Showing 9001 words to 12000 words out of 48742 words

Chapter 4 - INA ZAN GANSHI Complete Book By Xahra Bukar.txt

14 Jan 2025

2386


Bayan sun fito wani mugun sanyi jikin sa yayi, wani abun mamaki shine yadda Baba bai tambaye sa akasari suna daya bambamta ba, sai mai cema dayayi "Mamuda aure zaman hakuri ne, dan Allah banda niba kayi hakuri da yarinyan nan"
"Insha Allah" kadai ya iya furta mai, Babu wanda yace uffan cikinsu har suka karasa gida, ta bangaran Baba bai kawo komai aransa ba game da sunan, aganinsa Mamuda da ake kiransa dashi lakabine na gidansu.
Tsaye yayi waje Baba ya shigo gidan, turus yayi ganin Batula tsaye bakin kofar dakin hajjo da kodadan kayan jikinta, atunanin sa batayi wanka ba.
"dauko kayanki muje" Baba ya fadi.
Turo baki tayi "babu inda zani.." bata rufe baki ba taji saukar wayan rediyon bayanta, "wuce dan ubanki ki dauko kayanki" Hajjo tace tana shirin kara lafta mata.
Kaman zatayi kuka tace "banyi wanki ba, duk sunyi datti"
"Haka kuwa zaki kwashe su, idan kinje can kya wanke abunki"
K'in motsawa Batul tayi, saida taga Hajjo dagaske take sannan ta ruga daki tana kuka, kayanta dake cikin tsohuwar ghana must go ta daukA ta fito, hannu Baba yasa ya karbe suka fice waje Hajjo na mata fatan zaman lafiya.
Kuka sosai Batul take bata gama girgiza ba saida taga Baba ya jefa ganar cikin Napep ga kuma Mamuda agaba yana shirin ja, harara ta watsa ma cike da tsana, cikin muryar kuka tace "Baba babu mota ne ?
"Kedai shiga muje" baba ya fadi.
Rai bace ta shiga, sannan ya shiga ya zauna kusa da d
Ita. Kuka take ba k'agauta, ba auran miji ne ke b'ata mata rai ba sai cikin keke da za'a kaita, wato ma mijin matsiyaci ne, uwa uba yadda tayi planing ma kanta big wedding shine Baba da Hajjo suka k'askantar da ita, irin su Dinner, mother's eve, fulani day event dayawa datasa buri sun wuce ta, honeymoon da ake fita waje duk bazata samu ba, Allah ya isa kawai take ma dan iskan daya amshi Sadaqan ta kuma tadau alwashin ko waye sai yayi dana sanin amsarta.


Tudun wada layin yan kosai ne unguwar da Rasheed yayi parking Marwan, nan take ta kara fashewa da kuka da ganin gidan, tasan su talakawa ne, gidansu da take rainawa yafi wanan fasali nesa ba kusa ba, karamin gidane wanda rabinsa da salansa mai tsatsa aka kewaye shi, unguwar ma gabadaya ba fasali irin ghetto area ne da gwamnati batasan da zamansa ba.


Nasiha sosai Baba yayi mata sannan suka fito ya taka mata zuwa bakin kofa, yace "ki shiga kakarsa na ciki" acewar Baba.
Jiki sanyaye ta cusa kai ciki tana waigowa kallon Baba, ran Rasheed adakule yake amma saida ya dara, nikaina xarah saida na dara (hhhh), Marwan Baba ya koma rasheed yaja maida sa gida.


