jinjina lausassan gado da Sanyi Ac dakin, da wayota bata taba missing sallah asuba sai yau, istigifari tayi ta koma gadon taci gaba da baccin ta, sai kusan goma ta tashi.
Shigowa dakin Altine tayi da nikiniki kayan ta ajiye cikin wardrode sannan ta gaidata tace mata kayan sawane Aunty ta aiko akawo mata.
"Okay" kadai Batul tace cikin nuna rashin damuwa akansu, bayan Altine ta fita mikewa tayi ta ciro kayan tana kallo, kayane yan kanti masu matukar kyau da tsada, tsalle tayi tana taka rawar "if" na mawaki Davido.
Wanka ta shiga da axama ta fito ta shirya cikin riga da skirt na kanti daya amshi jikinta sannan tayi zaman tsantsara kwaliya, bayan ta gama, fitowa tayi sukayi kicibis da Mardiyya zata shigowa, murmushi tayi tace
Princess kin tashi"
"Eh" Batul ta fada tana kallon yadda mardiyya tasha kyau, kamar mai zuwa buki, duk saita rena nata.
Hannunta Mardy ta riko tace muje muyi breakfast, tsum tsum tabita tanai karewa gidan kallon in a Stylish way gudun kar su gano bata saba ganin hadaddn gida haka ba.
Dinning suka nufa taja mata kujera ta zauna sanna tace "minti daya barin dauko Sweetie" da sauri ta haura sama.
Haushi ne ya kama Batul ganin yadda Mardiyya ke wani rawan kai da Rmd, banda feleki miye saikin dauko sa" ta fadi aranta, shataf ta manta da wani mijinta Mamuda sai yanxu ta tuna shi, tsaki taja tanai kallon abinci dake jire gurin, karaf idonta yakai kan roasted chiken dake gurin, wani mugun yawu ta hadiya, Jira kadai take suzo afara.
Tsaye ta iske sa yana button din shirt dinsa, temaka masa tayi sanna suka fito tare saukowa, kallo daya Batul tayi masu ta dauke kai, wani irin xafi zuciyar ta ke mata, bata rai tayi ta daura kafa daya kan daya, karasowa sukayi Dinning din ya janyewo Mardiyya kujera ta zaunna sannan ya zauna gefenta, kallon batul yayi bata da niyyan gaidasa saima daure fuska da tayi, murumshi ya saki dan bakaramin kyau tamai ba, yace
"Good morning Princess"
Kaman jira take, princess daya kirata dashi yay mata dadi, wato shima ya yadda kenan, murmushi ta saki tace "morning My prince"
Atare Marfldiyya dashi suka ware idanu suna kallanta,.
Murmushi ta saki irin ta yan duniyan nan tayi tace "kuna yana yi dashi, dou i cnt recall his face, shi yaka mata na aure, datx y am trying so hard na tuna shi, i love him alot am sure shima yana can yana nemana".
Ran mardiyya yadan sosu, kasa boye kishinta tayi, haushi taji yadda Batul tace prince dinta na kama da mijinta, hannunta Rasheed ya riko, cikim murya kasa kasa yace "we have to support her idan har munaso tayi regaining memories dinta, plz be strong and trust me"
Kai ta girgiza alamar ta yadda da xancen sa, tana son Rasheed shiyasa kome ya fada mata take naam dashi, farin cikinsa shine nata.
Basu tanka Batul ba, suka fara cin abuncin bayan Mardiyya ta zubawa kowa a filet, sultan chips ne da roasted chicken sai tea hade a kowane cup, Satar kallom su Batul take tana ganin yadda sukecin abunci cike da yauki, jifa jifa kuma Rasheed ya saki Murmushi, ko tari babu maiyi cikin su tsananin yadda suke bawa table manners dinsa,
kasacin kazar Batul tayi saboda fork da table knife da taga suna ci dashi, gashi ba daman tasa hannu class dinta ya zube, daurewa tayi ta rike fork da wukan ahannu daya, kazar tayita cacakawa ta kasa dauka, mazewa kawai tayi ta ajiye fork din tadau tea din tana sha.
Duk a idon Rasheed, dariya ne kadai baiba ya dake, kadan kadai yaci a abinci ya mike tsaya ya karasa gurinta, "Princess har kin koshi ? Ya fadi yana murmushi
Yatsine fuska tayi tace "i dont eat much"
Fork din ya dauka yace "plz kici, baa zaman yunwa agidana" hannuta ya rike yasa mata fork din.
Wani irin yir Batul taji da hanusu suka game guri daya wani irin yanayi ta shiga da ita kanta bata gane ba, "tnx my Prince" ta fadi hade da kirkiro murmushin dole, gabanta sai faduwa yake, zuciyar na tuna mata tana da miji.
Barin Palon Rasheed yayi yahaura sama, Mardiyya ta mike ta maramai baya.
Tsulum