Showing 48001 words to 48742 words out of 48742 words
Chapter 17 - INA ZAN GANSHI Complete Book By Xahra Bukar.txt
bata da lapia ba, baka gani weird symptom game da ita" acewar Alhaji Bello.
"Ina gani, saidai symptoms din are not specific to renal failure, they can occur in other disease, kaman ni at first nadauka she was pregnant, amma dana lura da she is always confused yasa nafara tunanin ko tana da mental dis order"
Nisawa Alhaji yayi yace "dole naje Ghana gobe na bincike komai, i just cant belive Safara ta siyar da kidney din only dauta dita, for wat reason, anawa ta siyar, abunda kadai nakeson sani"
Sun jima suna magana, daga bisani Rmd ya yanke shawara suje Ghanan tare, kasancewar sunan wanda ya siyi kidney din na jikin takardar.
Washegari kuwa hakan akayi, suka dira a ghana batare da wata wahala ba suka samu gidan hamshakin mai kudi Alhaji Tafida charno, tarba mai kyau yayi masu, nan suka fadi mai abunda ke tafe dasu, sosai yayi mamaki dan kuwa ya jima yana neman Hajiya Safara, tun ranar daya biyata 25 million tayi donating ma yarsa Kidney din mardiyya bai kara ganinta ba, asalima tun kafin agamawa Mardiyya treatment ta dauke ta suka gudu, bai kuma jin labarin taba, nan ya kwashe komai ya fadi masu,
Kuka sosai alhaji da rmd keyi cike da tausayi, haka suka dawo nigeria, cike da baccin rai Alhaji bello ya saki Hajiya safara bayan ya hadata da hukuma, nan take kuma ya yanke hukuncin auren yar aikinta Biebee dee.
Kuka sosai Mom tayi da taji labarin abunda ya faru, sai yanxu ta tabbatar Safara makira ce ta karshe da tsananin son abun duniya, nan tahau bawa Rmd labarin ta da Baba. Tun asali ba sonshi take ba Babanta ya hadasu aure sakamakon yadda ta rena mutune da kin sanin darajan dan adam shiyasa babanta ya aura mata shi ko zatai hankali, rashin mutumci iri iri tayi ta shukamai bai taba damuwa har ta haifi rasheed, yana shekaru biyar a duniya babanta ya rasu yabarwa Baba rabin dukiyar sa sauran kuma yabaiwa kawu Habibu, kadan daya rage Babanta ya bata duk dan ta iya zaman duniya tasan kuma ba kudi ne komai ba, rana d'aya Hajiya Safara tazo ta zugeta tsaf akan lailai karta yadda, alokacin kuwa Bataji maganan kowa saita hajiya Safara, ba kunya ta amshe dukiyar daga hannu Baba sannan ta rubu dashi ta komo zaman kaduna duk dan abun duniya..
Kuka sosai Mom tayi, haka suka shirya duk sun ukun sukazo tayata baiwa Baba hakuri, cikin rashin damuwa ya nuna shi daman bai taba riketa azuciya ba, kuma dama yayi alkawarin sakinta duk ranar data sududa, nan take ya rubuta mata saki daya, kuka sosai tayi cikin rashin dadin abunda yayi, batai kasa a gwiwa ba, ta kwaso duka takardun dukiyar Babanta ta bashi tunda dama nashine, fir yaki karba, ya godewa Allah daya bashi rufin asirin saida kayan miya.
Bai karba ba ganin ta nace yasa ya karba ya mikawa Rmd hade da cemai ya basa kyauta halak malak, kin karba yayi saida yaga lailai ran Baba ya baci sanan ya amsa.
Life Goes on, kwanaki, watanni sun ja harma da shekaru.....
Mom an sadudu kullum cikin neman gafarar Ubangiji, da rokonsa Baba ya maida ta dakin ta.
Baba kam kasuwa ta bunkasa, shago babba ya bude na siyar da buhun kayan miya, koda wasa arzikin dansa bai tsone mai idano ba, kokari kadai yake ya samu na kanshi, dukda Rmd yaso yabar sanar fir yaki bari.
Rmd da Batul soyayya sai wanda ya karu, tuni suka koma zaman Abuj, zama cikin tsananin kwanciyar hankali da so da kaunar juna. tsaya fadin soyayyar su bata lokacine (Ramadan by the corner), zama mai dadi suke har Allah yasa ta samu ciki ta haifi yarta kyakyawa, taci sunan Mardiyya, sunai kiranta da BabynDiyyah.
*Alhamdulilah*
Godiya ta tabbata ga Allah daya bani ikon kammala littafin nan, kura kuran dake ciki Allah ya yafe mata.
Gaisuwa musammam ga yayar Mu *Aunty Maijidda Musa*Allah yasa ki gama da duniya lafiya.
My Die hard Fan *Hafsat Sani Maihula* Allah ya barmu tare.
*Na Sadaukar da Littafin nan ga Kawata, Diyata, Yar'uwata Nana Hafsat Xoxo, Allah ya barmu tare, You are such a Darling, ILYSMβ€β€β€β€*
My people i no forget Una...
Baby Nurse & her crew....π€Έββπ€Έββπ€Έββπ€Έββπ€Έββπ€Έββ
*Happy Sallah In Advance to all my fan*πππ