Showing 27001 words to 30000 words out of 37025 words

Chapter 10 - JININ ABBANA BOOK COMPLETE TXT By Zainab Habib Mom Islam.txt

25 Jan 2025

2109

sosai , kuma anyi taro lafiya , daganan aka kowa ya watse , washe gari ,aka saka amarya a lalle , kowa sai sambarka , washe gari Assabar d'aurin aure ,gidan su mom da Hajiya da Alhaji wanan rana suna cikin farinciki , Alhaji da dady da abokan Alhaji suka cika gurin masha Allah , an d'aura auran Basma da Harun akan sadaki mafi albarka , dubu d'ari , d'aurin auran yasami halartar manyan bak'i ta 6angarori da dama ,anci kuma ansha an godewa Allah ,ango na hango yana sanye cikin wata shadda gezna mai azabar kyau ga gashinan yasha gyara bakinan kamar ansa masa janbaki , ni a ganina ma sai naga kamar yayi haske , zaune yake a gidansu Mom d'inshi sunata yimasa nasiha dakuma sanin hakkin aure a musulunci , Alhaji ne ya kirashi lokacin yana shirin tafiya gidansu Asma'u , kasancewar ya kira ance masa an fasa suzo su kar6i kud'in su , Harun ne yashiga da sallama , samun Alhaji yayi a zaune yana waya, yana gamawa yace ”Harun ya fito da mota zasuje wani guri , cikin bin umarni ya fito da mota suka shige shida Alhaji sukabar gidan , wani katafaren company na Alhaji suka nufa , wanda ake sauke kayan sa na saudiya , turaruka da jallabiya da sauransu , katafaren shago ne mai girma ga tsari ,da shigarsu kowa yahau durk'usawa yana gaida Alhaji da Harun , Alhaji ne ya amsa tare da cewa ga sabon shugaba na kawo shine zai dinga kula da komai na shigar kud'i , kai kuma Bala kazo muje sabon company na zaka koma can da aiki."




Cikin zumud'i da godiya , Bala yabi su Harun ,shimadai sabon company d'in ya tsaru sosai , bayan sun koma gida ne Alhaji ya cewa Harun yanzu kabar aiki a waccan ma'ikatar zaka dawo tawa , kuma maganar auranka da ,wanan yarinyar iyayenta sunce basusan inda ta nufa ba , shikuma yaro nanda wata biyu inya kuma wayau Allah zai baiyana kamanninsa da ubansa , cikin farinciki Harun ya kalli Alhaji yana godiya , lokacin k'arfe biyar na yamma dayake ranar Asabar akayi d'aurin auran ,


Wayarshi ce tafara ruri , ganin number abokinsa yasashi fitowa , jinayi yace ”ganinan zuwa yanzu , ya kashe wayar , parking spice ya d'auki motarshi ya fice daga gidan , gurin abokan nashi ya nufa , hak'ik'a ,sunyi rawar gani kud'ad'e masu yawa suka had'awa Harun , shima yayi farinciki kuma yak'ara sonsu a zuciyarshi."


Kukan jariri ne ya karad'e gidan , Umma na idar da sallah ta nufo d'akin Asma'u , ganin babu kowa sai yaro da wata k'atuwar takarda yasata dogon tunani , kodai Asma'u ta shiga band'aki ne ?"to ina ma zataje da sanyin safiyar nnan?" tunani iri iri Umma tafara , goya yaron tayi ta lek'a bayi babu Asma'u ko ina ta lek'e batanan , d'aukar takardar mai cike da rubutu tayi , bata iya karatun boko ba ko hausa yasata nannad'e takardar ta kaita d'akinta ta 6oye , tunaninta shine ina Asma'u tayi ?"batada mai bata amsa yasa ta fito ta koma d'akin Asma'u , ganin kud'i turus a zube yasa Umma tsorata tafara ja baya cikin tsoro."


