Showing 6001 words to 9000 words out of 48742 words

Chapter 3 - INA ZAN GANSHI Complete Book By Xahra Bukar.txt

14 Jan 2025

2394

kusan minti 20 da tafiyar su. Allah Allah take kadai taje gida tama su Hassan kwalelen ice cream.
Cikin sa'a kuwa tasamu Marwan daya ajiye wasu tayi azama shiga tun kafin ma tahau ciniki, tasan idan ta tsaya ciniki saita kai dare babu wanda ya dauke ta.
"Yammata drop ne ? Taji muryar sa tamkar saukar aradu a kunnuwanta, shi kansan baisan itace ta fado mai cikin Marwan ba.
Dogon tsakin dataja yasa shi kyallero fuskan ta ta mirrro, ba shiri kuwa ya tsayar da niyyar taryarwa, batare da yace uffan ba ya tsaya jiran saukar ta.
Ganin ice cream dinta xai narke kafin taje gida yasa ta sausata murya , "eh drop ne muje ko nawane xan baka, kudi ba matsala bane"
Hmm" yayi yaja Marwan suka kaman hanya da niyyan yimata rashin mutunci indai bata mai biya mai tsoka ba.
Wayarta ce tayi ringing, Dubawa tayi taga Minal ce, guntin tsaki taja gashi wayarta saida speaker akeji, idan kuma tace xata dauka zataji iskar hanya. Tsinkewa call din yayi ta kuma ringing.
"dan Marwa dan tsaya xan amsa kira"
Baice komai bw yayi parking daga gefe, kallonta yayi ta mirriro sai wani yatsine take sannan tadau call din.
"Fatima kin wuce ne ? Minal ta fadi daga dayan bangaran.
Cike da iyayi tace "eh, kuna tafiya Daddy yaxo dauka ta, ina cikin Jeep dinsa yanxu"
"Eyya Daddy ya dawo kenan?
Rike baki Batul tayi shataf ta manta tace masu yana paris, mazewa tayi tace "yau yadawo, daga Airport yaxo dauka na"
"Okay, ina gaida shi, sai mun hadu gobe"
Bye" ta katse wayar hade da sauke ajiyar zuciya, Mamuda kam ya gama tsorota da yarinya mai babban suna, karya kiri kiri ba kunya balle tsoro Allah, gashi kuma ko ajikinta, bai gama mamaki ba saida yake ta ciro farin hanky daga jakarta tana shakar kamshi jiki hade da zuba murmushi. Idanuwa kawai ya zuba mata.
"Malam karka cinye ni man, ja muje" ta fadi tana harara sa, sai sannan ya dawo hayyacin sa, yakama kan kekensa sukayi gaba.
Baba ke tsaye baki titi da tulin tumatur da tarugu a kwando yafi mintuna 30 tsaye, akalla Marwa kusan bakwai sun wuce ba wanda ya kallesa yawanci dama basu fiya daukan masu kayan miyan ba acewarsu kar Marwan su yayi datti, hango Marwan da yayi yana tohowa yasashi adduaa Allah yasa ya daukesa.
"yammata saidai kiyi hakuri, ga wani tsoho can dole na daukesa" Mamuda ya fadi
"Bangane ba, drop fah na dauka kuma kudi xan baka ba kyauta ba.
"Nasani karki manta kudi naki ne, amma Marwan nawane, kina iya sauka kibin rabin kudina"
Tsaki taja, "matsiyaci dai baiji dadi rayuwa ba"
Bai tanka ba, ya tsaya daidai ina Baba ke tsaye, ya fito yana "sannu Baba" hade da daukar gwandan tarugu yasa kan sit kusa da ita, afusace ta fito daga Marwan tana fadin "waikai wane irin wawane, zaka batamin jiki da taruugu..." Makoshinta xancen ya makale, ganin Baba agefe yana kallonta, "baba ina wuni" ta fadi tana yak'e.
Ciki ya amsa fuska daure inda gayamai akai bazai yadda yar cikinsa ke zubar da kimar ta hakaba, Mamuda kam bai kawo komai aransaba atunaninsa kawai ta gaida Baba ne amatsayin girmama babba.
"Baba muje" ya fadi bayan ya saka dayan kwando, su biyu da Baba agaba, sai Batul abaya da ta rukub'e, tsoronta daya kar Baba ya mata fada gaban matsiyacin nan.
[10:00PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: 💖 *INA ZAN GANSHI*💖
Rubutawa
Xarah Bukar