Tsohuwar tagani zaune tana carafke adan karamin tsakar gida dako mutum 5 ya masu kadan su tsaya cikin sa, dukuna biyu ne kananu da bayi dake lungu tsakar gidan an kewaye shi da kwano, hannu Batul ta aza akai tana ihun ta shiga uku ta lalace, sai sannan tsohuwa mai Suna Inna kulu ta lura da ita, mikewa tsaye tayi tana guda "amarya ta iso yiririiii" karasawa kusa Batul tayi zata rikota, da azam Batul tayi baya tanai mata wani mugun kallo, "karki kuskura ki tabani"
Galala Inna kulu tayi tana kallonta, "kaji ja'ira miye aciki danta tabaki, jikana fa kike aure"
Harara takai mata, "jikanki ko matsiyaci, jifa gidan da kuke kaman akurkin kaji"
Bata ankara ba sai gab taji abakinta, Inna kulu ta buga mata dutse, hannu takai gurin taga jinin, kafin tayi magana Inna ta cafke kunnata, "bamu da tsiya agidan nan, bamu ganta ba bamu santa ba kina jina ? Kara damke kunnan tayi.
"Eh naji" Batul ta fadi cikin kagara, sakin kunna tayi, bata jira komai ba ta fada dayan daga cikin dakunan tana kuka, wayam dakin yake ko yar katifa babu sai tabarma a shumfud'e, ajiye Ghanar tayi bisa tabarmar ta kwanta tayi filo dashi, kuka kadai take daga bisani Bacci yayi awan gaba da ita, bayan Magrib ta walka kasancewa hutun Sallah take, jiki mace ta mike ta leko tsakar gidan, Inna tagani zaune tana can carbi, tsaki taja tace "tsohuwa yunwa nake ji"
Banxa da ita Inna tayi saida ta kare hade da shafa addua sannan ta kalle tace, "ba abinci agidan, saidai kici kanki".
Gyara tsayuwa Batul tayi, "Aikuwa saidai ku nemo, dan ban iya xaman yunwa ba, Hakkina ne jikanki ya ciyar ni" cike da tsiwa take magana.
Murmushin dabai kai zuci ba Inna kulu ta saki sannan tace "lailai kin tabbata matar Sadak'a, daga zuwa yau sai nema hakki, anya kina barinsa ya runtsa yau ?
Salamar sace ta hana Batul kai mata amsa, amsawa Inna tayi ya karaso ciki rike da bakar leda da kullin kaya.
kallon sa Batul tayi tace "nagodewa Allah, nasan Baba bazai barni agidan nan ba, bara nadauko kayana" ta fada hade da komawa cikin dakin da saurinta.
Kallon juna sukayi da Inna alamun ina xancen ta ya daso.
Ghanar ta dauko ta fito tana fadin "akurkin nan ba gidan zamana bane"
Kallonta kawai yake bashi da niyya motsawa, tace "Mamuda muje mana kar dare yayi,"
Zama yayi jikin wata rashe dake guri, yace "Muje ina ?
"Gida mana" ta fadi tanai mai kallon banza, duk atunanin ta Baba ya aiko a maida ta gida.
Cikin ko in kula da yanayinta yace, "kin taba ganin inda amarya ta koma gidansu bayan an kaita ?
Takaici ne ya cika, so take kadai subar gidan kafin jikin Inna ya dawo.
Inna kam ta gama kulewa da ita, tace "miye kake boye mata, kaine Mijin nata ba kowa ba, idan bata shima albarka ba ai bata zage kaba, in banda kai ma waxai amshi Sadawar ta"
Ware idanu Batula tayi jin kalaman Inna, saidai ta kasa gasgata shin mafarki take ko gaske, yama zaai ta auri Mamuda, mai yake dashi, waye ubansan, murya Inna data ciyo tana fadin mijinki ne yasa ta zabura hade da wurgi da Ghanar, ihu take tana nema agashi dan kuwa mutuwar tace kadai xai fiye mata akan taga mumunar rana irin tayau, kuka take tana fadin "Allah ya sauwake na zauna dakai, banza matsiyaci, talaka, bakauye, kashe kaina xanyi akan na zauna dakai" sambatun take kaman sabuwar mahaukaciya, kallonta kawai suke, zuciya Rasheed kaman ta fito dan haushi, kalamanta ba karamin zafi sukai ma, inda da gaske zata kashe kanta dayafi kowa farin ciki.
Iya k'ulewa Inna takai, gaftareran wuka dake bisa tagar dakinta ta dauko, ta cilla daidai inda kafar Batul, atsorace taja baya dan kiris ya rage bata kwaye mata fata ba.
"dan uwarki dau wukar ki kashe kanki, shegiyar yarinya, kin dauka muma sonki muke, kina mutuwa bamu da asara, keko uwarki da ubanki basu da asara, yar banxa tantiriya, gwara ki mutu mu huta" Inna ta fada cikin daga murya da tsananin bacin rai.
Cikin karaji Batul tadau wukar kamar zata cakawa kanta, ganin ko ajikinsu yasata cefar da wukar, tabbas basu da asara idan ta kashe kanta balle ma wana hauka yakai ta kashe kanta tun burinta bai cika ba, danne zuciya kadai zatayi ta zauna kafin kwana biyu ta san inda dare yayi mata.
Tsaki taja tadau ghanar ta koma daki, mikewa yayi yama Inna ido sannan yabita zuwa dakin, jikin bango ta rakube tana sauke ajiyar xuciya, ko fitila babu dakin sai hasken farin wata daya gauraye ta waje, ganinsa da tayi yasa ta mike tsaya hade da kaimai kallon banxa, ledar ya mika mata "ga abinci kici"
Ba kunya ta amsa, ya fice. zama tayi bata lura da kullin kayansa daya ajiye ba, bude ledar tayi taga
Kosai biyar da guntun biredi, tsaki taja, aranta tanai karajin tsanar Mamuda, in banda tsiya ko yar kazar amarye bai iya siya ba (ni xarah nace idan ya baki kaza, ke kuma ki bashi miye ). yunwar da takeji yasata cusawa dan dole.