Cikin sanyin jiki ta nufi d'akin malm da yake karatun Alqu'ani , ta durk'usa ta gaishe shi , gyaran murya yayi mata , hakan yasata ficewa da tunani iri iri a zuciyarta , misalin k'arfe bakwai na safe gari yayi haske , Umma ta lek'o waje ko zata sami yaro mai d'an wayo , cikin sa'a ta hango yaron ,mak'otansu ta kirashi , yana zuwa tace ”yazo dan Allah , shiga gidan sukayi , Umma tace ”ya shigo , yana shigowa ta mik'o masa takadda , tace ”dan Allah ka temaka ka karantamin , wanan , kar6a yayi yafara karantawa ....




_Aslamu Alaikum Umma nasan baza kiji dad'in tafiya ta ba gaskiya bazan iya zama da yaro a gabana ba da k'uruciyata , naza6i nabi k'awar arzik'i ki kwantar da hankalinki insha Allah munkusa fita daga talauci ga Muhammad nan ki kula dashi kuma nabar kud'i zasukai dubu d'ari, maganar aure kuma dama ba sonakeyi ba ,narasa mai bani shawar ne yanzukam nasamu fatan alkairi_






Zufa ce ke karyowa Umma duk sanyin da akeyi bai hana ta sharce gumi ba innalilahi wa inailaihirraji'un Allah gani gareka , Umma tasa kuka , shima yaron sai da yashare hawaye ya mik'e ya fice , bak'in ciki tashin hankali duk sun dira a zuciyar Umma kuka umma takeyi tana rok'on Allah sassauci , sako yaron tayi daga bayansa ta fashe da kuka , tana kallonsa ."




Misalin k'arfe takwas na dare ankai Amarya gidanta kowa sai yaba kyan gidan yakeyi , basu wani jima ba suka mik'e suka fice bayan iyaye sunk'ara yimata nasiha akan ladabi dakuma biyayya da hak'uri da soyayya , kuka Basma takeyi tana ruk'o mayafin k'awarta ,da haka suka watse suka barta ....✍️.






Ina kuma baku hakuri masu sharhi ko awane group akayi inhar ina ciki ina gani kuyi hakuri na rashin maida muku da martani kuyi hakuri 👏aiyuka ne sukayimin ywa amma ina ganin sharhinku nagode 🤙.


♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️.


_Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_




*Story and writing*
*By*


*ZAINAB HABIB*
_(Mom Islam)_


Zainabhabibu713 @gmail.com


Wattpad momislam2020




Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk




Telegram
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2


________________________________




*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com




https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w


_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




EPISODE 45 & 46




____ horn Zuby tayi a wani makeken gida kuma tsararre , tsayawa misalta tsarinsa ma 6ata lokaci ne dan zumu dad'e , mai gadi ne ya wangale get d'in tare da d'agawa Zuby hannu , rik'o hanun Asma'u tayi yayinda suka sauka , drivern gidanne ya d'auke motar a gurin ya maidata gurin ajiyar motoci , k'arasawa cikin gidan sukayi , babu kowa a gidan , hakan yasa ,Asma'u cire hijab d'inta ta lalubo wayarta data kashe ta duba lokaci , sbda bata lura da agogon parlorn ba , Zuby ce ta kalli Asma'u tace ”kifa saki jikinki wanan gidana ne kuma mallaki na , kinada right d'in yin komai a cikinsa , yanzudai kitashi ki shiga wanka ki wanke kan ki da sabulun wanke kai , akwai new brush kiyi using dashi , zan fido miki sabon kaya kisa kiyi sauri zanyi bak'i ne , lol tom Asma'u ta amsa ta shige toilet , tsaruwar toilet d'in ma abin kallo ne bare kuma gidan mai gaba d'aya , wata y'ar aiki ce mai suna Happiness ta kawo musu kayan abinci mai rai da lafiya ta jere a dining."