®NWA


xarahbukar.wordpress.com


26 - 30


K'ashe gari bataje makaranta ba, fuskarta gabad'aya kumbure tsabar kuka, tana jiyo Hajjo da k'annan ta a tsakar gida suna hira taki fitowa, ga uban yunwa da takeji tun abinci jiya bata latsawa bakinta komai ba har ila yau da sakaliya tayi. Wayarta dake kashe ta kunna ta kira wani saurayinta shehu da tuni ta dade da jefasa a k'wandon shara, matashi ne irin masu son aci duniya, Baban sa mai kudi ne sosai, yana son Batul saidai son jiki irin nasa yasa Batul bata son basa fuska, bugu daya ya dauka tamkar jira yake, kirarin daya saba mata yafara tuni ta dagatar dashi, tacemai lailai yaxo bayan magrib akwai muhimmaciyar magana da takeson yi dashi, sannan kuma wen coming yaxo mata kayan dadi, naam yayi da bukatun ta cike da jin dadin kota sauya shawara game dashi.
Kaste wayan tayi taja jiki zuwa bangon dakin ta shingid'e.
Baba ke zaune daga gefen teburin kayan miyansa yana alwala, Mamuda ya karaso da Marwan sa ya faka gefe ya fito suka kara gaisawa da Baba, bai jima da bari gurin ba. dayar butar dake cike da ruwa ya janyo yayi alwara sannan suka mike zuwa masallaci dake gaba dasu kadan.
Sadaf ta fito daga dakin rike da siliwas dinta a hannu, Hajjo ke sallah tsarkar gidan, ta tako ahankali ta bayanta tayi waje da azama, ajiyar zuciya ta sauke ganin babu kowa rumfar Baba, waigawa tayi ba alamun motar Shehu sai ganinsa tayi da kafarsa yana tunkaro ta hannusa rike da bakar leda.
"Miye haka zaka zomin da kafa, ina motar" ta fadi tana karasawa garesa.
Dariya yayi.
"Popcy na yanani daukan mota saboda reckless driving danakeyi, mashin ma naso zuwa dashi"
Harara takai mai, "Allah kiyaye kazo gurina da mashin, ai aji down kenan, yanzu dai miye a ledar ?
Daf da ita ya matso, yanai kai mata wani shu'umin kallo, yace "Tukun nadai, , nifa duk kin hargitsa min kwakwalla, wace magana zaki gayamin ?
Ja da baya tayi kadan tanai mai kallon bansan haka sannan tace "Shehu temako zakamin, gobe xan kawo frnds dina gidanku su kanga amatsayin wani cousin dina"
Kallon rashin fahimta yayi mata, waye cousin dinki, ya sunan shi
"I dont know, nasan dai Rmd ake cemai, i want you to act like him idan mukazo"
Galala yake kallon ta, baiyi mamaki abunda takeso yayi ba, dan kuwa yasan halinta sarai, farkon haduwan su ba yadda bata jifan shi da karya, daya gano gidansu ne yasata saduda ta koma real Batulan ta, yanxu kuma ba mamaki wata bomb take shirin ajiyewa.
"Okay ba matsala, saikun zo din, amma nikuma mai zan samu in return, kinsan dai gwamnati ta hana aikin banza" cikin zolaya ya fadi yana kai hannu zai rikota, batare da ya kai hannusa ba ta warce ledar zatayi gaba, saurin shawon gabanta yayi yana fadin "Batula babu kodan kiss" kiris yarage yakai mata kiss tayi saurin kawar da kanta gefe sukayi ido hudu da Baba da Mamuda dake tsaye suna kallonsu. Rai bace Baba nufeta yana cewa "mia kikeyi da yaron nan, ban hanaki haduwa dashi ba"
Jiki na rawa tace "dama assignment zaimin"
"karya kike" Baba yafadi yana kallon shehu da tuni yasha jinin jikinsa, "uban mi ya kawo nan ?
Shehu kam be boye komai ba ya zayyane wa Baba abunda ya kawo shi, salati baba ya saki, wana wace irin yarinyace, shi Rmb yake kowa, wayene, ina kika sanshi ?
Tsuru tayi tana kokarin boye ledar abayanta, warcewa baba yayi ya bude yaga bankararriya kazar yahuza, innalilahi kadai yake ambata ya mikawa shehu leda hade da korarsa, fashewa da kuka tayi ta ruga cikin gida, Mamuda kam kasa magana yayi, kila idan aka duba ransa yafi na Baba bacci, tir kawai yake da hali irin na Batula, wani irin tsanar ta ke sokanshi a zuciya.