Hira da dariyar Inna da Rasheed keyi, tana jiyo dariyar su amma bata tantance mai suke fada ba, tashi tayi ta sakawa kofar sakata sanna ta koma tayi kwanciyar ta. Mikewa yayi ya kwakwaso yace ta bude, tayi banxa tayi dashi, saida yace ta miko mai hula cikin kayansa sannan ta lura dasu, dauka tayi ta bude kofar bata mika mai ba tayi cille dasu waje hade da rufo dakin da sakata.
Bai damu ba, dan kuwa da gangan ya ijiyesu, tsince su yayi yakai dayan Dakin da Inna take ya ajiye sannan yay mata sai da safe yabar gidan.










TeamMardiyyah ❤
[10:00PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: 💖 *INA ZAN GANSHI*💖
Rubutawa
Xarah Bukar


®NWA


21 - 25


Daidai inda rumfar Baba ya tsaya duk suka sauko yahau agazamai sauk'e kwandon. Batul kuwa bata jira komai ba tayi gaba da azama.
"ke yazaki gudu baki bani kudi ba ? Mamuda ya fadi ayayinda yake kokarin dire kwando hannunsa, bata juyowa ba balle ta tanka banda saurin da takeyi, nisawa Baba yayi yace "ya'ta ce, zan biya gabadaya"
Sunne kai yayi, kunya Baba yaji ya lulub'esa, inda ya biyemata yaukam da girma ya fad'i, taimakon Baba yayi da wanke tumatir sannan ya tayasa kaso, albarka sosai baba ya shimai, dukda ba wata doguwar hira sukayi ba amma tsohon ya kwanta mai arai, yana shirin tafiya Husaini ya k'araso gurin ya gaida sa aladabce, ciro dari takwas Baba yayi ya mikamai, fir yaki karba, ba yadda baba baiyi ba, ganin yaki karban halal dinsa yasa baba yace Husaini ya kaisa gida yaci abinci kanan ya wuce, dukda Mamuda baiso hakan ba amma wata xuciyar ta tursasa mai son xuwa gidan.
Hassan tsaye gindin rijiyawa yana wanki, sai yusuf dake zaune daga gefe yana homework, Hajjo ta fita mak'ota barkan haihuwa, Sallama sukayi Hassan ya amsa suka karaso ciki ya gaida shi, "Batula fito ki sawa bak'on Baba abinci" Husaini ya fada daidai tsetin dakin, kayan jikinta take ragewa tasanya wani kod'adda tshirt da zani, tana jinsa tayi banza banda kokarin bude ostrich ledan ta da take, sake maimatawa yayi sannan ta amsa mai, "Batula yafita daga bakinka kafin na fito na wanke ka da mari"
"Tofah, Manya na magana" Hassan ya fada yana dariya, harara Husaini yakaima, ya kalli Mamuda yace kayi hakuri bara na zubo ma" tabarma ya shimfada mai sanan ya zubomai dambun hatsi da Hajjo tayi, murmushi Mamuda yayi hade damai godiya yahau cin abinci da tunda uwarsa ta haifesa bai taba gamo dashi ba, haka dai ya daure yana cusawa.