Zuby na waya jinayi tace ”yaufa ansami kaya kuma walh kud'inta daban ne , ni zaka dingaba kud'in ina bata , mutumin dake zaune a kujera a office ya juya yace ”bakida dama angama , ki kilace min ita zuwa yamma zan zo , okay Zuby tace ”tare da yin dariyarsu ta y'an duniya , ta kashe wayar , Asma'u na fitowa Zuby ta nuna mata wani had'ad'en bedroom ,acan tayi kwaliyarta , kaya tagani akan gado da alama shine wanda zata sa zaro ido tayi ,ta d'aga kayan , riga ce mai k'aramin hannu iya cibiya ,sai wando 3 quarter ma tsatse sai hula fara mai adon stone a jiki , sa kayan Asma'u tayi takasa fitowa , ta zauna tana tunanin yazatayi tayi rayuwa da wanan kayan cab , Zuby ce taji Asma'u shiru bata fito ba , hakan yasata mik'ewa ta nuf'i d'akin , murmishi tayi tace ”zomuje karki damu babu kowafa a gidan , kifito muci abinci gashi can a dining , mik'ewa Asma'u tayi jiki a sanyaye ta rufawa Zuby baya ."






Farfesu ne wanda yaji kayan k'amshi ,abin nema ya samu Asma'u zai tsotsar k'ashi takeyi tana k'arawa , Zuby duk ta karanci halayen Asma'u hakan yasa tak'ara samun k'warin guwaiwar kasuwanci da ita ."


Suna gamawa , Zuby ta ciro wata k'waya a aljihun wandonta ,mik'awa Asma'u tayi tace ”kinga wanan tana maganin gajiya , kuma kince jiya bakiyi bacci ba to yau zakiyi sosai , kar6a Asma'u tayi cike da gamsuwa ta d'auki ruwa tasha d'aya , ta mik'awa Zuby sauran , dariyar gefen baki Zuby tayi tace ”kozaki kwanta ne ?"a 'a Asma'u tace ”tana juya kanta da tafarajin mood d'inta yafara sauyawa , sai da Zuby taga magani yafara aiki ta rik'ewa Asma'u hannu ta kaita bedroom d'inta ta kwantar da ita , jiyo k'arar wayarta tayi tana ring a parlor , da sauri ta tafi gurin wayar , lokacin k'arfe shida na yamma , mutumin ne wanda sukayi waya d'azu , ganinan fa nashigo , okay Zuby tace ”tare da komawa d'akin Asma'u ,ta kuma shafeta da humra mai k'amshi ta bata wani magani na gari a cup ."


Fita tayi ta shigo dashi suna dariya , d'auko masa tiren abinci tayi da kanta ta mik'a masa , bayan yaci dankalin turawa soyayye yace ”hajiya ina ajiyata kinsan fa dan ita nazo tinda kika turamin pics d'inta wlh namatsu in ganta ."


Dariya , Zuby tayi tace ”tana cikin d'akina ta kwanta itama labarinka takeyi , zaro bandir d'in kud'i yayi yace ”nan dubu d'ari uku ne , amma somin ta6i ne ,inhar ta sanyani farinciki to fiye da hakama zan bata , wata munafukar dariya Zuby tasa tare da fifita da kud'in ,tace ”to kashiga ,ai kagane d'akin ko ?"eh yace ”tare da washe hak'ora , da shigarshi ya hango Asma'u kwance idanunta a bud'e sunyi jawur , yana matsowa kusa da ita ta cakumoshi , tana shirin mik'ewa , daganan nace barin lek'a gidan amarya Basma ."




Wasu dank'wala dank'awalan kaji na hango a plet , da Asma'u da Harun ne zaune ,fuskarsu cike da farinciki , fara bata yayi a baki itama ta bashi da haka suka ciyar da junansu , lemu ya tsiyayo musu a cup sukasha ya sunkuci , Basma yace ”tayi alwala , batayi musu ba , kasancewar tasha wa'azi kuma ta karanta ta gani , bayan tayi alwalar ne ta dawo bedroom ta zauna , shima alwalar yayi ya ciro mata hijab a drowa , ya sanya mata , raka'a biyu sukayi , suka zauna adu'a ,sund'au lokaci mai tsayi suna yiwa junansu adu'a suna gamawa ya mata tambayoyi akan wanka dakuma tsarki da sauransu , daganan yace ”to darefa 🙈 yayi muje mu kwanta, cikin fad'uwar gaba tabi gadon ta kwanta , Harun ne ya lulu6e su da blanket kasancewar lokacin ana sanyi , Basma ce ta juya bayanta , inalilahi ,Harun yace ”tare da juyo da ita ,kin mance zunubin da mace take kwasa inhar ta juyawa mijinta a yayinda suke tare ?" kunyace ta kama Basma ta juyo tare da mannewa a jikinsa , mik'ewa yayi ya kashe wutar d'akin yayi , tare da rungumo ta yafara kissing d'inta ta ko ina ."