Kwafa Baba yayi yace "yarinyan nan ga karya da kwadayi, tsoro na daya karta fara sata da bin maza"
Nisawa Mamuda yayi yace, "ayi hakuri Baba, kuruciya ce zata gyara nan gaba"
"A'a dai mamuda, i dont tink fatima zata gyaru, aurar da ita xanyi gobe goban nan kafin tajaza min abun kunya, Yekuwa xa'ayi a masallaci maiso na aura masa"
"Baba ayi haka kuwa, kasan fah Batula mai kudi tasa ran aura kar talaka irina ya ansan tayin"
Kur Baba yayi yana kallonsa sannan yace "Mamuda na baka ita, dan Allah karka ce a'a kaine daidai da ita ba wasu can maisu kudi datasa agaba ba"
Gaban Mamuda ne ya fadi, shikam mai xaiyi da yarinyar nan, shuru yayi baice uffan ba banda nauyin da kimar tsohon da yake gani.
"Nasan baka sonta, dan Allah ka amsheta amatsayin Sadaqa na baka ita" baba ya fadi cikin murya kaman xaiyi kuka.
Kasa cewa Uffan Mamuda yayi har suka taka zuwa inda rumfar baba, Marwan sa yanufa ya zauna zaija ya kalli baba da shima kallonsa yake, jiki sanyaye yace "sai da safe"
Baba yace "indai ka karbi sadaqa ta gobe xan ganka karfe biyu agurin nan da shirin daurin aure, bai iya amsawa ba banda jan marwan da yayi ya wuce, jan marwan yake amma gabadaya hakalinsa ba ya jikinsa, xancesu da baba kemai yawo akai, jin awani wawa horn abayansa yasa shi dawowa hayyacinsa, parking yayi gefen hanya hade da fiddo wayarsa, dannawa yayi ya kira Daddy Malam, magana daya biyu sukayi sannan ya katse.
Bayan mituna goma da parking dinsa wata arniyar Jeep ta karaso gurin, da azama Daddy malam da wani suka fito daga ciki, gaida Mamuda sukayi, bai amsaba ya fito ya shiga cikin jeep din, dayan da suke tare yaja Marwan yayi gaba, Daddy Malam na gefe shike driving suka isa wani karamin gida mai shegen kyau.
Parking yayi suka fito atare, Daddy malam yace "Mamuda ne ko Rasheed" ya karasa maganar cikin zolaya.
Fuskar daure yace "Rasheed ne"
Dariya Dddy malam yayi, "daga gani nagane wanan Rasheed ne, irin daure fuska haka, watx wrong ?
Ajiya zuciya Rasheed ya sauke, baice komai ba suka karasa cikin palon, zama yayi kan kujera, Daddy malam ya shiga toilet ya dauko spirit da detol ya zauna gefensa, yace
"tym to get back to real Rasheed Mohammad Deeni" ya fadi yana mika mai cotton wool.
Amsa yayi, ya cire kodaddiyar rigar dake jikinsa yahau goge ko ina na jikinsa dake shafe da bakin mai, har kafafusa saida ya kalkale, artificial mustache dake fuskar sa duk saida ya cire sannan ya shiga toilet yayi wanka ya fito fas ainihun Mr Rasheed dinsa, red tshirt da blue jean ya sanya ya fito palon.
Bai boyewa Daddy malam komai game da Batul da sadaqan ta da baba ya bashi.
Sosai Daddy malam ya bushe da dariya, yace "ka yadda kawai tunda tana sonka, kuma kai take burin aure"
Nisa wa Rasheed yayi,yacd "Rmd mai kudin takeso ba Mamuda talaka ba, nifah na mugun tsanar ta ba kadan, i cnt tolerate her, nayi disguise din kaina ne just to find true love ba wata gold digger can ba"
"Ni kuma i tink you should marry her, just to teach her a lesson, irin su they have to experience defeats kafin su shiga taitayin su" Acewar daddy Malam.
Rasheed yace "Hakane kuma, ka kawo point, i will personally deal with her to the extend idan taji mai sunan Rmd bazata tayi gigin cewa tasan shiba, matsala ta Mom ce, i dont tink she will accept"
"Karka damu, i have an idea," Daddy malam ya fada, matsawa kusa garesa yayi ya gayamani wasu magana dani kaina banji ba.
kai Rasheed ya kada yace "are you sure zata yadda?
Daddy Malam yace"Bata da matsala, i'll talk to her"
Sun jima suna tattauna nawa daga bisani kuma Rasheed ya mike ya wuce gida.