Fitowa tayi daga dakin rike da ledar tana shewa, batama lura dashi ba tadau kujerar tsugunno ta zauna tsakaiyar gidan, "yehoo ku fito yau party zamu.." Ido hudu sukayi ta kasa ida maganar, sai kuma ta dauke kai kaman bata sanshi ba gudun kar yayi mata magana su Hassan su dauka ko saurayinta na.
"Party nami" Hassan ya tambaya.
Ta gefe ido ta kalli Mamuda sanna tace "kayan dadi sabon saurayi na ya tsiya min, idan kunaso na baku zakamin wanki, shi kuma husaini yamin guga, auta kuma ya gogemin takalmi" ta karashe maganar tana kallo yusuf da tuni yawu ya tsinke mai, atake Hassan ya yadda ta mika mai burger ya karba yana santi, yusuf kuma ice cream aka bashi banda husaini daya hada rai bayaso.
Hassan yace "wai waye saurayin nan naki, yana zuwa nan ?
Fari tayi da ido, "mai kudi ne ba lailai ne kasan shiba, kana jin labari wani Rmd, most influential family a garin nan"
Yace "gaskia bansan shiba, halan shi ne saurayin naki ?
"Eh fah shine, very soon xai turo gaiswa".
Wage baki Hassan yayi yana kallonta, yasanta sarai da karya amma wanan kam ya wuce tunaninsa, kwashewa yayi da dariya yace " uwaka karya, ubanka karya, Batula kinayi ina jin dadi kina bari ina jin haushi, ina mai kudi ina talaka irinki, dan Allah ki rage ta gobe"
Kowa gurin saida ya kwashe da dariyar abunda Hassan yace, Mamuda kam harda rike ciki yana darawa, yarinya ga kyau amma ba kyau halin, saidai yadda take karya in a classy way ke kara bashi dariya.
Akule ta mike tsaye, "banxaye sai kuyi tayi dai, yan bakin ciki" fuu ta wuce daki da kunin rai, tana jiyosu suna kara darawa.
Mikewa mamuda yayi yamasu sallama ya fice dan kuwa idan ya xauna yana iya amayo kayan cikinsa, gurin baba ya nufa yamai godiya samlnna ya wuce.




****
A firgice ta farka tana karewa dankareran palon kallo, hamdala tayi da Allah yasa mafarki tayi ba dagaske bane da yau hankalin ta tashi xaiyi idan
My boy ya gano akwai boyayyan al'amari da take boye mai sama da shekaru talatin. Altine ta kwalla wa kira ta kawo mata fresh milk tasha ta shingide cikin kujerar tana kokarin kawar da rayuwar past dinta dake neman dawo mata sabon fill ababin rayuwarta na yanxu.
Sallama sa ce ta katse mata tunani, ta amsa cikin boye damuwar ta, karaso wa yayi kusa gareta, "Mom are you alright, naga your face is pale"
Murmushin dabai kai zuci ba ta sakar mai, "am, good, ya yau din ?
"Lapia kalau, i really enjoy it" ya fadi yana murmushi, itama murmusawa tayi cike dajin dadin ganinsa cikin farin ciki, bisa cinyarta ya ajiye kansa tasa hannu tana kwantar mai da lausasan gashin kansa, tace "Abdulrasheed yau kasani farin ciki, alway b happy kaji?
"I'll Mom" ya fadi yana kara fadada fara'arshi. Wayarsa ya laluba aljihu ya ciro yayi daillng no din Mardiyya, zaune take tsakiyar gadonta Tana tofa addu'ar bacci taga call dinsa, tsoro da mamakine ya kamata by diz tym ace ya kirata, jiki sanyaye ta dauka, tayi shuru.
Murya kasa kasa
Yace "Mardiyya hope dai ban tashe kiba ?
Dadi taji yadda ya kwantar da murya tace, "banyi bacci ba, ya daran ?
"Cool'
Shuru tayi tana juyo heart beat dinsa, nisawa yayi yace "mi kika dauka a office dina ?
Gabanta ne ya fadi itakam bata dau komai ba banda daya daga cikim hanky dinsa data zara amma kuma bata san inda ta ajiye ba, tace "ban dauki komai ba"
"Are you sure ?
Tsoron Allah ne ya shigeta, karya itace abunda bata iyaba, "am sorry Mr rasheed na dauki hanky dinka without ur consent"
Ajiya zuciya ya sauke, "ina hanky din yake"
Cikin rawar murya kaman zatayi kuka tace "i lost it"
Abinda yake sonji kenan, katse call din yayi, aransa yana tunatin where on earth ita kuma wacan tasamu hanky dinsa, Mom ce ta katse mai tunani da cewa "my boy nasan kana santa, ka aureta i promise you won't regret it"
Kallon rashin fahimta ya daga kai yay mata, tace "dont be silly, who else idan ba Mardiyya ba"
Yake kawai yayi ya maida kansa, zuciyar na bijiromai abubuwa da dama.