Ganin lamarin zai fara fin k'arfinta yasata cewa ,please bacci nakeji ,ina Harun yayi nisa ,nima Miyoshi nayi yana adu'ar da manzon Allah yace ayi ..


*BISMILLAHI ALLAHUMMA JANNIBNISH _SHAI'DANA WA JANNIBISH _SHAI'DANA MA RAZAKTANA."*




Wani uban salati najiyo Basma ta rafka , lokacin nikuma na koma parlor na kwanta dan nagaji da d'auko rahoto eheee su masu baza ida nuwa🤣..


Misalin k'arfe hud'u na asbha , Harun ne yafara farkawa , ya zare jikinsa a na Basma ya kunna glob haske ya baiyana , ya shige toilet yayi tsarki sanan yayi wankan tsarki tare da alwala , nafila yafara jerowa ,tare da adu'ar farinciki daya samu a gurin Basma , yasameta a matsayin budurwa , bayan ya idar da sallah ne yaje ya kwanta gefen da ta kwanta yafara kwararo mata adu'a yana tofa mata, hango fuskarta yayi da ruwan hawaye ya bushe , murmishi yayi tareda manna mata kiss a goshi, yafara yimata tafiyar tsutsa a k'afarta , bud'e ido tayi tasa dariya , rik'o mata hannu Harun yayi tare da , d'aukarta kamar baby ,ya kaita toilet ."




Ruwa mai d'an zafi ya tara mata a bahon wanka kana ya zuba delot a ciki ya sanyata , k'ara tasa ta rik'o masa riga, hak'uri yadinga bata , ruwan zafin ya ratsa jikinta hakan yasata yin shiru , d'agata yayi Yauma tara wani ruwan saida ya salamce ,ya tara mata wani na wanka bayan ya bud'e wancan ya tafi ya tara sabo , wanka tayi cikin jin kunya shiko angon yana tsaye yana kallonta , da niyar wanka da tayi duk yana hankalta , tabbas yayi sa'ar mata, fitowa sukayi tana cogala k'afafu , suka nufi gado , hijab da kayan da zatasa Harun ya ciro mata , bayan tasa ne ya koma d'akinsa ya sauya kaya yatafi masallaci , ita kuma ta shafa mai da turaruka ta sa hijab tafara sallah...✍️.




😫wayo hanuna🤏.


♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️.


_Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_




*Story and writing*
*By*


*ZAINAB HABIB*
_(Mom Islam)_


Zainabhabibu713 @gmail.com


Wattpad momislam2020




Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk




Telegram
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2




________________________________




*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
__wattpad


________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com




https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w


_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




EPISODE 47 & 48




____Tun Asma'u na dauriya tana biyewa duk wani salo nasa , yanzu kam takasa da alamu maganin yafara sakinta , shigo mutumin ko gajiya baiyi ba Alhaji Khalifa kenan ,ze iya yin sa'an k'anin baban Asma'u amma kasancewar sa mai nera , yasashi babu inda bazai je budurwa ta kusheshi ba kowace zumud'i takeyi sbda kud'insa suke so , gashi ya iya sarafa mace kamar k'aramin yaro ,baya gajiya gurin sxx da mace , yanada manyan y'a y'a harda masu aure da maza samari hakan baisa ya dena abinda yakeyi ba, sai da jikinta yai lilis sanan ya d'agata , batasan halin da take ciki ba hakan yasata bacin da bata shirya ba , shiga toilet d'in dake gefe da d'akin yayi ya watsa ruwa ya fito ya sanya kayansa , wayoyinsa ya d'auka ya fice , samun Zuby yayi a parlor tana danna waya , mik'ewa tayi fuska cike da fara'a tace ”ya akayi washe hak'ora Alhaji Khalifa yayi yace ”gobe zan dawo fa ga 50k tasi kayan shayi , dariya tasa tana rangwad'a ta kar6e kud'in ."