Kuka Batul tayita tsugawa a tsakar gida har Baba ya shigo gidan, takalmin kafarsa ya cira yana fadin kina tashi ana ko saina mauje ki" huf ta mike ta shige daki.
Hajjo da saura yaran dake zauna suna cin abincin a faratin daya ko ajikin su, yi sukai ma tamkar bata wajan.
"Mallam sannu da zuwa" Hajjo ta fadi hade da mikewa tsaye, yauwa Baba ya amsa mata ya kirata suka shiga daki, xayyane mata komai yayi da hukuncin daya yanke, sosai taji dadi danta jima tana neman yadda zata raba hanya da Batula sai gashi yau an badata sadaqa asauwake, fatan ta daya kar Mamuda yaki amsa, kodama yaki amsa saidai anemo ko waye alaka mai ita.


****


Yau friday tun Karfe goma na safe Batul ta fito da shirin fita makaranta, dakin Hajjo ta leka "na tafi" ta fadi fuska daure ko gaisuwa babu.
Kallon banza Hajjo takai mata, tace "babu inda zaki, ki koma daki ki hada kayanyi, yau zaki barmin gida"
"Ina da test ne, kuma ai nan gidan mune"
Harara hajjo takai mata
"Ayyo ashe dai matsiyacin gidan nan nakune bansani ba, toh baki da gado a gidan nan tuni Babanku yayi sadaqa dake, anjima kadan mijin daya temaka ya kwashe ki zai dauke ki ku tafi"
Ware idanu batul tayi tanai mata kallon rashin fahimta,
" kina bace min daga nan ko saina sharareki da mari" Hajjo ta fada cikin karaji da zare ido.
Tsum tsum Batul tayi ta koma daki ta cire kayan jikinta, tujajjiyar tshirt na tun lokacin siyasar Baba buhari ta APC ta sanya jikinta da tsohon zani ta fito gindin rijiya ta zauna hade da tagumi, ba xancen da Hajjo tayi ke damun taba, asalima bata gane inda maganar ta dosa ba dan kuwa babu yadda xaai ace an mata aure bada sanin taba.
yunwa sosai takeji baa mata tayin abinci ba, gashi Hassan da Husaini basa nan, yusuf dake daki tare da hajjo ba bari zatai ta aike saba, ganin yunwa xai halakata yasa tahau hada wutan gwarwashi dan dama koko.


Fitowar su lecture suka shiga mota zasu wuce gida, Minal tace "Allah yasa dai Fatima lapia, tun jiya batazo skull ba, ga wayarta kashe"
Kwafa billy tayi tace, "bana gayamiki ba, fatima makaryaciya ce, na tabbata ramin tane ya kure shiya hana ta zuwa".
"Billy kar kice haka, ki mata uxuri, am sure zuwa monday zatazo ta kaimu gidan Rmd"
Tsaki billy taja, "wlh ta raina miki yawo, nikam muje gurin Baba mai kayan miya na siyi Salad.
Haka dai kika ce" Minal ta fadi hade dajan motar suka nufi rumfar baba, baya gurin sai Hassan dake zaune yana jiremai, ganin su Minal sun tsaya yasa shi mikewa hade da gaidasu, amsawa sukayi, Billy ta siya salad na 300 masu kyau, harza su wuce Minal tace "kyakyawan yaro, billy baki ga kaman su da Fatima ba" karaf a kunna Hassan, kallosu yayi ya kara fadada fara'arsa.
Billy tace "aikuwa suna kama, amma bazaki hada ba, Fatima masu kudi ina ita ina hada iri da masu saida kayan miya".
Dariya sosai Hassan ya kece dashi, jikinsa kawai ya gayamai fatima yayarsa suke nufi, yace "aikuwa inada yaya Fatima, kamar mu daya da ita"
"Haba" suka fadi atare, ina take
"Ga gidan mu can, kuje tana ciki" nuna masu gidan yayi da yatsa.
Billy tace "bana gayamaki ba, yarinyar nan makaryaciya ce, muje mu gani"
"Kidaina saurin concluding muje dai" Minal ta fadi hade daja motan zuwa gaban gidan, sauka sukayi suka karasa gaban kofar gidan mai langalanga, babu ko sallama Billy tayi gaba ta afka cikin gidan.
Fatima na zaune gidin rijiya tana kurban koko a kwanan silba, tana ganinsu ta firgita, atsorace take kallon yadda suke mata kallon mamaki.
Sabule dankwalin kanta tayi tace "Minal sannu ku, kuma kunzo yin kitson ne ?
Kai kawai suka girgiza alaman a'a, tacigaba "gidan mu nacan baya, kitso nazoyi agidan nan"
Hajjo dake kokarin kama ruwa abayi kasawa tayi jin karyar da yarta take k'wandarawa, fitowa tayi bayan tayi adduaa fita bayi, kallon su Minal tayi da suma kallan ta suke, sannan ta kalli Batul datai tsuro tsuro da ido, tace
"Ba shakka gidan kitso kike zo, saidai bansani ba ko uwarkice makitsiyar....
[10:00PM, 5/26/2017] Xarah Bukar: 💖 *INA ZAN GANSHI*💖
Rubutawa
Xarah Bukar