****
Yau da wuri taje lec ta dawo kasancewar ruwa da akayi ta makawa yasanya yawanci lecturers basu zoba, tana ganinsa tare da Baba akaramin zauren gidan ta bata fuska, shishigin yafara isarta tun ranar daya sauke su akullum sai yaje teburin Baba hira, yanxu kam tamkar yaron baba haka ya zama duk wani aike da dauko kayan miya gurin tsari shi Baba ke aika, takai ma yanxu sun saba da Hajjo, har wani kwanan abincin daban take ajiye mai.
Baba sannu" ta fadi cikin hade rai, dama akulle ta dawo da haushi Billy yau data tsitsaye ta akan deceiving dinsu take, fada sosai sukayi saida Minal tasa bakin akan lailai gobe saita kaisu gidan su cousin dinta Rmd, karfin hali kawai tayi ta amsa masu da naam, ranta duk ajagule ta rasa mafita.


Kallon ta Baba yayi, yanayinta ya nuna ba lapia ba, yace "fatima mike damunki ?
Kuka ta fashe dashi "Baba nikam na gaji da talaunci nan, wai yaushe zakayi kudine, miyasa ma na fado cikin zuria ka" sosai tafashe da mugun kuka, kollanta Baba kadai yayi yana murmushi bayau mace tasaba cin zarafin saba, saidai kalaman fatima ba karamin fama mai ciwo daya dade da samun waraka azuciyar saba.
Ran mamuda kam ya gama bacci hannu ya daga da niyyan sharara mata mari, baba yarike hannusa "dukan mace bai kamace kama, karka kuskura" Acewar Baba.
Harara Batul ta kaimai ta ruga gida aguje, baba ya rike hannusa suka fice zuciyarsa na tafarfasa.


Gam Hajjo ta capke ta data shigo, dan kuwa duk abunda tace taji ta, kaman an aikota tahau Batul da dukam tsiya, banda ihu da kuka ba abunda take,
"Kafin ki kashe ubanki ni xam kashe ki" hajjo ke fadi cikin kunin rai tana mai kara kai mata naushi, saida tayi mata lillis sanan ta barta tana fadin "yar banxa yarinya, kasheki xanyi na huta da bakin cikin ki, nagode wa Allah daya azurtani da kannanki dayau kin kasheni abanza"
Kuka sosai Batul take, tana jawa bawan Allah mamuda Allah ya isa, aganinta tunda yaxo hajjo ke kirbanta, dan kuwa rannan abinci taki zubamai hajjo ta mata lilis yauma ba, wani mugun tsanan shi take ji aranta, ayyada zuciyarta ke tafasa inda zataga Rmd binshi kawai zatayi tabar masu gidan, dan kuwa shine kadai gatan ta yanxu.
"Oh ni fatima ina Xan Ganshi,.." Ta karasa magana cikin matsananci kuka, atunanin ta a zuciya ta fadi not knowing afili tafada, jim muryar Hajjo tayi akanta rike da ludayin miya, tana cewa , idan na fasa maki baki zaki ganshi da kyau"
Ba shiri ta mike da azama tayi cikin bayi da gudu tana kuka.
[10:00PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: 💖 *INA ZAN GANSHI*💖
Rubutawa
Xarah Bukar


®NWA


xarahbukar.wordpress.com

36 - 40


K'ashe gari da k'arfinta ta tashi, fuskar ta dauke da murmushi dan kuwa tayi alwashin daina zubda tsad'addan hawayen ta kan matsiyacin nan, ranar kin dillanci kadai take jira.
Kayan jinkinta ta cire ta dauro zanin wanka ta fito tsakar gidan, bayin ta leka taga babu ruwan balle famfo sai bukitin k"arfe marar hannu dake ajiye, tsaki taja aranta tanai tir da talauci, kofar Inna kulu ta nufa ta tsaya, babu ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login