Ware dubu d'ari biyu tayi a gefe da nufin shi zata bawa , Asma'u mik'ewa tayi ta nufi d'akin da Asma'u take kwance , tsamunta tayi kwance tayi sharf kamar mara nunfashi , cikin sauri ta k'araso ta dafata jitayi jikinta yayi zafi , a tsorace ,ta d'aga waya ta kira likitanta , kazo please da matsala dan Allah , doctor ne yace ”oky ganinan zuwa yanzu , ba'adau wani lokaci mai tsayi ba sai ga doctor ya iso , k'arar motarsa ce yasa ,Zuby ficewa da gudu ta isa gurin da yayi parking d'in motarsa , yana fitowa tace ”dan Allah ka hanzarta da sauri suka nufi d'akin da Asma'u take kwance , jikinta ya ta6a yaji zafi y'an gwaje gwaje yai mata ,yace ”zazz6i ne amma insha Allah zataji sauk'i , magunguna ya had'a mata Zuby ta bashi kudin da ya buk'ata ya fice tare da yiwa Asma'u fatan samun sauk'i ,dawowa d'akin Zuby tayi kasancewar tun kafin doctor ya zo ta gyara mata jikinta ."


Zuwa yamma Asma'u taji dad'in jikinta amma ta rame sosai , fitowa parlor tayi bayan tayi wanka ta kunna TV , Zuby ce tafito sanye da doguwar riga iya guwaiwa , ta zauna a parlor , kujerar dake kallon Asma'u ,tace ”ya jikin ?"da sauk'i Asma'u tace ”zuby ce ta mik'a mata kud'i , zaro ido Asma'u tayi tace ”wanan fa ?"karki damu dubu d'ari biyu ne karki damu yanzu kika fara kama dollars , murmishi Asma'u tayi , tace ”nagode sosai samun k'awa irinki wlh sai an tona suka tafa."




To yanzu ya maganar auran da kikace saurayinki zaiyi , yaushe zamuje gurin boka , Asma'u ce ta kalli kud'in hanunta tace ”banason ta6a wanan kud'in , dariya Zuby tasa tace ”karki damu ga 50k sai muje gobe , daganan suka sauya hirar tasu ga duniyarsu ."


Kwana uku kenan da bikin Bash ,soyayya kamar zasu cinye junansu , Basma tayi kyau a tsakanin kwanakin gashi tasami mazauni a zuciyar Bash , bata bari ranshi ya 6aci haka shima bayason 6acin ranta , da sallama ya shigo tanajin shigowarsa ta ruga da gudu ta rungumeshi juyi yafara yi da ita bai direta ko inaba sai tsararen gadonta , ya fara yimata wak'a tana dariya , zomuje muyi kallo , mik'ewa sukayi rik'e da hanun juna , Harun ya kunna TV ya rungume Basma 🙈lamarin n masoya ne lol , misalin k'arfe goma sha biyu , suka shiga kitchen sukayi girki , kowa ya shigo gidan su Harun baya fita bai d'auki wani darasi na soyayya ba."




Washe gari suka shirya zuwa gidan su Harun , siyayya sosai suka yimusu , tafiya sukeyi cikin nishad'i Bash na tuk'i hanunsa na kan na Basma idanunsa ma na kanta , a haka suka isa gidan , yana parking d'in motarsa suka fice , sukayi cikin gidan ,da shigarsu sukaci karo da mom , cikin fara'a ta tari Basma ta rungumeta , Hajiya na fitowa ta fara rawa tana cewa "ga ango ga kishiyata yau nice da ango sukasa dariya , zama sukayi aka fara gaisawa , kowa fuskarsa cike da fara'a ."


Girki na musaman aka yiwa amare ga farfesu na kifi dana kaza ga lemu da mom suka had'a itada Basma , mom taji dad'in samun suruka irin Basma batada duhun kai komai nata cikin nutsuwa takeyi , gida dai yacika da farinciki sosai ."


Da dady akayi bikin Harun sai dai bai cika shiga mutane ba sbda wani gargad'i da beauty tayi musu shida Bash , rabonshi da fita gurin aiki yayi sati

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login