®NWA


xarahbukar.wordpress.com


*For the world, it's just another day, But for you today is the best day of the year!* *Happee Bufdæ Biebee Isa, Wullnp..... It your Day Have fun🎉*

31 - 35


Shuru Batul tayi tana sosa gashin k'eyarta cike da kunya, ji take tamkar ta mike ta fad'a rijiyar dake fuskantar ta, kayan jikinta ma ya isa susan karya take ba gidan kitso tazo ba.
Murmushin dabai kai zuci ba Hajjo ta sakar masu sannan tace "yammata mungode da ziyara, saidai bamu dafa komai ba balle mu baku gashi yaune daurin auran kawar taku"
Cike da mamaki su ukun suka zaro idanu suna kallon Hajjo, hardai Batul da firgici ya bayyana fuskarta, atare Minal da Billy sukace "Auran gaske ?
Kallon baku da hankali Hajjo takai masu, ina aka tab'ayin auran karya koda yake sunan Batul na biyu karya dole su watso mata tambayar, bata amsa suba ta juya ta shige daki.
kallon tir da hali Billy ta watsa mata, "amma dai kinji kunya fatima, haihuwar irinki asara ce, banza, makaryaciya".
Haushi ne ya turnuk'e Batul, cikin borin kunya ta mike suka hau cece kuce, kasa cewa Uffan Minal tayi banda mamakin hali irin na batul da take, sau da dama ana bada labarin masu halinta bata taba yadda ba yau sai gashi ya faru akanta. Dakyar Minal taja Billy suka fice daga gidan, Hajjo dake jinsu bata lek'o ba, saidai asarar haihuwa da Billy ta fadi yay mugun mata ciwo, ita haihuwa k'yautar Allah ce komin ya yaro yake bai kamata ka dangan tashi da asara ko tsiya ba saidai ka bishi da fatan shiriya idan ya kauce hanya, tanaji da Batula har ranta halinta kadai yasa batason tsakan mata fuska.
Saida Batul ta tabbatar sunja mota sanna ta fad'a dakin hajjo, ba tambayar duniya daba tai mata akan gaskiar auren, banxa kadai Hajjo tai da ita tana mai cigaba da hajun gabanta.


Farar yadi wace ake kira da mamar ya sanya da hula buluwa, fuskar sa fayyus daka ganshi kasan baya cikin farin ciki, daure wa kawai yake, nan suka hadu da Baba a bakin massallaci, gaidasa yayi alabadce, Baba ya amsa, ganin yanayin sa baba yace "Mamuda karka damu, idan baka da kudin sadakin nizan biya maka"
Yaken dole ya saki yace "Baba ba matsla, akwai kudin".
"Madalla, Allah yayi ma Albarka"
Amin",ya amsa suka karasa ciki, bayan sun gabatar da Sallah aka dauran auran AbdulRasheed Muhammad Deeni da Fatima Muhammad Yero akan sadaki duba goma kacal.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login